Showing 90001 words to 93000 words out of 139687 words
tsawa yace “i said get out,if not...” ya faɗa yana nuna mashi ƙofa ba tare da ya ƙarasa faɗar abunda zai faɗa ba,juyawa kawai Dr fawar yayi ya fice yana girgiza kai,a shekaru ya girmi Irfan nesa ba kusa ba,kuma yana bashi girmanshi amma daga inda ya faɗa mashi gaskiya ajiye girmanshi da yake gani yake ya faɗa mashi magana san ranshi.
tashi yayi daga saman chair ya nufo ƙofa da cup ɗin wane da cigar yana ɗan layi kaɗan, alcoholic wine ɗin ta fara kai mashi karo,ƙofar office ɗin ya maida ya rufe harda key,a jikin ƙofar ya bar key ɗin,anan bakin ya zube.
ya Adnan lokacin da su ka iso hospital sun ga motar Irfan amma babu wanda yabi ta kanshi su ka nufo cikin hospital,da Dr fawar su ka ci karo a reception saukowarshi kenan daga office ɗin Irfan,da sauri ya nufesu, fuskarshi da ɗan fara'a,gaishe da su nurses ɗin dake wurin su ka shiga yi,da kulawa su ke amsa masu
“good evining mom,ai da kin kirani ba sai kinzo da kanki ba?” cewar Dr fawar
“ba damuwa fawar, patient gare ni,ƙonewa tayi”
“ayyah sorry” ya faɗa yana kallon Nainarh
“muje ko” ya faɗa yana kiran wasu nurses guda biyu,bin bayanshi su kayi ɗaya na kama Nainarh,su mom kuwa office ɗinsa yace wata Nurse ta kaisu,a bakin office ɗin shi suka tsaya, Nurse ɗin na ƙoƙarin buɗe masu ƙofa ya Adnan ya juya da nufin nufar sama,da sauri ya Naeem ya riƙo hannun shi dan duk tunanin shi Emergency ward din zaibi su Dr fawar
“ina zaka?”
“office ɗin wancan mara mutumcin,ya ƙone ɗiyar mutane amma ko a jikinshi” ya faɗa cikin tsantsar ɓacin rai
“calm down Adnan,ba sai kaje ba rabu dashi kawai,ai zai dawo gidan ya same mu”
“wallahi ka kyaleni na koya mashi hankali tunda shi bashi da hankali” girgiza mashi kai ya Naeem yayi “nace ka rabu dashi ko,zai dawo gida ne ya same mu” iska mai zafi ya Adnan ya fesar,cikin office ɗin su ka shiga dan mom da su Yumnah tuni sun shige sun barsu.
suna a nan zaune office ɗin sunyi shiru kowa da abunda yake saƙawa a ranshi,Dr fawar ne ya shigo da sauri ya Adnan ya miƙe yana tambayarshi wutar dai da sauƙi bata shiga cikinta ba,cikin office ɗin ya ƙaraso
“ku kwantar da hankali,ba wani sosai ne ta ƙone ba,kuma Alhmdllh zafin coffeen baikai har ya shiga cikinta ba,kawai dai fatan ta bata son zafi ne sosai,amma Alhmdllh da sauƙi,magunguna ne kawai zata sha sai cream da zata dinga shafawa a wurin” tunda ya fara jawabin nan hankalin su ya kwanta,dama damuwarsu kar ace wutan ya ƙonata sosai
“na bar Nurse Fatima ta shafa mata cream,data shafa mata zaku iya tafiya,Allah ya bata lafiya” da Ameen duka su ka amsa,ba'a wani jimaba Nainarh su ka shigo tare da Nurse ɗin dake riƙe ledar maganinta, Yumnah ta amshi ledar tana ma Nainarh sannu,sannu su ka shiga yi mata,sallama su ka yima dr fawar ɗin su ka fice,lokacin da su dawo gida,bedroom ɗin su Nainarh ta nufa ita da Yumnah da Fa'iza, ya Naeem tun a parking space yayi masu sallama ya wuce gida.
