Showing 18001 words to 21000 words out of 36031 words
yanzu abinda nafi nema shi ne fahimtar juna, tsakanina da ke don shi yafi komai a wurina, to amma tunda akwai wasu a bayan fage masu zuga ki to shi kenan na haqura da fahintar zan karvi budurcin in yaso sai fahintar ta biyo baya tunda na gane kin qi yarda mu fahinci junanne don kina ganin in anyi hakan akwai wani abinda zai biyo baya.
Gaba xaya na firgita, hankalina kuma yayi matuqar tashi da na gane Ado ya ji wayar da Anti Ramlah tayi min wacce na amsa a kicin ranar da nake yin abincin da aka kaiwa su Hajiyar Giyaxe, jikina yana rawa na ce mishi kayi haquri, bai kalle ni ba ya ce min kema na roqe ki kiyi haquri yau kaxai ai ni kin sha bani haquri ina haqura, don haka nina yau na roqe ki kiyi min haquri.
Ganin da nayi Ado bai da shirin haqura nema ma yake yayi amfani da qarfi wajen raba ni da budurcina sai naji gaba xaya hankalina ya tashi, na shiga tunane-tunanen da neme-nemen hanyoyin da zan bi wajen ganin na kuvutar da kaina daga gare shi, ina cikin hakanne wata shawara da Anti Ramla ta bani na kuma yi amfani da ita ta faxo cikin raina.
Kar ka taba ni, kashedi mai qarfi nayi mishi cikin tsananin firgita saboda na kai matuqa wajen tsoron abinda zai faru in har bai yarda ya qyale nin ba, bai ji ba baya ma saurarona abinda ya sanya a gaba kawai yake shirin aiwatarwa. A kiqxime cikin tsananin tsoro na shiga miqa hannuna karqashin filo ina lalube kan ka ce meye wannan na jiwo motsin abinda na ke neman wanda na daxe ina voye shi, saboda maganin vacin rana irin wannan na gwada fin qarfi da nuna zalunci da rashin adalci a zahiri.
Ado bai ankara ba saboda hankalinshi ya riga ya tafi inda ya tafi, sanda na jawo abin daga qarqashin filo na kuma taqarqare da iyakacin qarfina na kwantara mishi aka.
Sai da yayi tsalle kafin ya kai ga faxuwa a qasa cikin wani irin sauti mai tsananin firgitarwa, yana faxuwar ni kuma nakoma na kwanta cikin tsananin gajiya sai haki nake yi, ina maida numfashi a dalilin ya riga ya gajiyar da ni. Ina kwancen ina tunanin in ya tashi me zai faru a tsakaninmu? Ina qarawa gudumar da nayi dukan da ita riqo mai qarfi ta yanda in ya sake tasowa zan sake gunduma mishi ita akan nashi, sai kuma na ji shiru bai motsa ba, shirun yayi min yawa ta yanda har na kasa jurewa, na taso na leqo don ganin wane hali yake ciki.
Yana kwance a qasa shame-shame babu alamar numfashi a tare dashi, a firgice sosai na soma qurma ihu da iyakacin qarfina, ina faxin waiyo Ado, waiyo Kawu waiyo ka tashi ka zauna in ganka a zaune ka yafe min wannan muguntar da nayi maka.
Nan take wani tunani yazo min da gudu na shiga bayan gida, bokitin ruwan da na fara cin karo da shi, shi na fara jawowa ban yi tunanin yawan ruwan ba na kwara mishi shi gaba xaya cikin tsananin firgitan da ban tava ganin wanda ya yi shi ba.
Wani irin firgitaccen motsi yayi da ya qara tsorata ni da gudu na valle qofarnayi waje naje ina dukan qofar su Yaya Ibrahim da kyar suka buxe suka fito. Bayan sun tabbatar ba zan iya hangen abin da ke cikin xakin ba, ke menene haka? Yaya Ibrahim ne ya fara tambayata cikin tsananin kaxuwa na ce musu Ado, ne ku zo ku ganshi Baba ya ce ka ji ‘yar iska wai Ado take ce mishi ko da yake shima maganinshi kenan muje suka taso ni a gaba zuwa xakin, suna ganin halin da yake ciki suka juya da gudu, Mama kawai Mama kawai za ku kashe mata qaninta don kun ga yana ji da ita dama auren haxin baki ne, ni kam na takura wuri xaya in ban da kuka babu abin da nake yi.
Suna barin xakin na faxi jikin Ado ina ta faman kuka ina roqonshi gafarar abinda nayi mishi, tsorona kar ya rasa rayuwarshi a sanadin abinda nayi mishi ne ba tsoron abinda Mama zata zo tayi min ba.
