Showing 108001 words to 111000 words out of 162126 words

Chapter 37 - Abadan complete Hausa Novel

HUGUMA   

21 Jul 2024

29131

ya gama kunyatata,har ga Allah ta dauka da wasa yake ba wankan zaiyi ba ashe shi da gaske yake gaya mata sai qeya ta turo masa
''salon ta zaci wani abun mukayi''
''to haramun ne koma me mukayi din,'yar qauye kawai,ita innan ai ba yarinya bace,tafiyarki kawai zata kalla idan ma wani abu ne ta gane,idan baki wasa ba ma sai na gaya mata munyi wani abun inga ya zakiyi''
tayi imani,kadan daga aikinshi ya kum kunyatata saboda haka kufce ta fice ta hada masa ruwan wankan


yar halak inna kam dauke kanta tayi abunta tana faman jan mero da hira,maryam din ma zama tayi can gefe tayi tsuru tsuru cike da kunya tana son ganin reacting na inna wuri saidai babu abinda ta fahimta don hirarta kawai innar take,kafin ma abdallahn ya fito ta shige daki abunta ta kama wasu sabgogin,sai gun ya rage daga ita sai sister mero(lol)
maryam ta dan dubeta
''wai nikam na tambayeki mana๏ผŸ''
''ina jinki''meron ta fada cikin tsoro tsoron kada ko wani abun maryam din zata yi mata
''bakisan cewa haramun bane shiga guri ba tare da kayiwa masu gurin sallama ba''shiru ta danyi don babu inda ilimin nata yakai,na salla dai ta sameshi baina baina
''ai ina yin sallama,kune bakwa ji da wuri''
''waya gaya miki idan kayi sallama cewa akayi ka cusa kanka kawai,sallama na nufin neman izini,koda kayi sallama addini cewa yayi kada ka shiga sai an baka izini,haka Allah ua fada cikin qur'aninsa mai girma''yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah kada kushiga wami gida da ba naku ba face sai kunyi nemi izini kuma kunyi sallama abisa ahlin gidan,wannan shine yafi alkhairi a gareku ko zaku fadaka,idan baku samu kowa a gidan ba kada ku shiga har sai an baku izinin shigar,idan kuma akace da ku koma to ku koma,wannan shine yafi tsarkakewa a gareku''kin fahimceni naga kina raba ido zancan Allah na karanto miki cikin qur'ani''kai ta gyada mata kawai


sai ta dora''kinga zancan Allah na gaya miki ko๏ผŸso daga yau kada ki sake fado mana daki ba tare da na baki izini ba''sai ta dauke kanta can wani bangaren kamar bata jita ba,ran maryam ya dan sosu mai yarinyar ke nufi
''dake fa nake mero''ta fada cikin dan zafi zafi
''to ai abdullahi ne yaci na shigo ko''
''ba ruwa na na gaya mii daga yau kada ki sake sai na baki izini,ko shi ina iya hanashi shiga,idan kuma baki ji ba ni da ke ne''
sai ta danji tsoro don maryam din bata taba mata magana irin haka ba,a sanyaye tace ''to''

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

''duk abinda ta faru ko baki fada ba bintu na sani ba cikin hayyacinki kike ba,amma ki kwantar da hankakinki duk abinda yq samu bawa da sanin Allah,kuma abinda nakeso da ke,bana son ko kadan ki nunawa nene kinsan wani abu game da abinda ke faruwa din,abu na farko da zamu fara yi shine zamu raba sadaka makarantu makarantu na alarammomi a samu cikin addu'a,koda zamu nemi abdallah ba zamu nemeshi a bayyane ba saboda na tabbata babu wanda yasan halin da yake ciki koda qasa batasan wanne hali yake ciki sabida da ta sani da tuni na tabbatar an baza labarin cikin shafukan jaridu da mujallu,sabida haka yadda Allah ya rufawa al'amarin asiri muma cikin surri zamu ci gaba da bibiyarsa har Allah ya warware mana wanannan daurin gwarmai din,addu'a zaki duqufa yi masa babu dare ba rana domi, addu'ar mahaifiya karbabbiyace kan 'ya'yanta''