*UNITED STATE❤*
_*Las Vegas (Nevada)*_
daga ita sai Aunty Sophia ne a ward ɗin,miss Malika tunda ta fita bata sake dawowa ba,fira suke ba wani sosai ba Nailarh na bata labarin yanda taji lokacin da wannan mutumin yayi wining wasan,tana faɗa mata irin yanda zuciyarta tayi mata,lallashinta Aunty take tana bata ƙwarin gwiwa da kuma yi mata alƙawarin sai sun hukunta shi akan abunda yayi mata
“but Aunty ina zargin Dr dake kula dani kamar shine,abunda yasa ban faɗama mom ba na san data sani zata haɗashi da su Noah ne,na fi son saina tabbatar da zargina lokacin na warke,nafi son na hukuntashi da hannuna”
“nima bazan sanar da ita ba,zan so ki hukuntashi da kanki,duk ta yanda za muyi yayi daya sani za muyi,karki damu kinji” jinjina mata kai tayi
“sai ya san wacece ni,sai yayi daya sanin sa kanshi a hanyata” Nailarh ta faɗa
“dole ya san wacece ke,nima dole yaga ɓacin raina saboda wahalar man da princess da yayi” marairaice fuska Nailarh tayi “Aunty Sophi ba kiji zafin dana ji ba,gaba ɗaya naji duniyar ta yiman zafi,lokacin dana shaƙi wuyan rigar ki ji nake kamar zan mutu a lokacin” saurin girgiza mata kai Aunty Sophia tayi tana kama hannunta “kwantar da hankalinki kinji,dole ya gane kuskuren abun da ya aikata”gyaɗa mata kai Nailarh tayi, nocking ƙofar ɗakin akayi, izinin shiga Aunty Sophia ta bada,Nurse ɗin ɗazu ce ta shigo da food trolley,har bakin bed ɗin ta ƙaraso,gaishe da Aunty Sophia tayi kafin ta kalli Nailarh“good afternoon ma'am, it's time for lunch” kauda kai gefe Nailarh tayi,itafa idan zasu cigaba da bata wannan Yogurt ɗin zata daina cin abincin su, warmers ɗin dake saman trolley Nurse ta buɗe,sarving Nailarh ta shiga yi,lafiyayyan sandwich ta bata tare da gasashshen kifi.
Aunty Sophia ta shiga bata, Nurse ɗin na daga kan robber chair tana kallon su,turo ƙofar mrs Malika tayi ta shigo tare da su luna,kallonta Nurse ɗin da Aunty Sophia su ka yi amma Nailarh ko kallon inda take ba tayi ba,harta canza kayan jikinta da alama gida su ka koma dan harda basket ɗin abincin a hannun su luna,gaishe da ita Aunty Sophia da Nures ɗin su ka yi,amsa masu tayi yayin da idanunta ke kan Nailarh kamar zata haɗiyeta,tashi Aunty Sophia tayi daga inda take zaune lokacin data kammala ba Nailarh abinci, magungunan ta Nures ɗin ta bata kafin ta fice,bakin bed ɗin Mrs Malika ta zo ta zauna,hannun Nailarh ta riƙo a cikin nata ba tare da tace komai ba, Nailarh bata kulata ba, around 6 ɗaya daga cikin nurses ɗin ta shigo ta sanar dasu time ɗin da zasu bar Nailarh ita kaɗai yayi dama aroud six su ke rufe visiting,babu musu ko wani abu mrs Malika tace ok,kallon su Aunty Sophia tayi ta ce su tafi kawai,shirin tafiya su ka shiga yi,su luna su ka ɗauki basket ɗin da su ka zo dashi Aunty Sophia ma kaɗai taci abincin,kissing forehead ɗin Nailarh Aunty Sophia tayi haɗi da yi mata sallama su ka fice,mrs Malika ma kissing forehead ɗinta tayi without saying anything to her,fushi take da ita saboda abunda tayi ma mijinta,tun fil'azal Nailarh bata shiri da mijin Mrs Malika tunda ta fahimci ba shi bane Mahaifinta ba ta ɗauki karan tsana ta ɗora mashi,ga haushi da kishin kusantar Malika da yake da take ji,duk da itama ba wai ta damu da abunda ke tsakanin su can sosai dan bata da ra'ayi da ƙarfin tsiya ta hanyar alura Malika tasa abun yayi tasiri a gareta har ya zame mata jiki, har ya kai take kishin Malika,saboda ita yasa basa zaune waje ɗaya da Malika sai dai idan ta bar ƙasar ya bita inda ta tafi,sometimes saboda shi take barin US ta tafi wata ƙasar badan business ba saidai dan kawai su haɗu.
saurin kamo hannunta tayi,kallonta Malika tayi fuskarta a ɗaure,side smile Nailarh ta sakar mata
“are you angry with me because of your that black husband?”
