Showing 9001 words to 12000 words out of 21624 words

Chapter 4 - RASHIN SANI Oum yasmeen

29 Jun 2024

2428

zai samo miki wani baby tab lalle da sauranki

Wannan kenan

Mussa'af mussa'af mussa'af Wallahi ka fita a idona wato har zaka iya daukan mota kuyi yar tsaire a makaranta har kuna koƙarin buge dalibai

Dan girman Allah yaya kai haƙuri daga yau na dena

Karma Ka dena Wallahi dedai nake dakai a gidan nan ta shi ka tafi sannan daga yau driver ne zai dinga kai ka yana dauko ka baza ka sake daukar mota ba

"To, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi ,

Banza yayi mai ya dauki lapton ɗinsa ya fara duba saƙon da aka turomai

Washe gari

A sanyaye take komai shirya wa tayi tsab cikin Fararan kaya tas yau kuma hijabin tane pink colour haka ƙafar wando anmai ratsin pink wata hadaddiyar kimono baka tasa an mata adon duwatsu na golding glass dinta tasa ta dauki wayar ta tace

Lailai mu tafi 8:30 zai shigo tara yace inje

"Okay fanna kinyi kyau yau ina barimar ki ne ta faɗa tana danne dariyar da ta taso mata ?"

A fusace tace

" ban sani ba sai kin shaƙeni zan faɗa miki "

Ooo tawo matafiya

Harara ta hurga mata yawa idanunta zaso waɗu ƙasa ta fiya suke jikin nutsuwa

Wow tafida kalli wata hadaddiyar yarinya ita fa nake baka labari kaf makarantar nan ba wanda take kulawa sai wannan kanwar Giwa gaskiya ta haɗu

Boss aini kaga na kasa magana ji na shiga computer lab naji su munnir suna zancan ta anya wannan ba Balarabe ya ce ba kalli shigar ta fa

Tafida kenan ai daga gani ba tambaya sai de sufa basa auran bare

"Kai boss Wallahi ta tafi da imanina,

Ko ina ta huce kowa bin ta yake da kallo

Lecture suka shiga a layin farko ta zauna kafin malamin ya zo ta fara charting a wayar ta ji tayi an dena surutu da sauri ta ɗago wa zata gani zaro ido tayi ganin ya harɗe hannuwansa agirji ya zuba mata ido tuni ta shiga rudani lefi kan lefi cikin rawar murya tace

Sorry sir.....✍🏼




RASHIN SANI


By

Oum yasmeen



Chapter 56-60




Ƙara haɗe fuska yayi yace

Bani wayar ki kuma ki fitar min daga aji doka na sa duk wanda ana lecture ya dan na waya ko yayi surutu fita zai yi amma ke na shigo Bama kisan na shigo ba

Rumtsai idanuwanta tayi ganin kowa yana ganin ta ba ta ƙara cewa komai ba ta tashi jiki a sanyaye ta fita

Gu tasama ta zuba ta gumi wani baƙin ciki ya To kare mata zuciya ta nayi tana duba agogo har lokacin fitar sa yayi bayan ya fito sauran yan aji suka fito fanna

Da sauri ta ɗago ta kalli Laila cikin sanyin murya ta ce

"Na'am Laila ya fito ko ?"

Hmmmm ajiyar zuciya ta sauke tace

"Eh ya fito tashi muje ko "

Okay mu tafi

Fanna kinga mukiyaye duk abin da zai hadamu da Dr Giwa mu yi taka tsantsan

Kai kawe ta ɗaga mata domin bata da bakin magana har suka isa chamber mansion ɗin sa tun daga bakin filin da aka ƙawata da bishiyu aka zube security Laila tace

Sannu da aiki sir

Tsohon yace

"Yauwa ina zaki ?"

gun Dr Giwa shi yace muzo

Okay bara inyawa sakatariyar sa magana

kujerun da aka tana dar a gun suka sami daya daga cikin gabion chairs suka zauna sosai suka shiga damuwa in yace bashi da lokacin ganin su sun shiga ukku

