Showing 138001 words to 139687 words out of 139687 words

Chapter 47 - SHIRYAYYAR ƘADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

kwata kwata baya ganewa,ya fi son depression ya kamashi saboda sam”
“dan Allah second father kuyi haƙuri,uzuri ne ya riƙe shi amma ba da gangan yaƙi zuwaba,dashi mu ka yi shirin zuwa Allah ne bai nufa ba” Alyar ya faɗa,suna matuƙar son ɗan uwansu duk sai su kaji ba daɗi da maganganun su ya Naeem,duk da suma kan su basa jin daɗin halin da ya ke nunama dady,basu da yanda za suyi ne kawai
“uhmm kana son kareshi ne kawai Alyar,amma ni na san babu wani uzuri daya riƙesa,kawai yayi ne dan yaga halin da dady zai shiga,sai dai ya sani muddin dady ya faɗi ya mutu da ɓaƙin cikinsa Allah bazai barshi ba”
“ya subahanallah,dan Allah ya Naeem ka daina faɗar haka,da badan uzurin daya riƙesa ba da babu abunda zai hanshi zuwa,amma in sha Allah yana nan zuwa soon”
“dole na faɗin haka Alyar,sam ya matuƙar ɓata man rai yau,a iya sanina baya da jahilcin addini,ya san cewa iyaye ba abun wulaƙantawa bane,amma ya koma kamar wanda bai taɓa sanin komai a addininsa ba,shi ko tsoron Allah ya kamashi da alhakin mahaifinsa bayayi??”
“haka ne second father,in sha Allah komai zai wuce,nan da two days yana nan zuwa”
“wallahi kar Allah ya sa ya zo,ai duniya ce wanda bai zo ba ma jiranshi take bare wanda ke cikinta” girgiza kai Alyar yayi baya jin daɗin kalaman da ya Naeem ɗin ke faɗa,haƙuri su ka shiga ba su shi da James, ya za suyi da halin ɗan uwan nasu lamarin nashi ne sai Adu'a.
dady tunda su ka shiga mota ƙala baice ba kana kallonsa kasan yana cikin damuwa,haƙuri uncle Jonas ya sake bashi yana sake tabbatar mashi da uzuri ne ya riƙe sam ɗin amma yana nan zuwa kafin su tafi,jinshi kawai dady yake amma ya san babu wani uzuri daya riƙesa kawai baya son ganinsa ne,kullum cikin Adu'a yake Allah ya rage mashi son shi amma ina yanzu ya fara tunanin sonshi ne ajalinshi.
har suka iso gida babu wanda ya sake cewa komai.
mom tayi matuƙar farin ciki da zuwan kawun nata sai dai ta wani ɓangaren tayi takaicin ƙin biyo su da sam ɗin yayi sai dai ba ta nuna hakan ba ta barshi akan da sun tashi tafiya ƙafarta ƙafarsu,ita za taje da kanta ta dawo da shi.
babu wanda baiji haushin rashin zuwan sam ɗin ba musamman laatifa da Nainarh,dan Nainarh ɓoyewa tayi a bedroom ɗin su tasa kuka,taci burin ganinshi amma yaƙi ya zuwa,Abbah ma yaji haushin rashin zuwan sam ɗin,har kiran wayarshi yayi amma bai sameshi ba da yake gidan shi su ka fara zuwa,uncle Jonas baiji daɗin rashin samun uncle mutallab da mom Fatilah da yayi ba,yaso ace yayi masu ta'aziyya ido na ganin ido,sun ɗan jima a gidan Abbah kafin suka nufi gidan dady,acan su ka sa mu uncle Ubaid da uncle Hashim sun zo yi ma uncle Jonas barka da zuwa ba su san sun tafi airport ba da sun je tarbosu.
Tarba ta musamman uncle Jonas ya samu daga ahalin Abbah hakan kuwa baƙaramin daɗi yayi mashi ba,ya sake tabbatar da karamcin su,ba wannan bane zuwanshi na farko ba.
