Showing 15001 words to 18000 words out of 21624 words

Chapter 6 - RASHIN SANI Oum yasmeen

29 Jun 2024

2425

rolling da shi ya zame da yake yana da tsantsi kuma ita bata sa komai a ƙanta ba ƙauda kasan gefe yayi ya dauki wayar sa ya fito

Sumy kalli gayan nan ya gaji da haɗuwa jibe shi yawa ango a gaskiya manyan kayan da Dr Giwa yasa sun amshe shi

"Da sauri Sumy da mufeeda da nuratu suka ɗago ban da fanna da taka sufurin tsaki ta ci gaba da nazari akan test ɗin Physics da za suyi ,,

Nuratu tace

Wallahi tunda na shigo makarantar nan na kamu da son bawan Allah nan

Wani ban zan kallo mufeeda Niger tayi mata tace

"Ki ka mato a kansa ku na muto akan sa kinsa tunda naga hirar sa a BBC Wallahi naji na fara son sa shine dalilin zuwa na makarantar nan amma naga kamar hankalin sa baya kan mata to yanxu na haƙura gani anyi baikona amma kinsan da wannan mutumin be ta kura ba ba zan zo karatu ba sai da kuɗin sa a kai na ai Wallahi da ko ta wacce hanya sai na bi na mallake shi ,,

fanna ta dubi mufeeda Niger ganin irin furucin da tayi

Sosai Sumy take dariya harda ruƙe ciki ji akan na miji za suyi faɗa ......


RASHIN SANI


Oum yasmeen


Chapter 72-77


Sosai lailah take bin kowa da kallo domin lamarin na su mufeeda Niger ya fara mata tsoro tace

"Sumy lafiya ke kuma keke dariya ?"

Lallai ba dole inyi dariya ba ganin akan namiji jiyar da mufeeda take tada jijiyoyin huya kuma fa be ma san suna yi ba

Lallai ta ce

Hmmmm hakane Allah ya kyauta

Ameen

Nuratu tace jibi ba karatu saboda ɗaya da December

Lailah tace ni kuma ranar muna da biki su mai sunan uncle mansur (ya imam)

Wannan kenan

Ɗur ƙushe take gaban wani boka dan ba ace malami ba ta share gumin da ya wanke mata fuska tace

"Boka ba yarda za ayi ya aure ƴa'ta ruky domin ni yanxu bana son ya aure amal saboda ba zata bani haɗin kai ba aikin mu ya tafi daidai ,,

Wata iriyar dariya yayi yace

Ai kaf cikin ƴa'yan ki ba wanda zai aura sannan kuma asirin da mukai mai na hana shi aure ya kusan rushewa domin yanzu ya tsaya da ibada sannan mahaifiyar sa a tsaye take akan sa in kika matsa auran kine zai mutu sannan kowa zai san ke wace ce batt ya ɓace

Da sauri ta ta shi lalle kumai yana shirin tonuwa da baya da baya ta fito har ta fito daga dajin ta wahau mota gumi na wanke mata fuska wayar ta ce tayi ƙara ganin sunan ruky yasa ta ɗaga

"Hello hajja we kinji ɗazu naje gidan su Rumaisa ƙawata we ita Giwa zai aura?"

Ruky ina zan sani kin san ba komai Alhaji ke faɗamin ba sai ya gadama yawa nima ba a zuri'ar Giwa nake ba

''okay Kitt ta kashe wayar zuciyar ta na ta fasa ,,

Wannan kenan

Alhaji Dawud wata alfarma nake nema agun ka in zan samu


Da sauri ya dubi abokin kasuwanci nasa yace ina jinka Allah yasa zan iya

Ina so ɗanka ya aure ƴa'ta saboda mahaifiyar ta hankalin ta be kwanta ba karatun nan da take a wani gari sannan wannan yarinyar amana ce aguna tana tare da wasu sirri wanda sai lokaci yayi zaku sani kasan bani na haife ta ba to nida mahaifiyar ta muna tsoran dangin mahaifin ta su ƙwace ta bayan tun tana zanin goyo suka guje ta su kayi wa mahaifiyar ta sakin hulakan ci

