Showing 66001 words to 69000 words out of 88219 words

Chapter 23 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull

29 Jun 2024

18171

doctor a daren jiya ne ya fara shigowa. Sangamemen ƙato biye da shi da da ledoji a hannu. Muna haɗa ido da shi na kauda kaina. Shima nasa kan ya kauda, batare da ya sake kallona ba ya furta, “Waɗan nan naki ne zaki iya amfani da su. Bayan su duk ma abinda zaki iya buƙata akwaisa a ɗakin. Likitarki ta gama aikinta, har magungunanki gasu anan ta kawo”. Daga haka ya juya ya fita. Da kallo na bisa zuciyata na wani irin kai-kawo. Kenan dai da gaske mutanen nan ne sukai kidnapping ɗina. Sune kuma suka saka ake bibiyata? Hakan na nufin sun san na ɗauki wannan video recording ɗin dai kamar yanda nai tunani?. (Ya ALLAH ta yaya hakan ta kasance?) Na faɗa a zuciyata, a zahiri kam ina mai runtse idanuna dake cike da nauyi har yanzu. Na kai tsahon mintuna goma ina faman tunani kafin na yunƙura na tashi da ƙyar, dan dama yanayin da jikina ke ciki yasa bance da shi komai ba da ya shigo. Yanda na jiƙa wajen da jini ya bani tsoro sosai, kamar wadda tai ɓarin ciki jama'a, haka dai na daure na sakko, sai dai ganin an saka min abune a inda na kwanta ɗin ba ainahin gadon na ɓata ba na ɗan saki ajiyar zuciya. Abin mai kama da leda-leda katifa-katifa na tattare na ɗauke. Cikin ɗingisa ƙafata dake ciwo na nufi hanyar da nake ƙyautata zaton toilet ne. Shi ɗinne kuwa, sai dai ya tsaru matuƙa, dan da za'a bani zaɓin wajen kwanciya maybe na kawo katifata nan na shimfiɗa, bawai dan yafi ko ina ƙyau ba, kawai dai ya birgeni ne shima. Duk da rashin ƙarfin da nake ji haka nai ƙarfin halin gyara jikina yanda ya kamata, nai wanka da ruwa mai zafi sosai. Sai a lokacin kuma hankalina ke neman tashi tuna bani da pant balle azo ga batun bad, sai dai tuna abinda yace yasa na fito. Ledojin da suka ajiye na shiga buɗewa, ta farko abinci ne, ta biyu kuwa kayan ciye-ciye ne. Sai ta ƙarshe ce ke ɗauke da kayan sawa, a ciki na samu pants da bad ɗin. Duk da naji wani iri da ganin hakan banda damar ƙorafi, ɗauka nai kawai na koma ciki na kimtsa jikina na dawo ɗakin. Kayan na sake buɗewa na ɗauki doguwar riga na saka batare da na damu da sanin sauran abinda ke ciki ba. Bana jin yunwa, dan in har ina a wannan yanayin ban cika son cin abinci ba, sai masifaffen kwaɗayi kamar sabuwar mayya. Dan hankalina duk yana akan naman can dana gani, ko naso basarwa kuma bazan iya hakan ba, garama naci bai nak yanda zan samu ƙarfin sauke musu abinda ke kaina. Zama nai kuwa nacisa sosai har saida naji na ƙoshi, na fiddo magungunan dana gani na duba duk yanda aka tsara shansu suma nasha.
       A yanzu bana buƙatar zaman yin dogon tunani, tunda na fahimci a hannun waɗanda nake saɓanin kwanakin da suka gabata da nake canki canka da rashin tabbas. Yanzu babbar damuwata ahalina. Na tabbata duk inda Yaya Musaddiq da Mansoor suke hankalinsu a matuƙar tashe yake kodan kiran da nai a waya. Amma ina fatan askine yazo gaban goshi, dan nayi alwashin komi mutanen nan zasumin bazan taɓa basu video ɗin nan ba ko faɗa musu a inda zasu samesa, iyaka dai suce nima zasu halaka ni, ban damu ba, dan hakan da zasu yi shine mafi girman kuskure da zai tona asirinsu insha ALLAHU.

