Showing 93001 words to 96000 words out of 139687 words
da take,saman table ɗin dake gabanta Yumnah ta ajiye ledan “gashi inji ya Adnan” Yumnah ta faɗa,Enaaya ma ajiye ledan dake hannunta tayi tana juyawa da sauri tace “Allah ya ƙara sauƙi Aunty Nainarh,sai da safe” da kallo kawai Nainarh ta bita har ta fice daga ɗakin,maida dubanta tayi ga Yumnah, murmushi ta sakar mata “gashi nan get well soon ne ya kawo maki” kallon Yumnah tayi kawai without saying anything,she's just surprised about ya Adnan
“Nainarh!,ba kice kin gode ba” Yumnah ta faɗa, murmushi ta sakar mata “ke zan ma godiyar ne,ko ke ki ka kawo man?” ɗan zaro ido Yumnah tayi “oh na manta,ashe fa ba ni na saya maki ba” ta faɗa tana juyawa zata bar wurin,riƙo hannunta Nainarh tayi “dallah can wasa nake maki,nagode ki bani number sa nayi mashi godiya” taɓe Yumnah tayi tana zama saman Arm chair dake kallon wacce Nainarh ke zaune,ledan ta jawo tana buɗewa dan ganin miye a ciki,lafiyyan kebab ne with vegetables sai ƙamshi yake,ga beef shawarma,ɗan kallon Nainarh Yumnah tayi tana murmushi dan da ga kallon kebab har wani motsi kunnenta yake,ɗayan ledan ta buɗe kwalin pizza ne sai ƙatuwar robar Ice cream,ledar da Enaaya ta ajiye Yumnah ta jawo,fresh fruit ne
“wow gaskiya ya Adnan na ji dake,wallahi ba kiji yanda yawuna ya tsinke ba” Yumnah ta faɗa tana sake buɗe ledan kebab ɗin,ɗaya ta ɗauka ta kai baki,lumshe ido tayi tana wani gyaɗa kai irin na daɗin nan,murmushi Nainarh ta saki tana girgiza kai kawai,sake ɗaukar wani tayi ta kai baki,saurin janye ledan Nainarh tayi
“ki bari a kaima mom da Aunty Fa'iza mana” murmushi Yumnah ta saki “wallahi ba ki ji daɗin sa ba ne, kamar kunen mutum zai tsinke”
“yanzu dai fara kai masu tukun kafin kunen naki ya tsinke” dariya Yumnah ta yi,ledan pizza ta buɗe ciro kwalin da robar Ice cream ɗin tayi,a cikin ledan ta zuba ma mom da Fa'iza, ice cream ne kawai bata ɗaukar masu ba tunda ɗaya ne,ficewa tayi tana cema Nainarh yanzu zata dawo, kitchen ta nufa direct,a plate ta zuba ma mom fa'iza kuma ta bar mata a leda, bedroom ɗin mom ta nufa ta kaimata nata kafin nan ta nufi part ɗin mamy bata samu kowa masu aikinta na part ɗin su mamy kuma na part ɗin dady, bedroom ɗin fa'iza ta shiga har tayi shirin kwanciya,tana bata ta fice ta koma part ɗin su.
