Showing 18001 words to 21000 words out of 22737 words
? hmmmm wallahi wallahi kin ban mamaki ga mijin ki can yana neman yin aure ki, kina nan a zaune babu abin da ya shafe ki , yawo kika tusa a gaba ba dole yayi aure ba Hidaya baki san cin sa ba balle shan sa baki san ki kula da shi ba
ke dai mata kika rako duniya wallahi asiri ma idan kin ga yayi tasiri to akwai biyayya da iya kalamai ,bawan Allah nan dakyar muka samu ya aure ki baki ga irin kuɗaɗen da na ɓatar ba duk akan ki shine kika bada kofa shekara daya da wasu watanni zai miki kishiya dan uban ki haka kika tashi ko shara da yan gyare-gyaren gidan nan bakya yi , aini ban san haka kike zaune ba sai da samha ta faɗa min komai besan me lokacin da kike fita ba haduwa nayi dashi a harabar gidan nan ina ƙoƙarin tafiya ya ban hakuri na zauna da ya kira ki saboda ke kin iya karya kika ce kina gida dan uban ki, ina kika tafi?.''
cikin mamaki ta dafe kuncin'ta ta buɗe baki za tayi magana mommy tace '' yi min shiru bana so naji komai daga bakin ki wallahi mamakin ki nake gani nake kece zaki face da wannan gida nayi abin da nayi kika fito daga gidan wancan matsiyacin shine kika saka min da haka wallahi kin cuce ni Hidaya ke ba haihuwa ba anya kuwa ba wani abu kika sha kika ki haihuwa? kullum sujja nake Allah ya baki haihuwa Ubangiji ya saka kafin ki yaye kin haihu amma ke kin rufe idon ki kin toshe kunnuwan ki kin dauki hudubar sheɗan wa'yannan kawayen naki wallahi duk randa na kara ji ance kin tura mata a cikin gidan nan wallahi Allah sai ranki ya ɓaci shasha matsa min na huce.
tamkar wata doluwa haka ta matsa mata , ta huce gaskiya ta yarda inhar mutum ya kware gurin munafurci to zai iya raba da , da mahaifi da sauri tabi mommy tana cewa dan Allah kiyi hakuri inshallahu bazan ƙara ba.
mommy tace '' kima ƙara.,,
riƙe mayafin'ta tayi tana kuka tace '' dan girman Allah ki dawo.,,
tsayawa tayi ta ce sake ni.
sakin ta, tayi mommy dawowa tayi ta zauna
Hidaya itama zama tayi ta zuba ta gumi tace '' mommy waya ce miki zai yi aure?.''
uban ki ne ga labari ya baza media har free weeding pictures na gani ai na yiwa Hajiya magana sai tace min eh yana neman aure jifa amsar da ta bani a yadda muke da ita har ta bari ɗan ta yayi aure.
jikin Hidaya ne yayi sanyi rasa ina zata saka kan'ta tayi jikin ta duk ya saki tace '' ni be faɗa min ba kuma ni gani nake kamar faɗa miki haka tayi kawai.,,
wani kallo tayi mata , tace '' dallacan rufe min baki, ke mahaukaciyar ina ce ? ga zance daga mahaifiyar sa idan zaki gyara halin ki , ki gyara kin ga tafiya ta.,
da kallo ta bita dashi tace '' to shikkenan , ki gaida gida gobe zan zo sai musan abin yi.,
banza tayi mata , ta fita Hidaya da sauri ta , tashi ta fara tafiya buɗe kofar toilet tayi ta wanke fuskar'ta fitowa tayi ta ciro wayar ta a jaka ta nemo number saheer danna masa kira tayi ta ƙara a kunne.
be dauka ba ajiyewa tayi ta buɗe wata kofa wacce kai tsaye bangare saheer zata shiga ajiyar zuciya ta sauke ganin kofar sa a buɗe take da sauri ta shiga baya parlour dan haka sai ta shiga bedroom ɗin sa jin kar'ar zubar da ruwa a toilet zama tayi tana jiran'sa.
