Showing 15001 words to 18000 words out of 22968 words

Chapter 6 - A WANI COMPANY COMPLETE HAUSA NOVEL

25 Aug 2024

5570

na jefawa ganin ya ƙi faɗowa gashi ta gaji ya sa ta zauna agun tana haɗe rai Suhail da fitowarsa kenan ya na nemanta security ne ya ce masa ya ganta ta shiga lambun cen nufar gun yayi ya na zuwa ya ga ta haɗe hannu biyu a kumatu ta na hawaye da sauri ya ƙasa ya na tambayarta abunda ya faru nuna masa mangoro tayi kuma har lokacin ta na hawaye murmushi yayi kawai ya kira wani security bashi umarni yayi akan ya ciro masa mangoro da yawa ya kai masa mota ai ta na jin haka ta miƙe ta na murmushi jindaɗi "toh taso muje ko" babu musu ta bisa suka fita a lambu suna shiga cikin motar ta zauna lokaci zuwa lokacin sai ta leƙa ganin har yanzu security bai tahoba ya sa ta ƙara turo baki "menene kuma toh?" ta ce" bashine har yanzu bai tahoba" "ke kuma rashin haƙuri" juyar da fusakarta tayi ta na ƙara turo baki murmushi kawai yayi security na zuwa ya buɗe boot ya saka musu zagayowa yayi "sir an saka a boot" okay ya bashi amsa drive ya ja suka fita kai tsaye gida ya kaita suna isa ya sa aka ɗako mata ledar mangoro mai uban yawa sai murmushi take kamawa tayi ta na shiga cikin gidan sakin baki Mama tayi tana kallonta ganinta ruƙe da uwar leda ta ce "ke ko Menene acikin wannan ledar?" "mangoro ne" ta bata amsa tana murmushi "wato kefa na fahimci ma ba aiki kike ba a Company wallahi kawai shirma kike" turo baki tayi ta na shiga ɗaki da abunta tashi Mama tayi tana bunta a baya zama tayi akan tabarma ta na buɗe ledar "kuma fa walloh Mama ya nuna mangoro" "eh gashinan ai nagani sai ki bada himma kisha" ɗauka tai zata kai baki "amma ai kya wanke ko?" dafe kai tayi ta na dariya "wollah ni nama manta ana wani wankewa" ta ce" dama ya za'a yi ki tuna tunda yau ala ya haɗaki da mutumnin ki"



Suhailat ganin har yanzu Ayrah bata zoba kuma gashi lokacin ta shi ya kusa ya sa ta miƙe dan shirin tafiya gida ta na fitowa taga p.a ta sako daga saman "amma yawa Ayrah fa?" kallon sama da ƙasa tayi mata kafin tace "wacece kuma haka?" shiru Suhailat tayi bata sake cewa komai ba dan ta fahimci p.a bata da mutunci ko kaɗan kama hanya tayi tai wuce warta

"Ayrah!! Ayrah!! ki tashi daga bacci nan kin san fa babu kyau bacci yamma ko tun da kika dawo kike ta bacci ko abinci baki nema ba" buɗe idanunta tayi ta na kallon mahaifiyata