        Shan maganin ya ƙara saka min jin daɗin jikina. Sai dai damuwa data kasa ɓoyuwa a kan fuskata. Sai gajiyar zama waje ɗaya daban saba ba. Nida nake yini tsaye kan ƙafafuna ina faman bautar aiki, garama idan office naje akan ɗan samu sassauci tunda shi kusan daga zaune ne. Motsin sake buɗe ƙofa da naji ya sakani tashi daga kwancen da nake cikin kujerar ɗakin, ɗan kwalin abayar naja na rufe kaina zuwa ƙirjina da ƙyau. Dai-dai nan aka ƙarasa shigowa. Mutumin ɗazu ɗinne dai, daga bakin ƙofa ya tsaya yayinda ni kuma nake kallonsa a tsiwace. Dan sai yanzu ne komai ke dawo min game da sanin da nai masa. Tabbas shine yaron mutumin nan mai kama da ƴan daudu ko nace ɗan daba ma ko sara suka oho duk ya cancanta, shine kuma ya kira da PA ɗinsa a ranar wancan taron. Nai saurin kauda kaina ina ƙoƙarin dai-daita fuskata da jikina. Tsahon mintuna kusan biyu ɗakin shiru, kafin cikin son nuna jarumta na furta,
         “Dama kune kukai kidnapping ɗina?”.
      Maimakon bani amsar dana buƙata sai jinai cikin bada umarni ya ce, “Zaku iya shigowa”. Baima ko gama rufe baki ba kuwa garadan samari biyu suka shigo. Ko namiji yaga wannan samudawan dole ya ji tsoro balle ni, amma dai nayi ƙoƙarin dake zuciyata ban bari tsorona ya fito a saman fuska ba. Sai dai faman haɗiyar yawu nake da ƙyar zuciyata na faman kai da kawo a cikin ƙirjina. Umarnin tashi suka bani, bani da ikon yin musu ko dan bindugun dake a hannunsa, ɗaya daga cikinsu ne ya koma ta bayana ya ɗauro ƙyalle a saman idona, zanyi magana ya ce, “Shiii!! Young Lady, inba hakaba harsashi ya rufe miki baki”.
     Yawu na sake haɗiyewa mai kauri, daga haka ban sake magana ba har suka bani umarnin tafiya bayan sun saka min wani abu a hannu na riƙe. Tafiya kawai naji munayi batare dana san ina muke nufa ba, amma dai baka jin hayaniyar komai ko'ina tsitt sai kukan tsuntsaye daga ɗan nesa damu kaɗan. Da ace hannuna babu handcuffs wlhy sai na cire abinda aka rufen fuskar komai ma za'ayi ayi. A haka naji mun shigo wani waje mai shegen sanyi da ƙamshi na musamman. Nanma mun ɗan yi tafiya kafin naji mun tsaya cak a inda ƙafata ta taka wani lallausan abu.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_



