Showing 12001 words to 15000 words out of 21624 words

Chapter 5 - RASHIN SANI Oum yasmeen

29 Jun 2024

2424



Hajiya ga shi

Miƙa mata

Hannu biyu tasa ta amsa ta tattara sauran zata tafi da sauri kaltum ta tashi hawaye sun cika mata ido a nan ne nasami damar ƙare mata kallo

Wata irin lufaya ce a jikin ta duk ta koɗe wani gun ma ya fashe

Cikin faɗa hajiya salamatu tace

"We ke kaltum yau she zaki hankali ne Wallahi zan faɗawa matar ubanki,,

Jikin ta narawa ta koma ta zauna tace

bazan ƙara ba

muje in nona miki ɗakin ki

To bayan zuwan kaltum gidan mu ita take komai tun idanuwana basa kai kanta har na kamu da wata iriyar soyayyar ta ba ruwan ta magana bata dame ta ba rainon Giwa ya koma hannun ta duk da ƙarancin shekarun ta sosai sukai wata shaƙuwa in jadda ya dawo daga kotu to tana zaune a ɗakin ta har sai gobe da safe waka Hajiya ta faɗa mata

Abu ɗaya ke cikine zuciya shine

Family ɗin giwa basa auran bare musamman ƙabilal barebari saboda kowa yasani buzaye da barebari basa haɗuwa gu ɗaya har yau jadda besan a wacce ƙabila take ba domin inda ya sani to datuni tabar gidan sa ni kuma ba maganar dake haɗa mu da ita inba gaisuwa ba a sannu a hankali na fara janta da soyayya ta duk da na ƙasa hana kai na dena son ta duba da irin halin da zan shiga in Hajiya ta gane

Bayan wata biyar da zuwanta ni kuma na gama karatuna

Ina zaune a floor duk yan uwana sun zo taya ni murna mu tarane a gun mahaifan mu yaya Dawud sai yaya Abdullahi sai anty zulaihat sai anty Amina sai yaya sulaiman sai yaya Yasir sai anty Sa'adatu sai yaya mansur sai ni duk suna da aure ni da yaya mansur ne bamu da shi ko wanne a cikin su auran haɗi akai musu har matan a taron ne jadda ya faɗamin abin da ya kusan sandarar dani a zaune ta ƙarda ya meƙomin da sauri na ƙarɓa ina dubawa admission ne na tafiya America university of United Kingdom duk da son karatun da nake amma Wallahi ina tunanin in tafi inbar kaltum haka na ƙakalo farin cikin dole nayi mai godiya na ta shi na shiga ɗaki na alamar shigowa naji da sauri na ta shi zaune ganin Hajiya

zama tayi cikin damuwa yace

"Bature ina me baka umarni na shawara ba duk abin da kake yi a gidan nan ina kallon ka wanne irin halin kake so ka jefani a gidan nan kasan halin mahaifin ku ka fita a sabgar kaltum ko Wallahi in me da ita gida ,,

Dan Allah Hajiya karki rabani da kaltum

A fusace ta ɗaga hannu ta zabga mai mari tace .....✍🏼


RASHIN SANI


By

Oum yasmeen


Chapter 67-69



"Mahmud kana kuwa tunanin a bin da zai je ya dawo anya kasan me kake yar aiki fa zaka ɗauko min da wanne ido ka keson in kalli mahafinku da al'ummar duniya tun huri Wallahi ka zare ta a ranka ?"

cikin tsananin mamaki ya zubawa mahaifiyar sa idanuwa wanna shine karon farko tun girman sa da tasa hannu ta dake shi bakin sa na rawa yace

"insha'Allah Zan kiyaye "

Ta shi tayi tace

"Wannan kuma ya rage naka ita kuma a yau zata barmin gida dan ban yadda da tuban ka ba "

