Showing 6001 words to 9000 words out of 22737 words
murmushi tayi ta buɗe DP din wacce taji tayi wani voice to voice din ya dauki hankalin ta musamman ma muryar ta , sai ta haifar mata da wata kalasa babu picture din'ta sai picture din kyakkyawar kafa anyi mata kunshin nan na yan sudan ga sarkar kafa sosai ta shagala da kallon kafar to ina ga ta'ga me kafar .
shiga ciki tayi kamar za tayi mata magana sai ta fasa, domin bata son disgi da girman ta , tana matar babban mutum kamar Saheer ta tsaya wata mace na hulakan'ta ta..
contact din admin din group din ta shiga ta fara yi mata voice tana cewa hy bestie yakike ya harkoki am naga wata so ban san ko new comer bace Please connect me with her urgently Amrah has left, and I really need this as soon as possible ...
tura mata , tayi ta she datar ta ganin bata online.
tashi tayi ta fara tafiya , handle din kofar dakin ta , ta murɗa ta shiga wayar tace tayi ringing ganin sunan kanwar ta da sauri ta dauka tana cewa sai yau kika tuna dani.
ta faɗa tana murmushi.
daga can bangaren samha tace '' aunty kin san me yake faruwa kuwa? mommy ce tace sai na buga miki waya baki sanar da ita ba , wai mijin ki yayi aure labari ya karade social media ga wani picture dai babu fuskar matar sai dai bayan ta amma shi dai wallahi Allah ba Al bane shi ne zance dai kala kala wasu sunce karuwar sa ce ko fa minti talatin ba ayi ba da ɗora labarin amma ke kin ga uban liking da comments.''
Hidaya , tace '' aure fa kika ce ? hhhh wallahi karya ne, ni kai na be iya dani ba ɓalle yake ya dauko wata kin ga , ku kwantar da hankalin ku, saheer ba zai taɓa yin aure ba.''
Samha tace '' aunty bafa a shedar na miji.''
zama Hidaya tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya daukan lemo tayi ta sha ta ajiye ta saki wata uwar gyatsa tace '' nasan saheer sarai tun kafin na shigo cikin wannan gidan na gama karantar halin sa , bashi da burin aure aure mace ɗaya ta ishe shi tun kafin A'isha ta haihu be karo mata kishiya ba haka yayi hakuri har Allah ya basu da ta mutu ya dade be yi aure ba sannan ya aure ni abu biyu zuwa uku saheer ya saka a gaba ci gaban kasuwancin sa mahaifiyar sa ya'yan sa da yan uwan sa , Saheer wallahi ba irin mazan da kika sani bane yana da hakuri da kawaici amma baya daukar raini, ko ni da kika ga ina abin da nake so to akwai wani sirri a tsakanin mu.'''
dan Allah aunty faɗa min na dinga yiwa abban eman shi kinsan fa wallahi ba tun yau na san yana bin mata ba kawai hakuri nake , nake zaune dashi Allah aunty samin irin mijin ki sai an tona.
Hidaya tace '' hmmm ke Allah dai ya kyauta amma kusan haka maza suke ko ni nasha kama abbas da mace .''
ai gashi nan duk da ya sake ki, kin yi wani auren baki rabu da shi ba.
Cewar samha.
Hidaya tace '' ke sai da haka wannan rayuwar badai da aure na ba kuma ni yanzu wallahi na fi karfin namiji ya raina ni shima ai yasan wacce ni shiya saka har yanzu yaƙi rabuwa dani shekaran jiya, matar da kira na ,tayi tana kuka tana zagina wai idan na cika cikakkiyar mace na bari miji na ya sani ita bata ga amfanin auren da nayi ba nace sai naci abu takazar uban'ta , idan ta sake na fito to wallahi Allah zaman ta da abbas ya ƙare.''
Aunty kenan , me ya saka kike haka ni wallahi Allah ban ga amfanin wannan abin ba.
Hidaya tace '' ke yarinya ce , wallahi baki san me duniya take ciki ba , zuwa gidan ki kayi ne ?.''