*Uncle Hashim's house 😡*
Laatifa na daga kan chair zaune gaban table ɗinta tana opreting system ɗinta yayinda balqis ke zaune tsakiyar bed ɗinta,dukan su PJ's ne a jikinsu,ɓata fuska balqis tayi tana turo baki “wai Aunty laatifa magana fa nake kinyi shiru,mi yasa wai duk ku ka share ni ne keda momy,ni fa ba laifina bane laifin dady ne” still laatifa bata ce mata ƙala ba aikin gabanta kawai take
“dan Allah mi yasa za ku man haka idan da sabo ai yaci ace kun saba da halin dady,haba Aunty Laatifa idan ku ka haɗe man kai ke da momy ya ku ke so nayi,please Aunty nah”
iska laatifa ta ɗan furzar,juyowa tayi tana fuskantar balqis ɗin, murmushi balqis ɗin ta sakar mata
“Balqis ban san mi yasa baki jin magana ba,mi zai sa ki nace dole sai kinyi aiki a hospital ɗin nan,kuma da ki ke magana mun haɗe maki kai ba dole mu haɗe maki kai ba ince a gabanki mahaifinki yayi ma momy iya dake bareni da ba komai bace a cikin gidan nan,kiyi haƙuri kawai ki janye wannan burin naki,kiyi haƙuri kiyi aiki a in da yake so” tunda Laatifa ta fara magana yanayin fuskar Balqis ya sauya zuwa tsantsar damuwa,a halin nan na yanzu bata jin zata iya haƙura da Aiki a hospital ɗin nan
“sannan shawarar da zan baki wallahi wannan soyayyar ta SAM dake zuciyarki kiyi gaggawar kasheta,da ina ganin dady zai sauka ya amince amma yanzu na fahimci babu wannan,kiyi haƙuri Allah ya baki mai sonki wanda mahaifinki ke so amma ba SAM ba” wasu irin hawaye ne su ka taru a idon balqis dama tun da daɗewa zuciyarta ke raya mata ba lallai ta samu SAM ba duba da shaƙuwar dake tsakaninshi da yayarta sai take ganin kamar soyayyace tsakanin su kawai ta ɓoye mata ne shiyyasa kullum ta ke nuna mata illar dake cikin dagewar da take akan tana son SAM ɗin
“kiyi haƙuri duk da ba haka na so ba, amma ya zama dole, nayi maki sha'awar Auren SAM amma mahaifinki bazai Amince ba,shi kanshi SAM kafin ki samu soyayyar shi ba ƙaramin aiki bane balle a zo ga dadyn ki ya amince,kiyi haƙuri kawai in sha Allah zan tayaki da Adu'a Allah ya baki miji mai sonki fiye da yanda ki ke son SAM”
“mi yasa ki ke faɗin mahaifina ke ba mahaifinki bane?” Balqis ta faɗa hawaye na bin cheek ɗinta, murmushin takaici Laatifa tayi tana faɗin
“Balqis da nake ganin dady a matsayin mahaifina amma yanzu na tabbatar da ba mahaifina bane,ina zaune gidan nan ne saboda mahaifiyata amma ba dan kowa ba” jan hanci balqis tayi har time ɗin hawaye na zuba daga idanunta,laatifa ce ƙwarin gwiwarta amma yau ta nuna mata itama ta gaji
“Aunty laatifa dan Allah karki ce na haƙura da ya SAM wallahi ina son shi,son da nake jin bazan iya rayuwa babu shi ba” wani kallo laatifa tayi mata,fashewa tayi kuka tana faɗin “idan ki ka ce na haƙura dashi ya ki ke so nayi, wallahi bazan iya rayuwa ba tare da ya SAM ba” ɗan rintse ido laatifa tayi ta buɗe tana girgiza kai irin ya zanyi maki ki fahimta ɗin nan,tasowa tayi daga kan chair da take zaune ta nufo balqis ɗin,zama tayi kusa da ita,hannu tasa ta shiga goge mata hawayen dake bin cheek ɗinta “kiyi haƙuri Balqis duk wasu qualities da ki ke ganin SAM yana da su a irin mijin da ki ke so, ki sani akwai maza bila'adadin a duniya masu irin wannan qualities ɗin dama wanda su ka fishi,in Sha Allah zaki samu miji wanda yafi SAM,kiyi haƙuri kinji” wani irin kallon Balqis ɗin tayi mata kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce “Aunty laatifa kina son ya SAM ne!?” ta faɗa tana tsareta da idanu,kamar saukar aradu haka laatifa taji tambayar balqis a kunnenta,saurin zame hannunta dake kan fuskar Balqis ɗin tayi tana Binta da wani irin kallon