Kallonta Malika kawai tayi,dan ajiyar zuciya Nailarh ta sauke,sake riƙo hannunta tayi tana faɗin “If u continue to be with him, I will break the promise I made to you, I will also get married,I promise u” Nailarh ta faɗa babu alamun wasa akan fuskarta,wani irin kallon Mrs Malika ta shiga binta dashi
“you're going to do what!?”
“I know you heard me well” zame hannunta tayi daga na Nailarh,zama tayi kan chair dake gaban gadon “baby kin fi kowa sanin cewa duk dukiyar da muke takama da ita akwai tasa a ciki,Duk wani kasuwancinmu yana da jari a ciki,shine silar arziƙina”
“i don't care, I told you
If you want me to fulfill promise i made u,just break this useless marriage” wani irin wahalalliyar yawu Mrs Malika ta haɗiye,bata taɓa expecting jin haka daga gareta ba
“please Nailarh ki gane mana,rabuwa da shi tamkar na rabu da kaina ne,shine komai nawa fa”
“alright,but I want u to know that there is no any promise between us,I will marry,ko da baki so hakan ba” ta faɗa tana tsare Malika da ido,kamo hannunta Malika tayi “kiyi haƙuri kinji,kin san ina sonki fiye da kowa a duniyar nan,karki fasa Alƙawarin da ki ka man Please Nailarh,bazan juri ganinki tare da wani ba,kina so nima heart Attack ya kamani??”
“zanfi kowa farin ciki idan ya kama ki”Nailarh ta faɗa ba tare da nuna wata damuwa ba,kallonta Malika ta shiga yi,mi yasa sai da komai ya kusa zuwa ƙarshe Nailarh zata ɓullo mata da wannan tsarin,kenan abunda take zargi zai zama gaskiya
“baby that doctor ne ya ce kice man haka,dama that the reason yasa ya kawo maki flower,dama wannan shine dalilin da yasa yake wanan abubuwan akan ki,sonki yake kema kina sonshi ko?”
“wannan kuma matsalar ki ce,idan ma sona yake I will marry him” wata irin gigitaciyar tsawa Malika ta daka mata “idan har ki ka cigaba da faɗin haka i promise u I will kill him,I sewer” kallonta Nailarh tayi tana sakin wani malalacin murmushi “ if u kill him I promise u I will kill your husband” iska Malika ta furzar mai zafi,dan mi Nailarh zata mata haka sai da ta gama preparing komai zata ɓullo mata da hakan,nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,in a cool voice tace “please Nailarh ki daina faɗa man haka,nifa momynki ce,kuma kin san ina sonki,saboda ke ne kawai bazan iya rabuwa da shi ba,amma ke nake so ba wani ba, Please ki fahimceni”
“kin dai ji abunda nace maki idan kina son zaman mu tare to ki rabu dashi”
“please Baby,don't do this to your momy, please baby,mi ki ke so a tare da wani namiji wanda bazan iya yi maki shi ba,mi zai burgeki a tare da wannan doctor da ki ke magana”
“abunda yake burgeki a tare da wannan mijin naki” wani kallon Malika tayi mata,ganin fa da gaske Nailarh take idan har bata yi wani abu ba,plan ɗinta na tsawan shekaru Nailarh zata rusa,wanda bazata so hakan ba
“shikenan I will think about that,I promise u zanyi abunda ki ke so just give me a time”
lallashinta sosai ta shiga yi har ta ɗan samu Nailarh ta sauko “da gaske baby sai ki iya Aure that doctor”
“yes idan har ba kiyi abunda nace ba”
“zanyi,nayi maki alƙawari,but please ki dai na maganar doctor nan” jin jina mata kai kawai Nailarh ta yi,turo ƙofar ɗakin a kayi, Nures ɗin dake kula da Nailarh ce ta shigo
“time is over madam” ta faɗa tana kallon Mrs Malika,okhy tace,kafin ta miƙe sallama tayima Nailarh ta fice,a zaune ta samu su Aunty Sophia har sun gaji da zaman jiranta,ficewa su ka yi zuwa motocin su dake parking lot.
rufe ido tayi kamar mai bacci,maganganunta da mahaifiyarta na mata yawo a kai,ita kanta ta san she can't survive without her mother,ta riga tayi mata sabon da bazata iya rabuwa da ita ba ,kawai tace mata haka ne dan ta rabu da wannan mutum amma ba wai dan zata iya aikata abunda tace bane.