''na gode qwarai kawu,Allah ya qara girma ya bar zumunci''
''ameen bintu kamar diya kke a gareni,irin hiyayyar da kika yiwa iyayenki irinta kike mana,hakanan kowa naki ne babu wanda baya morar arziqinki komai dukiyarka kuwa,to don me taqi matsalar ta taso ba zamu shiga ciki ba,abinda nake dak qara jaddada miki shine ko a fuska kada ki nuna mata abinda suka miki ya sakeki,kici gaba da binta ahakan,nayi imani addu'armu Allah bazai wofantar da ita ba''
''na gode kawu''haj bintu ta fada idanunta fal da qwalla zuciyarta kuma cike da taqini da qauna cikin rahamar Allah

๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚

Kamar wani mahaukaci haka ya fado dakin futu futu da shi,tana kwance kan gadon dakin an tallafo bayanta da filo,tun daga ranar da mugu yayi mata wannan dukan bata qara iya yin komai da kanta ba saidai a yi mata,ga baki na magana ga ido ga kunne amma dai qafafun da gangar jikin basa aiki


''yaya,adnan ka samota๏ผŸ''ta tambayeshi cikin zaquwa
tsaki yaja ya zauna a gefanta cike da bala'i yace
''nifa na gaji,wallahi nene na gaji babu inda zan sake komawa,zuwana biyar dajin amma na kasa gane gidan sama ko qasa na nemeshi na rasa,shikenan mu haka zamu qare cikin wahala,wallahi baqin jininki muka debo wallahi,haba da Allah malam hauka ake๏ผŸ''
kwantar da murya tayi tamkar ita ce uwar ma
''haba adnan,zahariyya yar uwarka ce da baka da kamarta fa,ka daure kai kuwa mana da alamu wallahi tana cikin mawuyacin hali na neman taimakonmu''


a fusace ya kalleta kamar mai shirin sharara mata mari
''jaka ce ta yimin gula a ciki๏ผŸidan na koma wanann na zama alade,ke idan na koma ma Allah ya tsinemin,dazu fa ina tsammanin kurace ta tasanmin badan ina cikin mota ba da tuni yanzu na zama dan gari a lahira haka kawai akan wata banzar zahariyya da budurwata ma ta fiye min ita,nafsi nafsi fa kawai nene ehe''ya fada yana miqewa ta bishi da ido


janye janye janyen lokoki ya fara yi mata,da sauri tace da shi
''meye haka adnan,kasan fa na hanaka yimin bincike cikin daki ko๏ผŸ,akwai surrukana da ajjiye ajjiye na fa''wani kallon banza ya juyo yayi mata yana fadin
''dama kin kwantar da hankalinki don yau ranar diban kaso na ne,zan dibi duk abinda nakeso don ma fuskanci wannan tafiyar babu nasara,odan yaso duk ranar da kika samu nasarar kashe abdallahn ki nemo ki sai muci ganimar tare''iya bakin qoqarin hanashi da bakinta tayi amma a abanza,kallon tsiya ma bata isheshi ba balle yasa ran na arziqi,tana kallo ya dinga balle lockers dinta yana kwashe duk wata kadara tata yana hadewa cikin wata 'yar jaka,kaf ya kammala ya tako gabanta yasa hannunshi ya tsinke sarqar gwal da ke wuyanta wanda garin fincikar har biyo shi tayi sabida rashin qarfin jiki,kuka ta fashe da shi
''kada ka yimin haka adanan,nifa mahaifiyarka ce,ni nasha wuya gun haihuwarka na kawoka duniya''dariya ya sheqe da ita
''gaskiha nene kina da mantuwa,kefa kika ce farauta halak ce kuma ba'a barin ruwan gangare ace sai an dawo za'a diba,wanda ya samu dama ya dama,duk inda ka hadu da arziqi kayi qoqarin yagar rabonka don yanzu duniya sai kana da shi ake yi da kai duk fa hudubarki ce wanann,to kawai yau daya don ta dan ratsa da ke zaki hau raki,ai dama malami yanason ya koyawa dalibinsa karatu yaga yana aiki da shi pratically



''To banga abun damuwa ba don nayi aiki da hudubarki,kyan da dama.....ya gaji uwarsa,sai haduwa ta gaba nene''
ya fada yana shirin barin dakin
''wallhi adnan idan ka sake ka tafi min da dukiya sai na tsine maka albarka,butulcin da zaka yimin kenan matsouaciyacin yaro๏ผŸ''dariya ya sheqe da ita kana yace
''kin dade baki tsinemin ba nene,kinga idan ma kinso a sama miki lasifiqa a abaki duro ki hau kiyita gayawa duniya kin tsinewa adnan damuwarki ce,nidai na debe kasona don na gaji da gafara sa banqo qaho ba,idan na gurin abdallah ya samu kya iya kirana muci tare,byeeee''ya fada yana daga mata hannu tare da sake rungume jakar da ya lodawa duk wata kadara ta nenen yana fucewa adakin
ihun barawo take ta faman zabga masa saidai a banza don babu kowa cikin gidan idan ba security dake bakin aikinsu ba,su kuwa sunsan babu kowa cikin gidan daga ita sai danta don haka basu kulaa ba domin suna tsammanin ciwonta ne ya tashi wanda dukkansu sun dauka ciwon hauka ne ya sameta


