Showing 27001 words to 30000 words out of 36031 words

Chapter 10 - MIJIN TA CE Book 2

20 Aug 2024

4224

Habiba da sune to da tuni anyi nasarar korata daga gidan da kuma ba a koro wasu daga nasu gidajen ba, don haka aure daban kaya daban in ana maganar aure kuwa to miji shi ne maganar in aka yi dacen samun shi to shi kenan zance ya qare.
A fusace tace mijin da kike gadara da shi xin dai ai kawunmu ne kuma kema dolenki sai kin fito, na ce oho kin dai riga ni fitowar sannan ko Kawunki ne ba mijin ba ne tunda ba za ki yi abinda nake yi dashi ba, don haka kar in sake ganin kin zo kin xaukar mun wani abu ba ki sanar da ni ba.
Kin kuwa san duk yanda ki ka kai da gadara da abinshi saboda kusancin da ke tsakaninku, baki kaini ba, tunda kin sha faxo mana xaki babu sallama, kina ganin mu a shimfixa guda xaya, ko ba haka ba? Gidan Kawu ai ba abin gadara ba ne gidan miji shi ne abin gadara ba ki ga ni daga shigowana sai nayi kane-kane na kankane komai ba? Na wuce zan kai abinda na qwace a hannun nata kicin in ajiye.
Ado ya leqo daga xaki “Ke Humaira menene haka? Maida mata dasu, na ce to na kawo na bata ta karva ta fita ta tafi sai kuma gata ta dawo ta dangwarar mun da su ta juya ta tafi tana maganganu kici ki qara kece baquwar daxi na ce eh ni ce baquwar su na kuma gode da na yi sa’a na samu a gidan mijina.”
Nayi ta zuba ido ko zan ga Mama ta shigo da bulala ko kuma ta turo a kira mata Ado don ya amsa tambayoyi kan abinda ya faru tsakanina da Habiban, ban ji ba, a zuciyata na ce ta haqura kenan, sai da na gama abincin dare na aike musu da shi naga an dawo min da abincin gaba xayan shi wai in ji Mama ace min bata so in haxa duka in cinye ita tun kafin asan za’a haifi uwata ta same ta ne a duniya tana cin abinci, abincin ma kuma mai daxi tunda ita tuni tun da daxewa a cikin rufin asirinta take raye.
Na kalli Suwaiba da ta rattaba min bayanin nayi murmushi da gangan na kalle ta na ce mata Kawu mijina ne ina kuma son shi kamar kamar in yi ya ya? Ni kaxai nasan yanda nake jin shi a cikin raina, don haka babu wani abin da wani nashi zai yi min in ji takaici, balle Mama wacce uwata ce sannan da umarninta ne aka yi min wannan aure mai daxi ki bata haquri kafin in zo da kaina in bata.
Ta juya ta tafi ga alama kuma ta gane gatsen da nayi mata, na sake zuba idon ganin Mama ta shigo bata shigo ba. Cikin zuciyata nace in ma dai savanin Mama da Ado yayi tsananin da ta fita harkarshi ko kuma tana nan tana shirya abinda take shiryawa. Ko da yake dai a yanzu itama tana da matsalolin da suke kewaye da ita, ga Suwaiba da aka qi karvar aurenta daga dalilin xaguwa ga Habiba an ce ta dawo gida ta qara koyon hankalin zama da manya, ga Zubaida da yanzu ta watse musu kusan kullum sai ka ji ta tana zuba rashin kunya a cikin gida wai da Mama take yi daga baya kuma ka ji faxan ya rikixa ya koma tsakaninta da su Habiban.
Ga al’amarin su Yaya Ibrahim da ya riga ya baiyana har duk mutanen unguwa sun gane kusan kullum sai wani dattijo mai mutunci cikin mutanen dake ganin bari su bada haqqin maqwabtaka yayi sallama da Babana akan su yana tambayar shi anya Alhaji haka za’ayi ta zubawa yaran nan ido ba za a xauki matakin da ya dace ba?
Ga Anti Sha’awa daga zuwan Amarya kuma wai komai ya susuce mata, bini-bini sai ka ganta a gida ita da ‘ya’yanta wai tayi yaji saboda wai mijin yana nuna bambanci a zahiri, sai Maman ta kwaveta ta ce mata ta koma xakinta kawai taje ta duba taga irin matakin da ya dace ta xauka saboda a yanzu ba zai yiwu tazo ta zauna a gida ba, tunda ga Hajiyar Giyaxe ga kuma maganar Suwaiba da Habiba.