Around 10pm ceo ya shigo domin dubata,har bacci ya soma ɗaukarta,motsinshi a cikin ɗakin ne ya tasheta,a hankali ta buɗe idonta ta sauke su a kanshi,yana daga tsaye gaban gadon ya ɗan juya mata baya hannunshi riƙe da file ɗinta yana dubawa,from head to toe ta shiga kallonshi cargo pant ne a jikinshi haɗe da shirt mai gajeren hannun,breton cap ce a kanshi hakan ya ɓoye sumar kanshi,ɗan lumshe ido tayi kafin ta buɗe, a hankali ta furta “who Are You?” har cikin tsakiyar kanshi yaji maganarta...
*Ep 43_44*
____________________________
A hankali ta furta “who Are You?” har cikin tsakiyar kanshi yaji maganarta bai yi tunanin ba bacci take ba,juyowa yayi yana fuskantar ta,kamar ko da yaushe fuskarshi a rufe take da mask,bed ɗin ya nufo,zama yayi saman chair
“good Nailarh,I think we discharge u tomorrow”
“why are u pretend,i'm asking u who are you”
“i told you since,I'm your destiny” wani matsiyacin kallo ta watsa mashi
“who do you think you are,do I look like idiot to you?” girgiza kai kawai yayi ba tare da yace mata komai ba
“ko dan ka ganni kwance a nan yasa har ka samu damar shige man,do you know who I am” girgiza mata kai yayi
“i don't Know who u are Nailarh”
“that's why ka ke man shiga hanci da ƙudundune kenan,amma I will teach you a lesson,I will show you who I am,you regret all abubuwan da kayi man”
“idan zaki sa nayi regretting ki sassuta man kinji baby” wani banzan kallo ta watsa mashi,kamo hannunta yayi cikin nashi
“Nailarh!” ya kira sunanta in a serious tolk,cikin murya mai daɗi da tausasawa ya fara magana
“am sorry about what happen in N R T,am sorry Nailarh I don't mean to hurt you,bansan hakan zai jefaki a matsala ba,abunda ki ka yima wannan mutunanen ne yasa har nayi ƙoƙarin ganin nayi nasara a kanki amma ba da nufin hakan na zo ba,I just came to see you amma ba da nufin yin nasara akan ki ba,I am deeply sorry for hurting u, please forgive me”
“tsoro kaji ne ka ke bani haƙuri?” girgiza mata kai yayi
“i hate my self because I hurt you,duk hukuncin da zaki man i deserve it” kallon shi ta shiga yi
“Ohk but why Are You hiding your face?” murmushi yayi
“bana son na tsoratar dake da munin fuskata ne” dariya ta saki ba tare da ta shiryama hakan ba
“Who told you I'm scare?”
“ba kowa,but nayi expecting hakan ne”
“bana jin tsoro,na saba ganin fuskoki mabanbanta,taka bata isa ta bani tsoro ba”
“I will show you in a rightiouse time but not now”
“why not now”
“this is not the right time” wani kallo ta mashi ba tare da tace komai ba,tashi yayi daga saman chair ya nufi drugs ɗinta, injection ɗin dake ciki ya shiga haɗawa,ita dai binshi kawai take da ido ba tare da tace ƙala ba,inda take ya nufo bayan ya kammala haɗa Allurar “give me your hand” kallonshi kawai tayi ba tare da tayi abunda yace ba,ganin haka ne yasa da kanshi ya kama right hand ɗin ta ya mata Allurar,kafeshi da ido tayi kamar mai son ganin wani abu a fuskanshi,bata da wani buri bayan ta ɗau fansar abunda yayi mata,yanzu burinta ta ga fuskarshi,kwata kwata idonshi baya kanta Allurar da yake mata yake kallon harya kammala ya zare Allurar,unexpected yaji hannunta a saman mask ɗin dake fuskarshi tana ƙoƙarin zame mashi shi,saurin riƙe hannunta yayi,cire hannun yayi daga saman fuskarshi,kallonta ya shiga da tsantsar mamaki,sakin hannunta yayi haɗi da barin wurin batare da yace mata komai ba,ko fiv e minute ba tayi ba bacci yayi awan gaba da ita.
Kamar yanda yace washe gari a kayi discharge ɗinta,gagarumin party Malika ta shirya mata,sosai Nailarh tayi farin ciki ganin yanda maids ɗin gidan su ka damu da ita,hakan yasa ta sake jin wani kwanciyar hankali duk wata damuwarta akan abunda ya faru ta ragu,har dare shagali su ke gidan duk dan saboda Nailarh.