hakanan ta qaraci ihunta ta fashe da kuka mai cin rai tana tsinewa adnan mummunan tsinuwa a haka zubaida ta tadda ra,koda ta gama mata bayani dogon numfashi ta ja tana fadin
''tabdijan,nice zan tashi a tutar babu,wannan wace iriyar magana ce ma mara dadin ji,to wallahi bazan zauna da kyau na da komai ba rayuwa ta ta qare a tantal bataiti ba,a banza wancan tsinannen mai qirar sanudawa yazo yayi awon gaba da ni ko ya kasheni,gwara tun yanzu na samawa kaina mafita,zuwa zanyi na cire cikin nan na shiga sabuwar rayuwa,ga masoya ina sa su masu yawan gaske masu kudi na gani a fada,gwara naje wlh na yagi rabona nima na kafa kaina''tana gama fadar haka ta haura gadon ta fara cire dan kunnen gwal dake kunnen nenen mai hade da banguls da zobensu wanda ta tabbata adnan bai kula da su bane,domin da ya kula da su babu abinda zai hanashi yin hauzi da su kamar yadda yayi da wadancan


''au kema zubaida haka zakiyi min,ashe dukkanku matsiyata ne,yayana na cikina babu mai tausayi na kune masu rusani๏ผŸ'''tsayawa tayi cak tana kallonta
''tab lallai ma nene,ke don Allah baki ji kunyar kanki ba๏ผŸadnan ma yayi miki haka ballanta na ni๏ผŸ''
''yanzu don adnan ya yimin haka kema sai ki biye masa๏ผŸ''
''hmmm,sai kuma kiyi,ina ga kin dade baki bata yawun bakinki ba,ai tunda kika ahiga tsakani na da abdallah kika min asirin da aka ciren sonsa to wlh babu ni babu aure,rayuwar bariki ta fiyemin inda zan zuba jarin jikina na samu kudi''tana fadan haka tana sabule da lalube duk wani abu da yayi saura wanda adnan bai kai ga daukewa ba,cikin haka tayi katari da takardar wani gida ta dauke abinta,tana jin nenen na qwala mata kira har ta koma rsine mata itama amma kallon arziqi bata iaheta ba tayi gaba abinta,don ta riga ta sani uwar tasu ba imani gareta don me ita zataji tausayinta kuma๏ผŸ,ai raba arne da makami ibada ne


A ranar bata bari ta kwanan ba ta hada ya nata ya nata ta nufi gidan wata aminiyarta da ta jima tana mata hudubar shaidan kan cewa ta mori kyanta wlh ta qyale wani abdallah ta tsaya ta nace masa yana wulaqantata bayan ga samari nan da alhazawa na sonta ido rufe

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

Duka hidimar ranar ita ta karbeta don inna wuro da abdallah na gurin tsoho alhaji wanda ya sauka qasa nijeria da misalin sha biyu na rana,tayi mamakin ganin hisham shima ya iso a ranar
''ina sane da ranar dawowar tsoho alhaji a lissafe nake maryam,abdallah na raina da shi nake kwana da shi nake tashi ko yaushe''qwarai ta gasgata hakan tunda gashi taga zahiri


Gidan kusan a cike yake da yan sannu da zuwa wanda basu samu sararawar mutanen ba sai bayan sallar la'asar


Tsoho alhaji wanda asalin sunanshi muhammdu dattijo ne mai cikar kamala da nutsuwa,dattijo ne da ya amsa sunan dattijo bawai muna dattijo ba,dattijo ne da kallo daya zaka masa kwarjininsa ya cika maka idanu,yadda matarsa inna wuro(fatima)ke da kirki haka shima yake