“Aunty laatifa tuntuni ina lure dake kamar kina ɓoye man wani abu a game da alƙarki da ya SAM,a lokacin dana nuna ina son ya shi da kin faɗa man soyayya ku ke wallahi da ban wahalar da kaina ba,amma miyasa sai da nayi nisa a soyayyar shi zak...” bata ƙarasa ba a dalilin tsawar da Laatifa ta daka mata,kuka Balqis ɗin ta fashi dashi mai tsuma zuciya tana faɗin“mi yasa sai da ki ka bari soyayyar shi tayi man mugun kamu za kice na rabu da shi”
“zan mareki balqis idan bakin ki bai dai furta wannan maganar ba,dama kallon da ki ke man ke nan,ke ko wani yace maki zan iya soyayya da SAM ke sai ki yarda,kin bani mamaki Balqis,saboda na zauna ina baki shawara shine zaki kalli tsabar idona ki faɗa man wannan maganar,SAM he's just my favorite brother daga haka bashi da wani matsayi a zuciyata,kinfi kowa sanin bazan taɓa iya yima SAM son Aure ba,bari na tuna maki idan kin manta SAM he's my younger brother not my boyfriend” cikin muryar ku ka Balqis tace “idan ke baki sonshi shi yana sonki ai” girgiza kai Laatifa tayi, cikin ɗan ɗaga murya tace “balqis wai kin rasa tunaninki ne,mi ke damun brain ɗinki ne,kamar yanda yake favorite brother a wajena haka nake favorite sister a wajenshi, ke kin san da ace yana sona bazamu kai tsawan wannan shekarun ba tare da ya furta man ba,SAM bazai taɓa sona da sunan Aure ba idan ma wani abu ke maki yawo a kai ya daina”
“idan har ba sonki yake ba, mi yasa ya ware ki a cikin mu ke kaɗai yake kulawa, ke kaɗai yake saurare, ke ka ɗai ya ɗauka a matsayin ƴar uwarshi, saboda ke ya kawo S N J T Nigeria, yanda yake baki kulawa ko mom baya ba kulawa haka” wani kallo laatifa ta shiga bin Balqis da shi she's be came speechless akan maganganun Balqis
“how many times yake faɗin ki bar Nigeria ki dawo gareshi, idan har ba sonki yake ba bazai yi maki hakan ba” tashi Laatifa tayi daga saman bed ɗin rai ɓace,dan muddin ta cigaba da zama kusa da Balqis tana iya ɗauketa da mari saboda wannan kalaman da take faɗa,da wani yace mata Balqis zata mata wannan zargin bazata taɓa yarda ba amma sai gashi da bakinta take faɗa mata wannan kalaman, Balqis ba komai ya sata faɗar hakan ba sai yanda Laatifa ke faɗin ta haƙura da SAM, a rayuwa idan da abunda ta tsana to ace ta haƙura da SAM, wayarta dake ajiye saman Nightstand Laatifa ta ɗauka, number SAM ta shiga sa mata a wayar da yake ta haddace, tana gama rubuta number tayi mata saving da red heart ɗin emoji, in da Balqis take ta dawo “karɓi ga number sa nan na sa maki kina iya kiranshi ki faɗa mashi duk abunda ke ranki, idan ma binsa za kiyi har can Ni mai iya yi maki booking flight ne kije har can ki sameshi ki faɗa mashi kina son shi,sannan ina so ki sani wannan ya zama last time da zaki sake man maganar SAM, duk wani abu da ki ka san ya shafi soyayyarki karki ƙara tunkarata dan wallahi ranki ne zai ɓaci” kallon wayar kawai Balqis take tana sauraronta ba tare da ta amsa ba,ƴar tsawa Laatifa ta mata “zaki amsa ko sai ranki ya ɓaci” amsar wayar Balqis tayi, duk sai taji ba taji ba daɗi ganin yanda ran Laatifa ya ɓaci, ta san Laatifa na matuƙar ƙoƙari a kanta,bata da wani zaɓi ne bayan hakan.
“tashi ki fice man daga ɗaki” Laatifa ta faɗa babu alamun wasa tana nuna ma Balqis ɗin ƙofar fita, kallonta kawai Balqis ɗin tayi ba tare da motsa ba, bata taɓa ganin tsantsar ɓacin rai a idanun yayar tata ba irin na yau, juyawa Laatifa tayi ta nufi hanyar toilet tana faɗin “karki bari na fito na sameki a ɗakin nan” da sauri Balqis ɗin ta miƙe ta nufi Laatifa, hugging ɗinta tayi ta baya tana fashewa da wani kuka mai ban tausayi,ɓan ɓareta Laatifa ta shiga yi daga jikinta,ƙanƙameta Balqis ɗin tayi tana kuka “am deeply sorry about kalamai