Zuba mai ido yayi ya ce


"Zan yi shawara da jadda duk abin da ya ce zai faɗa maka ,,

Sosai ya ji dadin abin da ya ce mai haka taron ya tashi ya kuma hotal ya zauna da yake ya kusan ritaya shiya yanzu ya kama kasuwanci

Wannan kenan

*Giwa mansion House*

Cikin gaggawa aka kira meeting tuni ɗakin taron nasu ya cika barrister sulaiman honourable mansur alhaji Dawud Dr yasir shi kuma Abdullahi pilot ne suna zaune jadda na kan kujera cikin farin ganin ƴa'ƴan nasa yace

Alhmdllh ko yanzu na mutu Wallahi Ubangiji ya game min kumai ba komai ne yasa na tara ku ba anan sai bikin da ya taso mana sanin kanku ne tun shekarun baya na ruguje wannan al'ada na dole ahalin Giwa ba zai auri bare ma to alhmdllh duk da na ruguje ta ta cigaba da tafiya saboda su kansu jikokin nawa suna dai dai ta ƙan su sai dai yanzu wata dama ce ta zo mana tuni ya ƙwashe komai ya faɗa musu sannan yace ya kuke gani ya ɗace mu amshi auran nan ko Aa ni anawa tunanin zamu jefi tsintsu biyu da dutsai ɗaya domin nasa anyi binki can Dr buƙar bulama gana sannan tun danaga fusƙarsa nake tunanin ina na san shi ina ji ajikina jika tace zata dawo cikin ahalinta duba ga labarin da ya bamu inma ba ita bace za muyi kokari muga mun nemota

Tuni kowa ya Amin ce domin maganar mahaifinsu ita ce gaba da komai barin uba kamar jadda da hajiyan daura addu'a sukai na Allah ya ƙara haɗa kansu ya basu zaman lafiya tuni aka tsaida rana jibi za a ɗaura aure kamar ƴarda za ai na su Imam taro ya watsai bayan anci ansha

Wannan kenan

Fanna hutun nan da za ai zamu tafi gida da ke

Duban abie tayi tace

"Abbie da kamar ni za ai biki a gidan su lailai in banje ba bazata ji dadi ba,,

Daughter kiyi haƙuri zan bawa lailah haƙuri ni'matullah zata koma jibi kinga tana so ta ganki haɗo kayan ki

Shiru tayi ta fara haɗa kayan ta da yake lailai ɗazu ta koma gida saboda shagalin bikin da za ai

Ta fito suka ɗauki hanyar Maiduguri kai tsaye ɓangaran ammy ta nufa dan tana tsoran zuwa gun oum nana tana shiga ta rumgume tace

Oyoyo ƴata sannu da dawowa

Farin ciki ne ya bayyana a fuskar ta tace

Ammy na same ku lafiya

Lafiya qalau tawo mushi ga zama be sameni ba tunda lokaci ya ƙure min

Cikin rashin fahimta ta dubi ammy tace

"Lokaci ya ƙure fa kika ce ,,

Cikin ƙauda zan can tace

Ehmn ba ranar Monday zaki koma ba dudu kwana nawa zaki yi mana

Ni'matullah da Nana ne suka shigo

hira suka zauna sunayi tuni ammy ta kira mai gyara jiki zata fara gyara ta yau

Ita dai fanna ganin komai take ba dai dai ba wanne irin gyaran jiki ita daba amarya ba da kƴar ta yarda duk da tasan ammy ba zata cutar da ita ba

Da dare yayi bayan sun gama dinner gabaki ɗayan su har da mami abie ya dubi fanna yace

Daughter kin yarda da ƙaddara kinsan komai nufi ne na Allah yar da ya tsara haka zai kasan ce

Gyeɗa mai kai tayi yawa ƙadangaruwa domin tun safe da taga me gyara jiki gaban ta yake waɗuwa

cikin tausawa yace

Fanna buƙar bulama gana ni mahaifin ki na zaɓa miki miji kuma gobe za 'a ɗaura aure zaki ci gaba da karatun ki a karkashin kulawar mijin ki