Murmushi ya saki har ya dan fidda sauti bayan ya kammal jin dukkan wasu bayanai daga bakin maryam da abdallah hisham harma da inna wuro daga dan abinda ta sani
''in sha Allahu da izinin Allah indai sammun ne bi'iznillah na bada gaskiya ga Allag nan da kwanki bakwai zaka miqe abdullahi ka taka qafafunka komai yazo qarshe,zan yabaki miki maryam kinyi namijin qoqari qwarai da gaske tunda wuro ta gayamin ba haka kuka zo ba,kamar yadda naji bayanai daga bakinki,na abubuwan da kika dinga nasa amfani da su,ayoyo yine masu kyau matuqa da gaske,gakanna masu tasiri qwarai da gaske wajen ruguza sihiri ko wanne iri ne bi'iznillahi ta'ala,yanzu akwai wasu magunguna da saiwayoyi da Allah ya horemin saninsu,yau basai gobe ba zan fara hadasu guri guda insha Allahu baka wuce kwana bakwai ka warke abdullahi kaci gaba da haquri wannan wata jarrabawa ce Allah ya maka don ya gani shin zaka gode masa ne ko zaka butulce masa๏ผŸ,a baya ya maka duk wata ni'ima ta dukiya kyau ilimi nasaba da gata a yanzu ya amshe abinsa yayi ne duka don ya jarabci imaninka,to alhamdulillah bisa dukkan alamu ka karbi duk wata jarrabawa daga gareshi kuma ina maka kyakkyawan fatan samun cikakken lada''


cike da girmamawa ya duqar da kansa
''na gode qwarai da gaske alhaji,Allah ya qara girma,Allah ya qara lafiya da nisan kwana mai amfani''
haka hisham da maryam suka bi sahun tayashi godiya ga dattijon


Ya dubi inna wuro
''muje ki tayani duba kayan nan,don na san yanzu kin canza musu guri''bata ce komai ba ta miqe tabi bayansa
hannun hisham abdallah ya kama ya riqe
''ka taya ni murna abokina na kusa angwancewa''
dan satar kallon maryam yayi
''mtswee,har yau abdallah baka da kunya,ni kake wa irin wannan maganar๏ผŸ''
ya dubeshi a hagunce
''to akan me bazan maka ba๏ผŸ,rashin aure fa nasifa ne abokina ban sani ba sai yanzu''cikin rashin fahimta yake dubanshi
''like how,kana da mata kana kiran rashin aure a kanka๏ผŸ''
''neman wani auren nake cikin garin nan hisham na wata 'yar fulani''
wani irin kallo hisham din yake masa
''kanka daya kuwa abdallah๏ผŸ,kana da mata kake cewa wani auren kake nema๏ผŸ''
''tunda anqi ka meye na cusa kai hisham don Allah fa,matar tace bata yi zaka mata dole ne๏ผŸ''ya fada qwayar idanunshi na sauya kala,da alamu abinda yake fada din na taba zuciyarshi
''kuma a shekaru na bazan iya zama babu mace ba,kai ka sani da din ma rakawa kawai akeyi''
duk da maganar ta taba hisham yaji wani iri amma maganar abdallahn ta qarshe taso bashi dariya kafin yace komai mero ta kwada sallama bakin qofar dakin wanda duka wunin yau bata shigo gidan ba sai yanzu
''yauwa shigo ga abokina zaku gaisa''inji abdallah yana duban hisham din


jin haka yasa ta dago labulan ta shigo kanta a qas alamun kunya,gefe ta rabe ta gaidasu su duka banda maryam da da qyar ta iya amsaqa can qasab maqoshi,kasa sakewa meron tayi ta miqe zata fita abdallan ya tambayeta ina zuwa tace zata yiwa tsoho alhaji ne barka da dawowa
''idan kin masan ki dawo ina son ganinki''inji shi ta gyada kana ta fice hisham ya bita da kallo,sai da ta fice din baki daya kana ya dawo da kallonsa kan abdallah
''wannan kuma wace ce,yar fillo haka''murmushi ya saka irin mai hade nishadin nan yace
''daina saurin yabawa,itace wadda nake gaya maka ina neman aurenta a qauyen nan''


Wata guduma maryam taji ta sauka kan qirjinya,kanta da gangar jikinta sukayi mata nauyi gaba daya,a hankali ta soma fusgar numfashinya yana son qwace mata,sai ta miqe sama sama tana jiyo sa in sarsu shi da hisham,ganin tana niyyar fita ya sanya hisham kiranta,shi din ma sama sama take jin muryarshi don haka bata bi ta kansa ba ta lalubi hanya ta fice,ba kowa tsakar gidan kai tsaye dakin inna wuro ta shige,gadonta irin na qauye ne da ake kira gadon bunu mai rumfar shi ta haye,can qurya ta takure kanta tana jin wani abu na mata yawo cikin zuciyarta kuka take so tayi ko zata ji sanyi cikin zuciyarta,shin wannan shine kishin๏ผŸ,da gaske kishin abdallah take๏ผŸsune tambayoyin data ringa jefawa kanta ta kuma takurawa kan nata sai ta fidda amsarsu