Ina cikin haka naji kamar an yi min magana, a firgice na ce iye, na’am? A hankali ya buxe baki ya ce min yi maza ki kulle qofa kar Mama ta shigo ta same ki, da gudu naje na kulle qofar na dawo na durqusa a gaban Ado, kuka sosai nake yi yayin da shi kuma yake kwance bai motsa ba lokacin ne na gane tsoratar da nayi ne ya hanani gane ya farfaxo, tun sanda na ji atishawa da hamdala sai nayi zaton ko daga wani wuri ne.
Muna cikin haka na ji isowar Mama tana faxin “Lallai yau za’ayi wacce za’ayi, buxe min qofar in ga abin da yake ciki in bai tashi ba ai sai dai in haxa su za’ayi a haxa su gaba xaya in kuma nayi sa’a ya tashi to uwata zata ci gari na wayewa kuma zan tattara ta koma xakin uwarta.” Gwam-gwan-gwan, duka suke yi da iyakacin qarfin su nayi matuqar tsorata don ji nake yi tamfar zasu valla qofar su shigo, don haka na tsallaka can bayan katifar na maqure.
Ado ya tashi zaune nayi matuqar qara tsorata saboda ganin da nayi tanfar zai buxe qofar ne saboda yawan kiran da Mama ke mishi “Adamu! Adamu!! In kana nan amsa mana in ji ka.” Cikin qarfin hali ya ce, “Lafiyata qalau Mama, je ki gida kawai sai da safe.” Da kyar ta haqura ta tafi saboda ganin da tayi ya qi yarda da buxe qofar.
Har gari ya waye ban tashi daga inda nake takuren ba, yayin da shi kuma Ado ya koma falo ya zauna ban san me yake yi ba sai da na ji an yi kiran Sallar farko ban ga shigowarshi don yin alwala ba, lokacin ne na miqe da kyar na tashi saboda ciwon da jikina nima ke yi min na leqa shi yana zaune ne kan kujera ya kuma kwantar da kanshi akan masagalin kujerar ya kuma xora hannayenshi duka biyu a kan nashi alamar dai ya addabe shi da ciwo.
Durqusawa nayi da gwiwoyina duka biyu na ce mishi “kayi haqurin abin da nayi maka.” Da iyakacin gaskiyata haqurin kawai nake bashi ba tare da wani tunani ba, don na riga na tsorata na kuma yi nadamar xaukan wannan mummunan shawara da nayi, na yi amfani da ita da Ado bai farfaxo ba to da wanne hali zan shiga? Ba abinda Mama zata yi ne matsala ta ba, girman laifin ne na tsorata dashi.
“Kayi haquri.” Bai amsa ba, bai kuma motsa ba daga yanayin kwanciyar tashi, shiga Masallaci da ya ji anyi shi ne abinda yayi dalilin miqewar shi ya nufi banxaki sai da yayi wanka sannan yayi alwala ya fito yayi raka’atil fijr, sannan yayi sallar Asuba ya idar yana jan carbi nima na idar na shafa fatiha sannan na kalle shi na sake ce mishi “kayi haquri ka ji?” bai kula ni ba.
Aka soma buga qofa da qarfi kamar na jiya da daddare, gwan-gwam-gwan. Ya miqe ya buxe, Mama ta shigo da xamarar gyale a qugunta riqe kuma da sharveviyar dorina a hannunta, nayi maza naja can baya na maqure a jikin bango sai faman kaxuwa nake yi, don in ta soma dukana yau ban san wanda zai qwace ni ba, tunda shima Adon bai huce ba daga mummunan abinda nayi mishi.
Yau za ki gamu da ni, yau za ki san vakko miya ce in ma uwa ki ce ta turo ki ku kashe min shi to zaku san qarya ku ke yi yau zan yi maganinki ke da iyayenki masu koya miki mugun abu.”
Me ya faru Mama? ya yi maganar cikin natsuwa, ta xago ido ta kalle shi kamar zata yi mishi magana sai kuma ta fasa, wataqila don ganin da tayi tanfar vata lokacinta zata yi, don haka ta zabura ta xago bulalar da niyyar sharva min, ni kuma na takure ina sauraron ta inda zan ji saukarta, sai kawai na ji shiru.
Mama tayi maza ta waiwaya don ganin abinda ya riqe mata bulalarta ta baya, taga Ado a tsaye da bakin bulalar a hannunshi, sake min bulalata, tayi mishi maganar cikin tsawa, nan da nan yayi hakan tare da faxin na sake Mama, amma kiyi haquri kar ki ce za ki tava ta, ai in mun yi faxa ba rama min zaki yi ba, nima da kaina in kin bar ni zan rama ai ba fin qarfina tayi ba.