Tuni hawaye suka ƙafe mata sai bin kowa take da kallo ganin shiru yayi yawa yasa ammy ta taɓa ta ashe ta suma tuni ta waɗo daga kan kujerar dining ɗin

A ruɗe sukai kan ta

Abbie ne ya ɗauke ta ya nufi ɗakin ta da ita ya dubi su ammy yace

"Kar ku damu ta shiga yar ɗimuwa ne shi yasa ta suma zuwa anjima zata ta shi,,

Allah ya sa ƙar ta ɗaga hankalin ta har wani abu ya same ta

Amee abie yace

allura yayi mata tuni ta ɗinga sakin a jiyar zuciya

Dukan su suka baro ɗakin ban da mami da ita tana gama cin abinci ta koma sha shin ta dayake yau kwanan ammy ne

Wannan kenan

Ranar bata ƙarya tuni abokanan arziƙi da kusoshin gwamnatin da manyan yan siyasa suka cika masallacin da ke cikin Giwa estate ɗaurin aura aka fara inda aka ɗaura na mansur Abdullahi Giwa da amal Yasir Giwa akan sadaki dubu dari da hamsin sai na abdulhamid Abdullahi Giwa da naseerin ☯️ yunus Giwa tuni gu ya ɗauki kabbara sai a ka ɗau shiru sannan anɗaura auran sa'eed Dawud sa'eed Giwa da Fatima bukar bulama gana akan sadaki dubu dari biyu tuni wata juyawa take neman kada shi duk da azaune yake ga shi kuma a sahun gaba ba damar guduwa dan gashi ga jadda duban tsohon yayi

Wani murmushi jadda ya saki yace .........



RASHIN SANI


Oum yasmeen




Chapter 78-80



"Haba ango saki ranka zuwa gobe amaryar ka zata ƙara so,,

Sauri kauda kai Giwa yayi a zuciyar sa kuwa cewa yake tsofaffin nan sun shamma ce shi sun mai ba zata ya haɗa rai yayi kicin kicin da ransa ya tashi zai fita uncle sulaiman yace

"My boy ka tsaya za muyi photo tarihi"

Ba yaso ya musa mai kawe ya zuba musu ido tuni maroƙa suka shiga shela da waƙa 🎶

Cikin gida kuwa kuka aneesa take yar gidan anty zulaihat domin iya so ta nunawa giwa saboda shi taƙi kula kowa yayi da anty zulaihat ta daka mata tsawa tace

"Aneesa kina da hankali kuwa akan namiji kike kuka ƙarki manta namiji mijin mace hudu ne ai tunda suka haɗa baki ya aure bare kema sai ya aure ki ,,

Da sauri hajiyan daura ta kalli ƴar ta ta tace

"Zulaihat ƙar in ƙara jin wannan magana ta bare a baƙin ki sannan tun farko da yana ra'ayin auran ta ai da ya aure ta ,,

Anty Sa'adatu ce tace

"Haba hajiyan daura ki duba fa wannan magana ita wannan ba haɗa su a kai ba gida be ƙo shi ba a kai wa dawa duk nasan munafurcin wannan anty Maryam ne haka fa tabi ta shanye Mahmoud kuma kenan ta gama da ku jibi fa irin son da Ameera take mai amma duk kun rufe idanuwan ku ,,

Ban za hajiyan daura tayi musu ta fita ta basu gu sosai yan matan suka shiga wani hali kowa kan ta take dubawa da na ƴarta yayin da lailah ta shiga ɗimuwa tun jiya take kiran number besty ta ƙi shiga ga yau ta ji wata al'amara mai irin sunan ta ta aure dr giwa komawa tayi ta zauna aneesa ce ta dena kuka da dubi laila tace

"Wallahi in tasan wata bata san wata ba ba zan koma gida ba a nan zan zauna sai na matsawa rayuwar ta na hana su jin dadi ,,

