Showing 72001 words to 75000 words out of 88219 words

Chapter 25 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull

29 Jun 2024

18186

idan ba hakan ba. Aikinsu ne ai, sune kawai suke da dabarun bincike, dan a yanzu haka since wanda ya ɗauke ta a napep yana hannunsu ma, sai dai yaƙi amsa laifinsa”. Abbane yay maganar cikin katse Kawu Lurwanu. Kai Kawu Lurwanu ya girgiza, “To ai ban kai ƙarshe ba nima ka katseni Imamu, abinda nake so nace bafa zama zamuyi mu rungume hannaye muna jiransu su kaɗai ba. Kamata yay muma mu saka roƙon ALLAH tako ina. Sai dai kasan mu ɗin ba masu ƙarfi bane, kuma al'amarin yana buƙatar sadaka. Dan haka muka yanke hukuncin dawo da waɗan nan kuɗi na aurenta da aka karɓa, dan dubu ashirin kawai mukaci a ciki aka ajiye tamanin akan idan lokaci yayi zamu ƙara da wasu a rage maka hidima. Kaga kaima saika kawo wani abu daga cikin wanda ke hannunka a haɗa a sai abinci da wasu abubuwa aita sadaka ana addu'a sai kaga anci nasara ALLAH ya bayyanata cikin sauƙi. Dan yarinyar nan kullum kwanakin bikinta sake matsowa sukeyi, dan ma yaron kirki ta samu, kuma danginsa basu da fitina, amma wlhy da wasu ne da yanzu sun fara zame-zame akan al'amarin nan. Amma kaga yaron nan da shi aketa faman faɗi tashi na son ganin an samota har ma da iyayen nasa. Amma yaya ka gani shawara ce?”.
       A ɗan fusace Abba ya ce, “Ni gaskiya babu kuɗin nan yanzu a hannuna. Sai dai idan shi Musaddiq nada su ya aramin idan na samu zan bashi”.
     Kaf falon babu wanda bai ƙwalalo idanu waje dan mamaki ba.......✍️

      _Ai ni kaina idanun nawa a waje. Abba al'amarin ka ya fara ban tsoro da mamaki. Ya rabbi kasa mu rayu da ƴaƴanmu, maraici da banne wlhy a rayuwa😭_.



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_


........ Musaddiq ne kawai yay murmushi yana mai girgiza kansa. Ganin Kawu Musa na neman fusata dan dama shi akwai zuciyar tsiya yay saurin faɗin, “Uhm Kawu inaga babu damuwa ai. Kuma na wajenku ku barsu. In sha ALLAHU babu abinda zai gagara na sadakar. Ko daga gobe in ALLAH ya kaimu ake son fara duk abinda ya dace ni a shirye nake.”
     Sosai suke kallonsa zukatansu na ƙara rauni. Yaron jarumine na gaske da kowaɗanne irin iyaye zasu yi alfahari da shi. Gaba ɗaya halin Musaddiq irin na mahaifinsa ne. Ga sanyin hali ga haƙuri ga kirki da jarunta. Sun nuna masa zadai su bashi kuɗin amma ya dage kan bazai amsa ko sisi ba. Dole suka haƙura suka barsa. Ƙyawawan halayen yaron na sake saka musu jin kunyar wofamtar dasu da sukayi a lokacin da suke matuƙar buƙatar tallafinsu, amma kuma bakin alƙalami ya riga ya bushe yanzu kam sai dai haƙuri, dan ta wani ɓangaren suma ba laifinsu bane. Ƙanin mahaifiyarsu ne ya nuna musu shi ɗan boko ne kawai sjiyyasa sukai zuciya suka bar masa su.

