Showing 9001 words to 12000 words out of 76857 words
ba da sunan duka ki sa wannan a ranki,
aunty jiya fa murɗe min hannu yayi yadda kika san zai karya ni ita kuma muguwar matar sa , duk ihun da nayi ko motsinta ban jiba akan yaga video a wayata.
dariya aunty Hafsah tayi tace '' to ban da abin ki ya za ta shiga tsakanin ku, kefa da jawad me raba ku sai Allah ina muku fatan haka insha'Allahu mutu ka raba..,
da sauri Najlah tace '' kai aunty hafsah wannan wacce irin magana ce..,
kinga yanzu dai zan yi aiki in anjima zan kiraki mu ci gaba da magana.
to ki kirani dan Allah.
karki damu kanwata zan kiraki.
ta fada haka tana kashe wayar ta tashi najlah tayi domin ta saka kaya, ji tayi an turo kofar da kin ta da sauri ta rarumi hijabi ji tayi tamkar ta nutsai a cikin ƙasa Saboda kunya tasan ya riga da ya gama ganin ta gashi towel din ko mazaunanta be rufe mata ba kasa tayi da idon ta tana wasa da hannunta cikin deep voice din sa yace '' breakfast is ready kiyi sauri ki shirya,
kai ta gyaɗa mai fita yayi be ce komai ba da sauri ta buɗe wardrobe abaya ta dauko C-green an mata aikin beadwork a jikin ta yar Turkiya dauko riga da wando tayi ta saka sannan ta saka abayar tare da daura dankwalinta bata tsaya bata fuskar'ta ba wajen kwalliya kawai lipstick ta saka tushe hancinta tayi , ta feshe jikinta da turare saboda tana da asma slippers ta saka ta fito tun daga nesa ta jiyo kamshin turaren jawaher har makaki yake mata a maƙogaro ya mutsa fuska ga fuskar'ta taci uban make over to ai wannan kwalliya sai dai a kirata da make over tamkar jambaki zai yi magana a bakin ta ‘‘O‚‚ kowa akwai kiwon da ya amshe shi in banda haka ita ko iya shakar numfashi ba za ta iya da wannan uwar kwalliya ba , ga uban gashin doki, karasawa dauke kan'ta tayi da sauri jawaher ta tashi ta ja mata kujera dai-dai lokacin da takai hannu zata ja kujerar dining table ɗin ja baya tayi ta sarke hannun ta jawaher bayan ta ja mata tace '' kanwata bisimallah ya kwanan kaɗaici..?,
Najlah tace '' Nagode alhamdulilah..,
Hakan da tayi ba ƙaramin kimarta Jawad ya kara gani ba , yana so a nuna ana son jininsa ana ji da shi kallon jawaher yayi wani fari tai mai tace '' ya dai..?,
kafe ta yayi da idanuwan'sa tari ne ya sarke Najlah da sauri ya taso zai bata ruwa jawaher tayi maza ta dauko lemon gabanta ta miƙa mata tare da kamar na hannun JAWAD ta kai bakin ta, tana bin sa da wani irin kallo.
ikon Allah haka NAJLAH tace a zuciyar ta kasa shan ruwan tayi zama tayi tane cewa Alhamdulilah na dawo dai-dai.
wani miskilin murmushi JAWAD yayi ya koma ya zauna serving dinta tayi tun da ta fara cin doya dakwai da tea bata ɗago ba hankalinta ya mayar gaba ki ɗaya kan abin da take ko farfesun da ta zuba, mata bata jin zata iya ci saboda cikin'ta ya cika baza ta iya ci ba.
matsar dana gaban ta, tayi tace '' nakoshi..,
da sauri ya ɗago yana kallon ta abin ya bashi mamaki yace '' har kin koshi ko rabi baki ce ba na gani..,
kan'ta na ƙasa tace '' eh nakoshi..,
Jawaher ta ɗora hannunta akan nasa tace '' sweet inaga ta koshin ne tun da ba za taiwa kan'ta mugunta ba , bata koshi ba tace mai ta koshi kasan doya akwai cika ciki...,
Haka ne
ya faɗa yana ci gaba da cin abincinsa gyara zama tayi tace '' sweet ya maganar tafiyar tamu ne..?,
kije Allah ya kai ku lafiya wani ihu tayi tare da tsalle ta rungume shi tana yi mai kiss duk sai data ɓata mai fuska Najlah da ta fito miƙa mai waya anni za tayi magana dashi taga abin da ya kusan sumar da ita dan kunya ƙasa tayi da idanuwanta tamkar ƙasa ta tsake ta shiga, ita wallahi mamaki halin yaya take yanzu shi ya koma haka Allah me iko.