na,please Aunty Laatifa kiyi haƙuri, wallahi bazan sake furta irin wannan kalaman ba, kiyi haƙuri” kuka take sosai tana bata haƙuri,jin yanda take ku ka ne ya karya zuciyar Laatifa har cikin ranta take jin kukan Balqis ɗin “kiyi haƙuri Aunty laatifa bazan sake furta irin wannan kalaman ba,nayi kuskure kiyi haƙuri kar kiyi fushi dani” ajiyar Laatifa ta sauke ba tare da ta raba jikinsu ba tace“ki dunga sarrafa fushinki a yayinda ranki ya ɓaci,saam banji daɗin kalamanki ba,daga yau ki dunga sanin kalaman da zaki faɗa ma mutum idan ranki ya ɓaci,ba komai ya zo bakinki zaki faɗa ba”
“to in sha Allah bazan sake ba Aunty laatifa,ki yafe man” ta faɗa kamar zata sake fashewa da wani kukan “shikenan ya isa haka,komai ya wuce,ni mai iya sadaukar maki da komai nawa ne,ki kwantar da hankalinki babu wani abu dake tsakanina da SAM,bana burin SAM ya Auri ko wace ƴa mace sama dake” ta faɗa still ba tare da ta raba jikinsu ba
“na sani Aunty laatifa bazan sake maimaita wannan kuskuren ba”
Jinjina mata kai laatifa tayi “yanzu ga number sa nan na sa maki kina iya kiranshi,ki daure ki sanar dashi duk wani abu dake zuciyarki” a ɗan shagwaɓe balqis tace
“abuda ko na kirashi bazai ɗauka ba,please ke dai ki kira manshi”
“A'a gaskiya bazan kira maki shi ba,ki kirashi kawai na san in sha Allah yaga number Nigeria ce zaiyi picking”
“please Aunty nah”
“bafa zan kira maki shi ba kiyi fighting soyayyarki da kanki, ki daure kawai ki kira sa in sha Allah zan cigaba da tayaki Adu'a,Allah ya karkato da tunanin sa gareki yaji duk duniya babu wacce yake so sai wannan kyakkyawar ƙanwar tawa” wani irin murmushin jin daɗi balqis ɗin ta saki
“shikenan Aunty laatifa zan kirasa Please ki tayani da Adu'a Allah yasa dady ya Amince”
“in sha Al...” bata ƙarasa ba ta dalilin jin balqis ɗin ta fita daga jikinta da mugun sauri,juyowa laatifa tayi da sauri,wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi ganin wanda ke tsaye zufa ce ta shiga keto mata,har tsawan wane lokaci ya ɗauka a ɗakin,kuka balqis ta fashe dashi saboda azabebben zafin daya ziyarci ƙwaƙwalwar ta a dalilin mugun riƙon da yayi ma hannunta, laatifa kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito,wani irin kallon yake binta da shi,kallon da yake mata ne ya ƙara rikitar da ita,rawa bakinta yake magana take son furtawa amma ta kasa tsoron abunda zai biyo baya ne ya mamayeta,fisgar balqis yayi ya fita da ita daga ɗakin,da sauri tabi bayan su “dan Allah d...”tun kafin ta furta abunda ke bakinta ya juyo da mugun sauri,ji ka ke tasssss ya saukemata lafiyayyun maruka har sau biyu...
*Ep 43_44*
____________________________
ji ka ke tasssss ya saukemata lafiyayyun maruka har sau biyu,sakin hannun balqis yayi,cikin wata kalar murya wacce bata san shi da ita ba yace “who do you think you are da ki ke ƙoƙarin lalata man yarinya,saboda na barki a cikin gida na yasa ki ke ƙoƙarin lalata man tarbiyyar ƴa,tunda ya gama lalataki har yau kin rasa mai kallonki yace yana soki, shi ne ki ke ƙoƙarin ganin itama ya lalata ko,zaki yi mata booking flight taje ta sameshi ko,this should be the last time da zan ganki tare da ƴata, albarkacinta kawai ki ke ci yasa har yanzu muke tare da ke,daga yau baki ba ƴata nayi maki iyaka da ita,stay away from my Daughter if not wallahi wallahi wallahi rantsuwa uku nayi ko?...” nuna ta da index finger ɗin shi yayi yana girgiza kai irin kinsan mi zai biyo baya ɗin nan,wasu irin zafafan hawaye ne su ka wanke fuskar laatifa haka ma Balqis,fisgar hannun balqis yayi da nufin fita daga ɗakin,momy su ka gani tsaye fuskarta a ɗaure kamar wacce aka aiko ma saƙon mutuwa,raɓawa yayi ta gefenta ya fice daga ɗakin riƙe da hannun balqis dake kuka,a fusace momy ta juya tabi bayan su, a parlorn ya tsaya da Balqis,kunnenta ya riƙe gam,cikin kausasheshiyar murya ya fara magana “me na faɗa maki game da waccan yarinya?” rintse ido Balqis tayi saboda zafin da taji a kunnenta,sake murɗe kunen yayi,ƴar ƙara ta saki hawaye na bin cheek ɗinta “dan Allah dady kayi haƙuri,wallahi ba laifin Aunty laatifa bane,laifina ne dan Allah kayi haƙuri” tsawa ya daka mata