Ruf da ciki yayi ya rungume pillow wasu siraran hawaye na zuba a idon sa iya sanin da yayiwa Hajiya me tausayi ce da kyautatawa talakawa amma wannan bigeran ta ƙasa tausawa kaltum ba uwa sai uba

Wannan kenan

Washe gari dawo wata kenan daga masallaci naga hajiya salamatu ta zo laɓewa nayi inda naji ashe kai kaltum gida za ai da sauri na fita na tafi maƙotan mu domin bana so in dauki mota ta gane na bisu sallama nayi da abokina shima ban faɗa mai ba inda zani ya bani ina cikin mota har suka fito a hankali nake bin bayan su har muka isa tasha motar maiduguri ta sata ita ce ta ƙarshe tuni a motar dan haka suka fara tafiya har muka isa Maiduguri aka sauke ta awani ƙauye ta ke a cikin Maiduguri da sauri na fito

Bakin ta na rawa tace

"Kai ne?"

cikin farin ciki nace

Ni ne na biyoki ne domin a daura mana aure yau

Ƙasa nayi da kyawawan idanuwa na cikin rawar murya kuka na shirin subɓu ce min nace

"Ya ya Mahmud kama ta yayi muyi haƙuri da juna kaga a dalilin ka na rasa aiki na dan Allah ka koma ƙar ka sani a matsala Wallahi nima iyaye na baza su yar da ba "

Wayo nayi mata nace

Tom shikkenan hau in Kai ki garin ku kin ga wataran nazo muyi zumunci

Batayi musu ba ta hau ta na nuna min hanya wani gaban rushashshan gida muka tsaya fitowa tayi tace

"Na gode sosai Allah ya jikan mahaifa ,,

"Okay to kiyi wa baba magana mu gaisa ko ,,

Kai ta gƴaɗa min tace

Ina zuwa da yake zama dani ta iya hausa sosai shi ga cikin gidan tayi gaban tane ya yanke ya waɗi ganin falmata zaune tana jan carbi ga sauran mata da yan uwa a zaune ganina da sauri Innna falmata ta tashi tace

"Ga tanan ta dawo daga yawan ƙaruwanci sai yanzu ta ga damar dawo wa Wallahi malam da sunan ki ya mutu amma ke anyi a sarar haihuwa ''

Wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo min tuni jiki na ya ɗauki rawa na kasa tan tan ce a duniya nake ko a lahira itafa ta torani aika tau garin kano amma jibi yarda take jifana da mugayan ƙalamai zubewa nayi ban san wake kai na ba

da uncle Bature akai jana'izar mahaifin kaltum

a nan falmata tayi amfani da abin da a ke yiwa masu yawan banza in sun dawo a kore a gari saboda kar su lalata yan baya ta dinga Kuru ruwa tana faɗawa jama'a tuni kowa ya ɗauko maƙaman sa zai kashe ta gani haka liman ya ce a tsaya ga wani yace zai aure ta

Ai kuwa nan aka ɗaura mana aure a take anan na bada abin da ke aljihuna aka ɗaura aure muka tawo iya to zarta kaltum ta gani a garin su mun fito daga Maiduguri na dube ta nace

jibi zan huce America tare dake zamu tafi amma a yanzu zan kama miki hotel ki zauna kafin in faɗawa su hajiya

Hawaye ta goge ta ce kana ganin zasu amshe ni kuwa

insha'Allah zasu ƙarɓe ki a matsayin surukar su

Komawa tayi ta ƙwanta tuni wasu hawaye ke zubowa daga idanun ta zuciyar ta tayi nauyi muna isa Kano na kama mata hotel na kawo mata abinci nace bara in koma gida in anjima zan dawo na miƙa mata waya na nuna mata yadda zatayi amfani da ita ƙarfe hudu dai dai na shiga gida hajiya na samu da anty Maryam a zaune sun zuba ta gume suna gani na suka tashi tsaye

"Bature ina kaje tun safe muke neman ka ?"