*mrs muhammad ce*๐Ÿ‘‘


๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ *ABADAN*๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐Ÿ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–
ยฉ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ’ก
*_home of expert and perfect writers_*


โ–ถ5โƒฃ3โƒฃ




*_Daga Abu hurairah Allah ya qara ya yarda shi yace:Manzan Allah S A W bai taba aibata wani abinci ba ko kadan,idan ya burgeshi(abincin)sai yaci,idan bai masa(bai kwanta masa ba ko ba cimarsa bace)sai ya barshi (ba tare da ya aibata shi ba ko ya wulaqanta shi ba)_*


*ina kuke 'yan*

*huguma conversation and novels room*

*maman aysha hausa novels group*

*haske writers asso*

*DA*

*Z.B.I*

*_bazan gaji da sadaukar muku da shafuka na ba,ina yabawa qwarai da qaunarku gareni,ina roqon Allah ya tashe mu qarqashin inuwarsa ranar gobe qiyama,ya bar mu tare bisa soyayya ta domin Allah_*๐Ÿ™๐Ÿฝ๐Ÿ™๐Ÿฝ





Sake lafewa tayi kan gadon inna wuron tana matse idanunta don fidda hawayen dake maqale cikinsu
tun tana jiyo maganganun mutane masu ahigowa jifa jifa yiwa tsoho alhaji barka da dawowa har jin nata ya dayke baki daya,wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita

********

Qaton fili ne dake malale da koiyar ciyawa wadda ake kira da grass carfet jifa jifa kuma jajayen furanni ne ke dashe ta tsakanin ciyawar



Iska mai dadi ke kada fingilar rigar dake jikinta wadda bata da nauyi ko kadan sai santsi,kamar yadda gashin kanta keta yawo tsakanin kafadarta da fuskarta,dauke take da faranti fari qal wanda akanshi kofuna ne fuda uku da jug tsakiyarsa wanda cike yake da madarar shanu,a hankaki take tafiya yana daga nesa cikin fararen kaya hannayensa harde a qirjinsa,dukkan wani hankali nashi da tunaninshi yana a akanta ne,kyakkyawan murmushinsa kadai ya sata mance a ina rake har ta qaraso gareshi,hannu yasa ya karbe farantin ya ajjiye a tsakiyarsu kana ya riqo hannunta
''maryama''
''na'am''ta amsa masa kanta a qasa
''maryam ki kalleni tun kafin na zauce''
ya fada qasa qasa yadda dagashi sai ita kadai zasu iya jin abinda yake fada,babu musu ta daga kanta idanunsu suka mannu da juna,kallon juna suka shiga yi babu qaqqautawa tamkar zasu hadiye junansu,kowanne na ganin zallar qauna qarar cikin idanun dan uwanshi


Shi yafara bude bakinsa
''maryam,kinsan yadda nakeji game da ke cikin zuciyata kuwa''ya fada yana tura hannunta cikin qirjinsa bayan ya balle maballan rigarsa,take tafin hannunta ya mannu da fatar qirjinsa dake cike da gashi
''kina iya jiyo bugun zuciyata a haka๏ผŸ''kai ta gyada masa tana murmushi don tana jin yadda zuciyar tasa kera fat fat fat da sauri
kai ya girgiza
''abinda kika ji yanzu baikai kaso daya cikin dari na yadda nakeji cikin zuciyata game da ke ba,idan da zan iya zuciyar zan ciro miki dungurun gun na ajjiye miki ita wata qila kya iya ganin kaso hamasin cikin darin abinda nake gaya miki,ragowar hamsin din sai ni da Allah''


qayataccen murmushi ta sakar masa tana sadda kanta qasa,da sauri yace
''dago ki kalleni da kyau maryamu na,kallon da kike min kawai na rage radadin da nake ji''bata musa din ba ta dago taci gaba da kallon nashi fuskarta dauke da murmushi
ya matso kusa da ita har suna gwaren numfashi
''i love d look in ur eyes maryam''murmushi ta kuma yi tana dan kawar da idanunta
''i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login