A duk lokacin da na tuna Mama da irin iko da gadaran da ta gwada na ganawa wanda bata so azabar yunwa da ta wulaqanci da duka sai in ji kamar zan ji daxin abubuwan da suke faruwa da ita, wanda nasan mafi yawancin mutane dariya suke yi mata sai dai kuma in na tuna ‘yan uwana ne sannan Babana ba jin daxin hakan yake yi ba sia in ji tausayi ya kama ni, in ce ina ma dai a kanta abin yake faruwa ba akan ‘ya’yanta ba.
Rannan Ado ya dawo gida bayan Azahar, cefane ya sake kawowa mai yawa sosai da sauri na fito daga xaki na karve shi guda xaya, xayan kuwa qin bani yayi yace muje in kai miki wannan. Muna tafiya yana tambayata sau nawa ki ka yi aman bayan fitana?
Na ce, a’a ban ma sake ba ina jin fa dama tin nan ne ya xaga min hankali don nafi son da safe insha kunun gyaxa da alala, ya ce to ki jiqa gero mana, na ce to ko kuma in ce Inna tayi min qullin, ya ce a’a ina dalili baki taimake ta kin yi mata ba sai ki sa ta aiki? Ban yi magana ba na soma fiddo cefanen don in san irin adanar da zan yi mishi, tunda ko jiya yazo da wani sai na ji ya ce min za ki yi miyar ne ta soyu da kyau ta yanda zata daxe bata yi komai ba, ta Haiyar Giyaxe ce gobe zata tafi.
Da sauri na xago kai na kalle shi, tafiya zata yi?ya ce ina laifi goben ta ce watanninta uku kenan a gidan, na ce sai tayi ai kwanci tashi babu wuya, amma kuma har na soma kewarta tun kafin ta tafin. Ya ce, to ko zan je ne in gaya mata ta haqura ta bar tafiyar sia kin haihu an yi suna tukunna? Shiru nayi ban amsa mishi ba saboda ina jin kunyar irin wannan zolayar da yake yi min.
Da wuri sosai na gama aikina na kawo mishi ya gani, ya ce min to sai ki shirya in anyi Sallah sai muje tare kiyi mata sallama, na ce to. Cikin zuciyata ina murna zan shiga gidanmu har inga Innata, bayan kwanaki tamanin ban ganta ba, duk da ga ni gata saboda bata shigo ba nima bai bar ni na shiga ba. A wani gefen kuma ina fargabar ganin Mama saboda mun yi kwanaki ba mu sa juna a ido ba.
Wanka nayi sosai na xau kwalliya mai kyau sai sheqi nake yi ina xaukar ido, doguwar riga ce a jikina ta shadda gwan shep xinta yayi matuqar fitar da surata da kyau ga xinkinta yayi matuqar kwanciya. Ado ne ya saya min shaddojin guda biyu ya bayar aka xinka min su, na sanya qananan ‘yan kunne da abin wuyansu waxanda suma shi ya saya min su a dalilin sha’awar da suka bashi sai dai a hannuna ne na sanya wara-waran daham da zobunansu na kuma xaura wani xan siririn agogo da zoben G.L, suma kyautar Adon ne.
Ya kalle ni cikin wani yanayi da na tabbatar nayi matuqar burge shi, ya ce “Ba za ki fesa turare ba ne? ai gida kawia zamu shiga.’ Na ce ‘uh’uhn bana son turaren na jikinka ya ishe mu, bai ce min komai ba in ban da kallona da ya sake yi.
“Xan kawo min turame biyu cikin kayan aurenki aro.” Nayi murmushi na ce, zan fa xunka su, ya ce eh na ji kawo min dai, naje na kawo mishi akwatin ya zubawa zannuwan ido yana kallonsu, babu wata atamfa a ciki da ta wuce dubu xaya da xari biyar, ni nafi zaton ma zannuwan da dangin uban Ado suka zo dasu daga qauye ne na gudummuwa Mama ta zuba a cikin akwatin ta xora sabulai da man shafawa ta bayar.
Zavo min guda biyu masu kyau a ciki, nasa hannu na zavo mishi su ya kuma gamsu da zaven da nayi mishin ya sake maida kallonshi kan abinda ya saura a ciki, dama zannuwan shida ne? na ce a’a takwas dai kwanaki baka ari guda biyu ba?
