Showing 6001 words to 9000 words out of 36031 words
magana saboda yasan shirun da tayi alama ne na wai shi take sauraro, ya ce to Inna in na ce komai na gani sai nayi magana ba fa ba jituwa zamu yi da shi na gaya miki abinda ya faru sanda nazo da maganar yaran nan da aka kawo min labarin abinda suke yi zuwa nayi da qarfina don musan matakin da zamu xauka a kan su tun abin bai yi nisa ba sai uwar su ta ci mutuncina a gabanshi ta ce wai duk tsiyata dole in ga ‘ya’yanta in kuma haqura da su tunda an riga an haife su ba kuma zai yiwu in dunqule su in maida su inda suka fito ba.
Hajiyar Giyaxe ta ce, to kayi haquri, ni da kaina na baka haquri in cin mutunci tayi kuwa to ba kai tayi wa ba kanta tayi wa, gyara kayanka kam ai baya zama sauke mu raba, ba ga ta nan gasu ba, ko ni xin nan da ban san shaye-shayensu na zamani ba ina ganinsu na gaya musu kai ba sigari kaxai suke sha ba suka ce shi kaxai ne nace to bai karve su ba, su daina don duk sun rine sun zama wani iri.
Sannan ko ba komai waxannan yaran su Salisusu ai sa’o’insu ne shi Baba ma ya girme shi to ba gashi nan ba ya natsu ya zama babba har ga aure zai yi su wake ta tasu? Dama shi mutum in yayi kos xin iya shege ai in ya riqa sai ya koma yiwa kanshi, don haka ba don su taimake ni kasa a mayar da wannan yarinyar xakinta.
Ya ce to Inna, yanzu in na tashi daga nan zan tafi can gidan mijin nata in neme shi muyi magana in yaso da daddare sai in turo masu maida ita su maida ita, ta ce mishi to, tayi tasa mishi albarka Babana kuwa tayi mishi tas. Ba akan komai ba sai akan irin mu’amallarshi da Baba Yahaya ta ce shi kaxai ya riqe abotar da don ta Babana da tuni sun rabu.
Mama tayi ta kuka tana faxin wai dama can Hajiyar Giyaxe ba sonta take yi ba, ita kuwa Hajiya ko kallonta bata yi ba balle ta damu da kukan da take yi.
Mama bata xauki cewar da Hajiyar Giyaxe tayi na a baiwa Ahmad da Salisusu Atika da Aliya da sauqi ba, da farko tayi maganar qanqantarsu da Babana ya gayawa Hajiyar Giyaxe sai ta ce ai ita sanda aka kaita gidansu shekarunta goma sha xaya ne ba gata ba me ya same ta? To balle Aliya mai sha huxu a kaita xakinta kawai ta sake dawowa da maganar hidimar da za’ayin wai an riga anyi nisa babu su a ciki gashi ana matsalar kasuwa tunda kwanannan ma akayi wata asarar.
Don haka a xan xaga nasu bikin don a samu a xan tanadan musu wani abu, da Babana ya sake yi mata wannan maganar sai ta ce mishi kira min iyayen yaran in ji ta bakinsu, Mama da Inna suka zo Mama ta sake rattaba mata bayani da dalilan son xagawan da ta waiwayi Inna sai ta ce ita ana ta ayi hidimar ba tare da su an sanya su cikin waxanda za’ayi wa sayayyar ba, tunda ba a faro dasu ba a xaura musu aurensu kawai a kai su xakunan mazansu arzikin gidan miji ai yafi na gidan iyaye, don haka kar ayi musu komai ko da kuwa tabarma ce.
Innar Giyaxe ta ce, na gode miki ‘yar nan, Allah dai yayi miki albarka, je ki abinki kin ji Inna ta tashi ta tafi ta kalli Babana ta ce mishi kar kayi sayaiyar da su sun yafe a xaura musu auren a kai su gidajensu tunda uwar suma ta ce bata son sayaiyar, don haka na umarce ka ka aurar mata da ‘ya’yanta in kuma bani ka ke nema da magana ba.
An maida Anti Sha’awa gidan mijinta ko kwana bakwai ba ayi ba sai ga goro an kawo wai na tarewar amaryarta rana ita yau. Hajiyar Giyaxe ta ce, uhun ka gani ba? Gajiya yayi da irin qarantarku da kuke mishi, don haka zai yi wa kanshi maganin iya shegen ‘yarku ku kuma kun kama ta kun riqe kuna jira sai yazo, to ba don Yahaya yaje ya bashi haquri yasa an maida ita ba da amarya ta tare ita tana wurin yaji kaga kuma da girma ya faxi. Ko da yake yanzun ma dai sai dai ayi sha’ani.
