Showing 51001 words to 54000 words out of 76857 words
bayan ta gama ta wanke hannunta kwai ya dauka ta wanke shi ta saka a cikin ruwa.
buɗe fridge tayi ta dauko salad da tomato da onion ta wanke su sannan ta soma yanka su ta ƙara wanke su ta ajiye sannan ya sauke dan wanken ta ta tsame shi sauke kwai tayi ta dauko bowl ta zuba.
da yake taga suna da manja ta zuba ta saka yaji da magi sannan ya kawo wannan salad din nan da ta yanka da su albasa tumatur ta saka sai kwai daukan lemo tayi ta fito dai-dai lokacin jawad da Jawaher suke saukowa sarkafe da hannun juna da alama hirar da suke yi ne dad'i ce jawad sai murmushi yake dauke kai tayi,
tayi kamar bata gansu ba da sauri jawaher tace '' am sorry ganin honey ya mantar dani ban saka an yi miki girki ba shi dai ga nashi can..,
ta faɗa tana shafa gemun jawad...
dan murmushi najlah tayi tace '' lah ba damuwa ko sunyi balallai na iya ci ba saboda girkin na da nasu is different....,
wani abu ne ya tsayawa jawaher a makoshi wato ita da take cin na cooker's bata san darajar kan'ta ba kome..kallon Jawad tayi domin ganin wanne action zai dauka akan ta shi kuwa jawad nunawa yayi be ma san me suke faɗa ba ya wuce a zuciyarsa kuwa cewa yayi ashe bawasa na ajiye a cikin gidana.
najlah ma shiga daki tayi habaka da tayi ba karamin bakantawa jawaher rai yayi ba sun tafi sun barta sai ta ma rasa tsayuwar me take yi a gurin nan juyawa tayi ta hau sama ta fasa ma saukowa har taje ƙarshe taga idan ta fushi kenan ta nuna mata taji haushi da sauri ta sauko tana cewa honey honey wallahi yau ba ƙaramin farin ka sakani ba , bawai dan ka bani gift ba a'a ganin ka da nayi ba karamin jin dad'i nayi ba da farin ciki da na dawo naga baka nan gani nayi gidan nan yayi min baƙi na kasa sukuni ina jin kamar na rasa rabin jiki na raina duk yabi ya ɓaci shi ne fa wata kawar zeey ta shafa face ɗin ka na rotsawa shegiya fuska wallahi duk macen da tayi kuskuren aurar ka koda na wuni ɗaya ne sai ta bakunci lahira Jawad ba Jawaher ne , domin ni kaɗai aka halicce ka...duk wanda zai soka a duniyar nan bayan nice balle wasu mutane da suke nuna maka son karya a face a zuciya ba haka bane son manufa ne da kwaɗayin abin hannun ka..da karfi take fadar haka.
najlah kuwa tabe baki tayi tace '' kaga mahaukaciya kamar abu me kyau kike faɗa kema da kinyi zaman gidan yari...ke kinfi dawanau cin kai wallahi mahaukaciya ai gashi yan sanda sun miki dirar mikiya a cikin gidan ki dan ma yaya ne wallahi da wani namjin ne da tuni ya fasa miki baki ya kora ki gidan ku..
Jawad da ya zuba mata ido har ta karasa so zama tayi akan cinyar sa yace '' sweet me ya sakaki kai haka yanzu fa dole naje gurin su na basu hakuri..,
turo baki tayi tace '' face dinka fa ta shafa..,
to sweet ni ta taɓa..?
kwantar da kan'ta tayi tace '' ina son Ka
* MIJINA* duk ranar da aka wayi gari kai min kishiya mutuwa zanyi bazan iya jurar ganin ka , kana shiga dakin wata ba...,
dan murmushi yayi yace '' kidin ga addu'a idan hakan yana cikin kaddara ta Allah ya yaye miki wannan kishin naki..,
dan turo baki tayi tace '' beb mu dena maganar nan wallahi har naji zuciya ta na wani irin bugu..,
to shikkenan Allah ya kyau..