kallon ko ina take kamar mace komai tsaf tsaf kamar mace ta gumi ta zuba tabbas idan wannan zance ya tabbata ta shiga uku ita daman matar shege ce wata kila wacce zai aura , auren soyayya za suyi zata zama yar kallo kenan ina ba zai yiwu ba dole ta zubar da komai ta kama kan'ta tabbas idan bata yi wasa ba wankin hula yana neman kaita dare.
tana cikin wannan tunanin taji kar'ar buɗe kofar'sa.
da sauri ta , tashi towel ne a hannun sa amsa tayi mamaki ne ya kama shi ya riƙe hannun ta yace ''. Bar shi na gode.,,
girgiza kai tayi tace '' baka so na samu lada ne bani nayi maka .,,
ta faɗa tana ƙara karɓa jikin sa ta fara goge wa saheer yace '' barshi haka na gode.,,
ajiyewa tayi tace '' wanne kaya zan dauko maka.,,
yi yayi kamar be jita ba ya huce, dressing mirror jan stool yayi ya zauna.
zama tayi tana kallon sa har ya gama shafa mai , duk da saheer baki ne amma bawai irin can ba za'a kira shi da chocolate colour wani irin karfaffan mutum ne jikin sa baya nuna tarin shekarun sa.
duk inda kyakkyawa yakai to yakai ita kan'sa fatar sa abin kallo ce , tashi yayi ya buɗe wardrobe ya dauko riga armless da wando three quarter milk and coffee colour yan gidan Gucci turare ya fesa tace '' yau ka dawo da huri daman kullum haka kake dawo wa ba sai dare yayi ba .''
juyowa yayi yana kallon ta domin maganar ta , ta bashi mamaki , be taɓa zaton rashin kunyar ta , takai haka ba zama yayi akan kujera yana daukan laptop yace '' zan yi aiki ki faɗi abin da ya kawo ki kar kizo ina aiki ki katsai ne.,
maganar nan baƙaramin bugar mata zuciya tayi ba sai ta danne tace '' daman mace sai tana da bukata sannan zata je gurin mijin'ta?.''
be ce mata komai ba ya buɗe laptop din sa Hidaya tace '' wai da gaske ne za ka yi aure... ? Ka samu lafiya ne ?.''
ta gefen ido ya kalle ta daman shi dai yasan ruwa baya tsami banza wato shi ne ta canza halin ta, tana so ta gyara wasu kura'kuran'ta.
Uhmmm yace mata yana ci gaba da danna laptop din sa , Hidaya ji tayi tana neman faduwa haka dafa gado tayi ta riƙe kan'ta da yake juya mata , tace '' tambayar ka nake ka amsa min da uhmm da gaske ne ka samu lafiya kuma aure za kayi?.''
Saheer yace '' inshallahu ina fatan haka.,,
da sauri ta , tashi tsaye ganin yana shirin raina mata hankali tana tambayar sa yana fadar haka kuka ta rushe dashi tace '' kai min adalci kenan ? tsawon Shekara daya da watanni nayi ina jiran ka samu lafiya amma shi ne ka saka min da haka daman ai na lura da take taken ka wallahi Allah ba zan zauna da kishiya ba sai dai ka zaɓa ko ni ko auren da kayi kuma Allah nasan Hajiya bata san da wannan zancen ba.,,
duk wannan maganganun da take saheer ko ɗago da kan'sa be yi ba ɓalle ya kalle ta nunawa yayi kamar baya gurin ko baya fahimtar yaren da take magana dashi.
da sauri ta fita tana ci gaba da kuka tana shiga part din ta ta dauki waya ta dannawa Hajiya kira rabon ta , da ta kirawo hajiya tun ana sauran sati ɗaya bikin ta saheer.
