Showing 78001 words to 81000 words out of 162126 words

Chapter 27 - Abadan complete Hausa Novel

HUGUMA   

21 Jul 2024

29123

na gani a mafarki,a rayuwa babu dole a lokacin da ka roqa Allah ya baka a take,yana iya jinkirta maka gwargwadon yadda yaso,kuyi haquri kuci gaba da bin littafin a duk yadda yazo muku don mu samu cimma manufofi da alfanu da gaci da nake son kaiku,idan kuma abun na damunka ๐Ÿ˜‚,a shawarce ka tara littafin har sai an wuce inda baka son ji sai ka ci gaba da karatunka hankali kwance,na gode matuqa da gaske don nasan duka qauna ce,nima ina qaunarku a duk inda kuke,MRS MUHAMMAD DINKU CE*๐Ÿ‘‘

Ji yake tamkar ya kashe adnan,bai kuma jin ciwon lalurar data sameshi ba irin yau,saboda ya riga da yayi amanna dukkan wani abu da zaya samu bawa da sanin ubangijinsa,hakanan bazai jarrabceka ba tare da wata manufa da take alkhairi ce a tattare da kai
bai gaza ba ci gaba yayi da ambaton sunan Allah cike da neman agaji don yana jin cikin zuciya da gangar jikinsa matuqar wani abu ya faru da maryam mutuwa zaiyi

a gigice ta sake dawowa jikin abdallan ta maqale shi tana neman agaji ta cukuikuye jikinta ta dunqule guri guda,tsabar gigita ta mance da halin da abdallan yake ciki,cikin dariyar mugunta ya biyota,ya tsaua a gabansu dukkansu ya qare musu kallo kana yace
''kin daga hannu kin mare ni ga zatonki kin ci bulus๏ผŸ,bakisan dama na jima ina sha'awarki ba hanyar kawar da ita kawai nake nema๏ผŸ,sai gashi yau Allah ya ara min dama ta yaya zan yi sake ta kufcemin''
ya kalli abdallah da idanunshi suka kada suka koma jazur,dukkan wata jijiya ta kanshi ta gama fitowa rada rada
''hmmm,sarkin zuciya,ka qaraci quncin zuciyarka amma babu abinda zaka iya yau sai na cika buri na''ya sake yin kanta gadan gadan,ya miqa hannu da niyyar damqota
cikin qaraji da kuka mai quna tace
''kaji tsoron Allah,yana kallonka,yana kallin duka abinda kake aikatawa''

ga tarin mamakinta sai taga ya qyalqyale da dariya
''ki bari idan na kammala sai ki gaya min duk abinda kike son gayamin,amma a yanzu babu abinda nake ganewa kinji ko''
ya sake yunqura zai fincikota yayib da take sake lacewa jikin abdallah kamar zata koma cikinsa
cikin hikima ta ubangiji hannun sa bai qarasa kanta ba yaji saukar wani abu mai azaba a qeyarshi,ga mamakinsa ya juya don yaga wanda ya masa wannan aika aika,abdallah ne yana daga kwance yaji tamkar an kakkatse duk wani abu daya hana hannayenshi biyun motsi,cikin hikimar Allah ya bashi sa'ar janyo plate din tangaran da maryam ta zuba abinci dazu Allah ya sa mata mantuwa bata dauke shi ba,don bata barin kwano ko daya ba'a muhallinsa ba ko ba'a wanke ba

sai kuma ya juyo yayo kan abdallah,saidai ina tuni jini ya fara dibarsa ya sona tangal tangal,ganin gaka ya sa maryan saurin maida hijabinta,qofa taje ta bude ta dakin kana ta dawo ta dinga tura adnan da ragowar qarfinta tana hankadashi yana dawowa amma da yake jini yaci qarfin sa sai ta samu nasarar tunkudashi har qasan benan yana qoqarin biyota ta dawo benan a guje ta datse qofar falon kana ta shige bedroom din ma ta saka muqulli tana maida numfashi

babu abinda qirjinta yake sai dagawa sama da qasa kamar numfashinta zai dauke,har yazu tsoron bai saketa ba,ji take kamar adnan din zai dawo,hannu ta ga abdallah na dago mata da alamun ta taho,mafaka take nema ibda zata sanya kanta taji sanyi,inda zata sanya fuskarta tayi kuka,babu musa ta isa gadon cikin sassarfa ta hada jikinsa da nata,cusa kanta tayi cikin qirjinsa wani kuka ya qwace mata