Alyar basu wani jima a Estate ɗin ba su ka nufi gidan su shi da James duk da dady ya so su zauna part ɗin sam amma Alyar yace zuwa gobe za su dawo.
su uncle Ubaid sun jima sosai a gidan,fira sosai su ka sha da uncle Jonas,sai da dare yayi sosai tukun su ka yi mashi sallama su ka koma gida.
su uncle ubaid na tafiya dady ya rakashi bedroom ɗin dake kusa da nashi wanda mom ta gyaramashi,zama dady yayi,kwantar mashi da hankali uncle Jonas ya shiga dan ya lura har yanzu da sauran damuwar duk da yana ƙoƙarin dannewa,murmushi kawai dady ya mashi yana faɗin bakomai zai jirashi nan da kwana biyun,mom ce ta shigo ɗakin,tashiga ɗakin dady bata ganshi ba yasa ta zo nan,kusa da kawun nata ta zauna tana sake mashi sannu da zuwa da tambayar lafiyar mahaifiyarta da matarshi,duk suna lafiya yace mata yana tambayar Irfan da tunda ya zo bai sa shi a ido ba.
tunda safe ya fice daga gidan zuwa aso Villa,tunda aka yi rasuwar bai fita ba sai yau.
sun ɗan jima a ɗakin sosai suna buɗe wani babin firar yaushe gamo,sai da dare ya raba sosai tukun su ka yi mashi sallama su ka fice.
bedroom ɗin dady su ka nufa
“Naeem ya sanar dani komai daya faru,ni kaina banji daɗin rashin zuwan sam ɗin ba amma dan Allah kayi haƙuri ka cire damuwar sam a zuciyarka,ganin ka damu dashi ne yasa yake wahalar da kai,kuma bai kamata kana nuna tsantsar soyayyar shi a gaban ƴan uwanshi ba”
“Zulaihart ni kaina ban san wane irin so nakema sam ba,bana iya ɓoye soyayyar shi a ko ina”
“na sani ƴallaɓai amma daurewa za ka yi,ko dan saboda ƴan uwanshi,kullum burin su su faranta maka,Ni na san basa jin daɗin banbancin da kake nunawa tsakanin su da ɗan uwan su kawai suna daurewa ne yasa ba su taɓa nuna maka ba” ta san su ya Naeem kawai baza su faɗa bane amma dole suna jin ba daɗi da irin soyayyar da yake nuna ma sam ɗin
“in Allah zan gwada yin hakan”
“Allah ya sa” lallashin shi ta shiga yi tana sake kwantar mashi da hankali har bacci yayi awan gaba da su.
dady sai da ya tabbatar da mom tayi nisa a cikin baccin tukun ya tashi, toilet ya shiga bai wani jima ba ya fito,jikinshi da damshin ruwa da alama wanka yayi, dressing room ɗin shi ya nufa,mom na nan kwance tana bacci ya fito har ya shirya cikin suit silver color,wayar shi dake ajiye saman nightstand ya ɗauka,matsawa yayi kusa da ita, kissing forhead ɗin ta yayi kafin walking calmly
ya fice daga ɗakin.
lokacin da zai isa compound har driver shi ya fito da mota da alama ya jima da sanin tafiyar,back seat ya buɗe mashi ya shiga kafin shima ya shiga mazaunin driver,reverse yayi su ka ɗauki hanyar ficewa daga Estate ɗin.
tunda ya fito yake laɓe jikin Piller yana kallon su sai da ya daina ganin motar ta su tukun ya fito,baƙaƙen kaya ne complete a jikinshi,ya rufe ko ina a jikin shi,hannu ya zura cikin trouser pocket ɗin ya ciro waya,dialing wata number yayi,wanda ya kira na picking yace “boss yanzu nan ya fita daga gida” bana iya jin me na cikin wayar ke faɗa mashi sai ji nayi yace “ok sir an gama” zame wayar yayi daga kunnenshi,ya nufar bayan gidan.