A hankali ya ke sauka daga matata kalar bene sanye ya ke cikin white cuz ya haɗe gashinsa guri ɗaya farin ne tass gashinsa ya sauka har gadon bayansa da wani irin sauri security suka nufosa suna isowa gun gaba ɗaya suka rusuna ɗago kai yayi yana kallon su ya salam kyau iya Kyau kyakyawa ajin ƙarshe sanye yake da farin glass a fuskarsa gefan sa wata mata tace wadda aƙala zata haura shekaru (45) itama fare tass kamar dai shi sanye take cikin Black abaya mai duwatsu tayi rolling da belt na abayar hannuta ruƙe ya ke cikin na haka suka jera suna tafiya gwanin ban sha'awa suna isa bakin motar aka buɗe musu suka shiga kai tsaye kata faran gida dake maitama hills estate ya salam gidane iya gida girman gidan ya zarce misali gaba ɗaya gidan zagaye yake da security ta ko ina mai gadi ne ya buɗe get ɗin da jerewa motocin suka yi zuwa cikin gidan tun kafin su gama parking ta fito da gudu ta na ihu duk da tsakanin cikin gidan da pearking lot da nisa amma hakan bai sata ta howa da gudu ba ta na murna "Oyoyo Ammina Oyoyo ya Abrad" shine kawai abun da take furtawa ta na gudu murmushi yayi kawai ya kalli Ammi itama kallon na sa tayi da sauri ta faɗa jikin Ammin ta na murmushi cen kuma hawaye ya fara zuba akan fuskarta "Ammi shine kuka tafi kuka barni ni kaɗai ko?" "ohh Jiddah toh yanzu kuma menene abun kuka ai gashi mun dawo ko?" gyaɗa kai tayi ta na kallon Abrad jan hanci ta yayi ya na cewa "rigimama Ammi" murmushi tayi ta na turo baki "nifa fushi na ke da kai" "kaina bisa wuya na idan kikai fushi da ni ina zan kama" ya faɗa ya na yin gaba abunsa dan shi bai cika yawan magana ba wananan ɗin ma yayi ta ne kawai wani haɗaɗan falo ya shiga mai tsanani kyau irin falon nane da ko gidan shugaban ƙasa ba a samunsa a hankali ya zauna a kan kujera da ke gun ya na lumshe idanunsa wani irin sanyi ne ke ratsa masa zuci yau dai gashi ya dawo Nigeria duk da badan Ammai taje ta tawo dashi bana babu abun da zai dawo da shi

Ammi kama hannu Jiddah tayi suka shiga na su apartment ɗin sai surutu ta ke kamar redio dan Jiddah badai magana ba


Ayrah fitowa tayi cikin ƙanan kaya masu kyau da shaƙi kallonta Mama tayi tai murmushi "kin yi kyau sosai" murmushi tayi ta na zama akan tabarma "wallahi Mama na ƙagu gobe tayi naje aiki saboda za'a bani salary na" murmushi Mama tayi "waya ga su Ayrah da salary" wata dariya tayi mai cike da nuna zallar farin ciki ta


Tashi yayi ya haura sama ohh ya rabbi ashe ba komai na gani a ƙasa ba dankareren falone shima na alfarama bedroom ya shiga dan watsa ruwa

Ɗaure ya fito cikin white towel iya gwiwa hannusa na ruƙe da karami wanda ya ke tsane kansa da shi

Wani irin taunar cingom take mai bada sauti kallon wata ƙarama yarinya tayi wadda baza ta fi Sa'ar Jiddah ba "kinji na gaya miki wallahi kika sa ke kikaje wajan mutsiya tan cen ranki sai ya bacci sakara kawai" "rabi da ita Momy ita yarinya wallahi na fahimci tafi son Ammi" "eh ɗin nafi sonsu kuma ni wallahi duk abinda zakuce sai dai muce haka kuri ni dai wallahi Momy akullum ba zan daina faɗaminki kiji tsoran Allah ba kuma kisan zaki mutu" da sauri Momy ta bige mata baki "zaki rufemin baki ko kuwa sakarar yarinya sai anyi magana ki farawa mutane wa'azi angaya miki mu bamu san abunda ya dace ba ne?" tashi tayi ta haura sama tana ƙunƙuni
"Na fahimci yarinya nan sai na shiga dukanta zata dawo hankalin ta" "kema ce Momy tutuni nagaya miki ki kaita wajan durfus kawai ya rufe miki bakinta wallahi idan ba haka ba duk wani shirinki sai ta tarwatsa sa yanzu gashi su ya Abrad sun dawo Nigeria kuma da kince ance miki ba zai taɓa dawowa ba" shiru Momy tayi ba tace komai ba dan itama al'amarin duk ya ɗaure mata kai

Niko nace Allah kenan babu wani wanda ya isa yayi abunda Allah bai ba hajiyata[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ





A WANI COMPANY


BY.
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT.


