Showing 33001 words to 36000 words out of 36031 words

Chapter 12 - MIJIN TA CE Book 2

20 Aug 2024

4217

ina riqe da xankwalina a hannuna durqusawa nayi da gwiwoyina biyu a qasa na ce mishi qauye? Bai kalle ni ba bai tsaya amsa maganar da nayi mishi ba sai kawai ya ci gaba da yiwa Inna bayani, dangin mahaifina mutane ne masu karamci da zumunci, na kuma yi miki alqawarin matuqar ina raye cikin lafiyata to ba zan bar Humaira ta shiga cikin matsalar da zata dame ta ba, don haka na roqe ki ki qara yin haquri ki kuma yafe min abubuwan da nayi miki.
Cikin wata irin murya mai rauni naji Innan tana ce mishi to amma kai ma na roqe ka kayi haquri ka fara tafiya tukuna in yaso daga baya sai kazo ka xauketa.
Maimakon ya ce wa Inna to sai kawai naji ya ce mata a’a Inna, ai in nayi haka ya zama min kenan tanfar na rasa komai bayan kuma don in same ta ita kaxai xinne yasa na bayar da komai xin da nake da shi saboda haka zan tasa ta a gaba ne mu tafi. Ina jin ya faxi haka ban jira amsar da Inna zata bashi ba sai na ce mishi a’a babu wani qauye da zan bika mu tafi, ban tava zuwa qauye nayi kwanakin da suka wuce guda bakwai ba, bana iyawa. Sai kuma haka kawai in bika can in zauna? Ba a can aka haife ni ba mahaifiyata ma ba a qauye aka haife ta ba.
Ado ya tashi ya fita saboda jin sallamar Baba Yahaya, ya barni a nan ina durqushe ban gama lissafa mishi abinda na fara ba, yana barin xakin Inna ta kalle ni ta ce qauye kuma? Wannan wace irin fitina ce? Maimakon ta saurari amsar da zan bata tunda naga kamar tayi min tambaya ne sai kawai naga ta rushe da kuka, kuka kuwa mai tsanani irin wanda ban saba ganin tana yi ba.
A tsakar gidanmu gaba xaya mutanen da Ado ya nema sun hallara ana zazzaune har da Babana wanda yasha mur sosai don nuna alamar babu wasa, Mama ma tana gefe tun kafin a kira ta ta fito ta zauna. Liman yayi addu’a ta fatan a dace da duk abin da za’ayi ya zaman ya zamo shi ne mafi alheri kuma ayi komai lafiya a tashi lafiya aka shafa da amin.
Baba Yahya ya kalli Ado ya ce, to me ya faru ne Ado? Ado ya gyara ya soma rattabo bayani tun farko yanda aka yi Mama tasa shi karvar aurena al’amuran da suka yi ta faruwa bayan auren da sharuxxan da ta sanya mishi na cewar za su faru in har ya ce zai ci gaba da zama da ni da kuma yanda Babana ya kira mu muka zo ya ce ni in shiga xakin uwata shima ya shiga na tashi uwar shi kenan ya raba aure, magana ta qare. Kowa yaje ya riqe tashi.
Ya ce, to shi ne nace wataqila rashin cika waxancan sharuxxa da aka gaya min ne yasa aka zartar min da wannan hukunci, don haka na kira ku saboda ku shaida zan cika sharuxxan dan nima a bani matata in tafi da ita, kowa ya yi shiru yana sauraron abin mamakin da Ado ya rattaba yayin da shi kuma Babana ya shiga faxin lalle kai xin nan butulu ne ban sani ba, Mama kuwa kuka ta kama yi tana faxin wai bata tava zaton Ado zai qulla mata sharrin da ya qulla mata ba.
Liman ya katse su ta hanyar cewa, to amma wannan lamari da ban mamaki yake, ashe bani da Alhaji Yahaya ba ne muka je ba da haquri don iyayen mijin ‘yar uwarta su barta ta koma xakinta ta zauna suka qi muka dawo muna vacin rai da baqin cikin wulaqancin da aka yi mana na qin yarda ta koma ba?
Baba Yahya ya ce eh, to shi ne kuma kai da kanka kake cewa a dawo maka da wannan ka raba auren Alhaji a ina ne uba ya samu ikon qwace ‘yarshi daga wurin mijinta, alhalin ba mijin ne yace baya yi ba, ai daga faxin ka bayar an ce an karva to baka da sauran iko, kai Ado kana son matarka ka kuma shirya cika sharuxxan duk tsananinsu don a baka ita? Cikin ladabi ya ce eh Mallam, to kawo su.