Ran Mama ya kai matuqa wajen vaci, da ta gane ba zai barta ta buge ni ba, ta shiga zage-zage tana haxawa har da shi a ciki, kiyi haquri Mama, kar ka sake bani haquri, tayi maganar cikin tsawa da fusata, kiyi haquri Mama, ya sake bata haquri. A hankali kuma cikin natsuwa da nuna ladabi har ta xan sassauto tayi kamar zata juya ta fita, muje gida yanzu ina zuwa Mama, kamar ta yarda zata yi hakan sai kawai naga ta juyo da iyakacin qarfinta ta xaga dorina zata sharva min, da sauri ya sake kama dorinar ya riqe, ta sake juyowa tana kallon shi cikin qarin fusata, zaka riqe min bulalar ne kuma? Cikin natsuwa ya sake ce mata, mace a gidan mijinta Mama ya kamata ace tana da ‘yancin walawa, hukuncinta ya zamo a hannun mijinta ne kawai ba wai duk wani wanda ta yyiwa wani abu sai kawai ya zaro bulala ya ce zai buge ta ba, ba tare da ya sanar da mijin ta ba.
To ai nan ba gidan ka bane, balle ka ce na mijinta ne, cikin hanzari ya ce haka ne. Mama ta ci gaba da maganganu gidan mijina ne ni naga dama kai da ita ku ke zaune a gidan ita xin kuma ni naga dama ne na ce a baka ita ko nawa ka kashe a cikin hidimar auren?
Ya ce, babu, ta ce to babu inda zani yau sai ka rubuta takarda ka sake ta tukunna tunda dama komai akan alqawari muka yi shi da kai, ya ce haka ne to kije gida ina zuwa. Ta sake faxin babu inda za ni ai gidan mijina ne in naga dama na ce a nan xakin zan kwana kana da yanda zaka yi dani ne? A hankali cikin natsuwa ya ce mata babu, ya waiwayo ya kalle ni a inda nake takure ya ce min shiga ciki.
Nayi maza na tashi na shige cikin na bar shi a nan don yin hakan ya fiye min sauqi akan zaman da nake yi a cikinsu, ina ganin abinda ke faruwa. Ina so tabar min gidan a yanzu tunda na mijina ne, ya ce ai na ji Mama, amma na roqi arzikin ki xan yi haquri kaxan ki xan saurare ni ba wani lokaci mai tsawo zata xauka a cikin gidan ba.
Mama tasa kai ta fita, shima Ado ya koma ya zauna akan kujera, ni kuma ina can cikin xaki maqure wuri xaya, qirjina sai faman bugawa yake yi val-val-val saboda ban tava ganin abinda ya firgita ni irin na jiya da yau ba, Ado da Mama suna kace-nace bayan kowa yasan kullum Ado akan bin umarnin Mama yake.
Wajen qarfe takwas da rabi na ganshi yana shiri kamar in tambaye shi ina za shi? Sai kuma na fasa, saboda yanda fuskarshi take xaure gashi kuma dama ban saba yi mishi irin waxannan tambayoyin ba. Yana fita daga gidan na koma can cikin xaki na zauna ina tunanin in yanzu Mama ta shigo ko ya ya zan yi da ita? Oho.
Sai kawai naji sallamar Hajiyar Giyaxe da sauri na fita naje na tare ta, tana riqe da food flask xin da aka kai mata abinci a hannunta, nasa hannu na karvi food flask xin tare da faxin, gani ga ki amma ba ki tava shigowa ba sai yau, don na kai miki tuwo kin ji miyar amayar mai zaqi shi ne ki ka kawo min food flasks? To bari yau ma zan sake aiko miki da wani tuwon don gobe ma ki sake shigowa ki kawo min kwanon.
Tayi murmushi ta ce, oh’oh-oh’oh, ni ba don kwanonki na shigo ba, zuwa nayi don maigidan ya ce min in zo in zauna mishi a gidan kafin ya dawo.” Cikin zuciyata na gane abinda yasa Ado yin hakan, shima tsoro yake kar bayan shi Mama ta shigo ta same ni ni kaxai.
Muna zaune da Hajiyar Giyaxe mu biyu hira muke yi bayan nayi mata abin karyawa ta karya ta qoshi, sai sakucen haqoranta take yi da tsinken sakace a dalilin farfesun kaza da tasha, sanin da nayi cewar tun asalin dama can Hajiyar Giyaxe tana son Innata tana kuma matuqar sona ya sani sakin jiki da ita sosai, har na kwashe bayanin duk abin da ke tsakanina da Ado, da abin da ya faru daren jiya da abinda yasa ya turo ta taya ni hira duk na gaya mata, don kuwa neman abokin magana nake yi saboda damuwa tayi min yawa.