hmmmm Wallahi hajiya na tafi gun a bokane na ne na hostel yau za su koma gida

Anty Maryam tace

Amma tsakani da Allah ka kasa faɗa mana ga giwa ma tun safe yake kuka ba kai ba kaltum

"Yana ina ?"

yayi bacci

Okay bara inje ɗakina nayi wanka hajiya dan Allah kisa jadda ya ɓuɗemin account ɗina ina so innaje can in fara kasuwanci

To Allah ya buɗe zan faɗa mai

Cikin murna na shiga ɗaki nayi komai na fito ganin bani da hanyar dubo kaltum yasa na ɗauki waya na kirata bugu ɗaya ta ɗauka tace

"Ka zone ?"

Aa Wallahi ban san me zan cewa da hajiya ba in fito

To shikkenan

Yar yira muka taɓa sannan na kashe

Ina ta kaice maka labari har muka tawo America Ka ba wanda yasan nayi aure wata iri yar rayuwa muka shinfida da kaltum me cike da soyayya da ƙaunar juna har nama sata a makaranta sosai take ɗaukan karatun da ake mata in na dawo da dare muyi na addini hankali be ta shi ɗagawa ba sai da na lura tana da ciki bansan yan uwana ba ko zasu ƙarɓi abin da ta haifa sosai itama ta shiga da muwa haka dai mukai rainon abin mu cikin so da ƙaunar juna ƙwasam sai aka turani Turkiyya wani project nan na tattara na koma can da ita a ƙwai wani Dr buƙar bulama gana shi ya jagoranci tafiyar ta mu sosai wasu hawaye suka zubo a idon sa ya share bakin sa na rawa yace

Mrs haris wanna she ne ma somar rabuwar mu nida kaltum

Muna isa Turkiyya aka bamu wani guri ko wanne ɗalibi ya zauna

Jina yi na knocking da sauri na je na buɗe domin tun safe kaltum bata da lafiya amma taƙi yarda muje asibiti gaba nane ya yanke ya waɗi ganin jadda ya Dawud anty Maryam hajiya yaya sulaiman sun zo min hutu ne

Hanya na basu suka shigo domin kona ƙi kona so yau sai komai ya fasu sosai a fuska ban nuna musu komai ba ita kuma kaltum ta duba fridge na ɗakin ta ba ruwa yasa ta fito floor da sauri hajiya ta tashi da gudu Giwa ya rumgume ta yace

Anty kin tafi ki ka barni ko

Wani irin ta shin hankali su jadda suka shiga kallon tuma jadda yake min

Bakin hajiya na rawa yace

Bature mace ka ajjiye a gidan ka Bature irin sakayyar da zaka yimin sai ta fashe da kuka

Wallahi hajiya wannan mata ta ce a bin da kike zargi ba haka bane daman na ɗauki video na fara nuna musu cikin zafin rai jadda ya wanke Ni da mari yace

Wallahi a yau ɗin nan sai ka saki yarinyar nan domin bazan taɓa yarda bare ya shigo zuri'a ta ba

Tuni na ƙudar kaltum ta tashi ga baki ɗayan mu muka tafi a sibiti Dr buƙar ne ya amshi haihuwar ta iya huya ta shata duk me imani sai ya tausaya mata kuka sosai kaltum kiyi cikin tace

"Dan girman Allah ku tausaya min ko baku ƙarɓeni ba ku amshi yar da na haifa a matsayin jikar ku Giwa uban san yara tuni ya manne mata yana liƙa yarinyar da ta haifa yayi da nikuma hawaye na sunki zuwa sai kukan zuci kallo kowa nake bana fahimtar komai "