Copy is not allowed 🚫
EPISODE 5
Da sauri ya saki bakin jawaher da yake mata wani irin kiss jikin'ta a sanyaye ta miƙa mai wayar tace '' anni ce take son magana da kai..,
amsa yayi, ya kara akunne gaisawa su kayi sannan ta tambaye shi ya iyalin nasa alhamdulilah yace ,
anni tace '' to JAWAD na sanka ba dai iya mugunta ba yadda kasan kurtun soja ne ya raine ka , dole sai kai hakuri da halin NAJLAH yarinya ce a sannu a hankali kana nuna mata nan zaki bi wannan hanyar tafi zata koma yadda kake so, dan Allah ban da nuna isa su ya'yan yanzu lallabi da nasiha ke aiki a jikin su kar kuma inji wani abu ya biyo baya nasan ka sarai tun kana yaro dan haka , ka kular min da jika karatu tazo dan haka bana son jin wata magana..,
sosai ƙarshen maganar ta , ta bashi dariya shafa kai yayi yace '' insha'Allahu zan kiyaye amma ita ma ku ja mata kunne jiya video's naga ni a wayar ta , a haka za tayi karatun ga kallon fina finan yan Japan da Philippines..,
Dan Allah dai a kula kaji dan Allah barka
to yace sukai sallama miƙa mata wayar yayi lokacin jawaher ta bar gurin amsa tayi jikin ta na rawa ita kuma haka Allah ya haɗa ta da kaddarar zama da wa'yannan mutane da ba su san mece kunya ba juyawa tayi tana tafiya a hankali tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki.
tana shiga daki ta rufo dakin ta , ta kwanta dan ya mutsa fuska tayi tsoron ta ɗaya lokacin period dinta yazo ba karamar wahala take sha ba shiyasa kama abinci ta ci shi kaɗan, duk hankalin'ta ba a kwance yake ba.
sosai take juyo saboda cikin'ta ji tayi anyi knocking da kyar ta iya tashi gumi duk ta wanke mata fuska ta buɗe kofa yaya ne fa shirin tafiya wajen aiki zama tayi a ƙasa tana matsar kwallah tace '' yaya JAWAD mutuwa zanyi cikina ciwo yake min..,
da sauri ya ɗurkusa kasa ya tallafo habar'ta yace '' Najlah me yake damun ki..?,
cikin ta tayi mai nuna dashi ba ƙaramin tashin hankali take ciki ba kuka ta rushe dashi ta kifa kan'ta akan cinyarsa tana kuka jawaher ce ta shigo ta gama haɗa trolley din'ta tace '' to me yake faruwa sallama na shigo nayi mata..?,
kallon ta yayi yace '' har kin shirya..?,
kai ta ɗaga mai fuskar'ta cike da alhini ta durkusa tace '' me yake damun ta..?,
ta ƙara mai maita masa tambayar da dazu tayi mai ajiyar zuciya ya sauke yace '' cikin'ta ke ciwo..,
innalillahi sannu normal ciwon cike ne ko na period ta faɗa tana kallon Najlah.