Wani banzan kallo Ameera tayi mata ta ja tsaki domin ita ma abin da take saƙawa a zuciyar ta kenan ba inda zata je tana gidan nan sai taga abin da ya tirewa buzu naɗi

Ruky kuwa ita nata shirin da ban ne domin har su saita haɗa taci uban su sun ƙƴale mata masoyin ta ta aure shi

Cikin shigar alfarma basma da husna suka shigo cikin yan uwan nasu ganin kowa baya wal wala yasa zuka koma ɗan na waya suna yira su da lailah ƙar ɓar wayar lailai sukai suka shiga kallon pic din su ita da fanna sosai suka shiga yaba ƙyan fanna cikin sauri ruky ta ƙarɓi wayar tace

"Lailah zaki bani number ta kin san nifa na fison hurɗa da mata masu kyau da aji yar da ko a cikin ƙawaye na in biki na ya ta shi ba wanda zai raina ƙawaye na ,,

Hmmmm lailah tace ta ƙauda zan can

Wannan kenan

Sosai mutane suka shiga yiwa Giwa murna ana ta ɗauƙar photo sai murmushin ƙarfin hali yake wasu sai tsokanar sa suke wai yayi musu baza ta be sami ƙansa ba sai bayan a zahar kai tsaye sha shin sa ya nufa shi da dr birnin kudu sofa bed ya samu ya ƙwanta ya saki a jiyar zuciya

Yusuf ya ce

"Aboki na dan Allah za ku bani lailah Wallahi ina son ta ,,

Wani banzan kallo yayi mai ya rufe idanunsa yace

"To na mamajo ka rabu dani inji da damuwar da ke damuna kasan sai ɗazu naga alert ɗin kuɗin da abba ya ɗauko a she sadaki ma a kuɗi na suka biya tun da sune suka haɗa auran ai sai suyi min komai ga mom aysha itama ta ɗaukan min maƙudan kuɗaɗe wai zasu yi order kayan laife to Ni ina ruwana tun da su sukaga za su iya ai sai ƙar su taɓa kuɗi na ko,,

Hmmmm Allah ya kyauta a gaskiya kai dan gata ne gobe fa iwar haka kana tare da amaryar ka ka huta shan pills 💊 ko kayiwa kan ka injection

Ta shi zaune yayi domin ya rasa bakin magana gaskiya birnin kudu dan iskane lamba ɗaya wata da bara ce ta waɗo mai yace

"Alhmdllh gwara da ka nunamin ko kai wane domin bazan iya baka lailah ba saboda a she Kai jarababbe ne da ina tunanin faɗawa jadda Allah ya te maki yarinya ,,

Tuni gumi ya wanke birnin kudu yace

Haba my friend yanzu daga magana sai ka juya ta wani abun

Ta shi yayi yace

"Owo maka ni kaga shi gata ɗaki ,,

wayar sa ce tayi ƙara da sauri ya ɗauka ganin sunan Abba yace

Aslm brk da yamma

Yauwa giwa yanzu yan uwan matar ka za suzo yin jerai ka buɗe musu ɗaya ban garan da ke jikin naka da yake gu ɗaya ya ɗauka ya jera kayan sa saboda gun yayi mai yawa daman anyi shi tsarin mace biyu

Ba yarda ya iya yace

"To,, Abba

Yauwa Allah yayi albarka

"Ameen Abba sai sun zo ,,

Okay yanzu ba su tawo ba da yake jirgi za su hau

"To"

Kitt ya kashe wayar duban birnin kudu yayi yace

Kaga wani lamari ko

A Shema ba yar nan ba ce

Allah yasa haka shi yafi alkhairi

Wannan kenan

Wani irin kuka take yi ko wanka yau bata yi ba ta takure a jikin gado tun safe ammy ke lallaɓa ta tayi wanka taƙi

Anty naja ce matar uncle muzabfar yace

"Kin ga fanna taurin kai ba zai kai ki ba yan zuma jere za mu tafi ba zamu dawo ba sai an kawo ki dan haka aikin gama ya riga an gama aure ya ɗauro ,,