Ado ya shiga miqa takardu yana bayani har da na gidajen nashi da motar ya ce ita kamma direban ya ce min ya kawo ta suka ce eh mun ganta bayanin kuxi a banki da na hannun mutane da wanda su kuma ake bin su bashi duk ya bayar. Mallam Harisu ya ce amma Alhaji yanda yaron nan yasan komai na kasuwar nan taka da kuma dawo da wannan dukiya da yayi wacce da can baka san da ita ba baka ga kamar ka yafe mishi ka bashi matarshi suci gaba da zamansu kaima kuci gaba da harkokinku bai fiye maka ba? Tunda kowa ya san shi ya san shi ne a tare da kai babu kuma wanda bai san jarumtakar shi ba yana rabuwa da kai fa wasu a kasuwar a kuma kusa da kai za su qwace maka shi ba kuma zaka ji daxin hakan ba, kan Babana ya buxe baki yayi magana sai Mama tayi caraf ta ce, to ya tafi mana da can da babu shi Alhaji bai nemi kuxinshi ya samu ba?
Wannan neman kuxi da yake yi mishi ma ai neman kuxi ne na kashe mu raba, Baba Yahaya ya ce eh da ki ka sa shi yin hakan ba in ba haka ba a ina ki ka samu wannan dukiya da ya dawo miki da ita? Me ki ke dashi? Ko kina so ne in tuna miki da…da sauri Liman ya ce a’a Alhaji kai kuma me ya kaika yin haka? Baba Yahaya ya ce abin baqin ciki ne da matar nan Mallam, gaba xaya ta hana gidan nan zama lafiya, ka duba yanda aka yi da dalilin da yasa ta qulla wannan aure da kuma abin ya juya ta inda bata zata ba maimakon tayi nadama kan muguntarta tayi ta istigafari sai kuma ta tasa xan uwanta a gaba da masifa, to za ki rasa shi za kuma kiyi kuskure don shi ne komai na hidimar gidanku ke da mijinki.
A wurinka ba, kai kake ganin hakan ai ku ku ka shiga tsakanina dashi, Baba Yahya ya ce to ai shi kenan kai Ado a ina ka samu inda zaka koma xin? Ado ya sunkuyar da kai qasa ya ce can nake so in koma wurin dangin ubana, yana faxin haka Mama ta qyalqyale da dariya ta ce qauye kenan? Ai da can xin ku ka fi dacewa.
Gaba xaya wurin yayi tsit saboda babu wanda ya zaci Ado qauye zai ce zai kai ni, shiru aka yi na wani lokaci mai tsawo kafin Mallam Harisu ya gyara zama ya ce wa Ado, ka gani Ado in wani abu irin wannan ya faru haquri ake yi a kwantar da hankali a natsu kafin a san kuma inda za’a fuskanta.
Kai yaro ne mai natsuwa da girmama na gaba da kai, kowa ya sanka saboda kana da kwarjinin jama’a ka iya zama da su lafiya, kayi karatu.” Baba Yahaya yayi maza ya ce mishi ai digiri biyu ne da shi a yanzu, da sauri Mallam Harisu ya ce to ka gani? Babu wani dalilin da zai sa don wannan abin ya faru ka ce zaka bar birni ka koma qauye. A nan ma za ka yi harkokinka zaka samu kuma abokan harkar. Za kuma ka nemi aiki ai kayi ilimi shi qauyen nan da ka ke gani ka riga ka baro shi da daxewa ba iya zaman cikin shi zaka yi ba, don ka riga ka manta da rayuwar can duk da dai nasan kana yawan zuwa to sannan ita Humaira fa bata san qauye ba kar ka manta da wannan.
Gaba xaya aka sake yin shiru na wani tsawon lokaci saboda Ado ya ki tanka maganar da Mallam Harisu yayi mishi, sai Baba Yahaya ya kawar da shirun da tanbayar cewa to ko kuma zaka fara tafiya ne kai kaxai ka barta a nan sai kaje ka gano yanda zaman naku zai yiwu in yaso sai ka dawo ka xauke ta?
A hankali ya ce, a’a Baba, nafi so in tafi da ita, nafi so a bani ita, wataqila taurin kan Ado ne ya fusata Babana ko kuma yawan tsakin da Mama ke ja ne oho. Don jin shi kawai aka yi ya kama faxa yana faxin babu in da zaka tafi min da ‘ya ai bamu yi da kai akan in anyi auren qauye za ka xauke ta ka kaita ba, shi kuma Liman ya ce a’a wannan kuma ai ba magana ba ne shi dai a roqe shi cikin biyu yayi xaya, ko dai shi ya fara zuwa kafin ya dawo su tafi tare ko kuma kai Alhaji Yahaya ya yarda ka bashi aron wurin zama da shago a kasuwa tunda mun san duk abinda yake hannunshi ne ya kawo.”