Juyowa yayi ya kalle su yace

Yace ku shiga

Mun gode sai da suka huce e-potal San nan suka iso na shi bugawa sukai

Ta na daga zaune ta basu izinin shigowa

Lailai tace

Sannu da aiki Dr yana ciki

Wani banzan kallo lubna tayi wa fanna zuciyar ta yi wani irin baƙi ko tantama ba tayi wannan ita sir Yusuf birnin kudu yake cewa sun da ce da oga

Wayar ta ta dauka ta fara dan nawa tana taunar chingum jika ke ƙas ƙas tush ta fasa ƙwai

Kallal kallo a ka shiga tsakanin lailah da fanna tuni zuciyar fanna ta sosu domin ta tsani hulaƙanci cikin sanyin nan nata tace

"Baiwar Allah muna magana fa,

Tuni zuciyar lubna ta zu iya huya ta tashi tsaye tace

Kinga Malama da kata mini tunda kuka ga nace ku shigo ai kunsan yana nan

Hararta fanna tayi ta buɗe kofar sa bakin ta dauke da sallama

Be ɗago ba in ma ya amsa to a zuciya ya amsa ci gaba yayi da ɗanna loptop da alama aiki yake samin gu sukai suka zauna cikin rawar murya fanna tace

Itama lailai ta gaishe shi

"Good morning sir"

kan sa a ƙasa yace

''Me ya kawo ki nan ?"

Wane irin baƙin ciki ne ya to kare zuciyar fanna ga wani rainin hankali

Kace inzo kuma ka dinga maganar me ya kawo ni nan ai ba tasan tayi ka tiɓarar zance ba a she a fili ta faɗa da sauri ya ɗago ya cire glass ɗin sa ya zu ba mata ido yayi da lailah gumi ya fara wanke ta domin yau tsiwar fanna ta jaja musu

File ya ɗauko ya ce

"Ke ce Fatima bukar gana ?"

Kai ta ɗaga domin a yaran barebari fanna ta na nufin Fatima

Cikin husky voice ɗin sa yace

"baki da bakin magana ne ?"

ɗan ƙaramin bakin ta ta motsa yawa na jarire yayi pink colour har sheƙi yake tace

"Eh nice "

Kamar zai lumshe idanuwan sa sai kuma ya buɗe su yace

"David yayi test ɗin Chemistry inda ya haɗa ku da yan level two yayi muku ta zaɓen fitda gwanin shekara da muke yi in sababbin ɗalibai sun zo domin mu kara musu ƙarfin gwuiwar karatu,,

eh sir yayi

"Zan sake miki test ɗin domin inga da gasken ki ki kayi ko kuwa sata ki kayi domin doka ce a makarantar nan duk wanda yayi satar amsa ko rarshi za muyi

Wani ta ƙaici ne ya kama ta wato gani yake satar amsa tayi to Allah ne ya bata iƙon kayar da yan level two

"Kin shirya "

Eh na shirya

Ya dubi lailai tace

Ke koma waccan kujerar

Tashi tayi tace

"To sir ,

H.O.D na ko wanne dipertment suka shigo suka zauna harda sir Yusuf birnin kudu

Question paper ya miƙo mata yace

Bisimillah

Amsa tayi ta fara duba wa addu'a take yi cikin ran ta Allah ya te maketa tasa kimono a saman kayan ta da bata san ya zata yi ba mi ƙo mai tayi ta gama

Ƙar ɓar ta ƙardar yayi ya fara duba wa sosai yarinyar ta bashi mamaki a hankali yace

Good girl

matsowa kusa da shi birnin kudu yayi ya ce

"Oga yade ko ka ƙƴa sane ya kanne mai ido ɗaya ?"