Samha tace '' a'a yaji nayi.''
Ikon Allah yaji kuma me ya faru...?.''
cewar hidaya.
Samha tace '' aunty ki wacce mace ya gani yace yana so ni wallahi gwara ko aure ne yayi nasan aure yayi jiya kama shi nayi shi da budurwar sa akan gado na me yafi wannan muni shine na dake ta na yi fashe fashe a cikin gidan na fito.''
Ikon Allah to me mommy tace ...?.''
Samha tace '' wai muje gurin malami ni kuma nace a'a idan dai ba sakawa za tayi ayi min saukar Alqur'ani ba , bazan je gurin mashiriki ba , cewa fa suke yi kayi kaza kayi kaza abu mafi muni suce ka dauki period din ka , ka yiwa mutum abinci gaskiya ni bazan iya ba na kwanaki da muka je cewa yayi sai ya kwanta dani nace sam ban yarda ba da aure na haka kurum.''
Kuttumar uban ki da hallacan kashe min waya kaga shegiyar yarinya dan uban ki mu abanza muke juya mazajen namu da kika ga ba yadda suka iya damu ina cewa saki na da abbas yayi sai da ya kusan hauka..''
tana gama fadar haka ta kashe wayar ta , tana jan tsaki kiran bestie ne ya shigo wayar ta , da sauri ta daga tana cewa hajiyan yan air kwana biyu..?.''
Bestie women leader tace '' uwar gida kuma amarya yau jarabar ce ta motsa...?.''
dariya hidaya tayi tace '' tun da naga kiran ki nasan sakona ya je miki to ya an samu ne ?.''
bestie tace '' no ni ban ma gane wa kike nufi ba mene user name din'ta..?.'''
Hidaya tace '' pretty.''
oh tab wallahi wannan da kike gani yarinyar hajjo ce kuma bata ma kasar nan tana america.
dafa kan'ta Hidaya tayi tace '' innalillahi wallahi kin ga prevent din'na har tsiyaya yake yi gaba ki ɗaya na kasa samun nutsuwa tun ɗazu ki haɗa ni da ita ko Muryar ta naji muyi hira.''
dariya women leader tayi tace '' okay yanzu dai bata online idan na ta hau sai muyi magana amma mene lada na..?.''
Baki da dama zan tura miki wani abu ta account din ki.
Bestie tace '' godiya nake ranki ya dade .''
dariya tayi tana yi mata sallama, kashe wayar tayi ta ajiye
kome ta tuna da sauri ta dauki wayar ta , ta kunna data shiga Instagram tabe baki tayi ganin maganar kara auren saheer ake yi wasu har cewa suke sun san amaryar sai canki canka suke yi dariya abin ya bata kashe datar ta , tayi tana cewa aikin banza ba ku san dutsai bane da baku tsaya kuna ɓatawa kanku lokaci ba.
shiga toilet tayi ta cire rigar ta kunna shower tayi tuni ruwan ya fara ratsa tsakiyar kan'ta.
limshe idon'ta, tayi tana sakin dariya abinda ya saka ta dariya shi ne , wai saheer da aure tab Lallai akwai kallo to a ina zai saka ta yana dutsai bashi da amfani fa marabar sa da shi da babu duk ɗaya.
Wannan kenan.
kan uba lafiya kika tsaya min akai na ?.''
Kinga gaskiya ni nagaji uwani fito min da kudina ni na fasa adashin nan bani kudi na tun da bana ubale bane.
UWANI tace '' nimrah ni kike fadawa haka? to kudin ki na cinye bazan biya ba.''
wata uwar dariya ta saki tace '' kan uban can amma dai gaskiya baki da hankali yau zan nuna miki wace ce ni haka kurum kin cin yemin kudina to wallahi Allah yanzu nan zan dauki kayan kudina mu haɗu a police station.''
ta faɗa tana surar akuyar ta , salati uwani ta saki tana cewa nimrah ashe baki da hankali akan dubu goma zaki daukar min akuyar dubu talatin sauke min ita sauke min wallahi ko naci uban ki.