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS


Fallow my account.
Arewabook@hauwauomar




Page_16_17




Be ce mata komai ba ya buɗe idanunsa "Kin ɗauka na yi bacci ko shiyasa zaki gudu" girgiza kai ta yi alamar a'a "Jeki toh idan an kusa tashi sai ki dawo" "Okay sir" ta faɗa ta na fita dan zuwa office ɗin Suhailat

Ana tashi ta fito dan nufar office ɗin Mdee a hankali ta tura ƙofar tashiga ganin baya cik i ya sa ta zauna ta na jiransa. Fitowa ya yi cikin wasu fararan cuz masu kyau, tsayawa ta yi tana kallonsa ganin da marron ɗin cuz ce a jikinsa yanzu kuma ya canza kenan da wasu kayan ya ke zuwa Company? ta faɗa ta na cigaba da kallonsa zuwa ya yi dab da ita ya sunkuya "Madam shi kuma kallon fa na menene?" murmushi ta yi tana saurin kawar da kanta "Tashi muje ko?" babu musu ta miƙe tabi bayansa, suna fita su ka shiga cikin motar kai tsaye ya gida su ka nufa. Suna isa ta fita dan shiga gida "Baki jiba" juyowa ta yi danjin mai zaice "Ki gaidamin da Mama" "Toh insha Allah zan faɗamata"


Tsaye ya ke ajikin window apartment ɗinsa, sanye ya ke cikin treecotar black da white riga mai kyau haɗe gashinsa ya yi ya ɗaure guri guda idanunsa a lumshe ya ke wani irin jindaɗi yanayi ya ke garin lileɓe ya ke da hadari mai tafiya da iska mai sanya nishaɗi da gudu ta shigo cikin bedroom ɗin ta na kwala masa kira dafe kansa ya yi wanda ya ji ya sara masa "Ohh ya rabbi wai Jiddah yaushe zakiyi hankaline?" turo baki ta yi Kamar zata yi kuka "Toh ni ba Ammi ce ta biyo ni zata dakeni ba dan na ɗauka mata waya shine na zo gurinka, ka hanata dukana amma ka ke min faɗa ko ya Abrad" ta faɗa hawaye na zuba akan fuskarta "Dan Allah kiyiwa Allah kimin shiru Jiddah" banza ta ma sa ta cigaba da kukan ta tsawa ya daka mata, da sauri ta fita a ɗakin ta na kuka
Ammi da ke nemanta ganin tana kuka ya sa ta tambayarta lafiya? karasawa ta yi ta rungumeta "Wai ke lafiyarki ne kike min kuka?" "Ba ya Abrad bane ba ya yi min faɗa" "Da ya miki faɗa ke me kika masa"? "Ni Ammi babu abun da namasa ki tambayesa"

"Naji maza ki wuce ciki kiyi shiri islamiyya" babu mu su ta nufi bedroom ɗinta dan shiryawa ajere su ka fito ita da Yusra drive ne ya ƙaraso yana buɗe musu motar, shiga su ka yi hannusu ruƙe dana juna. Suna isa Jiddah ta dubi Yusra ta na dariya hararata ta yi "Mie kikewa dariya ke kuma?" "Babu komai kawai ina tuno darun da zakuyi keda ya Ustaz ne" "Toh ina ruwanki nifa Allah bana son gulma" gwalo ta ma ta ta na fita a motar da gudu, bunta ta yi itama da gudu su ka shiga gudu a makaranta Ustaz ne ya ƙaraso gurin ya na mu su magana tsayawa sukayi su na suraransa "Wai ku kullum sai kun shigo kuna gudu haba ya kamata ace kunsa kun girma fa" Jiddah ce ta turo baki "Ni dai Allah ya Ustaz ku daina cewa mun girma nawa mu ke ne nida Sis za'a na cewa mun girma" dariya ya yi kawai yai gaba abunsa dan yasan idan ya biyesuu sai sun bashi ciwon kai.