Cije lips ɗi sa na ƙasa yayi ya Jefawa birnin kudu wani irin kallo

yace

"Zaku iya ta fiya ,,

Cikin sanyin murya fanna tace

"Sir wayata ,,

Zuciyar sa yaji tayi sanyi ya yafe mata abin da tayi kuma ta sami wani matsayi a zuciyarsa wanda shima be san wanne matsayi bane miƙo mata yayi yace

"Ƙar ki ƙara "

Kai ta ɗaga mai suka fito cikin sauri lubna ta sha gaban su tace

"Wallahi yarinya kikiyaye dan ruwa ba sa'an kwando bane ki fita daga sabgar Dr "

Wani kallon sha sha fanna tayi mata ta huce

Cizon ɗan yatsa tayi ta koma ta dubi kawar ta tace

kinga abin da nake faɗa miki ko da kin barnin na naɗa mata duka yar da ba zata sake kallon office ɗin nan ba

Lubna kina haukane to ita rayuwar duniya siyasa ce ki jawo ta ajiki kiji ko soyayya suke sai kisan ta wanne ɓangare zaki rusa ta faɗa ba naki bane

Hmmmm nabihat ba zaki gane bane Wallahi kullum san Giwa ƙaruwa yake a zuciya ta

Wannan kenan

*Turkiyya Istanbul*

9:30 na dare

Wani dattijo ne ya fito daga wani haɗaddan super market hannun sa ruƙe da jaƙun kuna yana sanye da t shirt fara da wando baƙi yana amsa waya da sauri ya zubar da kayan dake hannu sa ganin wata matashiya akalla zata kai shekara ashirin da biyar tana sanye da bakar abaya hannunta ruƙe da jakar kayan da ta siyo alamun daga super market ɗin ta fito ta buɗe motar ta tashi ga

"da sauri shima ya buɗe motar sa ya shi ga ya fara bin bayan ta ganin ana binta yasa ta ƙara gudun motar ta ,

da sauri yake shara ra gudu idanuwan sa na zubda siraran hawaye tambas in idanuwan sa ba gizo sukai mai ba tambas ita yaga ni wani sha shi na zuciyar sa ya bashi tabbacin ita ce amma me ya kawo ta ƙasar bayan barin ta shekara goma sha takwas

Nima tuni na gyara biro na da taƙar da ta abin mamaki ne dattijo kamar sa yana kuka domin a ƙalla zai yi shekaru arba'in da biyar glass ɗin idanunsa ya cire yayi da ya kifa kansa alan sitiyarin motar sa domin motar da yake bi ta ɓacewa ganin sa kuka yake kamar ransa zai fita ya rasa damar sa

Wayar sace taki ruri alamar shigowar kira ɗago jajayan idanuwan sa yayi ya kalli wayar isham ne tushu ya dauko ya goge fusƙar sa ya daidai ta nutsuwar sa ya ɗaga kiran

Daga can matashi yace

"dinner is ready Abbu muna ta jiran ka ,,

A jiyar zuciya yayi yace

Isham ina kan hanya gani nan zuwa

Okay ya kashe wayar ta fiya yayi me nisa sannan ya isa wani haɗaddan mansion ba wani babba ne amma iya kyau da tsaruwa ya tsaru ya tsaru horn yayi getman ya buɗe mai a jikin get ɗin gida an yi rubutu da golding colour an rubuta Dr Mahmud sa'eed Giwa shiga cikin gidan yayi ya yi parking ya fito da sauri yaran suka rumgume mahaifinsu su muhibbat tace

" welcome back Abbu,

kiss yayi mata a kumatu

Yace

"ina Ummin ku take "

Da sauri miemie tace

Abbu tana ɗaki ta ce mana bata da lafiya

Dau kan ta yayi yace

Kuzo mu shiga ciki binsa sukai kallo ɗaya zakai wa yaran kasan hutu da jin dadi ya zauna musu miemie tana sanye da baby gownt sky blue an mata ado da white flower ƙafar ta sanyi da wani slippers me kyau an raba mata gashin ta gida biyu

Yayin da budurwa da ba zata huce shekara tara ba tana sanye da riga da wando

Wani haɗaddan floor suka shiga wanda ya gaji da haɗuwa ajjiye miemie yayi yace

My mommy na bara in dubu ummin ku

"Okay Abbu I m waiting for you ,

Kai ya jinjina mata bedroom din ummin ya nufa bakin sa dauke da sallama ya shiga tana kwance akan wani luxury bed ta lulluɓa a wani haɗaddan blanket milk colour a hankali wani sassanyan ƙamshi ke ta shi bakin gadon ya zauna cikin kulawa ya dube ta yace

"Ya jikin na ki ?"

