Showing 12001 words to 15000 words out of 36031 words

Chapter 5 - MIJIN TA CE Book 2

20 Aug 2024

4226

ba sai yaushe kike ganin zata dawo taci? Yaushe? Jibi ko gata ko baxi?
Shiru nayi ban tanka mishi ba, shima bai matsa sai na bashi amsar ba, yasa kai ya fita yana fita sai ga Sa’adatu ta shiga da sauri na tare ta cikin farin ciki ina tambayarta me yasa ba kya shigowa Sa’adatu? Sa’adatu sai yau?”
A hankali ta ce, “Inna ce ta hana ni, yanzu ma yaya Ado ne ya ce min kina nemana, da sauri na tambaye ta me yasa Inna zata hana ki zuwa wurina? Ta ce na gaya mata kin zagi Yaya Ado shi kuma ya mare ki, shi ne ya ce to kar in sake shigo muku gidanku.”
Nayi kamar in sake tambayarta wani abu sai kuma dai na fasa a dalilin shekarun nata ba wasu masu yawa ba ne tara ne da ita. Na jawo kazar da Ado ya kawo min jiya da daddare ban ci ba, na tura mata tare da kayan tea.
“Zuba yanda ya yi miki ki sha Sa’adatu, yi nayi wai don in burge ta in yaso in ta gama sai in ce mata taje ta turo min su Baba Qarami sai ta kalle ni ta ce min, na riga na qoshi. Da sauri na ce mata, naman kaza ne fa Sa’adatu, don nasan ita xin mai kwaxayin naman ne sai ta ce eh na qoshi ai muma muna dashi.”
Na ce, “To shi kenan Sa’adatu, ki gaida Innan ko?” na ce mata “To.” Ta tashi ta tafi cikin zuciyata sai murna nake yi, Inna ma al’amura sun fara canza mata, ko a ina take samun kuxi yanzu? Tunda nasan dai duk abinda take dashi ta kashe sai kuma na tuna ai surukaye ne da ita ga Ahmad xan wanta ga Salisusu xan Baba Yahaya na kuma san dukansu zasu ji da ita.
Na fito tsakar gida sanye da doguwar shimi a jikina wacce ta xan fara jiqewa kaxan a dalilin wankin kayan su Baba Qarami da na sa aka kawo min nayi shanya na ke yi a igiya yayin da su Baba da Ibrahim suke xakinsu suna sharholiyarsu tare da abokansu, sai ga Ado ya shigo riqe da ledojin sayaiya biyu a hannunshi.
Yana ganina fuskarshi ta sauya ban ce miki a tsakar gida kisa gyale ko hijabi ba? Nayi shiru ban amsa mishi ba, ya sake yi min tambaya cikin tsawa, “kina so ne wani ya ganki a haka?” na ce, “A’a, to su waye za su ganni ba yayuna ba ne?”
Yayi maza ya cukume ni ya shaqe yana faxin “Har abokansu da suke cikin xakin ma yayunki ne?” nayi shiru ina zaro ido cikin yanayin tsoro yana sakina ya nufi xakin su Baba ya xaga labulen.
“Kai duk ku fito nan bana hana ku shigowa gidan nan kuna mana shaye-shayenku ba?” “A’a Kawu, sigari ne kawai.” Abokansu ne masu bashi amsa, daidai suna fitowa suna barin gidan sum-sum ya sake biyo ni xaki bayan ya gama dasu ya same ni kwance a kan katifa ga cefane na kawo ki tashi kiyi girki, na ce ba zan yi ba na riga na fasa, ya ce kije kiyi ta fasawa. Ya juya ya fita.
Ado yayi matuqar tasa Baba da Ibrahim tare da abokansu a gaba har sai da Mama tayi mishi magana akan su sai kuma ya sake dawowa kaina da wasu dokokin nashi masu tsananin bi.
Rannan ya dawo gida da rana T.V da kafet Plasma tare da rediyo C.D da kafet na tsakiyar xaki alamar dai so yake ya xan gyara falon saboda rashin fasalin shi ya yi yawa, yana barin gidan sai ga Suwaiba ta shigo, bayan tunda aka yi bikinmu bata shigo min ba, amma kullum tana barin unguwar taje gidan Habiba.
Ban ji tayi min sallama ba, don haka na ci gaba da kwanciyata akan katifata a xaki ba tare da na tanka mata ba, ta shiga kunne-kunne da jone-jone ina jin ta sai naji qawarta tana ce mata mun shigo gida babu sallama babu gaisuwa mun kama yiwa matar gida tave-tave.