        Kaf abinda ya faru a zaman sai da Mum ta tsare Abba ya sanar mata. Aiko ta sake zugesa akan babu wata addu'a sun zo ne kawai su yaudaresa su amshi kuɗin. In ba hakaba wace addu'a ce za'a wani ce sai da kuɗi. Daga ƙarshe ta sake ingizashi kan ya binciki Musaddiq duk yanda akai yaron kuɗine da shi, in ba hakaba taya komai ya taso sai yace zai yi. Daram kuwa ya hau ya zauna ko kunyar ALLAH babu washe gari yay kiran Musaddiq yay masa tujara. Ya kuma ce yana buƙatar 1mil a wajensa da za'aima Samraah kayan ɗaki, sannan ya bada kuɗin kayan kitchen suma Mum zatayi masa list ɗin komai. Sai da ya gama sauraren Abba kaf sannan yay murmushin sa mai sanyi. Cikin nuna rashin wata damuwa a fuska ya ce, “Ba damuwa Abba ka saurareni zan samo in sha ALLAHU”.
      Sallamarsa Abba yay yana ƙara jaddada masa. Yana fita Mum tai wuff ta fito alamar dama laɓe tai musu. Zama tai kusa da Abba tana faɗin, “Bana gaya maka ba Abban Abbas. Yanzu ka yarda ko? To ALLAH kaɗai yasan mi yaron nan ya tara yake raina mana wayo ya barmu da nauyin hidimar rawuwarsu. Ana gama hidimar bikin nan ya kamata ka sashi ya bama Abbas jari yabar wannan gantalin rashin aikin, sannan itama Baby ta fito da miji dan nagaji da yawon nan nata haka nan”.
         Babu wani dogon nazari ko tunani a wannan magana Abba ya amsa Mum tare da bata goyon baya ɗari bisa ɗari. Daga haka suka cigaba da hirarsu cike da soyayya.

   A ɓangaren Musaddiq kam shi al'amarin su Abba kam ya fara bashi tsoro. Dan ya wuce abin mamaki ko al'ajabi. Amma dai a wannan karon zai ari halin Samraah ko kaɗanne ya gani ko zasu fahimci shi ɗin bawai sakarai bane. Yana binsu ne kawai da halayensu saboda wasu dalilai. Yanzu banda rashin adalci bama damuwarsu ɓatar ƴar uwarsa ba kusan sati biyu kenan, shi dama gani yake Mum da Baby kamar farin ciki suke da rashin Samraah a gidan. Ko mi tai musu haka da zafi oho ya kasa fahimta. Yasan Samraah fitinanniya ce, to amma duk abinta saika shiga sabgarta ne, kuma mafi yawan lokaci sune ke fara takalarta ita kuma ta maida murtani.
      Washe gari kamar yanda suka tsara aka fara gudanar da addu'oi. A masallatai da islamiyoyi, aka kuma dafa abinci aka dinga rabawa mutane musamman ƙananun yara da almajirai. Dan har tsangayoyi aka kai abincin ma. Acan gwarzo ma su Kawu Musa abinda sukai ƙoƙarin yi kenan da kuɗin da Musaddiq ya basu. Dan Mansoor ya taimaka musu sosai da yaji shirin nasu. Dan ko abincin nan ma da aka dafa anan shine ya bada aka dafosa da taimakon Mamynsa. 

      Kwana uku anata addu'oi da raba dafaffen abinci. Ga kwanakin biki nata sake matsowa daf. Gefe Musaddiq nata wasan ɓuya tsakaninsa da Abba da Mum. Yayinda su kuma suke zaman jiran a kawo musu kuɗi.....