ƙasa magana Najlah tayi sai juya kai take yi hannunta na kan mararta jawad ya kalli jawaher yace '' sweet kawai ki tafi Allah ya kiyaye hanya ba zan samu damar kai ki ba zan kirawo doctor kar na ɓata miki lokaci tun da shi jirgi baya jira..,
haka ne wallahi to Allah ya bata lafiya ta faɗa tana tashi daga tsugunan da tayi ranta fas tamkar zata , taka rawa fita tayi tare da ja musu kofa ɗago kan Najlah yayi yace ''sannu kinji ko bara na kirawo doctor ya duba ki..,
ƙara rushewa tayi da kuka ta girgiza mai kan'ta tare da riko hannun sa tace '' karka kirawo shi allura zai min a hankali zai sake ni bana so a ka kirawo doctor..,
haɗe rai yayi yace '' bana son zancen banza sai ma kin zaɓi abin da za ayi miki bacin kuma baki da lafiya..,
kuka ta ƙara rushewa dashi cire mata mayafin'ta yayi sannan ya balle mata riga ya cire ganin irin gumin da take yi itama ba tayi kokarin hana shiba saboda bata cikin nutsuwar ta.
kwantar da ita yayi a akan gado ya cire rigar sa ta lauya da wular da ya saka ya matsar da briefcase din'sa da wasu folder's da ya fito da su daukan wayar sa yayi ya dannawa doctor Kira bugu ɗaya ya ɗauka yace '' doctor Dan Allah kazo gidana akwai mara lafiya...,
doctor yace '' wallahi bana gari amma bara na turo maka sister zuwairat insha'Allahu zata so cikin gaggawa itama tasan aikin ta..,
okay ba damuwa sai ka turo ta ɗin ya faɗa yana kashe wayar sa ,
zama yayi kusa da ita kuka ta ƙara rushewa da shi ta riko hannunsa tace '' kiramin Hajiya ta zan mutu yaya..,
da sauri ya kalle ta , shi be san ya zai yi da yarinyar nan ba rakinta yayi yawa dauke kai yayi yace '' ina wayar ki, ki kirata da ita mana..,
kuka ta rushe dashi ta kwantar da kanta a cinyar sa tace '' yaya cikina ciwo..,
ya buɗa baki kenan zai magana wayar sa tayi ringing da sauri ya ɗauka saboda yana kyautata zaton doctor ce ɗagawa yayi ai kuwa ilai itace sallama tayi mai tare da gaishe shi cikin girmamawa amsawa yayi tace '' ina bakin gate masu gadib gidan sun hana ni shigowa...,
Okay karki damu suna kan aikin su ne , zan musu magana yanzu.
to tace mai ya kashe wayar gyara mata kwanciya yayi ya fita kuka ta ƙara rushewa dashi har suka dawo bata sani ba doctor zuwairat ta durkusa ƙasa tace '' innalillahi wainna ilaihir raji'un sannu me yake damun ta..?,
ta ɗago da kan'ta tana kallon Jawad cire medical glasses dinsa yayi yace '' ciwon ciki..,
oh Allah ya bata lafiya idan tana yi allura ake mata ko magani ake bata da sauri Najlah ta firgita tare da ja da baya hawaye wani na bin wani gaban ta na faɗuwa tace '' dan Allah karki yi min allura karki bani magani yanzu ma ya fara saki duk wata haka nake yin sa..,
dariya abin ya so ya bawa doctor sai ta danne ta zauna akan gado tace '' yanzu idan ban miki wa'yannan abubuwan da kika faɗi ba , me zan miki..? kefe mace, ce wannan ciwon da kike gani ko kwatan ciwon haihuwa be kai ba..,
da sauri Najlah ta ɗago lokaci ɗaya suka haɗa ido da Jawad hawaye ta share ta kalle sa tace '' cikin nawa ya dena yi min ciwo ba sai tayi min komai ba..,
haɗe rai yayi yace '' ni sa'an kine ko ita da kike faɗa mana haka..?,
murmushi doctor tayi tace '' na lura yar daru ce kawai bara na rubuta mata magani idan taci abinci ta sha zai saka ta bacci insha'Allahu kafin ta tashi cikinta ya cika kuma period din zai zo batare da ta ƙara wahalar da ita ba..,
okay ba damuwa rubutu tayi mai a takarda ta miƙa mai kuɗin'ta ya dauko ya bata tai mai sallama tare da godiya ta fita be biya takan Najlah ba , ya fita ya bawa me musu aike ya siyo mai zama yayi a parlour yana jin sautin kukan ta ransa duk a ɓace yake ciwon kai kuka yake saka shi , ga wannan kukan da take har tsakiyar kan'sa yake jin kukan nata.