Sai kawai naji Suwaiba tana ce mata, “to nata ne? na Kawunmu ne ba ki ji Mama ma tana cewa duk abinda zan tava a gidan in tava shi cikin gadara na Kawuna ne ba? Ita fa ga irin kayan da aka yi mata can.”
Ina jin haka nasan da hannun Mama cikin rashin mutuncin da tazo zata yi min, don kuwa ita dai nasan a yanzu tsorona take ji, a zuciyata nayi tunanin wata qila ta turo ta ne ta tsokane ni don muyi faxa da ita ta fake da wannan tasa Ado ya sake ni, don kuwa ko shekaran jiya ta shigo har gidan har cikin nan falon na gaishe ta taqi ta kula sai da Adon ya ce mata ana gaishe ki Mama sannan ta amsa.
Ina cikin xaki ina jin ta tana tambayar shi anya muna nan akan alqawarinmu kuwa Adamu? Yayi murmushi ya ce, me ki ka gani Mama? Ta ce vare-varen da ka soma yi ne yake bani tsoro, ya sake kallonta cikin natsuwa ya ce mata, ai ba na vare-vare Mama, me ki ka ga nayi? Ta ce me ka ke zuwa yi xakin uwarta? Cikin natsuwa ya ce mata gaisuwa ce kawai Mama don akwai nauyi mai yawa ace ‘yarta tana gidan nan a matsayin matata amma ace ba na gaishe ta.”
“Matarka Ado? A gabana ka ke kiranta matarka? Kaga yanda kasa na ji faxuwar gaba kuwa?” yayi maza ya shiga bata haquri, yana faxin ya yi kuskure ba kuma zai sake ba, ya yi ta lallava Mama tana ta faman tashin hankali da faxin wai ya wulaqantata tunda ya kira ni matarshi a gabanta, da kyar ya samu ta haqura ya miqe ya rakata har gida.
Don haka da na ji kalaman Suwaiba na gane turo ta aka yi sai na fito na same ta hannu na saka na kashe kallon na zare soket xin na ce, ko na Kawunki ne na hana ai na mijina ne xakinmu xaya ni dashi, shimfixar mu kuma xaya ni dake wa yafi iko da kayanshi?”
Ta ce, “Au, kwana nawa zaki yi a gidan nashi? Ai za ki fito.” Na ce to ko zan fito dai ai an xaura ya karva bai ce baya so ba, gashi kuma har yana zaryar gaida uwata.” Suwaiba tasa kuka ta fita wai nayi mata gori an ce ba a sonta.
Ban san yanda aka yi ba sai kawai na hango Mama tana shigowa gida da sharveviyar dorina da gudu na fito daga xakin ban yarda ta ritsa ni a xakin ba. Muka shiga kai-kawon zagaye gida a qoqarinta na son kama ni, ina yi kuma ina ihun wayyo Mama kiyi haquri kar ki buge ni, ko zan samu makwabta su jiwo mu su kawo min agaji.
Ganin ba za ta iya kama ni ba yasa ta shiga qwalawa Ibrahim da ke gida kira wai yazo ya riqe mata ni, da gudu na yanka nayi waje don nasan zai iya kama mata ni xin don ta buge ni, karab muka haxu da Ado a zaure.
Lafiya? Da sauri ya tambaye ni bayan ya buxe hannayenshi gaba xaya ya tare hanyar da nake nufin wucewan, jikina yana rawa kamar yanda muryata ma take yi saboda na riga na tsorata, Mama ce tasa Yaya Ibrahim ya kama mata ni wai zata buge ni.
Shiru ya yi na wani xan lokaci nuna alamar nazari kafin ya buxe baki cikin natsuwa ya ce min “To mu koma ciki.” Kuka na soma yi mishi saboda na riga na tsorata ba kuma na son gidan dama kuma a matuqar takure nake.
“Kiyi haquri mu koma cikin tare in kin yi min haka zan ji daxi don zanga kamar kin mutunta ni ne.” mun juya zamu shiga cikin gidan muka ji Mama tana cewa Ibrahim ai ni na fasa kwana casa’in xin ma da na xiban mishi tunda tun ba aje ko’ina ba har ya fara canzawa, ni ina tunani kar ma dai washa-washan da nake ganin uwar a ciki kwanannan shi ne.
Tana ganin na shiga ta katse maganarta tana tambayarta ai dawowa ki ka yi? Ai kuwa za ki…bata gama ba Ado ya shigo, ni na dawo da ita Mama ai bai kamata ta fita ta bar gidan Babana nan ba nine nan na ce ta tafi taje duk inda zata auren nata ya ishe ni haka, ai rannan ma da nayi maka magana kan zaman naku ya ishe ni cewa kayo to ko za’a rabu da ita ai za’a rabun ne akan tayi laifi, ba haka kawai ba, to yau tayi sai ka sallame ta.