Wata iri yar tsawa jadda ya buga min ya miƙomin biro da ta ƙarda yace

"Rubuta mata saki ukku ka bata ,,

Dan Allah kai haƙuri

Duka ya kai wa baki na abin ka da farar fata tuni bakina ya yafe ya fara jini

Ina rubutawa na zube a ƙasa ban san wake akai na ba

Sosai kaltum take kuka ta ruƙo kafar anty Maryam tana miƙo bamata yar tace

Ku dubi Allah ku tausaysmin bani da kowa ko naje garum ba amsa ta za suyi ba in kuka barni da yarinyar da na haifa bansan ya zanyi ba ina zan dosa ko Nigeria ce ko mai dani ƙar ku barni a garin nan

ba wanda ya saurare ta sosai anty Maryam take kuka haka Giwa da ƙƴar aka dauko shi a jikin ta jini ne ya ɓalle mata Ni kuma buɗe ido nayi na ganni a a Kano

Bayan nan nane mi Dr buƙar ance min ya koma garin su iya nema nayi a garin su amma ban same shi ba dana koma aka ce min shi ya ɗauki nauyin kaltum

Bayan na gama karatu na sami aiki a ƙasar Turkiyya aka auramin zainab

Wannan shine labarin kaltum

Hawaye Mrs haris ya goge yace

"Zaka je Maiduguri ko ta koma gidan su,

Naje garun nasu bangane ko ina ba duba da irin sauyin rayuwar da aka samu da ƙyar na gane gidan su amma ba sune a cikin ba wata mata ce ta cemin we ina gadar gidan tayi a hannun mahaifin ta da alama sai da gidan su kai

*Kano ta dabo*

Wani uban ihu Laila ta saki tace

Fanna kinga a she sauran wata daya muyi biki zanje gida

Wallahi lailah kin ɗaga min hankali na zata wani abun ne ya same ki

Uhmm Zama da kene yasa na koyi ihu

Abakin gado ta zauna

Fanna ɗaukan wayar ta tayi ta fara danna wa yau shine ranar ta ta farko data kira mahaifiyar ta bayan barin ta gida wayar na ring Amma ba a ɗauka ba ........✍🏼





RASHIN SANI


By

Oum yasmeen



Chapter 70-71




Ta gumi ta yi ta shiga tunani bata da wata damuwa sai ta mahaifiyar ta ta rasa dalilin da yasa mahaifiyar ta bata so su shaƙu bata shiga sha'anin ta can za a ƙalal kiran tayi bugu ɗaya ammy ta ɗaga cikin farin ciki ta ce

"Aslamu'alaiki "

Cikin kulawa da nuna ƙauna ammy ta amsa mata sallamar ta tace

"Ƴata yakike ya karatu ,,

Alhmdllh ammy ya su Nana

Wallahi lafiya qalau ƴata yi ce ko kina karatu

"Wallahi ammy ina yi "

A jiyar zuciya ta sauke tace

"To,, Allah ya dafa ,

Ameen ammy ko zaki kaiwa oum nana waya ?''

Shiru tayi na ƴan wasu saƙani tace

Bara in Kai Mata Amma in kikaji shiru to tana wani uzuri bata san damuwa

Cikin karaya da lamarin na mahaifiyar ta tace

"To sai anjima,,

Mu jima da yawa a kula sosai fa ban da kula samari ki mai da hankalin ki kan karatun ki har mahaifiyar ki tayi alfahari dake

To ammy na gode zan dage

Ka she wayar tayi ta koma ta kwanta




Maiduguri jahar Borno


Wata kyakkyawar mata ce zaune a kan luxury sofa tana ɗanna waya gawa ta yarinya kyakkyawa ba zata huce shekara goma sha bakwai ba tana kusa da ita da littafi a hannu ta da alama karatu take koya mata na Alqur'ani me girma idarwa sukai ganin abie ya shigo da gudu yar auta nana ta ta so ta rumgume shi ɗaga ta sama yayi yana yi mata wasa