tsaki yaja jin anyi knocking ya tashi ya buɗe kofa ya karbi ledar maganin yace '' riƙe canjin...,
godiya yayi mai ya rufe kofar kai tsaye kitchen ya nufa rasa me zai mata yayi gwara ya tambaye ta me take so komawa yayi dakin ya ajiye ledar maganin a kan bedside drawer ya zauna yace '' me za kici..,
ɗago da kan'ta tayi ta kalle sa tace '' dambu...,
da sauri ya kalle sa shi tun da yake a rayuwar sa ya taɓa kwatan ta dambu ko da yayi zaman hostel bayayinsa tunda wani aikin sai mata cikin mamaki yace '' dambu kuma...?,
kai ta gyaɗa mai ba tare da tayi magana ba
ajiyar zuciya ya sauke yace '' sai dai na yi miki oder take a way ni ban iya dambu, ba bana jin jawaher ma ta iya gashi ɗazu ta bawa me yin girki hutu sai ta dawo tun da gaki a cikin gidan zaki saboda tafiya za tayi..,
dauke kai tayi wato gata baiwa ko ta girkawa mijinta ban da ita mara hankali ce bama ta damu abincin wannan shi ake cewa mijinta ba Allah ɗaya gari bamban.
jin tayi shiru yace '' magana fa nake miki..?,
ya tsuna fuska tayi cikin ta na murɗawa tace '' a'a barshi kawo min yogurt..,
tashi yayi ya fita bajimawa ya kawo mata tsiyaya mata , yayi a cikin kofi amsa tayi ta tashi ta fara sha tas ta shanye sannan ya ballo mata magani da ruwa ya miƙo mata kwalla ce ta taru a idanuwanta ta kura mai ido zuciyar'ta tamkar zata faso kirjinta ta fito saboda tsabar fargaba hade rai yayi, dan haka ba shiri ta amsa ta saka a bakin ta amai ne ya taso mata , da sauri ta shiga toilet ta fara kwara amai gaba ki ɗaya abincin da taci sai da ta amayar dashi.
hankalin sa ne ya tashi da sauri ya shiga toilet din duk ta ɓata jikin'ta da amai gashi jikin ta ya saki dole sai ya temaka mata ta gyara jikin'ta,
KARUWAN CIKIN GIDA
Copy is not allowed 🚫
EPISODE 6
a hankali ta furta zan iya gyara jikina ka tafi aiki..
da sauri ya kalleta still har yanzu tana jikin'sa yace '' za ki iya kar na tafi ki shiga wani hali..?,
kai kurum ta gyaɗa mai zuciyar ta na wani irin mugu tamkar zata fasa kirjinta, ta fito, haka kurum ku sancin su yana jefa ta a wani irin yanayi dan baka bata so musamman kallon da yake mata be gamshe ta ba , bata aminta da shi ba.
tashi yayi ya fita da kyar ta iya cire kayan ta, sai dai tsantsin aman da tayi, ya kwashe ta, ta faɗi ƙasa ihu ta saka da sauri ya shigo rintsa idon'ta tayi, shikkenan ya gama da ita ya gama ganin komai kai ta girgiza tace '' yaya la fita faɗuwa nayi zan iya komai dan Allah ka fita..,
ganin yanayin da take ciki idan ya fita be mata adalci ba dan ba iyayen su be kamata ace ya wufuntar da ita ba.
kuka ta rushe dashi ta fara ture shi be saurara mata ba tas ya gyara mata jiki ya naɗeta a towel ya fito da ita tamkar wata jaririya, kwantar da ita yayi a gado sannan ya koma toilet din ya gyara shi tas wanka yayi ya fito, daukan kayansa yayi,ganin tayi bacci sai ya fita ya jawo mata kofar ta ,kai tsaye bedroom din'sa ya shiga ajiye kayan hannunsa yayi ya ɗauki wayar sa message din jawaher ya fara cin karo dashi kamar haka sweet yanzu muka tashi kai mana addu'a i love You limshe idanuwan'sa yayi ba ƙaramin sanyi yaji ba a zuciyar yi mata reply yayi ya ajiye wayar yana jinsa acikin wani irin yanayi duk abin da yayi ɗazu karfin hali ne amma yaki da zuciya shi ya riƙe shi be aikata abin da zuciyar sa take kawata mai ba.