Nimrah tace '' idan kin isa ki biyo ni wallahi Allah sai na tara miki mutane ashe ba dad'i ki bani kudina na sauke akuya idan baki bani ba wallahi Allah daga nan sai gurin me dabba ina zuwa bakin kasuwa magana ta ƙare cas zai cake min kudina ya bani.''
salati ta saki tace '' ke anya kuwa ina da hankali..?.''
NIMRAH tace '' asibitin mahaukata ne akai na.''
Wallahi Allah baki gado halin uwarki ba nazifa mutuniyar kirki
Owo dai ta faɗa tana fita da sauri uwani ta dauki mayafin'ta da yake kan igiya ta bita a guje nimrah gudu ta saka akuya sao ihu take .
haba baiwar Allah kamar ba matar aure ba kina bin wannan yarinyar me yayi zafi cewar wata mata da tazo shigewa.
tuff tuff aniyar kowa ta bishi ina ruwan ki dani da nake cewa ki riƙe min ita ai baki, riƙe min ita ba.
Cewar uwani.
Matar bata kula ta ba , tayi gaba , abin'ta.
NIMRAH a sosai take gudu da akuya ganin tayi wa uwani nisa sai ta saita tafiyar ta , da sauri uwani ta ƙara so inda take tana ganin haka sai ta kuma kwasa wani irin ihu akuya ta saki itama cin birki tayi amma ina sai da motar nan tayi gaba da ita akuya kuma tayi tsalle ta fita a guje tana zabga uban ihuuuuuuu.
UWANI tana ganin haka tabi akuyar ta , gana cewa ai gashi nan da yake banj da hakki a akan ki Ubangiji ya kama ki.
NIMRAH kuwa kuka ta dinga yi wani Irin rauni taji a kafar ta ji take kamar bata taɓa jin dad'i ba , a duniyar nan.
me motar fitowa yayi yana cewa ai wannan hauka ne ki biyo kan titi kina gudu horn nawa nayi miki amma aban za.
dakyar ta iya tashi tace '' wallahi Allah, Allah ya isana ban yafe ba ai wannan rashin mutunci ne baka bani hakuri ba sai ka tsaya kana faɗa min bak'ar magana.''
komawa cikin motar sa yayi yana cewa Allah ya isanki babu abin da za tayi min.
Nimrah da sauri ta ga ƙusa saka mai tayi aikuwa nan take tayar motar ta fashe fara dingisa kafar ta , tayi tana share hawaye.
dakyar ta ƙara so gida a zaure ta tarar da malam yana ƙwance da mafici a hannun sa Halifa yana kusa dashi yana cin gyada.
lafiya naga kafarki da rauni..?."
Malam ya faɗa yana tashi zaune.
zama nimrah tayi, ta fashe da kuka tace '' malam naje gidan uwani shi ne mota, ta buge ni.''
ba nace miki, ki barta da Allah ba tun da taji ta gani zata iya cinye kudin nan amma shi ne da yake kunne kashi gare ki , kika ƙi ji.''
share hawaye tayi tace '' malam yaushe zani gurin gwaggo?.''
Ranar duk randa kika ga dama ya faɗa yana komawa yana kwanciya.
tashi tayi, tana shiga cikin gidan wanke kafar'ta , tayi ta shiga dakin su fatima ce sai umaimah suna zaune suna hira kwanciya tayi akan matacciyar tabarmar ta duk tabi ta yage pillow ta jawo ta tada kan'ta dashi tace '' dan girman Allah umaimah dauko abin fifita kiyi min ko na samu sauki.''
Fatima tace '' a ina kika ji wannan ciwon?.''
NIMRAH tace '' mota ce ta bige ni.,,
Allah ya sawwake.
Cewar fatima.
Umaimah tace '' amin ya Allah gaskiya kin ga girkin dare nake yi na gaji wallahi bazan iya yi miki ba.''