Rannan Mama ta wuni tana zage-zage, tana faxin kaga min ja’iri mara mutunci bai da ko kwabo naja na tsaya na ce sai shi bayan ga mutanen da suka dace a ba su shi ne tun ba a gama fita daga zaman talaucin da ake yi ba zai kwaso wata tsiya ya kawowa mutane? Zubaida ta ce ai sai dai kar a kuma don wannan kam ya riga ya kwaso.
Gaba xaya Babana hidimarshi da maganarshi ta zama ta hidimar bikin da ya sanya a gaba na ‘ya’yanshi mata guda biyar, ga kumaxan shi na riqo wato qanin matarshi Ado, wai shima shi ne mai yi mishi komai sadaki da zannuwan aure duka ina jin mama tana cewa wannan kuxi da ka bayar na sayaiyar zannuwan auren Ado ai ba za su yi ba Alhaji, haka fa kayayyakin xakin yarannan da hikima na qarasa yi musu sayaiyar. Inna mai ‘ya’ya uku rus cikin lamarin ba a ko sha’awa da ita hankalinta kuma a kwance hidimarta kawai ta sanya a gaba.
Tuni tayi kasafi na abinda zata baiwa kowacce a cikinmu cikin ‘yan kuxinta da cikinmu ya rage mata da suke wurin juyi. Sai dai ni kam ba kayan xaki take shirin saya min ba, don Mama ta riga tayi furuci maganar kuma ta riga ta bayyana har mutane da yawa sunji ta cewar auren nawa da Ado za a yi shi na wata uku ne kawai, watanni ukun suna cika zai sako ni in dawo gida in yaso sai ya nemi wata qalleliyar yarinyar ya aura tunda ma ai kan nawa auren ko me aka yi bai da asara don ko qwandalarshi ba zai kashe ba, Babana ne zai yi mishi komai.
Ado ya yarda da wannan qa’ida da Mama ta sanya mishi, ya kuma yi rantsuwar yi mata duk abin da take so akan auren dama kuma kowa yasan shi xin mai yi mata biyayya ne.
Bisa wannan dalili ne Inna da ‘yan uwanta suka tsaida shawarar ni kar a saya min komai na kayan xaki ta saya min zinari tunda qadara ce ban da haka kuma zan yi kwalliya.
Kwanakin bikinmu sun matso gaba xaya abinda yai saura bai wuce kwana bakwai ba, hidima ta riga ta soma kankama in Mama tayi sammako ta fita tun safe to bata dawowa sai dare, wai tana can wurin hidima. Inna ma dai da bata zuwa ko’ina itama tata hidimar tayi nisa don Hajiya Kubra tana tsaye akan al’amarinta gashi kuma ta tsaya wajen ganin an haxawa Innar gudumowa mai yawa shi kam Alhaji Abba ma shi ta xora wa hidimar gadaje da kujerun su Atika, don haka masu matuqar kyau aka saya.
Rannan da hantsi na fita naje gidan Anti Ramla don ita tayi kirana wasu ‘yan dabaru wai take son koya min na yanda zan yi in zauna da Ado, tunda ga abinda ake cewa wai auren na kwana casa’in ne tana gama gaya min abinda zata gaya min xin nayi mata godiya na fito ba wani daxewa nayi ba da barin gida amma abin mamaki da yake an ce wai baya bata kaxan sai nazo na samu yanayin da na bar gidanmu ya canza, ganin mutanen gidan nayi a tsaitsaye kowa sai zare ido yake yi yana rarraba su.
Da sauri naja na tsaya ina tambayarsu me ya faru? An yi wani abu ne?ko wani ya rasu ne? shiru sai kallona ake yi na ce ha’a to menene haka? Zan fara kuka don ban san me ya faru ba gashi kuma ban ga Babana a cikin gidan ba, sai kawai Zubaida ta ce min ba fa wani abu ba ne maneman Suwaiba ne suka tuiro wai a xaga musu nasu bikin don ba su samu xaki ba, shi ne da aka ce musu a’a bikin ya riga yazo kuma ba ita kaxai ba ce don haka ba zai yiwu ba maganar xagawar shi ne suka ce to sun fasa auren.
A zuciyata na ce ina ma ni ce! Duk da irin rashin kyakkyawar mu’amallar da ke tsakanina da su ban ji daxin hakan ba, don haka sai na wuce naje na shiga xakin Mama don in yi magana da Suwaiba, kukan da take yi ya wuce gaban bayani, nayi qoqarin rarrashinta, naga ba za ta gane ma ina magana ba, don haka na haqura na fito cikin zuciyata dai na ji tausayinta don ta riga tasa rai da yawa akan auren.