        ✨★✨★✨★✨


Tabbas duk wanda ya miƙa al'amarinsa ga UBANGIJI babu shi babu taɓewa Bily, naga fa'idar hakan ƙwarai da gaske a wannan gaɓar. Domin kuwa duƙufar da nai wajen gayama UBANGIJI damuwata ya saka min ƙwarin zuciya da jin sabon ƙarfi na dawo Samraah ta tada. A daren da nake lissafin kwanakin aurena da Mansoor saura biyar kacal a bazata naji ana ƙoƙarin buɗe ɗakin da nake. Hakan ya bani matuƙar mamaki dan ba lokaci bane da ake kawo min abinci, kusan ƙarfe goma da wasu mintuna ake yanzu na dare. Hijjabina daya kasance ɗaya jal da nake salla da shi na ɗauka da sauri na saka. Bamma kai ga ƙarasa sakawarba har an riga an shigo. Baki na buɗe cikin ɓacin rai zanyi magana kawai ya jefamin wata muguwar harara. Ba kowa bane face yaronsa ɗin nan mai dogayen kunnuwa uwa na zomaye. Nima hararsa nai da mare baki, a fili na furta, “Daka daina burga dan baka da banbanci da damisar takarda. Kullum kana bayan wani kamar mai gadi”.
A take fuskarsa ta rine zuwa ɓacin rai, ya ɗaga hannu kamar zai ƙwaɗan mari sai kuma miya tuna oho masa ya fasa. Ya dunƙule hannun yana ɗan kaima iska naushi a cikin takaici. Ni dariya ma ya bani, amma sai na dake banyi ba. A cikin zafin rai ya furta “Shigo ki mata”. Ban gama hahimtar mi yake nufi ba likitar ranar data dubani akan matsalar ciwon mara ta shigo. Matar ƴar gayuce sosai. Da gani kuma kasan itama ƴar masu kuɗice. Murmushi tai min cikin tsokana tace ashe dai patient ɗina ta miƙe?”. Watsar da ita nai kamar banji mita faɗa ba, dan haka kawai bata mun ba, nama ɗauke kaina gaba ɗaya. Magana tai yunƙurin sake yi mai kunnen zomaye ya dakatar da ita cikin magana zafi-zafi ya ce, “Doctor kimata kawai”.
Itama amsa masa tai da to tana zaro syringe. Kambu idona idon allura na zabura zan miƙe, sai dai mi jinai kawai an damƙomin hannu an riƙe, kafin na farga ta saka min handcuffs. Ido rufe na buɗe baki zan balbaleta da masifa ta shamaceni kawai sai shigar allura naji a hannuna. Kafin wani dogon motsi ta zareta tana sauke ajiyar zuciya kamar daga jikinta take cirowar. Kaina ne ya fara juyawa na koma ganin ɗakin da su kansu bibbiyu, da ƙyar na iya ɗaga hannu ina nunasu amma na kasa magana. Dan idanuna lumshewa suke kaina na ƙara nauyi, a cikin abinda bai wuce minti ɗaya da wasu sakanni ba komai ya koma min ɗiff. Sai buɗe idanuna nai na ganni a inda banyi zato ko tsammani ba....