Ayrah na shiga gida ta sa ki ajiyar zuciya ta rasa mai yasa a yanzu idan ta na tare da Mdee ta ke rasa nutsuwarta ganin sai murmushi ta ke kamar wata zautaciya ya sa Mama da ta ƙaraso gun ta dafata firgigit ta dawo hayyacinta "Ke kuma lafiya kike murmushi?" "Babu komai ni kawai ji nayi ina cikin nishaɗi" "Toh Allah ya kyauta" "ameen" ta ce ta na nufar cikin ɗakin na su kwanciya ta yi saman tabarma ta na kallon silin ɗakin da ya sha wuya ya ke bukatar taimako. Abincin Mama ta ajiye mata "Ki tashi kici abunci kinji" miƙewa ta yi ta na janyo yar karama samira shinkafa ce da wake da mai sai salat da aka yanka, ba Ayrah ba ko ni sai da na yi sha'awar cinta😁 bismillah ta yi ta fara ci dama wata irin yunwa ta ke ji lumshe idanunta ta yi "Wollah Mama wannan abunci na ki ya yi daɗi sosai" murmushi Mama tayi "Kodai na sa miki waigi ne" dariya ta yi ta na cigaba da cin abunci


Su na tashi su ka fito dan tafiya ruwa ne ya fara zuba da sauri Jiddah ta karasa ta shiga motar jan luck ɗin ta yi ta rufe, Yusra da karasowarta kenan ta yi ta yi ta buɗe ta kasa drive ta ce ya buɗe ma ta wani kallo Jiddah ta watsa ma sa "Wallahi idan ka buɗe ma ta ko hmm" shiru ya yi ba ce komai ba "Wai sani me keke nufi ne ba cewa na yi ka buɗemin ba" dariya Jiddah ta yi ganin ruwa na ta dukanta, ganin jikinta ya fara rawa ya sa ta buɗe ma ta, da sauri ta shiga ta na ƙanƙame jikinta ko buntakan Jiddah ba ta yiba sani ne yaja motar su ka tafi. Suna isa gida da sauri Yusra ta fita ta yi apartment ɗinsu ta na shiga ta ga Momy zaune ita da Suhaima da gudu ta yi sama ta na isa ta cire kayan da ke jikinta ta sauya wasu faɗawa kan makeken gadon ta yi ta na sauke numfashi



Washegari da wuri ta fita zaune ta samesa ya na danna waya zama ta yi kan kujera ta na gaidasa amsawa ya yi cikin sakin fuska suna isa suka fito a jare zuwa cikin Company tun da su ka jero p.a ke kallonsu ita ma zuwan ta kenan ta na pearking mota ta ga fitowarsu, ji ta yi hawaye ya gangaro ma ta Allah ya sa ni ta na son Suhail shiyasa bama ta so wani ya raɓesa shin ta ya zata raba Ayrah da Suhail? shine tambayar da taiwa kanta


Ƙwafa ta yi ganin ta rasa mafita ta fito itama dan shiga ciki .Coffee ta aje masa akan table ɗin mug ɗin ya ɗauka ya na kaiwa baki, miƙewa ta yi dan barin office ɗin "Ina zaki" ya tambaye ta "Am dama zanje wajan Aunty Suhailat ne" "Shine kuma ba ki tambayeni ba" girgiza mai kai ta yi da sauri alamar a'a "Shikenan ki je amma karki daɗe dan anjima akwai inda zamu" "Thank you sir" ta faɗa tana murmushi

