Showing 21001 words to 22968 words out of 22968 words
jijiyoyin kansa sun tashi, p.a ce ta turo kofar tashigo sai da ta ambaci sunansa sau uku bai ɗago ya kalleta ba hakan ya sa ta ajiye file ɗin da ke hannuta ta yi ta fita ta na tunani ko menene ya faru da Mdee zama ta yi akan kujera da ta kasance mallakinta
Shin kodai taje ta faɗawa Mdee tana son zuwa gida Saboda Mamata bata da lafiya? a'a gasky bazata iya ba tashi ta yi ta fita dan zuwa cikin lambu da ke Company, tana zuwa ta zauna kan fararen kujerin da ke gun lumshe idanunta ta yi ta na jin wani irin ya na yi shiba damuwa ba shi ba farin ciki ba "Ya Allah ka sa Mama ta na cikin ƙoshin lafiya" ta furta hawaye na bin gefan fuskarta "Ameen" taji an ambata a bayanta da sauri ta buɗe idanunta wanda su ke kawo ruwa Oga Abdul ta gani tsaye ya haɗe hannusa biyu akan ƙirji murmushi ya sakar Ma ta ya na zama akan kujera da ke gefanta fine girl ya faɗa ya na murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa kawar da kanta ta yi da sauri kuma ta miƙe ta nufi hanya fizgota ya yi ta faɗa jikinsa, ƙoƙarin kwacewa ta ke amma ina gaba ɗaya ya ruke ta cizo ta gartsa masa da sauri ya saketa ya na dafe gun da gudu ta fita a wajan ta na haki dafe ƙirjinta ta yi ta na ambata sunan Allah
Office ɗin Suhailat ta shiga ganin har lokacin bata dawo ba ya sa ta saki ajiyar zuciya mai ƙarfi zama tayi akan kujera shin wananan wane kalar bala'i ne
Motoci ne yan uban su guda biyar ke shigowa cikin katafaran gidan da wani irin gudu Jiddah da ke tsaye a jikin window da gudu ta sako zuwa ƙasa a hankali ya sako ƙafarsa zuwa waje kyakyawan dattijo farine tass kana ganinsa zaka san cewa shine mahaifin Abrad saboda ya na yin Kamar su dai dai da kwayar idanunsu iri ɗaya ce rungumesa ta yi ta na murna "Oyoyo Abieeyna" "Oyoyo Mama" Abieey ya faɗa shima ya na rungumeta Yusra ce ta nufo gurin itama da buɗe hannusa ya yi ta faɗa jikinsa a hankali ya saki ajiyar zuciya ya na jin wani irin kewa da kaunar ya'ya na sa Momy ce ta fito ita da Suhaima itama rungumesa ta yi Murmushi Momy ta sa ki "urwelcome Sir"
Murmushi ya ma ta ya na kallon Ammi da ke fitowa daga part ɗinta wani irin sanyi yaji na ratsasa lumshe idanunsa ya yi da sauri ta ƙaraso ta faɗa jikinsa, a tare kuma su ka saki ajiyar zuciya mai ƙarfi haushine ya ya turnike Momy da sauri ta wuce abunta, Bunta Suhaima ta yi ita ko Yusra taɓe baki tayi alamar ko a jikinta waige-waige Abieey ya fara yi tuntsirewa Jiddah ta yi da dariya dan ta san mai yake nema juyawa ya yi ya kalleta "Mamana lafiya daiko"? "Abieey na san fa wa ka ke nema toh sai dai kayi haƙuri dan ya Abrad dai bayanan tun ɗazu ya shirya ya tafi zance" ta faɗa ta na karayin dariyata mai kyau da sauri kuma ya juya ya kalli Ammi ya na son jin da gaske ne abunda Jiddah ta faɗa taɓe baki Ammi ta yi "Kadai san yarinya nan da shirma kawai dai bai san zaka dawo bane yau shiyasa ya fita kuma kaine kace kar'a sanar ma sa zaka masa bazata" baice komai ba ya kama hannuta su ka nufi ciki bunsu su Jiddah su ka yi a baya Yusra ce ta ce
"Wai ke yarinya nan yaushe zakiyi hankali ki daina shirma?" turo baki ta yi gaba "Duk randa kika daina nima zan daina" Mtss Yusra taja tsaki dan gaba ɗaya Jiddah shirmanta ya ma ta yawa suna isa parlon ya haura sama dan hutawa bunsa Ammi ta yi "Nifa Ammi nasan yanzu kin daina kulamu saboda Abieey ya dawo ko" murmushi kawai ta yi tai gaba abunta dan ta san halin yaranan