“yi man shiru ko nayi ƙasa ƙasa dake a wajenan shashashar banza,wallahi daga yau ko hanya na sake ganin ta haɗaki da ita sai ranki yayi mummunan ɓaci,kina jina” ya faɗa yana daka mata tsawa
“naji dady,dan Allah kayi haƙuri karka rabani da Aunty laatifa” ɗayan hannunsa yasa ya bige bakinta “na sake jin ko sunanta bakin ki ya furta sai naci mutuncinki,baki ba ita nayi maki iyaka da ita,idan kuma har ban isa ba to” kuka balqis ta fashe dashi fiye da wanda take jin furucin dadyn nata akan ƴar uwarta, girgiza mashi kai ta shiga yi tama kasa magana sai hawaye dake zarya a cheek ɗinta “get out from my side useless kawai” ya faɗa yana sakin kunenta,da gudu ta nufi bedroom ɗinta tana kuka, Ajiyar zuciya ya sauke yana huro iska mai zafi daga bakinshi,juyawa yayi da nufin zuwa bedroom ɗin shi,momy ya gani sanye da hijab tana aikin tura box,da tsantsar mamaki yake binta da ido harta ƙaraso tsakiyar parlorn, trolley ta saki ta juya zuwa ɗakin Laatifa,da mugun sauri ya riƙo hannunta,a masifance ta fisge hannunta daga nashi,idanunta sun ƙaɗa jawur hawaye ne kwance a cikin su “how dare you to touch me,don't eve touch me again our marriage is over” juyawa tayi ta nufi bedroom ɗin Laatifa,sake riƙo hannunta yayi,yanzu riƙo yayi mata ba na wasa ba,fisgarta yayi zuwa cikin parlorn a saman sofa ya zaunar da ita
“baki da hankali ne maimunatu,ina ki ke tunanin zaki a wannan lokacin,ko baki san ƙarfe nawa ba ne??” ya faɗa yana nuna mata agogo dake manne jikin bango
“is not your business,ko ina zani bai shafeka ba”
“calm down,idan saboda abunda nayi mata ne ki ke shirin aikata haka,samunta nayi tana ƙoƙarin cusama Balqis wannan yaron har faɗi take zata mata booking flight taje ta sameshi a can”
“bai shafe ni ba,ka sani babu sauran wani Aure tsakanina da kai,yau bazan kwana gidan nan ba,ka biyoni da takardata har gidan iyaye na”
“kina hauka ne saboda wannan abun ki ke faɗin our marriage is over,zaki tafi gidan ku,ko dai kin fara shan wani abu ne ban sani ba”
“abunda ka ke sha shi nasha,wallahi sai na tafi,kuma bani ba kai,yanda ka tsani ƴata haka ni ma na tsaneka” kuka ta fashe dashi mai ban tausayi “kai azzalumin uba ne Hashim kuma azzalumin miji,wallahi haƙi na dana laatifa sai ya ga bayanka,macuci kawai wanda bai san haƙƙin dake kanshi ba,mai nuna wariya a tsakanin ƴaƴanshi,wallahi nayi dana sanin Aurenka a rayuwata,ka sake ni wallahi bazan cigaba da zama da...” tsawa ya daka mata wacce tasa dole tayi shiru,Laatifa na daga bakin ƙofar ɗakinta duk abunda ke faruwa akan kunenta,kuka take sosai bata taɓa jin muguwar tsanar Mahaifinta ba irin yau, tayi baƙin cikin kasancewar shi mahaifinta, tayi fatan ace ta mutu tun da daɗewa bata riski irin wannan baƙin cikin ba “ni ki ke furta ma waɗan nan kalaman?” ya faɗa cikin ɗaga murya yana nuna kanshi
“na faɗa maka haka, fiye ma da haka za kaji daga bakina, wallahi nayi dana sanin Auren ka,ka sawaƙe man” ɗan rintse ido yayi yana girgiza kai,duk fa abunda yake aikatawa da alƙarshi da mamy yana son mom maimunatu kuma baya son rabuwa da ita,tashi tayi daga saman sofa tana goge hawayen dake fuskarta, bedroom ɗin Laatifa ta nufa
“yau ba sai