......Kamar yanda d.c.o ya nema washe gari an sake kawo masa bayani akan ɗayan daya buƙata. Sai dai abin baƙin ciki shima layin na taƙaitaccen lokaci ne kamar wancan, ba kuma a taɓa kiran wani da shi ba. Nasara ɗaya da suka samu itace na shi wanda yay register ɗin layukan duk mutum ɗaya ne. Kuma a lokaci ɗaya yayisa. Sun saka a nemo musu shi a duk inda yake. Hakama abokin masu napep an samu nasarar cafkosa a safiyar yau. Bayan kamar awa biyu da kawosa police station ɗin aka kaisa office ɗin d.c.o kamar yanda ya buƙata. Sai da ya gama masa kallon tsaf daga sama har ƙasa kafin ya tura masa hoton Samraah dake gabansa.
      “Kasan wannan?”.
   Ya faɗa kansa tsaye idanunsa ƙyam akan saurayin. Hoton saurayin ya ɗauka ya kalla na kusan sakan talatin, ɗagowa yay ya kalla d.c.o sai kuma ya rissinar da kansa yana ɗan jinjina kai. “Nasanta ranka ya daɗe. Sam-G ake kiranta, tana gabatar da shirin matasa kuma ina ɗaya daga cikin fans nata da shirin baya wuceni ta redio ko shafukanta na sada zumunta  musamman YouTube da ake ɗora shirin, nakan je na kalla videos ɗinta”.
        Kai d.c.o ya jinjina masa da faɗin, “Masha ALLAH. Minene sana'ar ka?”.
     “Direban napep ne yallaɓai”.
  “Kozan iya sanin ranar goma ga watan nan kana ina? Da ga shida na safe har zuwa ƙarfe takwas?”.
    Jimm yay irin na mai son tunano abu. Har kusan minti ɗaya sai kuma ya ɗago yana girgiza kansa. “Na manta yallaɓai. Saboda kwanakin sun ja da yawa”.
      “Uhhm yayi ƙyau” d.c.o ya faɗa yana kallon yaronsa. “Azo da yaran nan su duka”.
   Kai yaron nasa ya jinjina cikin girmamawa. Fita yay babu jimawa sai gashi ya dawo tare da samarin farko da aka fara kamawa. Yanda suke kallon saurayin haka yake kallonsu. Duk da babu duka ko zagi da akai musu zaman waje ɗaya da ɗan karan Dauda yasa duk sunyi wujiga-wujiga dasu....
     “Kasan waɗan nan?”.
   “Eh yallaɓai na sansu, su duka abokaina ne. Tare ma muke harkar napep ɗin ma.”
    “Kace ka manta mi kayi ranar goma ga watan nan da safe ko?”.
   “Eh yallaɓai a gafarceni”.
D.c.o baice dashi komai ba. Sai abokinsa ya kalla ya ce, “Kai tuna masa”.
     Kai tsaye abokin nasa ya ce, “Kazo ɗakinmu ni da ƙanina bayan sallar asuba dan gari ma bai gama haske ba. Kace na baka makulin mashin ɗin Imran zakaje amso saƙo tasha kai taka tayar na gareji dan naka babur ɗin ya samu matsala tun jiya sai barinsa ma kayi ya kwana a gareji kan yau zaka kai musu tayoyi da zasu canja maka. A gaban ƙanina Isa akai komai kuma”.
      Da sauri ya dafe kansa ya ce, “Tabbas anyi haka Salisu. Tabbas abinda ya faɗa gaskiyane yallaɓai, amma a gafarceni inada yawan mantuwa ne wlhy. Na amshi mashin ɗin, abinda nace kuma zanyi naje nayi da shi”.
      “Masha ALLAH haka muke son ji ai dama. Ina ka kai yarinya to? Sannan waye ya sakaka kidnapping ɗinta? Ko raɗin kanka ne kawai?”.
     “Ya salam kidnapping kuma? Ni banyi kidnapping kowaba ranka ya daɗe. Duk wanda ke tare dani kuma yasan wannan ba aikina bane ba inada sana'a. Taya ma kuma na rasa wanda zan ɗauka sai Sam-G”.
      “Ƙarya kake yi, a waccan ranar ba gareji kaje da napep ɗin abokinka ba Yakasai kaje layin gidan su Samraah. Kai zaman jiranta na kusan mintuna talatin da huɗu. Zata iya yiwuwa kasan dama zata fito a lokacin ne. Dan haka tana fitowa da shirin tsaida abin hawa kazo ka ɗauketa. Ka tsaya a dai-dai fita anguwar ta titin bayansu gaba ɗaya. Ka cire wayarta da facemask da eyeglasses ɗinta ka ajiye saboda maybe kana tunanin za'a iya ganeka ko kuma wanda ya saka ka aikinne ya baka umarnin yin hakan. Ɗan saurayi ban kawoka nan dan ka raina min hankalina ba. Amma kana da zaɓi guda biyu. Fitomin da komai a yanda yake dan ka samu sassauci ko cigaba da raina min hankali na saka ka faɗa ta dole wanne ka zaɓa?”.
Ɗan jimm yay na wasu sakanni, sai kuma ya sauke numfashi da faɗin, “Zan faɗa maka gaskiya yallaɓai.......

   🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟

      Cikin fisgar zaren da suka ɗaure min ido naji sun warwaresa. Har sai da na ɗan ciza lips saboda yanda naji zafi, amma dai na dake ina mai buɗe idanun nawa a hankali, dan zan gama da ogansu ne sannan na dawo kansu shegu masu suffar bakaken aljanun kan kuka. Sosai gabana yay masifar faɗuwa dan kai tsaye idanuna akan mutumin dake zaune cikin kujera yay crossing ƙafafunsa idanunsa a tab.. dake a hannunsa suka sauka. Ga wani daddaɗan ƙamshinsa da ya cika min hanci da gauraye falon gaba ɗaya. Fuskarsa ciɗin-ciɗin kamar bai taɓa sanin abinda ake kira dariya ba ko saƙon wani bala'i ya riskesa a yanzu. yauma akwai kitso a kansa guda biyu rak da suka zanu tamkar an zana a takarda dan zaka rantse ba hannu ya kitsasu ba, sai farin sirrin gilashi da ya zauna masa ɗaram a fuska tamkar an haliccesa da shi ne. Yatsunsa biyu ya ɗan juya, da sauri sangama-sangaman samarin nan da suka rakoni da bindiga duk suka fice aka bar abokin cin mushen nasa kawai. Sai lokacin ya ɗago ya zuba min cat eyes ɗinsa. Kallon ido cikin ido mukaima juna. A take naji ciwon marata na neman dawowa sabo fil, ba shiri nai saurin duƙar da kaina ƙasa zuciyata na wani kalar masifaffen bugu kamar zata faso ƙirjina ta fita. Amma cikin ƙarfin hali na murguɗa masa baki bayan na saukar da idanun.
     Shima janye nasa yay cikin yanayin isa da ƙasaita. “Sit!” ya faɗa a daƙile yana maida kansa ga tab ɗin tasa. Duk da na gane dani yake banyi abinda yace ɗin ba har sai da yaronsa ya sake maimaita min a ɗan tsawace. Ta ƙasan ido na hararesu su duka, kafin na kai zaune saman lallausar kujerar falon, amma sai yaron nasa ya daka min tsawa da mun nuni da wai na zauna ƙasa. (Munafuki ɗan baƙin ciki) na faɗa a raina, a zahiri kam hararsa na sake yi sannan nayi yanda yace na zauna ƙasan carpet ɗin da ko makaho ya laluba yasan ya haɗu. Jikina na ɗan takure a waje ɗaya, na tallafo ƙafafuna duka da hannayena biyu idanuna na kallon carpet ɗin. Sai da kusan mintuna uku suka sake shuɗewa babu alamar zai sake magana, sai kuma a cikin daƙilalliyar muryar nan tasa ya ce, “Wa kike ma aiki a kaina?”.
        Sosai tambayar tai matuƙar bani mamaki, har takai na ɗago na ɗan kallesa. Amma a mamakina bama ni yake kalloba, wasu files ne a hannunsa yan rubutu a ciki ya ajiye tab ɗin yanzu. A hankali na maida kaina na duƙar, nima sai da na kwashe wasu sakanni kafin cikin siririyar muryata da yanayin gafara na bashi amsa, “Ni nafi ƙarfin yima kowa aiki ai, dan ni ma ɗin gayyace”. Shiru baice komai ba, dan haka na cigaba da ƙunƙuni ƙasa-ƙasa batare da tunanin zasu ji ni ba. (Ni ai nafi ƙarfin aiken wani, sai dai zuwan kai da kai. Dan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE ai. Idan kuma baka san haka ba kaje kayi bincike. Ashe ma matsoraci ne, tunda har baka iya fito na fito sai ta YAƘIN SUNƘURU...)