Hajiyar Giyaxe tayi min wani lalataccen kallo ta ce, to abinda ya rinqa yi wa uwarki ba sa shi aka yi ba? Yanzu ma kuma za’a sa shi yayi ne? ba gashi nan ba a yanzu kullum yana kai-kawo a tsakani kuma da ban sani ba ai nasan ba da gangan yake yin abinda yake yin ba, to kuma in ban da shirmenki da kayi cuta ka cuci abokin zamanka ai gara shi ya cuce ka, tunda babu wani abin da ba ayin sakayya akanshi musamman ma ace shi wannan abin kan lamarin aure ne. yanzu ace Innarku bata soma ganin sakayya ba? Innarku fa surukaye uku tayi rana xaya, wane arziki ne ya wuce wannan? Kuma kana ganinta ma a cikin gidan ai kasan walwalarta ma ta xan sauya jinin jikinta ma ya soma dawo mata saboda wahalarta ta soma raguwa, gashi yanzu kullum zaka ganta a wadace cikin harka ni a zatona ma na ce ko mijinki ne oho, na ce anya shi ne kuwa surukayen nata waxancan xin ai dukansu ‘ya’yanta ne, ta gyaxa kai ta ce oho ban sani ba, amma ina ganin mijinki ma yana cikin aini ba yarinya ba ce nace haka ne Hajiya.
Hajiyar Giyaxe ta gyara zama ta ce, to ko wannan tijara da ja’irar yarinyar nan mara kunya tayi wa Babanki da wannan mata shekaran jiya in ban da alhakin Innarku da ya kama su me ya kawo hakan? Nayi maza na vallo varin goro na miqa wa Hajiyar Giyaxe ta shiga goga shi a magogin goronta tana watsa shi a bakinta, ni kuma na qara mannewa da jikinta kafin na qara tambayarta ni me ya haxa su ne Hajiya?
Ta ce, uhun in ban da iya shege menene wai kama su tayi suna yin wani abu ranar girkinta bayan kuma dama da nata girkin da natan duk ita kaxai aka haxawa, na sunkuyar da kaina qasa cikin yanayin jin kunya, cikin zuciyata dai cewa nake yi lalle yarinyar nan da kafirin iya shege take, yanzunnan Babana ta yiwa irin wannan iya shegen? Ita kuwa Hajiyar Giyaxe babu ruwanta, sai bayanin ta take yi amma da maganar tazo wurina na gaya musu dukansu ita mijin nata na gaya musu dama gulma da munafurci ne ya saku yin hakan, don ku cutar da Binta, to gashi nan abin ya koma kanku.
Ni kam ban yarda na tofa cikin wannan zancen ba, illa iyaka dai na amsa sallamar Hajiya ‘Yar dubu, itama riqe take da food flask xina a hannunta na kalle ta nayi dariya nace, kema kwanona ki ka kawo min? ta ce, oh’oh, wane kwano ne zai fiddo ni a ruwan nan? Uwarki ce tayi wa Mallam waya ta ce mishi wai mijinki babu lafiya, gabana ya yanke ya faxi me Inna ke nufi da wannan wayar da tayi kar dai itama zafina take ji?
Ina yake yanzu, ko yana ciki ne a kwance? Tayi tambayar bayan sun gama gaisawa da Hajiyar Giyaxe, sun yiwa juna ban gajiyar biki har tana faxin ai ban san kina nan ba Hajiya da na zo miki hira, Hajiyar Giyaxe ta ji daxin hakan da ta gaya mata ta kwashe zance duka ta yi wa Hajiya ‘Yar dubu, har da yiwa bayanin kwaskwarima na ce ah Hajiya…kan in faxi abinda zan faxa Hajiya ‘Yar dubu ta daka min tsawa ke tafi can ki baiwa mutane wuri akan zai tava ki ne ki ka kwantara mishi qarfe kina neman kashe shi?
To zauna ya bar ki ba shi kenan ba sai ki rinqa jiqawa kina sha ko ki kai inda za ki kai. Hajiyar Giyaxe ta ji takaicin maganar, ta ce a’a Hajiya wannan ai ba zancen da za ki yiwa yarinya ba ne, sai kiyi mata faxa kawai irin wanda ya dace da ita.
Rannan cikin dare na yi wa Inna waya don in gaisheta, bata xauka ba kamar yanda dama kullum nake mata washegari ma da sassafe na kira ta bata amsa ba, gashi kuma ina ji ta bugo waya ta gaida Ado da jikinshi, a zuciyata na ce ha’a to me na yi wa Inna? Me babban allo yazo gaida Ado wai da jiki, ya gaya mishi gani nan zuwa zai turo ni don in gaishe shi amma naje zauren shima ban