Baba Yahaya yayi maza ya ce har kayan zan sa a bashi in yi mishi lamuni ai duk an san shi, da Liman ya waiwayi Ado don jin abinda ya zava sia ya shiga basu haquri yana faxin shi a yanzu zai fi son a bashi matarshi ya tafi da ita wurin dangin ubanshi. Baba Yahaya ya ce to ina ganin tunda yarinyar nan itama tana da hankalinta da wayonta a kira ta tazo nan muji ra’ayinta, in ta yarda zata bi ka qauyen shi kenan, amma in bata yarda ba ba za mu tilastata ba, Babana yayi maza ya ce bin shi kuma yana nufin ta tafi kenan ba za ta sake dawowa ba.
Ado ya xaga ido ya kalli Baba Yahya cikin natsuwa da ladabi yayin da tsoro ya baiyana qarara a idonshi ya ce mishi na roqe ka Baba kar ka bata zavi akan aurena, don zata ji tsoron maganar da Baba yayi mata.
Baba Yahaya ya ce ba zavi ba ne haqqinta zamu bata in ta ce zata bi ka shi kenan, amma in ta ce ba za ta bi ka ba ba zamu sa ta ba, domin ya kamata ace kaima kayi sassauci akan tafiyar taka tunda mun maka alqawura mun baka zavi mun kuma roqe ka a matsayinmu na waxanda suka haife ka, amma baka yarda ba to hakan ba yana nufin ita xin zamu tirsasata ba ne.
Mama tayi dariya tare da gyaxa kai ta ce ai gara dai kuma ku gani wai shi nan a dole shi mai taurin kai ne.
Fitowa nayi a xaki a dalilin kiran da aka yi min har kafin fitowar tawa kuma Inna bata daina kukan da take yi ba, tana faxin qauye kuma? Haba wane irin qauyea? Na durqusa a qasa da gwiwoyina duka biyu cikin sauraron abinda Baba Yahya zai gaya min, zuba min ido yayi yana kallona cikin wani yanayi da yake baiyanar da tausayin shi a gare ni, ni baki da lafiya ne ma ko Humaira? Na ce mishi eh Baba, sai da ya qara xaukan wani lokaci mai tsawo cikin nazari da tunani kafin ya daure ya ce min to Humaira kin dai ji duk abinda muke ciki da mijinki, amma a yanzu zavin ya rage naki, za ki bishi ku koma can qauyen nasu? In za ki bishi to babu laifi ba zamu hana ki ba, domin aure ne shi kuma aure babu inda ba ya kai ‘ya mace, sannan mijinki yaron kirki ne jarumi kuma mai neman na kanshi, ni nafi kyautata kyakkyawan zato a gare shi, in kuma ki ka ce ba za ki bishi ba to babu mai sa ki saboda mu xin iyayenki ne zamuyi miki adalci baki san komai ba game da rayuwar qauye a xauke ki a kai ki can ki koma da zama ba zai zamo mai sauqi ba a gare ki.
Don haka me ki ka ga ni, za ki ko ba za ki ba? Ya waiwaya wurin sauran jama’ar da suke tare ya ce ko ba haka ba Jama’a? suka yi maza suka ce wannan shi ne gaskiya, ya sake waiwayowa ya kalle ni ya ce, To Humaira zavi yana wurinki, yi maza ki gaya mana wanda ki ka xauka don ki kawo mana qarshen wannan kai kawo kin ga ai tun safe muke wurin nan ko kasuwa ba mu samu mun je ba.
Xago ido nayi da nufin baiwa Baba Yahya amsa sai ka rab idanuwana suka haxu da na Ado, ni yake kallo ko qibta idon nashi baya yi saboda tsananta kallon da yayi, maqwalwuyanshi sai kai kawo yake yi alamar tsananin damuwa da alama kuma wata maganar yake son gaya min wataqila da ya san zavin zai zo wurina da yayi hanzarin gaya min ita tausayinshi yayi matuqar kama ni da na tuna kalmomin da ya furtawa Inna cewar tafiya babu ni xin zai zamo mishi tanfar ya rasa komai, gaskiya ne tafiya babu ni tanfar rasa komai ne a wurin Ado, tunda ya bayar da komai nashi to amma kuma anya tausayin hakan ya isa yasa in zavi Ado in bar kaina, da mahaifiyata? Anya tausayin nashi ya isa ya hana ni tausayin kaina da mahaifiyata?