amin tace tana tashi daga kan cinyar sa abincin sa ta soma zuba mai soma ci yayi kwata kwata abincin be mai dadi ba kallon ta yayi yace '' anya kuwa ba zamu canza cooker's ba wannan abincin be mun ba..,
Najlah da ta fito daga daki ta saki murmushi ta ƙaraso tace '' yaya ga wannan nan na dafa amma kaɗan na iya ci daman cin girkin arna sai wanda yayi niya amma ni sam ba suyi min ba..daga masu yawo da mini skirt sai masu yawo da three quarter kuma a cikin gidan hausawa musulmai tamkar babu kishin addinin Muslunci ba..,
wani abu JAWAHEER ta haɗiya tace '' najlah ya ishe ki haka ya ishe ki Jawad kana kallon ta , tana gasa min magana wannan fa maganar da take yi dani fa take ni bana yiwa na ƙasa dani rashin kunya idan kuwa nakasa dani yayi min komai gatan shi sai na hukunta shi domin wannan ba , tarbiyya bace..,
da sauri jawad ya kalle ta haka ma najlah ran'sa ne ya ɓaci daga wannan maganar kallon JAWAHEER yayi yace '' shut-off....stop don't tell me anything jawaher tarbiyar da aka bawa najlah ita aka bani me najlah ta fadi da har zaki wannan maganar..? eyeee..,
ganin yadda ya zame mata tamkar zaki tsoro ya shigi zuciyar'ta bata , taɓa zaton jawad zai iya yi mata wannan shouting din ba ja da baya tayi ta ruga sama da gudu kuka na shirin subbuce mata tunda sukai aure yau ne kaɗai suka sami matsala har Jawad yake ɗaga mata murya wato najlah annoba ceee..
juyowa gurin najlah yayi da sauri ta ajiye bowl din hannun'ta ta tafi daki da gudu binta yayi zata , rufo kofa ya tare ya shiga durkusawa tayi tana kuka tace '' dan Allah kai hakuri wallahi banyi dan ranta ya ɓaci ba..,
dake nake magana kika sako baki daman kasa kunne kike kiji wacce hira muke yi..? maganar da nayi ba da karfi nayi ta ba amma har kin ji najlah kinsan halina..,
ture dankwalin kan'ta tayi tana kuka tace '' wallahi kawai nazo wucewa naji banyi haka da wata manufa ba kayi hakuri bazan sake ba..zanje ma na bata hakuri amma dan Allah karka dake ni..,
KARUWAN CIKIN GIDA
Ga channel dina kuyi min subscribe Dan Allah wai ina masoya na suke.
https://www.youtube.com/@nasreenminallah
https://vm.tiktok.com/ZSBRtRQmN/
Domin samun update kuyi following dina
Book ¹
EPISODE ¹⁹
ta faɗa tana tashi tsaye takaici ne ya kama shi wai karya dake ta kamar daman can din yana dukan ta.
cikin ɓacin rai yace '' nidai na faɗa miki wallahi karki sake na gara ganin kin ƙara abin da kikai yanzu..,
da sauri ta gyaɗa mai kai cikin daure fuska yace '' ɗazu wanda ya tambaye ki number kin basa ko..?,
da sauri ta girgiza mai kai hawaye nabin kuncin ta tace '' wallahi Allah ban bashi ba..,
wanni kallon kin raina min hankali yayi mata da sauri taja baya tana kuka tace '' Allah da gaske nake..,
juyawa yayi zai fita zama tayi akan gado tana cewa haka kurum kace ba wanda zai kula bayan kana nema kayi min aure..
ashe be tafi ba sai ji tayi yace '' what..,
da sauri ta juyo jikin ta har rawa yake.
tace '' Allah ba abin da nace..,
idon sane ya kaɗa yayi ja lokaci ɗaya ɗaga hannun sa yayi zai mare ta sai kuma ɗunkule hannunsa ya juya, ya fita bece komai ba.