shafa kanta kawai abdallah yake yana hadiyar zuciya,godiya yake ma Allah maras adadi da ya bashi damar tserar da mutuncin iyalinshi,maryam ta riga da ta zama jinin jikinshi,sukan qirjinshi kukanta yake,saidai babu bakin hanawan babu kuma cikakkiyar lafiyar rarrashi,a hankali ta dinga jin nutsuwarta na dawowa,ta dinga sauke ajiyar zuciya kadan kadan
hannun abdallah ta tuna taga yana motsi dazun,a hankali ta zagaya hannunta ta saman cikinsa ta laluba dayan hannun abdallahn,tafin hannunta ta zura cikin nasa ga mamakinta sai taji ya sanya yatsunsa cikin nata ya hade hannayan nasu gam,wata sassanyar ajiyar zuciya ta saki
''alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus saalihaat''ta fada cikin zuciyarta tare da rufe idanunta,wani farinciki taji yana ratsata,atleast tasan cewa wani ci gaba ya fara samuwa game da lafiyar abdallahn
dukkaninsu a daren babu wanda ya iya runtsawa,zuciyoyinsu tamkar anyi gobara kada ma abdallah yaji labari,ita kam takan samu sassauci kadan duk yayin data motsa yatsunta dake cikin nasa wanda yaqi sakinsu taji nashi hannun ya motsa

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

zaune yake gabanta qasan carfet din dakin kansa nannade da farin bandeji,zahariyya na agefansa saman kujera nene na kusa da ita ta zubawa danan ido
''adnan,wanne irin mahaukacin yaro ne wai akau,sau nawa ina gaya maka ka fita hanyar yarinyar akwai lokaci ka bafi idan yazo sai kayi duk abinda kake buqata๏ผŸ,yanzun inda ta samu dama kasheka fa zatqyi๏ผŸ,baka lura da irkn yadda take mana wani irin kallo ne,dukkan zarginta ina mai tabbatar maka ita da abdallan a kanmy yake don babu bakin magana ne''

cikin fushi ya dago ya dubi nene
''to wai nene ke wanne mataki kika dauka yanzu,na rantse da Allah ba za'a zubar min da jini a banza ba''wani shu'umin murmushi ta saki
''ni yanzu duk wani mataki nawa nafison abdullahi ya wuce tukun shine babbar matsalarmu,yaron ne shegen taurin ran tsiya kamar kyankyaso.....amma yanzun bamu da nutsuwar da zamu tattauna wanna batu ku tashi kuje jibi zamu zauna,na kira malam na hayi yace baya nan sai jibi zan kira shi naji mataki na gaba,zan sanar da bintu abinda yarinyar tayi don bani da burin da ya wuce ta sata ta bar gidan saidai abun mamaki duk irin aikina bata kudina da nake taqi sallamarta hakanan ko ma samu sauqin tafiyar da aikin....''

itakam zahariyya ma kasa cewa komai tayi
''amma fa nene,naga hannun abdallah ya dawo aiki''ya fada yana kallon nene,da sauri zahariyya ta tashi zaune daga kashingidar da adazu tayi tana kallon fuskar nenen tana zazzare idanu
wani murmushin ta kuma saki tana girgiza qafa
''ko duka jikin abdallah ne ya dawo aiki wanna karon naci alwashin abdallah bazai qara sati guda araye ba,don nima......''
tilas suka katse maganar kowa ya watse sakamakon shigowar zubaida dakin
nenen ta bita da kallon mamaki don tayi zaton ciwon ABDALLAH zai sata a wani hali sai ta lura ma sam tunda ya fara cutar ko hanyar part din bata yi,hankalinta kwance kamar bata da wata damuwa da shi,hakan ba qaramin dadi ya yiwa nenen ba

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

Su uku ne cikin bedroom din,hisham da abdallah sai maryam dake zaune kan ressing chair data janyota bakin gadon inda abdallah da hisham ke kai hisham na bawa abdallan kunun gyada bayan masa wanka da canza kaya da aka masa ckkin baqin t shirt da trouser da suka sake haska shi

farinciki ne fal zicjyar hisham sakamakon ci gaban motsa hannun da abdallah ke iyayi yanzun,yana bashi kunun suna hirar da maryam duk da nata bai wuce eh ko a'a,ba gwanar magana bace ama sanann bugu da qari kallon da abdallan keta tsareta da shi ke dada takura ta,wani kallo ya koya daga wayewar gari zuwa yanzun,duk wani motsinta na kan idanunshi,lafiyarta yakeson ji amma babu bakin tambaya
''kai man,irin wannan kallo haka ko na baku guri ne๏ผŸ''inji hisham yace da abdallah cikin zolaya,kallonshi kawai abdallan yayi ya saki murmushi,duk sai suka zuba masa ido don tunda ya fara ciwon wannna ne karon farko da suka ga murmushi kan fuskarshi