har ta gama ringing bata dauka ba ci gaba da kiran'ta, tayi amma ina Hajiya bata dauka ba danna mata kira ta kara tana cewa ai ni nasan abin munafurci ne gashi nan taki ɗagawa a wannan karon ɗagawa tayi kuka ta ƙara fashewa da shi tace '' Hajiya wai da gaske ne aure zai yi wallahi Hajiya idan yayi auren nan mutuwa zan yi.,
Hajiya tace '' subhanallahi haba Hidaya sai kace haramun zai aikata tabbas kishiya akwai ciwo amma haka za kiyi hakuri ace bashi da shi ne , shi ne zan iya hana shi amma tun da yana da hali ki yi addu'ar Allah ya saka kin samu abokiyar zama ta gari Allah ya saka hakan shi ne yafi alkairi ,,
Hajiya alkairi fa kika ce kishiyar ce alkairi ke me ya saka alhaji be miki ba har ya mutu idan alkairi ce ? Wallahi to dole na tona asiri bashi da lafiya tun da yayi hatsari gaban sa ya samu matsala.
HAJIYA tace '' ke ce dai baki da lafiya yaron da ko kwarzane jikin sa be yi ba a hatsarin da suka yi zaki zo min da wannan zance ke ce dai mara lafiya sai dai ki karkace ki saki katon kashi ba ki iya kashin mutum ba aikin ki kawai kici ki sha kiyi kashi ke har kina da kunyar da zaki kalle ki, kice bashi da lafiya ya'yan da ya haifa kece kika haifar mai su? Ina miki kallon me hankali kina kokarin shiga dawa kishiya hauka ce har da zaki faɗa min haka .,,
Hidaya kara rushewa tayi da kuka ta kashe wayar ta ajiye ta , bata taɓa tunanin hajiya zata faɗa mata haka ba kenan ma da sanin ta , za'a yi mata kishiya.
shiru tayi tana share hawaye dole tabi mommy domin tasa inhar za tayi mata abib da take so kishiyar nan da za ayi mata labari zata zama ba mamaki ma yar gidan babban mutum ce.
★★★
Talatu talatu, da sauri talatu ta fito tana cewa haba yaya hadi lafiya kake min wannan kiran ka shigo cikin gidan nan babu ko sallama.
Ke bana son rashin kunya harkar arziki ce ta , zo mana amma Umaru yana so ya saka bakar kafar sa ya ture mana arziki.
ya faɗa yana gyara malin malin din sa.
Talatu tace '' kayi min bayani yadda zan gani?.''
to yanzu nan ina zaune ƙuda nabin baki na saboda tsabar talauci da yake damuna hinin yau babu wanda yazo ya siya dabino ko sai wata bakar mota katowa fa wallahi fuskata tas sai da ta fito a jikin motar, ta tsaya wani hamshakin mutum ya zuge Glass da sauri na , nace mai alhaji kwano nawa za'a baka ? mutumin nan talatu sai yace '' gidan malam hadi yake nema.,,
nanfa jiki na ya fara zikiri nace wanne wanne hadin bashi da inkiya yace mahaifin nimrah yar gidan malam Umaru sai nace me hadin yayi nayi haka ne naji idan wani abu ne tofa nace ban san sa ba , banci nanin ba nanin zata cine ne
cikin zaƙuwa talatu tace '' kai sauri ka kara samin labarin ni dadi na da kai idan ka tashi bada labari komai sa ka faɗa.