NIMRAH tace '' dan Allah kina gamawa ki kwasa min nawa mamanku muguwa ce ba , bani za tayi ba sai tace ita , tayi sana'a ta samu kudin ta ni ba zanci ba kuma kinga ni idan na samo haduwa ake yi a rufawa juna asiri.''
Umaimah tace '' to.,,
nimrah a hankali bacci ya fara daukar ta ,
Wannan kenan.
N.D.C quarters.
ma'aruf wannan duk zancen banza ne kai kasan yayan ku ba zai taɓa aure ba , ba tare da na sani ba.
Cewar Hajiya zakiya.
ma'aruf yace '' hakene daman kawai faɗa miki nayi ina su miemie?''
tayi bacci shi kuma faruq yana gurin baba jummai.
tashi yayi yana cewa ga wannan chocolate din ki basa ya ajiye mata wata ledar shopping a kasan capert.
to tace , tana mayar da hankalin'ta gurin labaran da ake yi, gaban tane ya faɗi lokacin da aka hasko picture ma'aruf ya rike wata mace wacce bata san ko wacece ba tsayawa tayi tana jin me ake fadi kamar haka.
ayau ne larabawa ake zargin sharararen dan kasuwan nan Alhaji Saheer dallahat ya daura aure amma na sirri hankalin mutane ya rabu kashi biyu wasu suna cewa wacce me sa'ar ce ta samu nasarar auren sharararen dan kasuwan nan me faɗa aji number daya a jakar nan tamu a ɗaya bangaren kuma inda yan yarfe suka ce wa ba aure yayi ba budurwar sa ce to zantuka dai kala kala mun yi kokarin jin ta bakin sa amma abin ya faskara domin na tuntubi me magana da yahun bakin sa yace mu dai jira komai ake ciki zan mu gani.''
tufa ta dauka ta gutsura tana mamaki to kodai gaskiya ne amma ai tasan wane saheer ba zai taɓa yi mata haka ba duk yadda aka yi akwai wata a kasa.
daukan wayar ta , tayi tana ƙoƙarin kiran sa , sai gashi nan ma ya shigo hannun sa rike da faruq ajiye wayar tayi tace '' kaga daddy ku ba zama ko.''
saboda taga bakin yaron yaƙi rufuwa.
saheer ɗurkusawa yayi yace '' Hajiya ina wuni?.''
Hajiya tace '' lafiya qalau alhamdulillah.''
zama yayi a ƙasa faruq ya hau kan cinyar sa yana dariya tare da riƙe hannun abban nasa , tausayin su ne dukka ya kama ta , tace '' saheer a kawo maka abinci?.''
Saheer yace '' eh amma ba wannan yarinyar bace tayi ba ko?''
yana nufin ihsan.
Murmushi tayi tace '' ni ce nayi saboda yau bana sha'awar cin wa'yannan girke girken nasu su ke nan kullum ace basu da abincin ci sai kayan maiƙo ni yanzu shekaruna sun ja ga rashin lafiya daman ina fama da ita dakai na nayi tuwon shinkafa miyar kubewa idan zaka ci na saka a zubo maka.''
Saheer yace '' zanci.''
Baba jummai baba jummai.
da sauri matar ta fito ba wata babba nace can kenan kawai suna taci dan Hajiya ta girme ta , tace '' Hajiya gani.''
zubowa saheer wannan ragowar tuwan.
Yallaɓai ina wuni sannu da zuwa ta faɗa tana durkusawa amsawa yayi yana tambayar ta ya aiki alhamdulillah tace , ta juya ta bar gurin faruq ban da murmushi babu abin da yake can yace '' daddy dani zaka tafi ko? mu dinga yin breakfast tare.''
tausayin yaran ne ya kama shi baya jin zai iya kai wa Hidaya ya'yan sa , haka kurum sam be yarda da ɗabi'ar ta ba , ajiyar zuciya ya sauke yace '' a'a kai zaman ka a gurin hajiya.''
ba dan ya so ba yace '' to.''
tashi yayi Hajiya ta bashi chocolate din da ma'aruf ya bashi tsalle ya dinga yi yana murna.