cikin dariya hisham yace
''kai mutumina,anya daren jiya ba soyayya aka sha ba kuwa๏ผŸ''kunya ta kama maryam ta duqar da kanta ,yayin da abdallah ya sake wani murmushin yana duban fiskar hisham bisa dukkan alamu akwai abinda yake son fada wanda ya kasa fada
''Allah ya baka lafiya abdallah''inji hisham yana dafa kafadanshi,ya dubi maryam
''me kikace dazu yana buqata๏ผŸ''
kanta na sunkuye tace
''shaving za'a masa,naga kanshi yayi suma da yawa''
ya dan duba agogonshi ''eh gaskiya ya kamata,bari na masa na kai ke sqi kiyi masa na fuskanshi''
''ai ban iya ba''
''eh,ya kamata ki koya madam,zan nuna miki,akwai meeting da zamu shigavda ma'aikatan kamfanin suger na abdallah,don ina tsammanin gwara kawai a rufe kamfanin har zuwa lokacin da zai samu alfiya,saboda barnar da ake cikin kamfanin tayi yawa''

''Allah ya taimaka'' ta ce bayan ta miqevta dauko masa kayan askin,ya kammala kana ya nuna mata yadda zata masa na fuskar ya musu sallama ya wuce ta bishi da godiya

gefanshi ta dawo ta zauna ta fara matso cream din,a hankali take shafa masa a gefe da gefan fuskarshi,idanunahi qyar cikin nata,nauyi takeji da kunyarsa duk lokacin da ya zuba mata idanunshi,a hankali ta janye qwayar idonta tana ci gaba da shafa masa din,ta kammala ta dauko shever ta fara masa askin,ajiyar zuciyan da ya saki ya sata saurin kallonshi cikin tsoro,cikin sassanyar muryarta tace
''ko na yanke ka๏ผŸ''murmushi ya mata ba tare da ya nuna alamun a'a ba,kusan sakanni uku sannan taci gaba,a hankali taji ya riqe hannun nata da take shaving di dashi,ta sake waiwayo ta kalleshi shima din ita yake kallo
ta langabe kai
''da zafi ko๏ผŸ,dama na ce masa ban iya ba.....''bata qarasa ba taji ta kan qirjinsa sakamkon janyota da yayi ya rungumeta tsam

dukan uku uku qirjinta ya shiga yi,tayi yunqurin tashi taji ya sake maidata,idanunshi a lumshe kamar yadda nata yake,dukkansu suna jin bugun zuciyar junansu da ta qara gudu fiyeda yada take bugawa,sannu a hankali taji kasala na kashe mata duk wata gaba ta jikinta,jikinta ta saki batasan yadda akayi bacci yayi awon gaba da ita kan qirjin nasa ba,shi din ma yanayin ya masa,ji yake amar ya tsaida lokaci don su dawwama a haka,tun yana jin saukar numfashinta har shima baccin yayi gaba da shi

๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

kusan lokaci daya suka farka,da hanzarita ta miqe daga jikinsa don tunawa da cream da ta bar masa a fuska,idanunshi a lumshe yake kallonta,sai taga ya kai hannunshi gefan kunnenta ya ciro wani abu ya nuna mata,cream dinne da sauri ta dauki madubin dake hade set da shaver din ta haska,ai kuwa gashi nan ta kwaaheshi ya bata mata fuska ta dubeshi suka hada ido sai suka saki murmushi tare,dan towel din askin a janyo ta goge fuskarta ta matsa ta dauki shaver zata ci gaba da askin,dora hannunshi yayi saman nata hannun da sauri ta janye hannun nata saboda tsigar jikinta da taji ta tashi,ya karbe abun askin ta fuskanci me yake nufi don haka ta dinga haska masa yana askin da kansa,idan ya gaji ya tsaida hannun nashi ya huta tunda har yanzun ba wani qwari ne da shi ba
towel tasa mai mai kyau ta goge masa fuskan bayan ya gama,tana shirin miqewa taji ya riqo hannun nata ya sanya tafin hannunshi cikin natan ya matsa su sannna ya gyada kai ta fuskanci godiya yake mata,murmushi kawai ta saki ta sunkuyar da kanta kana ta zame hannun nata ta sauka daga kan gadon tana tattara kayayyakin da sukayi amfanin da su har yanzu idonshi a kanta yake,yanayinta kadai burgeshi yake,kominta anutse cike da tsafta tausayi da kulawa,ya maida idonsa ya lumshe bayan yaga fitarsa yana addu'ar Allah ya bashi damar da zai nuna mata nashi kalan halaccin koda bata sonshi

