Showing 87001 words to 88219 words out of 88219 words

Chapter 30 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull

29 Jun 2024

18179

nace bai san da zuwana wajen ba. Dan ko motsi baiyi ba balle ya ɗago ya kallan, aikinsa kawai yake hankali kwance cike da ƙwarewa.
          A matuƙar harzuƙe hawaye masu zafi na rige-rigen sakko mini cikin daka tsawa na ce, “Da kai nake magana malam!!”.
   Cak ya tsaya daga danna keyboard ɗin laptop ɗin da yake yi. Nasan kuma yanda nai tsawar ne da matuƙar ƙarfi ga jikina na girgizar tashin hankali da ɓacin rai. Na sake zabura zan masa wata tsawar ganin nan ma bai amsa min ba yay wata irin juyowar da ta saka ni yin tsalle a lokaci guda da zuciyata saboda tsabar kiɗima. Sai gani rijif a ƙasa wanwar.
       “Ba'a min tsawa”.
    Ya faɗa a dakensa cikin silent voice ɗin nan nasa na gadara babu alamar damuwa da halin da yaga na shiga kuma. Sai ma ɗauke kansa da yay ya sake maidawa ga screen ɗin laptop ɗin. Yaraf kake jina na ƙarasa zubewa ƙasa gaba ɗaya. A hankali sai kaina ya fara juyawa, yayinda lips ɗina ke wata masifaffen rawa ina nunasa da yatsana da shima ke rawar. Tun ma ina banbance tsakanin haske da duhu har hakan ya fara neman gagarata. Tuni na tafi luuu ƙasa gaba ɗaya alamar ina neman suma. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba sai farkawa nai na sake gani na a inda na faɗin yashe. Da ƙyar na iya miƙewa hannuna dafe da kaina dake faman juya min. Kai tsaye inda nasan yana zaune na kai idona. Wayam babu kowa daga shi har laptop ɗin nasa. Sai mug ɗin nan na shayi kawai ajiye. Falon na juya ina sake ƙarema kallo. Yanzu kam ni kaɗaice a cikinsa da alama, sai zuciyata ke ayyana min kodai mafarki ma nake yi ne? A gaskiya sai dai mafarkin kuwa, dan wanda idona ya ganarmin a gidan nan nafi fatan ya kasance a mafarkin ne. Kasa daurewa nai, cikin layin juyewar kai tamkar wata ƴar maye na nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton hanyar fita ce. Da ƙyar na iya lalubar handle ɗinta na buɗe, cikin yanayin dishi-dishi na dinga bin harabar gidan da kallo, ba wata babba bace dan bata wuce ɗaukar motoci uku ba suma a ɗan takure. Motar da nake ƙyautata zaton an ɗakkoni a ciki jiya kawai ce a ajiye. Saukar idanuna akan buzun dake zaune a gate yana fifita wuta alamar shayi yake dafawa yasa ni jin ƙarin gwiwar nufar can. Sai dai ina kai rabin harabar wani mahaukacin farin kare mai kama da tumakin turawa a gashi ko nace zaki a ƙarfi da girma ya wani irin zaburowa kaina daga inda yake kwance a saman motar yana haushi na hauka ga harshensa waje. Daburcewa nai na rikice dan na tsani kare. Balle irin wannan mara ƙyan gani da suffa, sauƙinsa ɗaya daya kasance fari. Ganin yana gab da iskoni na ƙwalla ƙara ina durƙushewa a wajen na ƙanƙame jikina dake rawar mazari.
       “Laalah!”.
     Aka faɗa a ɗan tsawace, sai dai hakan bai hana fitar muryar tasa acan ƙasan maƙoshi ba. Sannan karen ya tsaya cak bai ƙaraso inda nake ba. Sai kallonsa da yay yayi haushi sau biyu yana kallona kamar mai son masa ishara dani. Da alama ya fahimci mi karen ke nufi, dan a daƙile ya sake faɗi, “leave here”.
     Abin mamaki tinƙas-tinƙas karen nan yabar inda nake ya koma saman motar daya taso yay kwanciyarsa kamar bashi ba. Sai lokacin na samu damar sake fashewa da kuma. Ganin ya juya abinsa zai koma inda ya fito na miƙe a zabure nima. Kusan atare muka shigo falon. Batare dama nasan mi nakeyi ba a tsawace na furta, “Ina ka kaimin mijina? Mi kayima Mansoor ɗina? Miya kawoka gidan aurena? Yanzun ma kidnapping ɗina kayi?”.
         Bai ko kallan ba ya cigaba da tafiyarsa zuwa bedroom ɗin nan mai katifa. Ai bamma san lokacin dana daka wani uban tsalle ba nabi bayansa nima. Dan amsoshin tambayoyina kawai nake buƙata. Dole kuma ya bani, inba haka ba kuwa zaiga tsagwaron tashin hankali, kuma a wannan karon saina tabbatar masa da kaidin mace, dan ko dare bazan sake kaiwa a gidan nan ba. Ina isa ƙofar ɗakin yana rufota bamm, handle ɗin na kama da rawar jiki na fara murɗawa da jijjiga ƙofar amma ko motsi batai ba alamar ya kulle ta ciki. Wani irin kuka mai tsuma zuciya na sake fashewa da shi ina cigaba da jijjiga ƙofar da bugata a haukace amma mutumin nan ko tari baiyi ba. Galabaita ta sakani silalewa jikin ƙofar zuwa ƙasa wasu zafafan hawaye na rige-rigen sakkomin da masifar gudu. Cikin jin karaya da sarewa na shiga furta, “Awwab why? Why Maash? Why zakamun haka a ranar da tafi kowacce rana muhimmanci a garemu. Mike shirin faruwa? Ina mijina Mansoor?!! Miyyasa ka sake satoni zuwa nan a ranar auren...” kuka ya sarƙeni na kasa cigaba da maganar✍️