hmmm ke waya ke harkar tsiya, ki tsaya na zube miki ita a fefe yace '' zai bani dubu hamsin nanu mai gidan.,,
sai nace to faduwa ta zo daidai da zama ni ne amma gaskiya na saka ran da dubu hamsin din nan ka bani ita tun safe babu wanda yazo ya tsaya min anan gurin da sunan yazo siyan dabino
sai yace '' alhamdulillah za mu iya magana dakai.,,
nace a'a bani kudi na sai ka faɗa min duk wata magana da zaka faɗa min mutumin nan talatu sai ya dauko rafar kudi ta yan dubu dubu guda uku ya biyu dubu dari cif na karaba ina godiya kin san wani abin takaici wai ashe auren nimrah yake nemawa ɗan sa Umaru yace a'a wai yafi karfin nimrah shi talaka ne
Salati talatu ta saki tace '' kai ashe daman bashi da hankali ga arziki yazo mana yana ƙoƙarin ya saka kafa ya ture shi bara na sako hijabi mu tafi.,,
tsaya tsaya mana dad'i na dake son kuɗin ki, yayi yawa wallahi sai nace mai ni ne wan umaru uwa daya uba daya bani sadakin ta gobe ka dawo a daura musu aure.
Kinga miliyan daya ya bani da dubu dari biyar ya bani yanzu zuwa za muyi , gidan sa mu haɗa hannu da hannu mu taushe shi gobe ayi abin da za ayi kar ma makiya suji ni wallahi ace ina da yarinya bashi zanyi matsalar, kinga rafi'atu baka ce su kuma masu kudin nan suna son farar mace shi ya saka ma bance gata nan ba.
ban da abin ka yaya hadi ga zulai nan ai da dan hasken ta.
wani kallo yayi mata, yace '' kin ga bana son shir'man banza sako hijabin ki muje dole ya amshi sadakin nan wallahi yarinyar nan idan ta auri Alhaji saheer ai sai mun gaji da keta hazo idan har ba kaza bace ci ki goge baki nama amshi number sa ma.,,
Wallahi kuwa ta faɗa tana saka hijabin ta , gaba yayi tana bin sa a baya tafiya suka yi me nisa sannan suka isa gidan su nimrah a soro suka ci karo da malam yana cin abinci washe baki yaya hadi yayi yace '' malam umaru dan uwana rabin raina abinci kake ci haka...?.,,
mamaki ne ya kama malam yace '' yau kune a gidan nan Allah ya saka lafiya.,,
haba kai ko kunya baka ji ba laifi ne dan ɗan uwa , ziyarci dan uwan'sa.,
suka faɗa suna zama a kan tabarma talatu tace '' yaya umaru magana ce ke tafe damu.,,
Ke rufe min baki ni zan fara magana ya faɗa yana zaro kudi ya zube mai gaban sa , kallon mamaki Malam yake musu yace '' yaya talatu ina kuka samu kuɗin nan haka
dariya hadi yayi ya hade gurin waje ɗaya yace '' naka ne sadakin yarinyar nan ne nimrah da Alhaji saheer dalhat ''
kai ya hadi sadaki fa ka ce ? yaya da bakai gaggawar amsar wannan kudin ba wallahi ficikar sa bata burge ni duk da a yi a bincike da nayi da kuma nazari ba na gansa da wani mugun abu ba wallahi mutuncin ya'ta yafi min wannan kudin.
kana kuwa da hankali umaru kalli gidan da kake ciki kuma gidan haya idan shekara tayi , wallahi Allah ni nasan baka da kudin da zaka biya na haya ba siyar da yarinyar ka , kayi ba aure haramun ne daman ai shi kowa yasan yana son talaka to Allah yayi daga gare mu fashewa yayi da kuka ya ci gaba da cewa mahaifiyar mu da zata mutu ni taba wa amanar ku a iya sani na , na kula daku shine yau zakai mana bakin ciki arziki ya zo kace a'a idan ka zauna da yarinyar nan Umaru ka faɗa min idan ta zauna zaman me za tayi maka ? Wallahi Allah yau dana tashi babu ko, kobo a guri na amma kanin mahaifin Alhaji dubu dari ya bani.