Suhailat ce ta shiga office ɗin ta zauna "Kin jini shiru ko siste" ɗaga ma ta kai ta yi alamar eh "Wallahi muntsaya wani aiki ne shiyasa ni kaina duk na gaji, ta so muje muyi sallah" babu musu ta miƙe tabi bayanta su na isa masjid ɗin su ka ɗaura alwala shiga su ka yi ciki, bayan sun idar Ayrah ɗa ga hannu tayi sama ta na rokan Allah akan ya bawa mahaifiyata lafiya ganin tana hawaye ta na addu'a ya suna fitowa Suhailat ta tambayeta lafiya ta ke kuka? rungumeta ta yi ta cigaba da kukan "Please Ayarh kiyi shiru ki faɗamin karki sani nima cikin damuwa" "Aunty Suhailat Mamana Mamana" "Menene ya faru da ita" "Bata da lafiya jiya da na je gida ko buɗe idanunta ba ta yi" "Ya salam shine kuma kikazo aiki yau Ayrah why' "Itace ta ce na zo yau saboda jikin na ta da sauƙi" "Okay toh kiyi shiru kinji kar mutane su ga kina kuka Insha Allah Allah zai bata lafiya" goge ma ta hawayen da ke fuskartata ta yi "Smile" ta faɗa duk dan ta sa ta cikin farin ciki murmushi ta yi _Yawwa Hajiyata ko ke fa kinga yadda ki ka yi kyau? da dariya nan kamar wa ta Ashwariya 😁" "Kai Aunty Suhailat ni ina na isa na zama Ashwariya" "Allah har kin fita Ayrah ki godewa Allah ke ɗin mai kyau ce"
"Kinga zomu shiga ciki" binta ta yi su ka nufi ciki office ɗin
Insha Allah anjima page 20 zai sauka wanda ya kasance page na karshe a free page shin me kike jira yar uwa har yanzu baki payment ba kin san dacewa yanzu nema wasan zai fara ohh ya rabbi Allah sarki Ayarh ko zataci jarabawoyin da suke bibiyarta sai dai muce Allah ya bata ikon cinsu Ayrah baiwar Allah
*Littafi*
*A wani Company*
*₦300 babu tsada idan kinyi shirin biya*
*9165855674 hauwau umar Abdullahi opay*
*Zaki turo evidence ta wannan Number*
*09165855674 *
*Jinjinata agareku masoya na ina matukar ƙaunarku.❤️ Sosai kamar yadda kuke ƙaunata
*MUCH LOVE LOVER'S*
*_~MEEYRAT CE~✍️_*
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
*A WANI COMPANY 🏬*
*HAUWA'U OMAR*
Cute Meerat.
*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*.
# SQUAD 2024.
Page_20
*Last free page*
Juyi yake cikin haɗɗaɗen office ɗin mai kamada fadar shugaban ƙasa idanunsa a rufe suke dan mutum na iya zaton cewa bacci yake a hankali ya furzar da nunfashi lokacin da yake buɗe idanun nasa wowwwww!! Masha Allah Mdee Suhail kenan cikakken matashi mai ji da kansa tattausan hannunsa ya sanya ya janyo telephone pole ɗin dake gefensa wasu ƴan nambobi ya danna sannan ya kai kunne cikin wata irin kasalalliyar murya mai nuna buƙatuwa akan wani abun ya furta "Ayrah!" Abinda ya iya furtawa kenan sannan ya ajiye wayar, P.A ɗin ta fahimci abinda yake nufi hakan yasa ta mike dan kiran wacce ya ambata ɗin.
Wani irin kallo ta bisu dashi kamar na nuna ƙasƙanci sannan ta taɓe baki kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce" keee!... dukkanninsu suka fuskanceta dan basu san da wacce take a cikinsu ba, haushine ya turniƙeta hakan yasa cikin fushi ta ce"kee ba dake nake magana ba Ayrah?" kallonta Ayrah tayi da lulu eyes ɗinta bata ce komai ba dan yawan magana ba ɗabi'arta ba ce "Mdee na kiranki Malama" ta fice daga office ɗin a fusace. Numfasawa Ayrah tayi sannan ta miƙe jiki babu kwari tayi waje.