da uammain mubarak ya kawo wheelchair da hisham yace ya kamata a fara dora abdalla atleast zai dinga jin dadi idan an fita dashi daga bedroom zuwa parlour zuwa balcony din saman tunda ba zata iya saukowa da shi ba falon qasa,yaji dadi kuwa don alamu sun nuna afuskarshi,yawanci idan la'asar tayi aka dorashi zata yita shawagai da ahi daga parlou zuwa kitchen zuwa balcony din wani sa'ilin ma ya mata alaman su zauna cikin kitchen musamman idan tana girki,ganin zaman shiru suke yi yasa tana girkin tana bashi labaraimasu debe kewa,hakan kuwa na matuqar sa farinciki a zuciyarshi,don zata ga fuskarsa ta fadada sosai da murmushi alamun yana jin dadi

saidai kallon qurillar da abdallah ya koya tilas yasa take zama da hijabi,don ba qaramin kunya yake bata ba,ko ina yaso kalla kallonsa yake kanshi tsaye,da sun hada ido kuma ya wani lumshe ido ya basar kamar bashi ba,wani lokacin murmushi take cikin zuciyarta tace
''hali zanen dutse,babu abinda ke saiyawa dan adam halinshi,har yau halin abdallah na basarwa da waskewa na nan cikin jininshi''

*mrs muhammad ce*

๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ *ABADAN*๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐Ÿ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–
ยฉ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ’ก
*_home of expert and perfect writers_*

โ–ถ4โƒฃ3โƒฃ



*_An karbo daga nana Aisha Allah ya qara yarda a gareta tace:naji manzan Allah S A W yana cewa ''ya Ubangiji duk wanda aka dora mishi wani shugabancin na al'umata,ya tsananta musu Allah ka tsananta masa shima,wanda aka dora mishi wani shugabanci na al'ummata ya tausasa ya sassauta musu Alla ka tausasa masa ka sassauta masa shima_*






Qarfe biyar da rabi ne na yammaci mai cike da ni'ima da dadi kasancewar ko kusa garin babu rana sai lullumin hadari da ya lullube sama,su biyu ne zaune cikin falon yana kan wheel chair tana kan kan kujera saidai suna facing juna ne
novel ne a hannunta take karanta mishi sannu sannu cikin daddadar muryarta,tunda ta kifa fuskarta alittafin data kare fuskarta da shi bata dago ba saboda nauyin da kunyar kallon da abdallahn yake mata,gashi hakanan yaqi yarda yau a saka mashi kaya complete,duk wanda hisham ya ciro sai ya wurgar shi daminshi suke,wando three quater ne ajikinshi da riga armless duk wata qirar jikinsa ta bayyana


A hankali yasa hannunshi ya riqe littafin yayi qasa da shi tavdago kanta suka hada idanu,ido daya ya kashe mata yana murmushi don ya fuskanci abinda ya sata qin sakewar,littafin ta sakar mishi ta dora fuskarta saman cinyarta cike da jin kunya,taba kanta taki yayi sai taqi dagowa,ya daga littafin ya dan buga mata kadana akanta tare da cusa mata shi.


A hankali ta dago da zummar dauke littafin taci gaba da kare fuskarta,rubutu ne baro baro a bangon littafin I LOVE U,wani feeling ta dinga ji tana sake maimaita rubutun tamkar yau ta fara ganin kalmar,a dan sace ta rage tsawon littafin idanunta suka fito,karaf suka hada idanu da abdallahn daya zubawa cover littafin ido,tayi azamar maida littafin saidai tuni ha riqe da hannunshi daya yana ci gaba da kallonta,ji tayi bazata iya hada qwayar idanunsu ba saita sauke qwayar idanun nata kan cinyarta tana kallon yatsun hannayenta.