Da sauri ta ke sauka daga kan stap ɗin ta na sauka ta ga p.a da Oga Abdul tsaye da'alama wani abun su ke wani kallo ya watsa ma ta ya na tsaki da sauri ta ratsa ta gefe ta yi wucewarta "Munafuka ce yarinya nan wallahi" p.a ta faɗa cikin hasala tana isa ta sameta zaune ta na dube dube a laptop.
Zama tayi a kusa da ita murmushi Suhailat ta yi "Jiya ina ki ka shiga ban ganki ba" "Da wuri mu ka tafine shiyasa" "Ohk wai ni kam na tambaye ki man" "Eh ina jinki" "Kina zuwa sloon kuwa?" girgiza ma ta kai ta yi alamar a'a "Gaskiya toh ya kamata yau na kai ki saloon naga idan angyara miki gashi ya zaiyi" murmushi ta yi kawai mikewa ta yi tana kama hannuta "Zo muje kinga mu tambayi Mdee ko zai bari" tashi ta yi tabita su ka fita, su na isa Suhail ya ɗago ya na kallonsu "Sir dan Allah idan ba damuwa zamu fita da Ayrah" wani irin kallo ya ma ta da sauri ta sunkuyar da kanta "Idan kunfita kuje ina" taji ya ambata "Saloon" ta bashi amsa shiru ya yi na wani lokaci kafin ya ce "Shikenan muje na kaiku murmushi jindaɗi su ka yi su na kallon juna


Baya suka buɗe za su shiga su duka "Ni ɗin drive ku ne da zaku shiga baya" "Sorry sir" "Ayrah ki shiga gaban kinji" "A'a Aunty Suhailat ke ki shiga" wani kallota ma ta wanda ya sa ta saurin buɗe gaban ta shiga, murmushi gefan baki ya yi dan dama hakan ya ke da buƙata beauty saloon su ka isa da ke garin abuja babban gurine na musamman wanda ya kayatu, akwai wajan saloon da lalle, wajan make up duk agun, fitowa su ka yi su ka nufi wajan saloon ɗin zama ya yi a gurin su kuma su ka karasa cikin wani glass "Madam gulo ce ta fito ta na tambayarsa abun da ya ke so nuna ma ta su Ayrah ya yi dake zaune cikin glass "Ki tambayesu" ya faɗa ya na ɗora kansa a jikin kujera lumshe idanunsa ya yi wani irin bacci ke fusgarsa
Suhailat ce ta basu umarnin su yiwa Ayrah saloon mai kyau sannan ida sun gama su ma ta kalba kanana zaro idanu ta yi ta na turo baki "Allah ni Aunty Suhailat kar'amin kitso kedai kam anyi raguwa wallahi" "Dan Allah Aunty Suhailat" ta faɗa cikin shagwaɓɓa "Allah fa ke daina marairaice wa dan sai an miki" shiru ta yi kawai ɗago idanunsa ya yi dai-dai lokacin da ake warware mata kai masha Allah ya ambata cikin cool voice ɗinsa, cikin muntina da ba su wuce 30 ba aka gama mata komai bakaramin kyau kalba ta ma ta ba zubawa kan nata idanu ya yi tabbas yarinya Allah ya yi mata baiwa kala- kala "Sir" da sauri ya kalleta ya na mamakin yaushe ta iso nan? mikewa ya yi su ka nufi ƙofar fita su na shiga kai tsaye su ka sauke Suhailat a gida kallon Ayrah ya yi "Kin yi kyau sosai da wannan kitso" murmushi ta yi tana mamakin yaushe yaga kitson na ta "Kina mamakin yadda nagani ko?" ɗaga ma sa kai ta yi dan har ga Allah ta yi mamaki


Buɗe murfin ta yi ta shiga ɗa ga ma ta hannu ya yi ya na murmushi, ta na shiga gida ta ga babu kowa a tsakar gida karasawa cikin ta yi Inna lilahi wainna ilayi rajiƙun
Mai ta ke gani haka







Ina ma'abota sun littfin a wani Company na ce ko kinsan har yanzu ba'a fara wasan ba ko kinsa cewa yanzu ne ƙadarorin Ayrah za su fara ohh ya rabbi ki hanzarta biya danjin yadda zata kaya
Idan kinyi shirin biya
9165855674
Hauwau Umar Abdullahi opay.
Ki turomin evidence ta wannan Number
09165855674
Karki bari a baki labari yar uwata.. littfina ₦300 ne babu tsada
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ


A WANI COMPANY

BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT



MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS


fallow my account
Arewabook@hauwauomar05



Mikiya writer's Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login