Wannan kenan
Nailah tashi tayi dakyar kanta na mata wani irin ciwo dafe shi tayi tace '' deeya bani maganin ciwon kai , wallahi kaina ciwo yake..,
tashi deeya tayi ya buɗe drawer din'ta ta miƙo mata magani tare da bude fridge ta dauko mata ruwa watsa su tayi a bakin ta ta kora da ruwa sannan ta saki ajiyar zuciya ranta duk a ɓace pauzy ta kalla tace '' haɗa min ruwan wanka gida zan tafi...,
Gida kuma..? cewar deeya
gyaɗa mata kai tayi tace '' gida nake son zuwa kudin hayar da DAZ ya kama mana ya ƙare ko daman ace be ƙare ba ina son tafiya gida nagano wanne hali su baba suke ciki..,
Mahaifinki fa
Cewar deeya
jingina tayi da , allon gado tace '' hnmm ba abin da zai min iya yakaci yace zai dauko yan sanda su fita dani kuma yayi tabanza ba inda zani wallahi gwara duk abin da zanyi na zauna a gidan iyayena su kan'su sun sallama ni ina da right din da zanyi abin da na ga dama..,
to Allah ya kyauta pauzy ya faɗa tana tashi daga kan gadon deeya jin ana buga kofa suka yi da sauri deeya ta tashi tace '' anya kuwa ba Yusuf ne ya dawo ba..,
da sauri nailah tace '' Yusuf kuma daman ya sanar miki zai dawo..,
gumi ne ya wanke mata fuska ta gyada kai tace '' yadai ce min a cikin satin nan zai dawo tun da naji bugu da safiyar nan to ba mamaki shi ne wallahi..,
jikin'ta na rawa tace '' maza dan Allah ku tashi ku saka kayan ku..,
ai bata ƙarasa ba taji wayar ta tana yin ringing da sauri ta dauka tuni sunan da tayi saving number sa ya fara yawa a screen din wayar ta kallon pauzy tayi tace '' wallahi Allah shi ne..,
dariya pauzy tayi tana saka bra tace '' to mana ki ɗaga ba abin da zai zarga tunda ba gardawa ya gani ba..,
Kina kuwa da hankali kinsan me kike fadi wanne ba abin da zai zarga kinsan maganar da mutane suke faɗa mai a waje kuwa matar sa tana tara mata bana arziki ba matar sa kaza da yake shi ya aminta dani sai dai ma yazo ya bani labari..
tashi Na'ilah tayi tace '' ni na hakura da wankan nayi a cikin gidan mu, bara na kwashe kayan can da mukayi amfani dasu akwai kwalaban da muka sha da shisha ke sai kije ki ji dashi..,
okay Dan Allah maza ki dauke zan daga wayar sa ,
to tace mata , ta fita ita kuma ta dauki wayar tana cewa my love ina toilet ne kai hakuri ka kirawo bana kusa..,
daga can tana iya jiyo zallar farin cikin da yake ciki yace '' okay ba damuwa fito kofar gida...,
cikin nuna mamaki tace '' na fito kuma me ya faru..?,
honey ki fito mana ki ganewa idanuwanki.
daukan mayafin'ta tayi tace '' to bara na dauko mayafina na fito hice ko ba mazan da suke taruwa yan zaman banza ni wallahi bana son haka , su dinga kallon haramun..,
cikin jindadin riƙe mai amanat sa da tayi yace '' to ai lahira akwai darmar lahira haka kurum ku dinga zama akan hanya
27, July 2025
Maryama
Dan Allah oum yasmeen nayi nayi ya shiga rin na karanta yaki Yi sai book 1 yake ta nuna min