najlah ta , tsorata da taga yanayin sa zama tayi tana dukan bakin ta , tace '' nima wanne tsautsayi ne ya kai ni da faɗar haka bayan nasan ban bayar ba kuma ga yaya da mugun ji uhmm koma mene aishi ya jawo ta faɗa tana kwanciya a kan gado.
jan wayar ta , tayi ta soma charting jin anyi kiran sallah magarib, ta tashi.
tayi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito.
shinfiɗa daduma tayi, ta zura hijabi ta tada sallah.
bayan ta idar ta zauna tana lazumi sosai gidan ya zama tamkar ba kowa ko motsin mutum ɗaya bata ji ba duk da daman ba wata hayaniya take ji ba amma Jawaher tana kunna kida tai tabin waka to yau ba wannan.
dariya tayi da ta , tuna irin faɗan da suka yi ta ci gaba da jan carbinta bayan an tada sallar isha ta tashi tayi sallah tana idarwa ta fito domin hanjin cikin ta ta fara motsi yunwa take ji.
ta koma tare da zuro kan'ta tana kallon hagu da dama domin tana tsoran haduwa da yaya.
ganin jawaher tayi taci uban wasu kananan kaya rigar kwata kwata bata da hannnu iya cibiya ga wando nata ko cinya be rufe mata ba ga wani uban hil da ta saka kai kace irin arnan nan ne na kudu wanda basu san ma mene Musulunci ba.
kanta yaci attachment brown colour ga uban gashin ido kare mata kallo tayi tas ana mamakin anya kuwa matar nan ba mahaukaciya bace kai biri yayi kama da mutum duk yadda aka yi ta taɓa hauka koma yanzu tana cikin sa kallon hannun ta , tayi duk farata kallar kayan da ta saka bayan kuma ɗazu babu shi a hannun'ta kauda kai tayi ta fito tana addu'ar Allah karya haɗa ta da yaya.
keee gaban tane ya faɗi jin sunan da Jawaher ta kira ta , dashi amma sai ta dake ta nuna ma bama tasan tana yi ba.
taci gaba da tafiya cikin ɗaga murya tace '' ke dake fa nake..,
banza tayi mata da sauri jawaher ta , tashi tace '' najlah..,
sai a lokacin ta juyi bata kalle ta ba sai ma kau da kan'ta da tayi tace '' yes..,
da sauri jawaher ta , tofar da chingum din da take ci a ƙasa eh lallai matar nan kan uba tab tace '' tun ɗazu ina kiran ki kin min banza yanzu kuma kince min yes ni sa'ar wasar kice ke yarinyar nan ko sharing miji muke abin da za kiyi min kenan..,
wani kallo najlah tayi mata tace '' kin gama na tafi dan wallahi yunwa nake ji...?,
JAWAD JAWAD JAWAD wallahi sauko sauko bazan iya ba dole ki tattara kayan ki , kibar min cikin gida sai kace wacce muke sharing din miji kike min wannan uwar gadarar to gidana kika zo dole kibi dokata kuma karki sake ki shigar min kitchen tunda ke baki da kunya..
wani kallo najlah tayi mata , tace '' wannan ne kuma baki isa ba tun da ke ba ke kika siyo abincin ba...,
hannu ta ɗaga zata mare ta da sauri ta rike dai-dai shigowar Jawad ashe baya cikin gidan a tare suka juyo tare da sakin hannun juna..
da wani kallo ya bisu na tuhuma ganin haka najlah tace '' yaya sannu da , dawowa hannun aunty ne ga buge na fito ne naji ihun ta..,
da sauri jawaher ta kalle ta , ta shiga uku yarinyar karama ta iya munafurci da kissa kasa magana tayi sai ma sakar baki da tayi tana kallon ta..
shi kuma yace '' okay sannu hice ko baki ji ciwo ba..??
tamkar wata kadangaruwa ta ɗaga mai kai.
good yace ya zagaye su ya huce.
ajiyar zuciya najlah ta sauke tana barin gurin jawaher da ta rasa gaba ki ɗaya abin da ya dace tayiwa yarinyar nan.
shiga kitchen ta dauko madara da zuma ta fito , har yanzu tana inda ta barta da alama mamaki ya kusan kashe ta.