      💫💥💫💥💫💥💫


    Duk da tasowar hadari mai ƙarfi na farkon damuna bai hana Musaddiq tashi ba jin an ƙwalla kiran sallar asubahi. Ya fara alwala aka fara yaf-yaf na yayyafi. A gagauce ya ƙarasa ya wuce massalaci. Kamar jira ruwan nan yake a idar da salla ya fara sauka da ƙarfinsa. Kusan duk wanda ke a massalacin da gudu-gudu ya fita domin shiga gida. Hakance ta kasance tsakanin Yaya Musaddiq da Abba. Kusan a tare suka ja wani bahagon birki a ƙofar gidan sakamakon cin karo da abinda basuyi tunani ba ko zaton gani haka. (Tabbas Samraah ce ba gizo bane, ba kuma mafarkin daya sabayi bane ba). Musaddiq ya ayyana a zuciyarsa dake faman gudu da uban sauri a cikin ƙirjinsa. Da sassarfa ya ƙarasa inda take. Dai-dai nan ta fara motsa jikinta sakamakon ruwan sama dake sauka da ƙarfi. Kuka Musaddiq ya saki tare da durƙushewa a gabanta. Gaba ɗayanta ya wawuso ya rungume a jikinsa. Hakkane ya saka Abba dawowa hayyacinsa shima ya nufesu. Cikin rawar murya data jiki ya furta, “Musaddiq da gaske Samraah ɗin ce?”. Bai jira amsarsa ba shima ya kai durƙushe gabansu. Duk wanda yazo gittawa ya gansu sai ya tsaya. Kafin kace mi maƙwaftansu sun ɗan taru a wajen. Duk mazane da aka dawo daga massalaci. Maƙwafcinsu da suke katanga ɗaya ne ya bada shawarar a shiga da ita cikin gida. Wannan shawara tasa ta saka Musaddiq miƙewa ɗauke da Samraah. Ta farfaɗo amma bata iya banbance komai kamar wadda ke a buge cikin maye. Wannan yanayi nata yasa da yawan wanda suka taru a wajen ransu ya ɗarsu da abinda bashine ba.
     Abba ne ya shiga kwala kiran sunan Mum. Sai gata a firgice. Da alama ma ita sai yanzu take tashi sallar. Su Baby ma ihun Abban ne ya tashesu a nasu barcin suma duk suka fito. Kowa yaci karo da Samraah sai yay wani irin ja da baya yana zaro idanu. Musaddiq ne kawai keta ƙoƙarin ganin ta buɗe idanunta da take lumshewa da buɗewa da ƙyar tamkar me maye. Kusan mintuna biyar kafin ta buɗe idanun da ƙyar sosai ta kallesa. Cikin siririyar muryarta data surka da mayen barci ta ce, “Yay..a Mu...sad...diq”.
     Jikinsa har rawa yake wajen amsa mata da, “Na'am Samraah! Kandalata nine. Buɗe idonki da ƙyau ki sake ganina. Alhamdullah ya rabbi Alhamdullah.” yanda yake sambatun yana hawaye ga dariya sai ka ɗauka ya zautu ne. Su dai su Mum na tsatstsaye ciko-ciko kawai suna kallonsu. Musaddiq da duk ya gama rikicewa ya zaro wayarsa da sauri. Mansoor ya fara kira, dan abokin kuka shi ake fara gayawa mutuwa, wani ihun farin ciki da Mansoor ɗin ya saki sai da ya janye wayar dan jin zai fasa masa dodon kunne. Daga nan yay kiran d.c.o shima dan ya sani. Shima yanda yake ta jera Alhmdllh zai tabbatar maka yaji farin cikin. Suma yan gwarzo yay kiransu ya sanar musu. Ai kafin kace mi anata shigowa gidan, dan Mansoor ma cikin ruwan nan ya taho duk da gari bai gama washewa ba, sai daga baya jama'ar gidansu suka biyosa. Sanda suka taho an wuce da Samraah asibiti domin duba lafiyarta kamar yanda d.c.o ya bada umarni. Dan sam Samraah bata cikin hayyacinta saboda allurar da sukai mata.......✍️



_Hummm dangin Samraah sai a barmu mu hyaƙata, ga ƴarku nan mun sakar muku. Su o'e duk an addabemu dama🚴🚴😞._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_