Ya ce, af, haka aka yi to zuba min waxannan sabulan da man in haxa mata, na ce to ai ka kwashewa Hajiyar Giyaxe kayan auren nawa. Ya ce eh ai ba kya son su, da kina son su da tuni kin xinka su kin saka, na ce to ai yanzu ina son su zan kuma xinka su in xaura don ma dai bani da keke ne da da kaina zan xinka abina.
Bai amsa ba iyaka dai ya tasa ni a gaba muka fito, bayan yasa makulli ya kulle qofar xakinmu ya kuma sake kulle qofar gida. Na sake xaga ido na kalle shi daidai sanda yake kulle qofar gidan, idanuwanmu suka haxu na xan kawar da kaina gefe ya ce, uh sai dai ki faki ido ki kallan mun kwalliyata amma ba ki san ki ce tayi miki ba, ban tanka mishi ba iyaka dai nasan yayi kyau ba kaxan ba.
A tsakar gida Hajiyar Giyaxe tana alwala ta amsa sallamar da muka yi tare da yi mana oyoyo mai yawa, na ce hala Hajiya Sallar Isha’i zata yi? Ta ce uh’uh me zan zauna yi har yanzu ban yi Sallah ba? Alwalar kwanciya nayi, na ce to kwanciyar ma har da alwalarta? Ta ce eh, muka bi bayanta zuwa xakinta wanda dama shi ya fi kusa da qofar zauren gidanmu har muka shiga bata gama yi mana bayani kan muhimmacin wannan alwalar ba, muna zama kan shimfixar da tayi mana ta koma bakin gadonta ta zauna tana kallonmu.
Ni in ce ko dama iya shege ne kawai ya saki yin abinda ki ka yi ba qin auren kike yi ba? Na yamutsa fuska naqi yin magana, yayin da Ado ya ke dariyar maganar tata da tambayar ta me ki ka gani Hajiya? Ta ce eh to abin ne nake kallon shi wani iri, ashe dama ana so ake kaiwa kasuwa, an je don iya shege har ana qwale miji da guduma, yanzu kuma sai naga ana ina aka saka dashi ba aso ko quda ya sauka akan shi.
Ado ya kama dariya yayin da ni kuma na shiga shure-shure cikin yanayin shagwava da jin kunya ina cewa bana so Hajiya, bana so.
Kin gani Hajiya za ki sa ta tayi shure-shure duk ta shuire kwalliyarta ta lalace, yana maganar yana kallona cikin murmushi ga alama daxi ya kama shi an ce ina wai ina aka saka dashi, ai ni da cewa nayi Hajiya tafiya tun yanzu ba za iki bari sai wata daga cikin amaren ta sauka anyi suna kafin ki tafi ba?
Hajiyar Giyaxe ta qyalqyale da dariya ta ce, kai dai gaya min kawai in sani cewar taka amaryar tana kan hanya.’ Xaure fuska sosai nayi naqi kulawa da zancen nasu, iyaka dai na jawo kayan da muka zo mata da su na ajiye mata a gabanta na kuma ciro kuxin da ya bani ya ce in bata na haxa tayi ta godiya tana sa mana albarka, tayi man addu’ar samunzaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma zuriya mai albarka. Ado ya ce amin.
Ta miqe ta xebo wasu kayan tana nuna mana daga gidan Atika aka kawo su, nayi murna nayi musu addu’a na tashi na bar Ado yana sa hannu a aljihu alamar zai mata wata kyautar ta daban.
Ina barin xakin Hajiyar Giyaxe can wurin Mama na shiga, samun Babana da nayi a xakin baisa ta sake min fuska ta amsa gaisuwar da nake yi mata ba, shima Babana amsa gaisuwar tawa a yanaayin kadaran-kadahan na dai san sau biyu na ganshi yana fakon idon Mama yana kallona.
Ga dukkan alamu kuma nasan canzawar da nayi ne yafi komai bashi mamaki, gashi kuma nayi kwalliya ta xaukar hankali, ban wani ja zance yayi nisa ba, saboda ganin irin karvar da suka yi min na miqe na fita. Ban tambayi su Habiba ba don kuwa nasan dukkansu suna jin shigowata suka yi kamar basu ji ni ba.
A kusa da qofar xakin Inna na ci karo da wani lafiyayyen injin xin wanki mai matuqar kyau sai da na qare mishi kallo sannan na shigo cikin xakin nata tana zaune kan kujera, gaskiya ne da Hajiyar Giyaxe ta ce min ta fara murmurewa. Ina murmushi na miqa hannu na xauki Adam karo na farko da na ji ina son shi tare da sunan da aka sanya mishin.