Can cikin zuciyata na ce, oh’oh ko menene mai daxi haka cikin auren da za’ayi mishi irin wannan son? Oho.
Ko kwana xaya da faruwar abin bai cika ba sai kawai Mama ta soma yin waya tana gaya wa mutane cewar bikin babu shi kwata-kwata ma ba za ayi ba don ba zai yiwu ayi biki babu Suwaiba a ciki ba. Kan ka ce menene wannan sai ga Babana shima yana qoqarin gamsar da Mahaifiyarshi dalilan da suka sa shi zai xaga bikin zuwa wani lokaci gaba kaxan, ita kuwa ta ce ina! Akan mutum xaya sai a fasa bikin ‘yanmata huxu? Ba zai yiwu ba sai dai ko ita Suwaiba da uwarta su fito da wani mijin kafin ranar don a haxa har da ita ko kuma ayi babu ita.
Hakan kuma aka yi ranar xaurin aure yazo an kuma xaura auren ‘yanmata guda huxu babu Suwaiba a ciki, don ita da Mama sun kasa fiddo da wani mijin ko da kuwa cikin ‘ya’yan dangi ne, a zuciyata na ce oh’oh wato Inna dai ba qaramin rufin asiri ke gare ta ba da aka bata wa’adin kwanaki uku in kawo miji aka kuma kawo har guda biyu da aka hana su ni kuma aka ba su qannena suka karva saboda ba donni da qannena dama za su yi auren ba don ita Innan ce sanin halinta da suka yi mutuncinta da kuma haqurinta.
Anyi biki irin wanda ba’a zata ba, zan ma iya cewa ba a tava yin irin shi ba a unguwarmu gaba xaya saboda ba Mama da Babana ne kaxai tsaye akan bikin ba, balle don sunyi mishi saki lecece ya kasa yin armashi.
Baba Yahaya da Alhaji Maikuxi sunyi wa bikin hidima ta ban mamaki dangin Inna rannan basu wani saurari dokar Babana ta hana su zuwa mishi gida ba, tururuwa kawai suke yi suna shigowa Inna tana can cikin xakinta ko ganinta ba’ayi.
Itama Mama danginta da qawayenta sun zo da yawa, to amma kuma ta riga taki bakin sai zage-zage da neme-nemen tashin hankali take yi, Inna Balki ta ce kar wanda ya kulata ai mu ba ma hidimar arziki muyi faxa. Duk wani abin da suke buqata shigo dashi kawai suke yi ko loma xaya na gidan basu nema ba balle aje ana vacin rai.
Ni kam nayi kwalliya ko in ce mun yi kwalliya don kuwa Atika da Aliya kayan aure aka yi musu tanfar ba za su qare ba, saboda yawa to amma kuma nima dama Innata da Hajiya Kubra sunyi min tanadin kayan ado masu daraja, don haka ko kallon akwatin da Mama ta bayar guda xaya na kayan aurena da zannuwa biyar a ciki babu wanda ya sake yi. Sai ma da Hajiya ‘Yardubu taga irin wulaqancin da ake yi wa Akwatinne taja shi ta adana tana faxin “Wannan akwati fa ba shi ne auren ba, miji shi ne aure.
Gaba xaya aka fara magana shima mijin ai ba auren yake nufi ba, Hajiya ba ki ji abinda suke faxi ba ne cewa a kwana casa’in zai qare? Tayi murmushi ta ce, to ko na kwana bakwai ne in ya zamo mai albarka ai shi kenan, ba dai an xaura ba? Suka ce, “Eh” ta ce to ai shi kenan.”
Cikin kwanaki biyun da bikin ya kankama wato Juma’a da Asabar hidimar da aka yi ba qarama ba ce, abin mamaki kuma shima Ado yayi hidima yayi ado yayi gayya, danginshi na uba da abokanshi masu yawa suka zo, qanin Mahaifinshi ne wai ya karvar mishi auren.
Ranar Asabar da daddare Amare gaba xaya aka kai su gidan mazajensu, sai dai ni kam fita da ni kawai aka yi daga gidanmu aka sake shiga dani xaya gidan namu.
Inna Balki tana zaune a gefena kan wata ‘yar tabarma da muka samu a shimfixe don Mama bata sa anyi jere ba, ta ce sai gobe, sannan gaba xaya kayan alatun da Ado ya kamata wurin shi da su ta kwashe wai sunzama nata tunda yayi aure. Ta xan faki idon mutanen dake cike a xakin ta matso da bakinta kusa da kunnena ta ce min, mijin naki fa xazu na ganshi da yazo angwanci santalelen saurayi ne, ina ganin maimakon fito-na-fito da rashin kirki ko za ki gwada yi mishi kirki ne? nayi maza na ce mata a’a bana son shi ba zan zauna dashi ba, ta gyaxa kai ta ce to shi kenan, amma baki ga kamar…kan ta gama nace mata bar shi kawai Inna ba zan iya zama dashi ba, ta ce to yanda tayi dai muna miki addu’a na ce to na gode.