Qarar bugun da akayiwa qofar dukkansu sai data basu tsoro,kusan a tare suka kalli qofan,mami ce ke shigowa a burkice idanunta a kansu, qaraso gabansu ta ja burki
''sannunku qananun 'yan ta'adda,wato har kisa kuka so yimin cikin gida na ko๏ผŸ,to wallahi baku isa ba matuqar kuka ci gaba da yunqurin taba lafiyar wani cikin gidan nan zan iya tattarku kubar min gida tunda dai ba naku bane,kada ku kiskura ku sake aikata wani abu mai kama da haka don ba gidan 'yan ta'adda bane nan''duk maganar da take kan maruam na duqe a qasa,yayin da abdallah ya zuba mata ido cikin qunar zuciya da tashin hankali,me ya sami maminshi haka๏ผŸme ya canza masa mami๏ผŸ,mamin da bata qaunar taa ko sauyawa fuskarshi tayi,mami mai tattali da qaunar farincikinsa,mami dake qauqnr maryam ta dauketa tamkar diyarta ta cikinta


ta kalli maryam''kuma ki gaggauta zuwa ki nemi yafiyar nene da danan idan ba haka ba wallahi sai na wulaqantaki,idan banda ma ke butu ce shegiya mara mutunci daga zuwa ya duba lafiyar mijinki sai ki masa irin wann mummunar sakayyar,na baki nan da minti talatin kije ki basu haquri''ta juya zata fota suka hada ido da abdallqh,hara ra ta wurga masa saboda jin wani abu na son taba zuciyarta,sai kuma wani abu daga can daban ya taso ya danneshi


shiru ne ya ratsa falon bayan fitarta,dukkansu kansu na sunkuye zuciyoyinsu na saqa musu abubuwa mabanbanta,ganin ya kusa gota mibti talatin din da mami ta bata ya sanyata miqewa da sauri,hannunta taji an damqo,ta waiwayo sai taga abdallah ne,a hankali ya dao idonsa suka hada ido,da sauri ta kawar da kanta saboda tashin hankalin da ta gani cikin qwayar idanunshi basu musaltuwa,fararen qwayar idanunshi sun juye sun koma ja baya ga jijiyar kanshi da ke tashi,kai ya girgiza mata alamar ba zata je ba,itama kan ta girgiza kana ta dawo gabanshi ta durqusa tace
''kayi haquri ka bari inje din,umarnin mami nake qoqarin cikawa ba donsu zani ba,kada ka manta har yau mami na matsayin uwa ne a garemu kaga ya zama dole mu bi umarninta don gamawa da duniya lafiya indai ba ya sabawa addini ba''


shiru yayi ma wasu 'yan daqiqu kana ya daga mata yatsunshi guda biyar alamun minti biyar ya bata,guada kanta tayi sanan ra miqe ya bita da kallo har da fice


tana gab da shiga waitin falo inda anan qofofin bangaren nau yake ta hango adnan,muta ne uku ne zabga zabga baqaqe,cikin baqin kaya masu qirar samudawa biye da shi,kallo daya zaka musu ka tabbatar cewa babu masaukin imani cikin zuciyarsu,mamaki ya cikata duk da tasan cewa lokaci lokaci zaka ganahi da ire iren mutanen a matsayin abokanshi,sai ta kasa wucewa ta rakube har suka wuce,tazarar minti biyar ta bada tasan zywa lokacin sun shiga koma ina zasu ahiga sannn tabi bayansu,a qofar waiting parlour din suka kusa karo da mami wadda ke sanye da kayan aiki da alama asibiti zata fita taja da baya ta bata hanya,harara ta watsa mata mamin kana ta fice,girgiza kanta tayi kawai tabi ta da kallo,kallo daya zaka mata ga wanda ya santa yasan cewa ta canza,tsaftarta har yanzu tana nan saidai duka gayun nan babu shi,bata mantawa shekaran kiya doctor safara'u abokiyar aikin mamin ta kira maryam take tambayarta me yake damin mamin ne,kullum tazo office bata da aiki sai kuka,tambayar duniya kuma ba zara gaya maka abinda ke damunta ba,magana daya zata gaya maka shine babu komai


Ganin babu kowa cikin falon qasan ya sanyata nufar sama,tana atep din qarahe na matattakalar ta soma jiyo maganganu,tamkar an dasata agun ta kasa gaba ta kasa baya
''yace saidai mu mu qarasa aikinmu,dalili kenan da yasa nace ka nemo min su mugu,wanna karon zamuyi aikin qarshe kan abdullahi,jibi da daddare nake so ku kashemin abdullahi,kafin ranar zansan duk abinda zanyi na kori yarinyar daga gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login