Na sake kallonta cikin murmushi na ce “Inna rowar yaron nan take yi sai in yi ta aiken a kawo shi kina hanawa, bata kula zancen ba, ta miqe taje ta kawo min yugurt mai sanyi mara sugar ta ajiye min, nayi murmushin farin ciki saboda ganin canjin da ta samu, na ce Inna ashe injin xin wanki kika samu shi ne nake ta aiken ki ba da kayan wanki in yi miki kina cewa babu, ba ki gaya min ba. Wa ya saya miki?
Ahmad ne ko Salisusu? Ta waiwayo a hankali ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min shi mijinki fa? Ba kiyi tunanin shi ya saya min ba, sai ki ce Ahmad ko Salisusu? Shiru nayi ban ce mata komai ba, itama ta xan yi shiru sai jimawa kaxan ta kalle ni ta ce min to, wanda ba kya zaton ne ai na xauka ya gaya miki ne shi yasa ban ce Sa’adatu taje ta gaya miki ba.
Amarya ce yau a gidan tayi maganar cikin murmushi nima na xan yi mata murmushin kaxan ta shigo har cikin falon Inna ta zauna muka gaisa, ta miqe zata fita tana faxin kai amma xinkin nan naki yayi min kyau a ina aka yi miki? Na ce a’a ban sani ba, haka naga an kawo su a xinke ta sake cewa kai ai auren wayayyen miji mai son matarshi daxi ne dashi.
Shiru nayi ban tanka mata ba, ta fita na kalli Inna cikin mamaki na ce har cikin xakin nan yanzu Zubaida take shigowa? Bata tanka ba ta ce min sha nonon mana, na ce uh’uh Inna ina dashi a gida ta ce haka ne ai daga wurin naku aka kawo to me za ki ci? Na ce ban son komai Inna sai dai ina so kiyi min qullin kunu tayi maza ta kalle ni tana tambayata yau kuma qullin kunu kike so? Naga kuma aike ba mai san kunu ba ne shiru nayi ban ce mata komai ba, itama sai kallona take yi na kuma san kyau taga nayi.
A’ah auren naku fa ya xan kwana biyu kai tafiyar lokaci bai da wuya, na ce me ki ka gani Inna? Ta ce, to ko wannan canzawa da kika yi ai ya isa a san ba shekaranjiya bane ban ce mata komai ba, ta xan sake yin murmushi ta ce ai dama tunda naga maigidan yana maida jikinshi na ce to an zauna lafiya kenan.
Shi dai aure ai kin san ba komai ba ne illa yi nayi bari na bari in zaka zauna da mutane kuma to ka zauna da su akan gaskiya nace to Inna.
Ado yayi sallama ya shigo Inna tana yi mishi sannu da zuwa ga dukkan alamu dai ya zama xa sosai wurinta cikin zuciyata nace kai Ado ma dai da qoqari yake ko da dai shi da bakinshi ya sha kiran kanshi da ‘namiji’.
Inna su sa’a basu taso ba ne? ta ce mishi eh in ma sun tashin ba su riga sun iso ba ya zauna suna hira da jin hirar tasu kasan sun riga sun zama abokan hirar juna sosai, a hirar da suke yi na fahimci Ado ne ya sanya Sa’adatu da Baba qarami a Makarantar Islamiyar unguwarmu ban dai tsoma musu baki cikin maganganun su ba.
Suka yi hirar su suka gama da ya ce mata zamu tafi sai ta ce mishi da jira nake yi Sa’adatu ta shigo don ta raka ku da kai da kafin nan ko sai da safe a kawo muku? Ya ajiye xan makullen da ya kulle qofar gidan ya ce mata gasi in ta dawo ta kai mana ta rufe gidan ta kawo makullin nan sai mun dawo zan zo in karva ta ce mishi to muka fito.
Ba mu dawo ba sai wajen goma da rabi na dare saboda unguwannin masu yawa muka je har gidan mai babban allo da gidan Alhaji mai kuxi da gidan Musa abokin Ado wanda shima bai daxe da zama ango ba, a hanya muna dawowa tun daga nesa Ado ya hangi Mama a tsaye a qofar gida cikin damuwa yake ta nanata faxin me kuma ya fito da Mama waje tare da waxannan sakarkarun yaran?
Dama dai ayi sa’a ba wata fitina suka xauko mana ba na ce to amin muna isowa yayi maza ya fito daga cikin taxin in ban da ma na tsaya na xauko mana ledar sayayyar da yayi mana da mai taxi ya tafi dashi.
Lafiya kike tsaye a waje a cikin sanyin nan Mama? Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login