a zuciyar NAJLAH kuwa cewa tayi kaɗan kika gani yar iska me kama da zubin karuwan Lagos..
huce ta , tayi tana dariyar mugunta kasa ƙasa da wani kallo jawaher ta bita da shi sai kuma ta hau sama da dan gudun ta kai tsaye study room din Jawad ta shiga yana zaune ya baza takardu a gaban sa ga computer agaban sa da hannu yayi mata nuna ta fita da alama zoom meeting suke yi domin taji Muryar mutane.
tamkar ta kurma ihu haka ya jawo mai kofa ta rufe.
to ita yanzu ina ta kama ne..?
bata da wata madogara fa hmmm dole tasan abin yi kafin yarinyar nan ta zame mata ciwon idanu..
kar fa wata ran tace tana son Jawad wata zuciyar ta jefo mata wannan maganar a fili tace '' da kuwa wallahi nayi gunduwa gunduwa da ita..,
wayar tace , tayi ringing ganin sunan inna da sauri ta dauka daman bukatar inna take saukowa tayi tana cewa wallahi inna ina cikin matsala ina bukatar temakon ki inna komai ya fara lalacewa, ban san ta ina zan fara ba inna yau Jawad ni ke ɗaga min murya , daman can be kama shi ba yadda muke so amma yanzu yafi da lalacewa inna wayyo Allah na shiga uku inna ga hassimi ya dawo kar fa Jawad ya neme shi suyi magana kwanakin baya , ya yi min maganar sa inna.
ta karashe maganar ta , tana buɗe dakin ta key tayi mai ta rufe ta zauna Inna kuwa dariya ta dinga yi tace '' da kika ce bakya ji..wato jawaher ke kaza ce ci ki goge baki da yaya kika aure she ..? wanne irin fadi tashi ne banyi da ku ba amma duk kunna namin ku ba yan goyo bane wai yanzu takai ta kawo hajiya bilki ni zan ɗaga waya na kirata taki ta daga wato buƙatar ku , ta biya kun mata da inna kun mai da inna juji..,
wallahi inna ba haka bane ba , so nake na siya miki gida ki dawo nan ko na gina miki wani acan kinga kya zuba yan haya kudin ne be hadu ba..
oooh yaushe rabon ki da zuwa *BINYERI* ...? tun fa ranar da aka dauke ki aka kai ki ɗakin Jawad yau shekara nawa sai dai muyi waya kuma nasan kina nan kina halin naki sai ma abin da yayi gama na sani saboda son abin duniyar ki ba zai barki kiyi zaman aure ba.. dan haka turo da dubu dari biyar zan je gurin malam za ayi mai abin da ma zai manta iyayen gidan nashi..
inna yayi yawa wallahi bani da wannan kudin a haɗa a har UMMEE..
cikin faɗa inna tace '' to sai an jima duk randa kika samo kudin kya kira ni..ita kuma wannan ba abin da ta isa tayi na riga da , na dade da gamawa da ita, ke kinga ko kallon banza tana yi miki ballantana baraza..?,
da sauri jawaher tace " a'a dan Allah kiyi hakuri zan turo miki..,'"
wata dariya ta saki tace '' oh sai anjima dan katina yana karewa..,
kit, ta kashe waya kafin ma Jawaher tayi magana dan cije lips din'ta, tayi ita kan'ta tasan dole INNA taci kudi kafin tayi mata aiki amma ba yadda za tayi dole ta ɓatar da koma nawa ne ganin asirin ta ya rufu..
★★★★★★
duk wani magani da , aunty ta bata sha tayi na turaren nan ne kawai ba tayi ba ta yi brush tayi wanka kayan bacci ta saka ta kashe komai ta kwanta tana janyi wayar ta..
wani murmushi ta saki lokacin da taci karo da sakon ya MUNEEF da sauri ta shiga alamun kuka ya saka yana cewa beauty kin barni cikin kewa ko ..? ko iya bacci bana yi..
rungume wayar ta , tayi tare da ɗagowa ashe ma yana online video call ya kira ta.