“Me tayi?” ya buqaci sanin cikin natsuwa, Mama ta kwashe bayanin da Suwaiba tayi mata ta gaya mishi. Ya ce, “Kiyi haquri Mama, amma ya yi daidai ace an sake ta akan Suwaiba? Ni nafi so ki bari sai tayi wani abinda ya shafe ni ko ya shafe ki wanda kowa ya ji da ma yasan muna da hujja ba za’ayi ta zarginmu ana vata mana suna ba, amma Suwaiba ai qanwarta ce kuma ni Kawunta ne mutane ba za su gamsu da hukuncin saki akanta akan Suwaiba ba, sannan kai Ibrahim kar ka fara ace maka ka kama ta ka mata.’
Da sauri Mama ta tambaye shi to don me zaka faxi haka shi ba wanta ba ne?ya ce wanta ne Mama amma ita xin matar aure ce, shi auren kuma Amana ne, daga nan kuma zuwa ranar da zan ce bana yin shi to zan tsare wannan Amanar, don haka kar ya fara yin hakan kawai, kalaman na Ado da yanayin da fuskarshi ta nuna yasa daga Mama har Ibrahim jikinsu yayi sanyi, a hankali ta matso kusa da shi tana tambayar shi anya Adamu ba suyi maka komai ba?
Anya ba xanxani haukaci aka sa maka ba? Tsoro fa nake ji kar su juyar min da kai, su qwace ka, dubi yanda ranka ya vaci akan al’amarin ta wai har ni ka ke wa faxa?
Ya ce, Babu mai qwace miki ni Mama, kuma ni ba a kanta raina yake vaci ba, aurena da yake kanta ne ba zan iya yin haqurin da za’a wulaqanta min shi ba, ace Ibrahim ya kama matar da aurena yake kanta Mama don a bugeta? To me ya hana shi ni ya buge ni? Ni fa inda ana mutunta min aurena to da wata qila sai ayi a gama komai cikin hanzari, in ta yi laifi a matsayinta na matar aure a gaya min a ga abin da zan yi, ba a xauko bulala ace za ayi mata duka ba, wannan wulaqanta min aure ne.
Hukuncin hukuntata nawa ne nima kuma na iya dukanta tunda kema kin ce an gaya miki sau biyu ina mata duka a zuwan da tayi, har ki ka qara jaddada min in ci gaba da haka, don kar ta ce zata raina ni na ce miki a’a ba zan bar ta ta raina ni ba, ai da gaske nake yi ba zan barta ta raina ni ba, haka kema ba zan barta ta raina ki ba, to amma kuma ba zan bar wani itama ya wulaqantata ko ya hanata ‘yancinta na matar aure ba, ba kuma don ita ba sai don aurena da yake kanta.
Amma ta rasa yanda zata yi da wannan curarren bayani nashi na ba don ni ba don auren shi yake yi, ya saki auren kuma ya qi ya ce sai an yi laifin da ya dace ayi sakin ko kuma a saurari zuwan kwanaki casa’in xin da aka ambata tun farko.
A haka Mama ta haqura ta tafi gida bayan ya yi mata alqawarin yana idar da Sallar Isha’i zai shigo ya same ta don su qara tattaunawa. Mama tana barin gidan ya kalle ni fuskarshi a xaure ya ce min, ke haka ake yi? In an zo za’a buge ki ba za ki yi maza ki shiga xakinki ko kicin ki kulle kanki ba har kafin in dawo sai kiyi waje da gudu? Kina da hankali kuwa? Ke kin san darajar kanki kuwa?
Hawaye suka soma zuba a idona, ya roqi in mutunta shi nayi mishi hakan yanzu kuma ya zo zai yi min faxa.
Yanayin fuskarshi ya xan sauya a hankali kuma ya soma yin magana, yi haquri kar kiyi kuka nasan kin tsorata ne to amma ya kamata ki san kina da daraja jikinki ba jikin da ya dace ayi ta buxewa ba ne wasu da ba su dace ba suna ganinshi, kishi mai yawa nake yi a kanki ban san dalili ba, da dai ace kin tava barina na tava ki ne to wataqila da nima na yarda da maganar Maman cewar xanxani haukaci aka yi min.
To ban xanxani komai ba Humaira, kowa ya gane abinda nake ciki vare-vare nake yi akanki amma babu ruwanki, na ce akan aurenka dai, yayi maza ya ce eh akan aurena, to amma waye auren nawa? ban tanka mishi ba, shima ya kawar da zancen ta hanyar tambayata yanzu nan har yau ma ba za ki yi girki ba?