Hajiya tace '' saboda me kaki yarda su faruq su koma hannun ka ? bana jin Hidaya ko bera zata iya cutarwa balle mutum musamman ma wanda ya fito daga zuri'ar mu ko baka ga yadda muke ba ni da mahaifiyar ta? gaba ki Dayan su Mutanen kirki ne.''
ƙasa yayi da kan'sa yana da zurfin ciki, yana so ya fadawa Hajiya shi be aminta da ita ba amma besan yadda zai mata wannan bayanin ba matar da kudi ne a gaban ta , za'a yi bata su domin a cutar mai da ya'yan sa yace '' insha Allahu zan gyara .''
yayi haka ne baya so maganar tayi tsayi.
baba jummai ce ta kawo mai abinci da ruwan wanke hannu, wanke hannun sa yayi ya dauke robber.
bismillah yayi ya fara ci Hajiya ci gaba tayi da kallon ta .
baba jummai ce ta fito hannun ta dauke da afrah yarinyar ta tana ganin sa ta fara dariya tana cewa daddy jummai ajiye ta , tayi ta tafi gurin sa da gudu ta faɗa kan cinyar sa tana cewa Allah daddy yau sai na bika
zuciyar sace tayi rauni, da ace A'isha na raye duk da basu shiga wannan halin ba tun tana yarinya ƙarama ta mutu bata sam mahaifiyar ta shafa kan'ta yayi da aka raba shi gida biyu yace '' afrah wayayi miki kitson kanki...?.''
uhmm aunty ihsan ce amma ba kitso bane kalba ce
ta faɗa tana wasa da hannun lis ɗin sa da ya cire.
saheer yace '' yayi kyau.''
Daddy zaka tafi da ni da faruq ko?.''
Hajiya tace '' kai kuwa ko dan nacin da yaran nan suke yi ka tafi dasu da ni nayi zatan sai ta dan kwana biyu yau zaka mayar da su amma na lura sam zaman su anan yafi maka kwanciyar hankali, yaran ka suna da kulafici bana gudun su wallahi tausayin su nake ji idan ka tafi kuka suke yi kafin su dawo dai-dai Wallahi ana daukan lokaci me tsayi.''
zare hannun sa yayi daga cikin plate ɗin yace '' Hajiya ba ko wacce macece za'a kai mata ya'yan da bata haifa ba ta riƙe kin ga Hidaya bata taɓa haihuwa ba , bana tunanin tasan yadda za ta kula da su.''
saheer kenan kawai kafi son zaman su anan amma Allah na tuba ita daman mace ai yar raino ce yarinya karama idan aka siya mata yar tsana kai zaka kayi mamakin yadda take kula da wannan yar tsanar nan tata.''
shiru yayi bece komai ba , Hajiya tace '' da gaske ne aure za kayi?.''
dam dam haka kirjin sa ya bada wani irin sauti dakyar ya iya saita kan'sa yace '' daman maganar da ta kawo ni kenan aure nake so na ƙara.''
Hidaya tana wani abu ne wanda baka so?
Hajiya ta jefo mai wannan tambayar yace '' a'a.,,
HAJIYA tace '' bazan hana ka ba Allah ya sanya alkairi amma saheer ban ji dad'i ba auren ku shekara ɗaya da yan wasu watanni kace zaka ƙara aure yarinyar nan tausayi take bani duk mazajen da take aura basu da kirki ita haka kenan haka ƙaddarar ta , take wallahi ranar da na ganta a waya naji dad'i ganin yadda ta yi kiba alamar tana jin dad'i duk da kai sai dai kazo badai ka kawo min ita ba , ka kyau ta kenan? bansan me kake tunani ba baka so ta rabi yaran ka wallahi karka bari ta gane haka idan ta gane ba zata ju dad'i ba.''
Saheer yace '' Hajiya ba haka nake nufi ba , amma ni kin ga ba zauni bane ba na bata dama taje in dai gidan su ne da gidan mu to bansan bata zuwa ba.''
hmmm Saheer ban sanka da karya