Zuba mai ido tayi tuni wasu hawaye suka zubo mata

Sa hannu yayi ya goge mata hawaye yace

"Me ya same ki ?"

Me maƙon ta bashi amsar sa sai tace

"Hmmmm yaya dan girma Allah ka dena neman ta ni baka ga yarda ka koma ba duk kabi ka rame kullum da irin zancan da za'a fada maka ni da ya'yan mu mun isheka rayuwar duniya "

What Please zainab ki bar ɓatawa kanki lokaci neman ta yanzu na fara me isa kika damu kai ki akan abun da bazai yiwu ba ƙar ki ɓata mana zaman lafiyar da muke ciki nida ƴa'ƴa na

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo a kuncin ta tace

"ko dan kaga auran haɗi akai mana shi yasa ka fifita bare akai na ,

Da sauri ya tashi ransa a ɓaci yace

ta soni alokacin da bani da komai ta zaɓi zama dani ta guje ahalinta ta fuskanci ta kura gallazawa a cikin yan uwanta da yaranta ta sadaukar min da farin cikin ta dan haka ƙar ki ƙara kwatan ce da ita

ya fita a ɗakin da sauri ta bishi har ɗakin sa wani haɗaddan hoto ne ya kusan cinye rabi bango da sauri ta sa hannu ta fusgo shi tuni ya bashe ya waɗo ƙasa tana haƙi tace

Dan kaga na ƙƴale ka har a cikin gidana ka samin hotan banza ƙabila

bata ƙarasa ba taji saukar mari tuni idon sa yayi ja abin ka da farar fata fusƙar shi tayi ja yace.........✍🏼



*RASHIN SANI*


By

Oum yasmeen


Chapter 61-66



"Wallahi zainab ki kiyaye ni kinsa nayi miki abin da ba halina bane kamar wani kububuwa ya huce fuuu ya bar ta dafe da kuncin ta ,,

Kamar wata zararriya ta ɗurƙusa a gaban pic ɗin da ya waɗo tace

"Kin zame min matsala nida iyalina wasu zafafan hawaye ne zuka zubo mata da yar dar Allah kin mutu ba zai saƙe ganin ki ba a rayuwa

Wannan kenan

Tamƙar ba abin da ya faru haka suka dinner tare da ƴa' ƴan sa cikin farin ciki da ƙaunar juna knocking bells yaji anyi da sauri ya tashi daman sunyi da abokin sa ɗan ƙasar Algeriya Mrs haris mahir zaizo cikin fara'a ya tarbe shi gaisawa sukai

Cire takalmin sa yayi ya shigo sosai yaran sukai farin cikin gani daddy Fahad barin miemie da Fahad yake abokin ta a school aguje ta rumgume shi cikin harshen Turkiyya tace

"Daddy Fahad ina Fahad yake ?"

Ja mata kumatu yayi yace

"yana gida amma nayi miki alkawari zuwa na gaba da zanyi da shi zan zo "

murna tayi ta sauka ƙasa cikin tarbiyya su isham suka gaishe da daddy Fahad suka bar gun

Favor favor cikin sauri yar aikin nasu ta zo baturiyar Birtaniya ce cikin ladabi ta gaida shi

kitchen ta nufa ta buɗe cabinet ta dauko plate sannan ta buɗe Fridge ta nufa ta dauko cake da lemo ta zuba acikin plate da ta ɗauko cikin ladabi ta ajjiye me matsawa tayi ta basu guri

Mrs haris yakake

Lafiya ƙalau Dr Mahmud

sai da ya bari ya danci cake da lemo sannan ya dube shi yace

"ɗazu na ganta ,,

Cikin sauri ya goge bakin sa yace

"Da gaske "

To inma ba ita bace me kamarta nagani sai yanzu da nake tunani ita wacce na gani yarinya ce amma Wallahi kamar su ɗaya da ita

Hmmmm anya kuwa abokina lamarin nan ba ya fara taɓa kaba dan Allah yau kabani labarin ta