*A ROUND 3 AM*

Ƙarar wayarta ne yayi sanadiyar farkawarta,hannunta ta zura tana laluben switch ɗin bed-side lamp ta kunna,hasken ne ya ɗan haska gadon,idanunta ta kai ga dady dake kwance kusa da ita ga mamakinta baya nan, tunanin ta fara ko yana toilet,
a hankali ta kai hannunta ta jawo wayar tana duba mai kiran nata,faɗuwa gabanta yayi ganin number dady, saurin kallon agogon dake manne jikin bango tayi wanda ke nuna ƙarfe 3:40 na dare kafin ta kalli wayar tana mamakin to ina yaje a wannan lokacin da har yake kiranta a waya,har kiran ya katse ba tayi picking ba wani ya sake shigowa, picking tayi tana kara wayar kunnenta,on the other side taji wata murya saɓanin ta dady nayi mata sallama,saurin sauka tayi daga saman bed ɗin gabanta na wani irin mummunan faɗuwa,to waye wannan me ya kai wayar mijinta hannunshi,da ƙyar ta samu tayi ƙarfin halin faɗin “bawan Allah waye kai,ina mai wayar yake ⁉️”
“dan Allah da katte nake magana” bugun zuciyarta ne ya tsananta jin sunan da na cikin wayar ya ambata,cikin rawar murya tace “Eh itace,waye kai,ina mai wayar yake⁉️”
“ya gamu da haɗari ne a...” ai tun kafin ya ƙarasa ta saki wayar hannunta,kamar saukar aradu haka taji zancan nasa,ficewa tayi daga ɗakin kamar zata tashi sama ita kanta bazata iya cewa ga halin da take ciki ba,tana shiga main parlor ya Naeem da ya Adnan na faɗowa,tana ganin su kawai ta yanke jiki ta faɗi.....
*INNALILLAHI WA INNAH ILAIHI RAJI'UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA'AKLIFLI KHAIRAN MINHA,LAHAULA WALA QUWWATA ILLAH BILLAHIL ALIYUL AZIM*

*ina dady zashi,waye ke sanar da fitowarshi,wa yake sanar mawa,ta ya akai wannan haɗarin ya faru da shi⁉️*
*Shin bari mu koma baya*
*Wacece wannn baturiyar data haihu a ɗakin hotel har tayi sadaka da ƴarta ba tare da ko taji ɗumin jikinta ba,sannan su waye mata da mijin data yima sadaka da ƴarta⁉️*
*Su waye ke bibiyar rayuwar Nainarh,taya akai Abid ya rayu bayan an shida ma court mutuwarshi,wane flash ne mahaifin Nainarh ya bata,ina Flash ɗin yake,shin da gaske ne yumnah ce ke bibiyar Nainarh,su waye su ka kashe mahaifin Nainarh⁉️*
*Shin da gaske Zaabith na tare da uncle Mustafa ko dai kawai zargi ne⁉️*
*Waima waye ya kashe Noor,wace masifa ce tasa kanta a ciki,su waye bayin Allah data taimaka,menene a cikin Flash ɗin data ba Irfan,wane zaɓi ne take cewa tayi mashi⁉️*
*Shin kuna ganin hukuncin da uncle mutallab ya ɗauka akan mom Fatilah ya dace❓*
*Wacece Carol ne❓*
*shin kuna tunanin Nailarh ta rayu bayan duka da Allurar da mahaifiyarta tasa aka mata,waye CEO dake bibiyar Nailarh,wacece Aunty Sophia,Allurar mecece taba Noah ya ba Mrs Malika,waye mijin Mrs Malika,wane yara ne Nailarh ta gani a container lokacin da mahaifiyarta ta turo masu da kaya,Mrs Malika wace irin uwa ce ita dake neman ƴarta,wace irin uwace da zata lalata rayuwar ƴarta,wane irin business ne ma take yi⁉️*
*Club ɗin waye su Irfan ke kula da shi,wacece yarinyar da aka yima opretion su waye su ka yi mata opretion ɗin,shin kuna ganin mom maimunatu zata koma gidan uncle Hashim ⁉️*
*Wanene SAM,me ye asalin abunda ya haɗashi da dady,shin duk laifin da dady yayi mashi ya cancanci yayi fushi da shi,kuna ganin zai zo kuwa bayan two days ɗin da su Alyar su ka ce⁉️*
_Masu karatu tambayoyin fa da yawa,kuma ko wacce na buƙatar amsa,dan jin wannan amsoshin kukasance dani taku Queen Kainart a cikin wannan labari mai taken SHIRYAYYAR ƘADDARA,ku kasance dani a season two dan samun amsoshin tambayoyin ku._

*Alhmdllh Alhmdllh Alhmdllh anan na kawo ƙarshen littafin shiryayyar Ƙaddara season one game buƙatar two 500 ne za'a tura kuɗin ta wannan asusun 9131306012 Hadiza mukhtar opay bank sai a tura shaidar biya ta wannan nambobin 08133650574/09163957890*

*Daga Alƙalamin Queen Kainart...✍*
*Chat me via WhatsApp*
*08133650574/09131306012*











Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login