Da sauri buɗurwar ta ta shi ya ce

"Abie sannu da zuwa ,,

Cikin kulawa da soyayyar yaran nasa yace

"Yauwa tunda kin sami sauki jibi zaki koma Turkiyya ki ci gaba da karatunki,,

"To, abie dan Allah bani number ya fanna na tambayi mami tace bata da ita ,,

"Okay kawo in samiki ,,

Miƙo mai wayar tayi ya samata zamin gu yayi ya zauna

Ita kuma mami tun da tayi mai sannu da zuwa bata ƙara cewa komai ba

Abie a wacce makaranta ya fanna take ina so kafin in koma Ni da uncle muzabfar muje mata

"S.D Giwa midwifery and nursing ,,

Tuni kan mami ya shiga juyawa da sauri ta dafe kan ta cikin ta shin hankali tace

"Ni'matullah dauki Nana Ku tafi ɗakin ki ,,

"Mami lafiya naga kin ruƙe kai ?"

Lafiya qalau

Daukan ta tayi suka shiga ɗaki cikin Muryar kuka tace

"Abbie dama makarantar wayan nan azaluman mutanan ka kai ta ?"

Cikin rashin fahimta yace

"Oum nana ban gane me kike nufi ba fahimtar dani ?"

Tuni idanun ta sunyi ja kan hancin ta har ja yake saboda kuka abin ka da farar fata tace



GIWA FAMILY

Giwa family kuma mai sukai

Wani kallo ta watsa mai tace

"Na gwammace wannan yarinyar ta zauna babu karatu da ta zauna tare da ahalin Giwa ta saba da su alhalin a lokacin da muke tsananin buƙatar su amma suka tsallake suka bar mu da badan kai ba da bansan yarda rayuwar mu zata kasan ce ba dan haka a yau ka dawo da ita gida duk ka aurar da ita ga duk wanda ya dace ,,

"Oum nana lafiyar ki qalau kuwa ?"

Ɗur ƙusawa tayi aƙasa ta haɗa hannu wanta biyu tace

"dan girma Allah ka duba irin walal da na sha ka duba maraici na ko a inane Ka aura Mata aure ka temake ni karabata da makarantar nan ,,

Ɗa gota yayi yace

"Kiyi haƙuri ta gama karatun ta sannan kin manta ko waye zai aure ta sai ya bu ƙaci sanin ahalin ta ,,

Kuka take sosai ta ɗago ta kalle shi tace

"Nidai ko wane ka aura Mata inde yana da hali me kyau ,,

Tom shikkenan zan yiwa wani abokin kasuwanci na magana na yarda da halayen sa da na ɗansa shi ya ma yace ya bani gurbin mutum ɗaya a makarantar ta su tunda wahala take ba kowa ke samo ba

Ajiyar zuciya ta sake tace

Nagode sosai

Amma karki manta abin da Ubangiji ya nufa ko ana muzuru ana shawo sai ya faru barinta makarantar ba shine solution ba amma aurar da ita kinyi abu mai kyau domin koni ina tsoron wata ran su amshe ta amma inta na gidan mijinta ta basu isa ba


Wannan kenan



KANO TA DABO



Yau da huri ta tashi domin karatu ya fara ƙankama suna shirye shiryen jarabawa kimono tasa brown colour an mata layi layi da golding colour ta hau kan Fararan uniform ɗin ta tayi rolling da da mayafin rigar tasa glass dinta ta rataya ja ƙarta tace

"Laila ta so mu tafi ko kinsa lecture ɗin 7:00. dai dai ce damu ,,

duban ta Laila tayi tace

"Okay mu tafi ƙar mu makara ,,

Tafiya suke a jere gwanin ban sha'awa alokacin kuma motar Giwa ta shigo cikin school ɗin parking space ya nufa ya ajjiye ta ya fito idanuwan sa ba su sauka a kan kowa ba sai a kan fanna da suke zaune a kujerun da aka tana dar da zaman dalibai su biyar ne a gun da yake kafin su shiga aji suna zama suyi bitar karatu zama da lailai yasa fanna sabawa da ƴan ajinsu suma suna da tarbiyya shi yasa ta sake da su saboda tsabar abin da take ya ɗauke mata hankali bata san ɗan mayafi da tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login