Shiru yayi yau tsawon shekaru goma sha bakwai suna tare ya kama ya faɗa mai labarin sa cikin tsananin damuwa yace

in na baka labarin ta babu komai a ciki sai san zuciya da dana sani da ƙabilan ci bara amfani mahaifina ya nuna ƙarmin ikon da yake da shi a lokacin ya rabani da ita sai yanzu yake dana sani mara amfani

Please yau dan Allah da Manzonsa ka bani labarin ta

Kwallace ta taro a idonsa yace

"A shekara ta 1991 a nan na haɗu da ƙaddara ta

2:30 pm na rana a gajiye na taso daga federal college of education Kai tsaye gida na nufa gudu nake sosai har an isa unguwar jan bulo da a nan muke kafin mu tashi mu koma darmanawa parking mota ta nayi a waje na tora gate ɗin gidan mu wata mata nagani da yara alkalla yaran za sukai su bakwai da wata mata Hajiya salamatu da ke kawo wa Hajiyan daura wato mahaifiyar yar aikin ta tayi aure shine ta ce akwo mata wata

Aa Mahmud kai ne ba magana zaka wo ce ni

Juyowa yayi ganin ta gansa yace

Hajiya salamatu ina yini

Lafiya qalau ya karatu

Alhmdllh

Kaga na zo Hajiyan daura bata nan

Au daman bata dawo ba

Ehwllh

Ƙarar mota mukaji da sauri dukkan mu muka juyo ganin Hajiya ce ta dawo

Fito wa tayi cikin fara'a tace

aa Hajiya salamatu sannun ki

Yauwa Hajiya andawo lafiya

Lafiya qalau tawo mushi ga daga cikin

Hajiya ni zan shiga ɓangaran yaya domin Wallahi na ƙwaso yinwa

Uhmm a cici sai ka dawo

Kai tsaye ya huce ɓangaran anty Maryam wato mahaifiyar giwa

Wani haɗaddan floor suka shiga zama tayi a ƙasa yayin da yaran suka ra ƙuɓe a jikin bango

Hajiyan daura ta tashi ta shiga kitchen ta dauko plate ta ɓuɗe fridge ta dauko ruwa me sanyi da yake lokacin zafi ne da kofi sai ɗan kayan motsa baki ajjiye musu tayi ta ce bisimillah

La hajiya har da ɗaweniya Wallahi da kin bar shi saboda na biya wani gida nan bayan ku

Hijabin cikin ta ta cire tace

Ko yaya ne ko taɓa

"To, hajiya mun gode Allah ya ƙara girma ku ba ku iya gaisuwa ba ne ?"

Cikin rawar murya suka h
Gaishe da Hajiyan daura ban da wata me kama da sadakar yallah ta sadda kanta ƙasa tana wasa da ɗan ya tsunta

Wata uwar tsawa haniya salamatu tace

Keee kaltum uwar ruƙon nake bata koya miki gaisuwa ba

Cikin rawar jiki hausar ta bata fita tace

"Kayi haƙuri ta koyamin ,,

Haba hajiya salamatu be kamata kiyi mata haka ba

da sauri ta juyo tace

Wallahi Bature yaran ne sai da haka

Zuba musu ido hajiyan daura tayi ajiyar zuciya ta sauke tace

Hajiya na zaɓi wacce ta nuna wacce aka kira da kaltum

To to hajiya ba matsala

Amma kin faɗa mata aikin ta sannan bana son ƙazan ta

Wallahi hajiya duk na faɗa musu sai da sukai sati ɗaya a gidana na ƙoya musu abubuwa tuƙunna na kawo miki su ki zaɓa

"Nawa"

Wallahi hajiya bazan faɗaba duk yarda ki kabani dedene

"Okay Mahmud jika ɗaki ka buɗe cabinet ɗin jikin gadona ka buɗe zaka ga kudi ka dauko min,,

To hajiya

Wayar ta ta shiga ɗannawa ɗago wa tayi tace

Na tora miki kuɗin ki ta account ga kuma wanda zaki bawa iyayen ta

To to ina godiya Allah ya ƙara girma da daukaka

Ameen tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login