Tsakanin gobe da jibi ne fa naji Baba ya ce wai Hajiyar Giyaxe zata tafi, da sauri na ce mishi kai? Ya ce, uhun, dama zata yi ta zama ne? na xan kalle shi kaxan kafin na kawar da kaina gefe, wani lokaci na kan ji kamar in saki jiki kawai da Ado muyi zamanmu, to amma in nayi wani tunanin sai kuma in ga to ai zan iya sakin jikin nawa dashi muzo muna cikin zaman kwanaki casa’in su cika ace min ki tafi aure ya qare, in akayi haka wa aka cuta? Ni tunda ni ce zan rasa wani abu shi bai rasa komai ba, to in kuma ma ba ace min in tafi ba zama da Ado yana nufin ci gaba da zama cikin ukubar Mama da wulaqantawarta, don haka sai in ga to gara min kawai in ci gaba da jajircewa har lokacin rabuwarmu tazo in je in yi aurena na ‘yanci da mutuntawa da ganin darajar mahaifiyata.
Na shiga kicin da nufin yin girki karo na farko a rayuwar aurena ni da Ado cikin kwanaki goma shataran da muka yi tare saboda in yi girkin da zan aikawa kakata Mahaifiyar Baba abincina don kar ta tafi bata tava cin girkina saboda na yarda da maganar da Ado ya gaya min cewar yawan rai ne ya sata ganin auren nawa, don shekaru tamanin da huxu ke gare ta, bai kamata in bari ta tafi bata xanxani girkin nawa ba, tun da ban san randa zata sake zuwa ba.
Na fara shirye-shiryen xora girkin kenan bayan na gama tsabtace wurin, sai Ado ya leqo cikin natsuwa ya ce min ko za ki yi ne har da mai babban allo? Ban tanka ba ya juya ya tafi, ga dukkan alamu dai ya ji daxin ganina a kicin xin, shawarar da ya bayar ta sanya ni faxaxa girkin sosai. Tuwon semovita nayi miyar kuka don a sanina tuwo shi ne abincin da yafi daxi yafi sauqin ci a wurin Hajiyar Giyaxe, to ko shima mai babban allon yasha gaya min cewar a dole yake cin wani abinci matuqar ba tuwo ba ne.
Na kammala komai ya kuma yi daxi sosai, don wadatattun kaji na zuba a cikin miyar ina tunanin Inna gama in aika a gayawa Inna ta bani inda zan zuba abincin sai ga Ado ya shigo da su food flask har guda uku da wasu kwanukan silver masu murfi masu kyau set biyu da dinner set guda xaya.
Nasa hannu na karvi wasu, wasu kuma shi da kanshi ya shigo ya ajiye su ya kuma koma gefe ya tsaya yana kallon yanda nake malmala tuwon ina naxe shi cikin leda ina ajiyewa cikin food flask da kwanukan da ya kawo. Wannan na waye? Ya buqaci sani ba tare da na kalle shi ba na ce mishi nasu Yaya Ibrahim, to wannan fa? Ya sake nuna wani, na gaya mishi na ce na Baba ga na Hajiyar Giyaxe da na gidan mai babban allo da ka ce a sa.
To na Inna da Mama fa? Na ce ai wannan da na ce na Baba ne malmalar ciki na da yawa duk mai so sai ya xiba, ya ce to ya yi ina gama zuba miya nasa manshanu da yaji, Ado ya juya zai kira Yaya Ibrahim ya xaukan musu nayi maza nace mishi a’a bari shi zan je in kai musu jin haka da yayi ya sa shi xiban kwanukan a hannunshi yaje har xakinsu ya kai musu. Cikin zuciyata ni kam ina jin takaicin yanda Ado ke tafiyar da su Ibrahim duk da dai shi xin qanin mahaifiyarsu ne, to amma kuma na sani in banda su xin sun lalata kansu da shaye-shaye da qin karatu da zaman rashin sana’a babu yanda za’ayi ya rinqa yi musu haka. Koda yake akwai adawa mai yawa a gidanmu tsakanin ‘ya’yan wannan xakin da na wannan wanda nake ganin kamar Mama ce tayi dalilin aukuwar hakan, ko da yake dai Maman da kuma Babana suna faxin cewa wai Inna ta ce tayi sanadin faruwar komai to amma kuma hakan ba zai hana zuciyata sa min cewar Baba da Ibrahim dama duk wani xa da Mama ta haifa ‘yan uwana ne ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login