Bin Ado qauye kenan yana nufin rayuwata ta shiga wani hali musamman ma da yake nasha jin mawaqanmu na Hausa masu basira suna faxin wai kowa kaga ya bar birni ya koma qauye to wannan zaman duniya tasa ce ta gigita. Ban da wannan ma ni da kaina na sani ba sai an gaya min ba, shigana cikin matsala yana nufin Inna ma tana cikinta tsundum, na kuma sani da ita ce ta samu damar da aka bata irin wannan zavin da aka bani da tuni ta kawo qarshen maganar ta hanyar faxin babu inda zani.
Waxannan dalilai sai suka sanya ni cikin wani hali na kai-kawo da bugun zuciya wanne zan zava? Rufe ido zan yi in zavi kaina da kwanciyar hankalin Innata in bar Ado da xan guntun kunyarshi da xan vacin ranshi ya kama hanya yayi tafiyarshi qauyensu ko kuwa? Tunda ai yayi kyakkyawar rayuwa babu ni, gaba xaya son da yake tutiyar yana yi min kwata-kwatanta daga wata uku ne, a baya ni xin ba komai ba ce a wurinshi, sannan dukiyar da yake ikirarin mayar wa don ya same ni na sani jarunta ne yin hakan, to amma kuma ai ta wani vangaren taimakon kanshi yayi tunda dama bata hanyar halal ya same ta ba, tana cikin asarorin qarya da aka yi ta cewa Babana yayi.
Sannan ko Ado bai tafi da komai ba zai tafi da iliminshi wanda babu wanda ya isa ya qwace mishi shi digiri biyu kuma ke gare shi, sannan ban da waxannan dalilan duka bani da tabbacin cewar zan samu karvuwa wurin ‘yan uwan Ado da yake ikirarin maida ni cikinsu in suma suka zamo min kamar Mama fa yaya zan yi haka nan shi kanshi Ado wane tabbaci ke gare ni akan shi tunda tun ina ‘yar qaramata nake jin iyayena mata suna faxin wai shi xa namiji ba xan goyo ba ne, to musamman ma kuma wannan da shi da kanshi ne yake yi wa kanshi kirari da cewar shi xin namiji ne.
Iyayena kuwa da dangina tuni suna sani zama da su yana nufin zan ci gaba da zamana a cikin gatana musamman Innata wacce nasan babu wani wanda zai cike mata girbina balle ya xebe mata kewata tun daga ranar da ta haife ni take sona kowa kuma ya san hakan, kowa ya bada wannan shaidar cewar Inna bata tava son wani xa kwatankwacin son da take yi min ba, haka nan zan ci gaba da rayuwa ta a birnin da na sani, birnin da aka haife ni, birnin da na rayu, zan ma iya komawa Makaranta in yi karatuna tunda ina da wannan burin.
Mama kuma in babu auren Ado a kaina ba za ta sake takura min ba don kuwa ba zan sake yarda ba saboda a yau kan ungulu ya riga ya waye xan auren nan da nayi na kwanaki tamanin da bakwai ba qaramin buxe min ido yayi ba.
Tuni zuciyata ta shiga kai-kawo mai tsanani na kasa gane menene abin yi? Wanne zan yi? Wane zan bari? Hankalina ya yi matuqar tashi na rasa wanda zan zava cikin niyun Inna da sauran dangi tare da Babana mai faxin bin Ado yana nufin na bar gidanshi kenan zan xauka in bar Ado?
Tunda shi Ado ai zai tafi da iliminshi ban da haka ma zan haifar mishi abinda yake cikina yazo ya xauka abin shi, ko kuwa Adon zan bi min soyayyar wata uku muje can qauyen nasu cikin danginshi mu yi zamanmu?
Duk yawan kirarin da yake yiwa kan shi na cewar shi xin namiji ne, alhali kuma mu mata mun sha jin iyayenmu mata suna jaddada mana cewar shi namijin ba xan goyo ba ne…?

Mu haxu a littafi na uku jama’a don jin kafin nan in ku ne wanne zaku zava cikin biyun?
Godiya mai xinbin yawa a gare ku bisa qaunar da kuke nunawa rubutuna.
Na gode da zumuncinku, Ubangijinmu Allahu ya sada mu cikin Aljannarsa ta Firdausi don rahamarsa, Ubangiji yasa mu dace da samun dukkan alherin da yake cikin wannan wata mai albarka na Ramadan, watan da Manzon Rahama (S.A.W) ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login