Sai da kirjinta ya buga sannan ya dauka tuno da fadan yaya tayi MUNEEF yace '' najlah bana ganin ki kunna fitila..,
dan murmushi ta saki tace '' uhmm a'a..,
Saboda me nima bara na kashe ki dena gani na mene amfanin ke kin ganni ni bazan ganki ba gwara kenan na kira ki normal call, na dade da sanin ko shekara nayi ban kira ki ba....ba zaki taɓa nemana ba..,
turo baki tayi tace '' Allah ba haka bane yaya muneef kasan halin yaya shine ke hana ni wai ɓata lokaci ne kwanaki har cewa yayi zai fadawa su jadda aure nake so...ba karatu ba...,
dariya MUNEEF yayi yace "' da kuwa nafi kowa murna kinga sai nazo na dauke ki mu tafi tare mayi karatun tare Allah ya mallaka min ke najlah Allah idan na dawo zan wa ya haidar magana yayi wa yaya ko jadda Insha'Allahu tare dake zan koma..,
dan shiru tayi tana tunani can tace '' ya muneef su nihila zasu yadda...?,
me ya saka kikai min wannan tambayar ina ruwa da abin da ke cikin zuciyar'su wannan su ta shafa Allah ya ganar da su gaskiya..,
Wallahi ina jin tsoro kar tace a'a bata sona ban san dalili ba..
karki damu bame raba mu idan ba ikon Allah ba wanda ba yadda za muyi da shi ina ma neman tsari da shi.
to Allah ya shige mana gaba mana.
cewar najlah.
wani dad'i ne ya shige sa..., yace '' amin ya Allah bye naji kina hamma Allah ya tashe mu lafiya kin dai ki barina, na ganki..,
bye Amin ya Allah tace tana kashe datar ta da wayar baki ɗaya ajiye ta , tayi.
tayi addu'a ta kwanta.
wannan kenan.
honey kayi hakuri idan ma akan fadan ɗazu kake fushi dani..
ta faɗa tana kamo hannun sa.
zare hannunsa yayi yace '' JAWAHEER ban taɓa zaton zaki iya kallon idona ki faɗi haka ba hajiya fa kinsan irin matsayin da Hajiya take dashi a gurina kamata yayi inhar kina yi min son gaskiya ki so duk wani wanda ya shafe ni.. Najlah kuma nayi mata fada tace kiyi hakuri zama ta baki hakuri amma ita ba , tayi haka domin ta ɓata miki rai ba... wallahi inhar kina son zaman lafiya a cikin gidan nan to ki kauda ido akan najlah komai tayi yarinta ce ke babba ce be kamata ace kina biye mata ba...,
wani abu ne ya tokare mata.. zuciya dannewa tayi tace '' to shikkenan Insha'Allahu zan gyara ba komai , wallahi komai ya wuce..,
ta karshe maganar ta , tana kissing din sa biye mata yayi wayar ta ce tayi ringing da sauri ta cika shi ganin wanda ya kira ta shiga uku besan tana da aure bane ya kira ta a wannan lokaci kallon Jawad tayi da gaba ki ɗaya hankalin sa na kanta...
KARUWAN CIKIN GIDA
Ga channel dina kuyi min subscribe Dan Allah wai ina masoya na suke.
https://www.youtube.com/@nasreenminallah
https://vm.tiktok.com/ZSBRtRQmN/
Domin samun update kuyi following dina
Book ¹
EPISODE ²⁰
Sauri tayi ta kashe wayar gaba ki ɗaya tace '' wayyo Allah waya ta , ta mutu ba chaji ni wallahi shaf na manta ban saka ta a chargi ba gashi gobe ina da lecture tun 8:30 clock zan fita wata kila sai yamma zan dawo.
shiru yayi tamkar me nazarin wani abu jikin jawaher ne yayi sanyi
27, July 2025
Maryama
Dan Allah oum yasmeen nayi nayi ya shiga rin na karanta yaki Yi sai book 1 yake ta nuna min