Haba yaya mene na kuka ni da nimrah duk kana da iko da mu Amma ka duba abin da nake son ka gane wannan kudin kamar mun siyar da yar mu ne shi ya saka ma da yazo nace mai a'a
Salati talatu ta saki tace '' yaya umaru kayi wa Allah da manzon sa ka amince da auren nan mu bishi da addu'a Allah ya saka ayi a saka Ubangiji ya kade fitina dan girman Allah ka amince.,,
Malam shiru yayi yana sauraran su yace '' bawai ina ja da ku bane amma ni gaskiya ba zan siyar da ya'ta ba.,,
Hadi yace '' to shikkenan ka zaɓi yar'ka akan mu ko ba komai Umaru ya faɗa yana dafa saitin zuciyar sa yana cewa talatu ki sheda idan na mutu dan uwana ne ya kashe ni.
kuka ta saki jikin Malam ne yayi sanyi ganin halin da ya'ya hadi yake ciki bashi da sama dasu, su uku mahaifiyar su ta haifa sai kuma yan uban su , su wa'yannan zaman gaba suke yi tun da ran mahaifin su yaso ya sasanta abin Amma suka ki , da yake matsalar agurin su take mahaifiyar su fita tayi mahaifiyar su malam ta shigo shine suke ganin ita ta kore mahaifiyar su.
zai yi addu'a inshallah komai zai zamo da sauki yace '' to shikkenan na amince amma kace wannan kudin yayi yawa.,,
tsayawa hadi yayi ya a '' ban gane yayi yawa ba ? Kana da kudin da zakai mata kayan daki ne ? ..''
a'a ya faɗa yana kallon kudin.
Hadi yace '' to kaga ke talatu ungo dubu daya ladan ganin ido kai kuma Umaru dauki wannan kudi ka ajiye duk abin da ya kamata sai ka dauka kayi dashi ka bar mata wani abu kar mu cinye mata sadakin mata duk ka .''
ba dan ransa ya so ma haka ya amsa Hadi lalubo wayar sa yayi ya dannawa saddam kira domin shi a tunaninsa kahun saheer ne yana dagawa yace '' kira ni bani da kudi.,,
Malam girgiza kai kurum yayi domin shi be so suka ji wannan maganar ba Allah yayi musu son zuciya ga wauta yana tunanin NIMRAH su ta gado domin kusan halin su ɗaya.
aikuwa ba jimawa ya kira Hadi yace '' to alhamdulillah komai ya tafi yadda ake so na bawa ma mahaifinta kudin gobe sai ku zo ayi abin da ya dace kar kaga ina yin magana da sauri kasan halin garin nan katin naira dari dakyar zai iya yi maka magana me yawa.,,
Saddam yace '' to Allah ya kai mu baba zan fadawa ogan nawa yace ma wannan kudi a bar shi a matsayin kudin nagani ina so sa rana .,,
To to masha Allah amma ina da tambaya Alhaji.
saddam yace ''' to baba Allah ya saka na sani.,,
amin ya Allah da man na ganka ba wani babba ba naji kuma kana cewa zaka fadawa ogan naka ka bani labarin abin da ya faru da farko kai ne wan mahaifin sa ko wani ne ko kai wakili ne...?.''
gaban malam ne ya faɗi jin maganar da wan nasa yake ki yi malam yace '' yaya kai da baka ai be ƙara sa ba ya rufe mai baki yana cewa kai shiru mana idan ana magana da me kuɗi ba'a magana sai ya gama.
ya faɗa yana sakin speaker wayar da yake dan newa yayi yace '' Alhaji ina jin ka.,,
saddam yace '' ni yaron nasa to inshallahu gobe yan uwansa za su zo dashi sai ayi abin da ya dace.,,
to to dan samari ni daman wallahi kai na ya kalle nace kaga tsoho da jikin yara.
dariya saddam yayi sukai sallama.
talatu tace '' ni fa ban gane ba ya naga ana ƙoƙarin gama komai ban ga nawa kason ba wannan dubu dayar daka miko min ita almajiri zan bawa ko wa...?.''
sakar baki Hadi yayi yace '' a'a uban almajiri zaki bawa talatu ki, kiyaye ni wallahi idan bakya so bani