Turo ƙofar ta yi a hankali ta shiga gaba ɗaya bata jin wani ƙwari a jikinta ganin idanusa a rufe ya sa ta karasa ta zauna akan kujera murmushi ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anarsa sai da ya kai kusan five minute a haka kafin ya buɗe idanunsa da su ka yi wani irin ja tsoro ne ya kama ganin yanayin idanunsa ya sauya launi, miƙewa ya yi bai ce ma ta komai ba ya nufi bakin ƙofar ganin yasawa ƙofar luck yasa tsoro ya kamata dan hakan bai taɓa faruwa ba juyowa ya yi ya na kallonta ya ɗau tsawan lokaci ya na tsaye kafin ya cije laɓansa wani irin abu ya ke ji wanda bazai iya misaltawa ba shifa yau yaci alwashin cimma burinsa kuma tabbas zai bi zaɓin zuciyarsa.
"Sir!! Sir!!"
Murmushi ya yi lokacin da yake sake tunkarota har sannan kuma bata fasa kiran sunansa ba idanunta sun kaɗa sunyi jaa zallar tashin hankali ya wanzu akan fuskarta inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun wace irin mummunar ƙaddara ce ke neman tarwatsa rayuwarta me yake shirin faruwa ne??, Jin da tayi ta gagara yin baya ya tabbatar mata da cewa tazo ƙarshen bangone yayinda Suhail ke gabanta so close wanda har suna iya jin numfashin juna. Zufar da tagama wanketa take ƙoƙarin gogewa amma abun ya faskara bakinta sai rawa yake da alama akwai abinda takeson furtawa amma harshenta yayi mata nauyi hannayen Mdee da taji yana yawo akan fuskarta shine abinda ya ƙara tayar da hankalinta me Mdee ke ƙoƙarin aikatawa ne?, Daman ƙaddarar data kawota Companyn kenan?, wane wanda zai ceceta cikin wannan mummunan lokaci ya Rabb Ayrah ta furta cikin ranta, iskar da yake hura mata ita ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga ashe da gaske ba mafarki take ba! Da gaske *A WANI COMPANY* ne haka ta faru?, da gaske ita Ayrah ke cikin wannan mawuyacin halin?, Me zatayi wanda zata kuɓutar da kanta daga wannan masifar? Tamkar a mafarki haka zuciyarta ta ayyana mata wani abu wanda lokaci ɗaya ya yi tasiri cikin ranta har ta ɗauki hakan matsayin hanyar da zata kuɓutar da ita hakan yasa ta kalli gefenta hankali tashe glass cup ɗin da ke kan table ɗin ta janyo nufar wuyanta ya yi ya na shin-shina lumshe do yayi saboda wani ƙanshi turare da yaji wani zafin nama taji ya zo mata da sauri ta ɗaga kofi ta sauke ma sa aka da sauri ya ɗago ya na kallonta da runani idanunsa kafin ya yanke jiki ya faɗi agun dafe ƙirji ta yi tana zare idanu "Nashiga uku ni Ayrah me na aikata haka" da sauri kuma ta buɗe kofar ta fita da gudu ta wuce p.a ta sauka zuwa ƙasa ganin ta fito da gudu ya sa p.a ta shiga cikin office ɗin ihu ta saki ta na kuka "Nashiga uku ta kashe shi fita ta yi zuwa ƙasa ta na ƙwalawa security ku tareta karku bari ta fita ta kashe Mdee Inna lilahi" abun da ke fita a bakinta kenan lokacin kuma tuni Ayrah ta daɗe da fita gaba ɗaya daga Company dan gudu karma a ganta ta get ɗin baya tabi...
Wani irin azababben gudu ya keyi dalilin kiran da aka yi masa tuƙin kawai yake amma a zahiri tunaninsa baya wajen sosai kwakwalwarsa ta shagaltu da tunanunnuka wanda suka yi masa ƙawanya cikin ransa,kyakkyawar bugawar da zuciyarsa ta yi ya sanya ya ja wani uban burki ji kake ƙiiiiiiiiiiiiii! a matuƙar tsorace da kuma tsananin tashin hankali yake kallon gabansa gabaɗaya tunaninsa ya tsaya cak meya aikata ne haka?, something fishy!.
*_Kowacce ƙaddara tanada mafarinta kamar yanda ƙaddarar Ayrah ta kasance ƙarƙashin WANI COMPANY wanda yake da mabanbantan mutane masu mabanbantan halayya da kuma ɗabi'a
Alhmdllh wannan page shine karshan free page hajiya ta ki zo ayi tafiyar da ke dan ni nasan bazaki dana sani karanta Novel ɗina ba...
Shin ina Ayrah ta tafi? Mdee na raye ko ya mutu? dama Mdee ya na da wa ta manufa kenan akan Ayrah?
Idan kinyi shirin biya.
9165855674 hauwau umar Abdullahi opay
Sai ki turomin evidence ta wannan Number
09165855674