Waxannan suka kawo ni suna barin gidan abokan Ado suka shiga kai-kawo suna tambayar ‘yanmata, abinda suke buqatar a kawo musu.
Wata zaqaqura ta ce musu katifa don ba mu ga yanda za’ayi amarya ta kwanta kan wannan tsohuwar tabarma da aka yar a qasa ba, suka ce kin faxi gaskiya ‘yanmata, suka juya suka fita. Jimawa can sai gasu da qatuwar katifar sunbuqa sabuwa dal a cikin ledarta, har bargo shima sabo duniyar kule kan ka ce meye wannan sun wadata wurin da kayayyakin ciye-ciye da shaye-shaye iri-iri.
Washegari ranar Lahadi rannan wuni muka yi daga ni sai qawayena sai dangin su Mama da suke shigowa jifa-jifa ganin amarya sai ko ‘ya’yana su dake kai-kawo amma dangin Inna babu wanda ya leqo don su dama sun ce sun gama da gidanmu tun jiya sun dai zo sun sheda xaurin aure, to yau za su yi hidimar su a tsakanin gidajen amaren su Atika da Aliya da kuma gidan mai babban allo, don su a wurin su shima Salisusu xa ne saboda Baba Yahaya.
Har bayan Azahar ba a zo aka yi min jere ba, abincin ranar ma ba a kawo ba, wataqila don sun leqo sun ga angwaye sun kawo abin karyawa shi yasa ko suke zaton za su kawo na rana oho.
‘Yanmata suka nemo redio suka shiga sanya kaset suna cashewa, don su xebewa kansu takaicin zaman shiru.
Sai bayan La’asar lokacinne naga ana shigowa da wasu katakwaye da ‘yan kujeru waxanda rabon da inga irin su tun a hotunan mutanen da, tunda nasan ko a qauye ba za ayi amfani da waxannan ba yanzun. Nan da nan masu jere suka yi jere suka gama ko awa xaya basu cika ba suka yi tafiyarsu dama kuma ‘yan uwan Maman ne masu jeren.
Wajen qarfe shida saura kwata na yamma sai ga Anti Ramla ta shigo tasha kwalliya tayi matuqar yin kyau da kyar maganar take fitowa ga alama ba qaramin jiki ta ji ba a bikin, menene wannan? Ta shiga waige-waige tana qara kallon xakin na ce mata kayan xaki ne ta kwashe da dariya ta ce, kanta kayi wa kamata ta muzanta tunda shi ne zai hau kai ya kwanta ko kuwa na ce mata eh.
Ta ce, kai baki ga gidan su Aliya ba da Atika, nayi murmushi na ce sun yi kyau ko? Ta ce ai ba a magana, Salisusu yana faxamar mada na ce sabon gidan Baba Yahaya kenan, ta ce eh to ita kuma Atika tana C.B.N Quarters, Alhaji Abba ya baiwa Ahmad vari xaya amaryar shi shima tana xaya, na ce kai sun more gidaje, ta ce eh an kuma yi musu kaya, don ban da na Alhaji Abba shima Alhaji Babba yayi musu wasu gadaje da kujerun a zuciyata na ce Alhaji Maikuxi kenan.
Labari sosai ta bani na irin hidimar da aka yi na bikin Atika da Aliya, nayi murna sosai don nasan Inna tana cikin farin ciki. Daga baya ne kuma na ji tausayi, sai dai maimakon in ji tausayin kaina tausayin Babana ne ya kama ni.
Gaba xaya abokanshi a yanzu arzikinsu ya zarce nashi, saboda suna da tsayayyun ‘ya’yan da suka tallabawa neman arzikin su a lokacin da suka soma buqatar hakan saboda shekaru sun soma yi musu yawa. Shi kuwa bai samu nashin sun kintsa ba, balle shima suyi mishi irin wannan taimakon sai Ado.
Ado kuwa ta’adin da suke yi mishi shi da Mama yawanshi ba kaxan ba ne.
“Tashi kiyi kwalliya ga waxannan kayan Hajiya Kubra ta ce in zo miki da su.” Na ce mata “To.” Sai da na sake wanka na zauna na sake shafa mai tana taya ni don mun riga munyi matuqar shaquwa da ita, sannan na sanya sabbin under wears waxanda suma a cikin kayan tazo dasu na sanya kayana