 
🤔🤔🤔😞

Alhamdullah 🙏. Anan zamu dakata a book one na wannan littafi mai suna TSUTSAR NAMA. sai kuma ALLAH yasa muna da rabon kaiwa bayan salla.

★Tofa masu karatu yaya take ne?.

★Mike shirin faruwa?.

★Ina Mansoor ango?.

★Miya kawo Maash a madadinsa?

★Kidnapping Sam-G ya sake yi kamar yanda take tunani itama kokuwa yaya al'amarin yake?

★Waye yay kidnapping Sam-G a farko tunda Maash ya tabbatar mana bashi bane?.

★Waye Maash ya kashe ma wai?

★Wake amfani da sunan Samraah wajen amsar kuɗi maƙudai haka a wajen Maash? Tunda tace ba ita bace.

★Maash zai samu nasarar amsar videon a wajen Sam-G kuwa?

★Magana fa ake ta an kawo amarya gidan mijinta amma ango ya rikiɗa zuwa wani daban.

★Hhhhh masu karatu akwaifa gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon shima. Hargitsi da cakwakiyar dake cikinsa kuwa. Hhhhumm ba'a magana, dan bama mu fara komai ba sai a book 2 da zai zo bayan salla, kuma komai da kuke buƙata yana a cikinsa ne.

★Dan shi kansa Maash fa akwai wani ƙunsashen al'amari a tashi duniyar dako fara taɓota bamuyi ba.

★Kai kar dai na cikaku da surutu, ku shirya kawai tsaff zuwa bayan salla idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya domin samun duka wannan amsoshin a TSUTSAR NAMA BOOK 2 har ma da wanda baku sani ba.

★Ya rabbi ka karɓi ibadunmu, ka gafarta mana ka yafe mana kurakuran mu. Ƴar uwa! Ɗan uwa! Duk wanda naima ba dai-daiba ya gafarceni. Nima na yafema kowa. Kada ka bari ko ki bari ku zama cikin jerin mutanen da zan iya kaima UBANGIJINA kuka a kansu a acikin wannan watan mai tunkaromu. Wannan shawara ce. Dan nima bazanyi fatan nazama cikin wanda kuma zaku kai ƙarata wajen UBANGIJINA ba. Fatana kumin addu'ar fatan alkairi nima na muku tare da iyayenmu baki ɗaya.


Taku har kullum👎
    BILKISU IBRAHIM MUSA
            (Bilyn Abdull 💞)


(C)2024.


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login