       Harara yaron nasa ya zuba min. Kafin cikin kakkausar murya ya furta, “Hattara dai ƴammata. Dan ba'a ado da furuci wani lokacin takobin yanka wuyan mai shi yake zama. Nan ba gidan jarida bane, fadar SARKI ce mai cikakken iko kike.”
      Murtanin harar nima na maida masa ƙasa-ƙasa. Sai dai na gagara iya cewa komai saboda yanda ogan nasa ya tsareni da shegun kaifafan idanunsa na maguna. Tsahon lokaci falon shiru, yayinda tuni ya janye idanun ya maida ga abinda yake yi. Sai zuwa can a wani irin daƙile ya furta, “A duk sanda wani ya nema shiga min hanci nakan ji farin ciki da mazantakar fyatosa. Shiyyasa abinda yafi birgeni a duniya sune mutane irinki masu taya business ɗin da bai shafesu ba. Well ba tabbatar miki da ni waye yasa nasa a kawoki nan ba, dan inada tarin ayyuka na kai da kai matuƙa. WAYE YA AIKO KI WAJENA?”.
       Takaicin maganganunsa yasa bamma san sanda na furta, “Umarnin kaina nake bi ni, na kuma faɗa ai”.
     A harzuƙe yaronsa ya katseni da faɗin, “Be careful ƴammata. Walƙiya ba tana nufin ado ne kawai ga sararin samaniya ba. Takan zama gargaɗi ga ma'abota shagala ne. Jirgin ƙasa duk ƙawatuwarsa a hanyarsa kawai yake iya tafiya, saɓanin hakan faɗuwar baƙar tasa zaiyi ta yanda ko kufansa bazai moru ba balle ma'abota shiga cikinsa. Ki dinga bambance tsakanin sama da ƙasa a duk lokacin da kikai tunanin hawa tsani da tunanin taɓa rana ko farin wata. Dan batun wanda zashi sama ya taka leda zance ne kawai irin na masu iya magana.”
       Baki na laɓe tare da watsa masa harara ta ƙasan ido. Cigaba yay da faɗin, “Kina da zaɓi biyu, bada abinda ke hannunki ki koma ki cigaba da rayuwarki cikin salama, ki kuma sakama ranki baki taɓa ganin komai ba a wacan ranar, ko nuna taurin kai ki dawwama anan har ƙarshen numfashinki, kin buƙaci 500m an baki rabinsu, amma ke kin kasa cika naki alƙawarin duk da an tabbatar miki idan kin bada za'a baki sauran 250m ɗin. Ke kin san kuwa dawa kike tare ana?”.
     Yanzu kam sosai na ɗago a razane matuƙa, tare da wurga masa hararesa dan naga yama fi ogan nasa zaƙewa. A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_


.......A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?. Aikin naku ya wuce kisan kai da kidnapping harda sharri kuma. Lallai tatsuniyar gizo da ƙoƙi kenan young man, kasan kuwa gaibu ce dan hikimace kawai irin ta masu iya zance da rubuta hikayoyi. Idan har ka yarda ba'a mutuwa a dawo, to ka ɗauka abinda duk yake a hannun Samraah Gwarzo mallakinta ne ita kaɗai, ko a mafarki bazan taɓa cinikayyarsa da wani ba. An gaya maka nima faƙiriyace bana neman na kaina ne da zan zauna neman a bani fansar kuɗin jinin mutane akan video?. ALLAH ya sawwaƙe, Banyi lalacewar baƙar tasa ba ai, banga kuma wata dukiya da wani zai tara taja hankalina ba dan nima dai kasuwancin nan inayinsa. Ɗan jarin nan na dubu ashirin da ake rainawa na tara wataran sune zasu koma miliyan dubu ashirin ɗin. Dan haka kuma nema wanda ya amsa kuɗinku tun wuri amma ba ɗiyar Abdul-wahab ba. Idan kuma kaine ke yawo da hankalinsa ka faɗa masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login