Ihu ta ƙara zun du mawa da sauri ya gana ta shi go ƙanwar ammy tace

Wallahi fanna zan ci uban ki bar ganin ke a marya ce zan biki duka zo ki ci kazar nan kuma Wallahi kar inga kin tauna kashin ta

Sanin halin ya gana yasa ta sakko ƙasa domin Wallahi tasan wannan ƙaramin aikin ta ne domin masifafiya ce ta bugawa a jari da

Tana ci tana kuka har ta gama ci ruwan turarai ta haɗa mata ta ce ta shiga ta zauna duban sa tayi taga har tururi yake saboda zafin sa ganin ta ƙara haɗa rai yasa tayi saurin cire kayan ta ta ɗauki towel ta ɗaura wani kuka ta saki.......



RASHIN SANI


By

Oum yasmeen

_________


Chapter 81-86




Ya gana fitowa tayi ta bar ta bayan ta ce mata tayi wanka

A ɓangaran Mani kuwa ba kowa domin ita ba wanda ta gayyata yar uwar ta ma wacce suki uba ɗaya sai jiya ta ji zancan shine ta zo sosai yan zu Inna falmata take Jin kunyar haɗa ido da ita bayan kowa ya san me ta aika ta komai na bikin da ya kura ake yi ita kuwa mami idone nata yau zata raka ni'matullah filin jirgin saboda yau zata koma Turkiyya tun safe ta fita sai yan zu ta dawo hannun ta nuƙi nuƙi da kaya numfashi ta sauke ta dubi ni'matullah tace

''yi sauri ki haɗo kayan ki nan da anjima in Kai ki kinsan yau Abbie baxai Sami damar kai ki ba ,,

Zubawa mahaifiyar ta ido tayi tace

"To, Bara inje gun ya fanna in mata sallama ,,

Banza tayi mata ta ɗauki wayar ta tana charting sallamar ya kura ce yasa ta ɗago ta amsa cikin saƙin fuskan

Gu ta samu ta zauna tace

"Anty kaltum yanzu za mu tafi Kano ko akwai kayan da kika siyawa fanna mu tafi da shi duk da a gaskiya abbien fanna yayi ƙo ƙari domin Company da ya siyi kayan har sun je gidan mu suke jira kin san order yayi mata a Turkiyya da yake suna da reshe a nan har kayan kitchen a can yayi mata ?"

Gir giza kai tayi tace

"Babu ,,

Da sauri ni'matullah ya ɗauko wani kwali a kayan da suka siyo tace

Anty ya kura ga wannan gift ɗi nane ki bata

Murmushin tayi tace

"Mun gode Allah ya ƙara haɗa kan ku ,,

Cikin jin dadi tace

"Ameen ,,

Ɗauka tayi ta fita ganin ta fita yasa mami ta shi ta shiga ɗakin ta ta kwanta ta ƙwantar da nana

Tuni koma ya shirya a ɓangaran mami ya kura ce kawe su anty ya gana da anty naja sai yayar ammy anty bilkisu ita kuma anty Hafsah da Hajara sai gobe za su zo saboda kawo fanna tuni suka hau jirgi cikin ikon Allah suka isa Kano ƙarfe 3:00 kai tsaye Giwa estate suka nufa kowa yaba ƙyan gidan ya ke Musamman shashin Giwa haka sukai jera mata kayan ta

A ɓangaran hajiyan daura tuni ta naɗa anty Amina da Sa'adatu su kai musu abinci cikin dauki na samun dama suka ta shi inda aneesa da Ameera suka roƙe musu kayan abinci saƙar baki sukai da hanci ganin irin uban dukiyar da aka saka mata yawa yar gwamna wani baƙin ciki ne ya kara to kare zuciyar anty Sa'adatu ciki ciki suka gaishe da su

Cikin fara'a da sanin ya kamata suka amsa tare da yi musu sannu da zuwa

Bayan sun gama suka shiga shashin jadda domin kai gara tuni gun ya ɗi ke da jama'a ganin irin yar masu hannu da shuni Giwa ya aura domin ko ganin irin dukiyar da suka zuba ga kayan abinci da na sawa da suka kawo ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login