.......Lokacin da goma tayi gidajen rediyo dana tv da yawa sun sanar da ganin Samraah. Gidan tvn su ne ya fara fitar da batun, dan danan sai ga ƴan jarida. Sai dai an hanasu kowace irin dama ta ganin Samraah, dan har lokacin barci ma takeyi ita. Ƴan gidansu ma da ƴan gidan su Mansoor duk suna daga waje ne. Sai wajen sha ɗaya ƴan Gwarzo suka iso suma. Nan fa asibitin ya ƙara cika. Dole doctor ya roƙa su ragu. Dan ana buƙatar sanda zata farko ta farka a cikin hayyacinta. Gamsuwa da hakan yasa aka ragu, Mansoor da Yaya Musaddiq da Abba sai Kawu Musa kawai aka bari, sauran duk suka wuce gida.
        Ƙarfe ɗaya da wasu mintuna Samraah ta farka. A lokacin babu kowa a ɗakin dan wanda aka bari asibitin duk sun wuce massalaci salla. Sai Nurse da aka bari ta kula da ita dan zata iya farkawa a koda yaushe. Hakance kuwa ta faru. Sai dai tana buɗe idanunta bakinta da addu'a Nurse ɗin nan ta miƙe. Sannu ta mata da farko, sai kuma ta ɗan fita kamar zatayi kiran Doctor ne. Babu jimawa sai gata ta dawo. A lokacin Samraah ta ɗan daddafa ta tashi dan wani irin fitsari take ji. Matsowa Nurse ɗin tayi gaban gadon tana mai cire wayar dake a kunnenta tai ɗan danne-danne da bai wuce sakan biyar ba ta nuna wayar akan fuskar Samraah dake kallonta. Dan ta rufe fuskarta ruff da face mask idanunta kawai ake iya gani. Baki Samraah ta buɗe zatayi magana da ƙyar dan ganin Nurse ɗin ta saka mata waya a gaban fuska. Amma saita mata nuni da wayar alamar nan zata kalla. Babu musu ta juya kanta a hankali tare da buɗe manyan idanunta da suka kumburo sosai sukayi ɗan ja a jikin fatar amma cikinsu tar-tar ta sauke su akan fuskar wayar. Numfashi ta nema janyo wa da sauri, amma hakan ya gagara sakamakon cin karo da fuskar wanda batai zato ko tsammanin gani ba shima ya zuba mata idanun nan nasa tamkar zai cinyeta ɗanya da su. Zaune yake ƙafa ɗaya kan ɗaya da salon zaman ƙasaitar nan tasa. A yanayin location ɗin da yake zai tabbatar maka da ba'a Nigeria yake ba ma. Duk da ta cikin wayane jinai kallonsa na neman yamutsa min kaina. Amma na dake a zahirance, sai ma wani irin mummunan kallo da nima nake jifansa da shi batare da nasan ina yi ba. Ƙara tsatstsareni yay da idanun cikin yanayin irin ke baki da kunya ko. Niko na yamutse fuska irin eh banda kunyar sai yaya.
       Hannunsa ya kai ya shafo gashin dake a haɓarsa, cikin salon ƙara tamke fuskarsa cike da gizago shi a dole bai san raini murya a kausashe ya fara magana da ƙyar dan yanda lips ɗin ma ke motsawa kaɗan-kaɗan sai ka ɗauka bazaka iya jin abinda yake faɗa ba. Amma kuma sai na dinga jin muryar tasa raɗam a kunnena kamar ba'a waya yake ba.
    “Ganinki cikin zur'arki bashi ke nufin wasan ya ƙare ba. Sai dai kina da zaɓi biyu. Bakin ki ya kasance shiru ki cigaba da rayuwa da waɗan nan mutane biyun”. Hoton Hafizzullah da Yaya Musaddiq ya bayyana. Bamma san sanda na waro idanuna waje sosai ba ina ɗan zabura. Shiko hankali kwance ya ciga da faɗin, “Ko ki buɗe sa da zance a kaina ni kuma na rufe miki shi ta yanda ko mai irin harafin farkon sunana kika ji sai kin firgita. Na barki lafiya”.
       Da sauri nima cikin jin wani ƙarfi na ce, “Yaƙin sunƙuru ai na mai tsoro ne. Idan ka cika namiji kabar laɓe-laɓe a bayan ƙarfin dukiya kazo muyi gaba da gaba sai a banbance waye jarumin tsakanin ni da kai. Ita Sam-G a ko ina Samraah ɗinta take, bana ado da wasu domin kare suna ko ƙarfin iko na. Sannan garkuwa da wasu domin cimma buri ai tsohon salo ne. Video ne dai bazan bayarba, kuma har abada bazaka taɓa sanin inda yake ba, kai ni kaina bazaka sake gani na ba”.
        Wani jahilin murmushi ya saki da sai da ƙirjina ya harba dan wani kalar mugun ƙyawunsa ne ya sake bayyana. Idanunsa ya ɗan lumshe da sake buɗewa a kaina cikin yanayin kallon ƙasa-ƙasa, bamma san na murguɗa masa baki da janye nawa ba. Ya ɗan taɓe baki cike da basarwa. Tare da motsa lips ɗinsa a daƙile ya ce, “Ina matuƙar son wasa da mutum irinki mai taurin kai da kaifin baki. Dan haka kar kiyi gaggawa, in dai yaƙin gaba da gaba ne yana tunkaro ki, dan haka jekiyi shiri na musamman, dan yaƙi da Awwab

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login