*ABUJA NIGERIA*
Alhmdllh jikin Nainarh kamar yanda Dr fawar yace ba wani ƙonewa tayi ba fatanta ce bata son zafi,kulawa sosai mom ke bata duk bayan ƴan lokuta sai ta leƙo ɗakin ta dubata,haka Fa'iza a ɗakin nasu ta wuni tunda su ka dawo daga hospital ɗin,Yumnah ma Ba'a barta a baya ba dan duk tafi kowa shiga damuwa,ya Adnan ma sai da dare yayi sosai tukun ya tafi gida,Irfan tunda ya fice daga gidan bai sake dawowa ba,Nainarh ta ji haushin rashin nuna damuwarsa akan abunda yayi mata,wani sabon tsanarshi ne ya rufeta,saƙe saƙen ta yanda zatai taking revenge dan shima yaji zafin da taji.
Yanzu ma zaune take gaban door glass ita kaɗai a ɗakin,skert ne a jikinta haɗe da riga mai hannu ɗaya saboda ciwan dake chest ɗinta, sai mayafi dake saman kanta,ta yaye curtains ɗin dake jikin door ɗin,zuba ma cikin Estate ɗin ido tayi tana kallon securitys ɗin dake kai kawo,turo ƙofar ɗakin da aka yi ne yasa tayi saurin kai dubanta ga ƙofar,Enaaya ce ta shigo da gudu tana buɗema Nainarh hannu,riga da wando ne a jikinta,kanta babu scaf anyi mata space buns,ga wasu baby ribbons da aka sa mata masu kyau, kamar ko da yaushe fuskarta na manne da glasses, murmushi Nainarh ta saki har ta ƙaraso inda take,side hug tayi mata saboda ciwan jikinta
“sannu Aunty Nainarh,ya jikin?” Enaaya ta faɗa da tsantsar kulawa tana kallon ciwan dake jikin Nainarh
“naji sauƙi Enaaya,ke da momy ku ka zo?”
“A'a,momy na gida,dady ne ya kawo ni na gaishe dake”
murmushi ta saki tana shafa fuskarta “nagode sosai,ya ki ka baro momy?”
“tana lafiya,ki zo muje parlor dady na can”
“no ba sai naje ba Enaaya”
“please ki dai zo muje,sai ku gaisa ya sake maki ya jiki” Enaaya ta faɗa tana marairaice fuska,gyaɗa mata kai Nainarh tayi,tashi tayi daga saman chair,ƙofar fita daga ɗakin su ka nufa Enaaya na riƙe da hannunta,suna isa bakin ƙofar ana buɗe ƙofar,sauri dakatawa su ka yi,ya Adnan ne ya turo ƙofar, blue Black ɗin yadi ne a jikinshi mai taushi,kanshi sanye da hula,sai ƙamshi yake kamar wanda zaije zance,da sauri Nainarh taja mayafin dake kanta ta rufe jikinta,saurin sakin hannunta Enaaya tayi tana bi ta gefan dadyn nata ta fice daga ɗakin,ɗan sadda kai tayi tana gaishe shi da kulawa ya amsa mata
“lafiya lau Nainarh,ya jikin na ki,hope dai da sauƙi?”
“da sauƙi Alhmdllh”
“Allah ya ƙara afuwa,fatan dai babu inda ke maki ciwo, sannan wurin ya daina zafi”
“Eh ya daina,babu in da ke man ciwo”
“masha Allah haka ake so,Allah ya ƙara lafiya”
“Ameen,ya Aunty Nadiya?”
“tana lafiya”
“ina gishe da ita” gyaɗa mata kai yayi,shiru su ka yi babu wanda ya sake cewa komai, Nainarh jira take yace mata sai anjima,shima jira yake tace mashi,ɗan ɗago da kai tayi kalleshi ganin ita yake kallo ne yasa tace “yaya ko akwai wani abu” saurin girgiza mata kai yayi “ba komai Nainarh, Allah ya ƙara afuwa sai anjima,ki kula da kanki”
“in sha Allah,Nagode” gyaɗa mata kai kawai yayi ya juya ya bar bakin ƙofar,maida ƙofar tayi ta rufe ta koma cikin ɗakin,bayan tafiyar ya Adnan da kamar five minutes Yumnah ta shigo ɗakin hannunta riƙe da ƙatuwar ledar Eatery Enaaya na bayanta riƙe da wata ledan,da mamaki take kallonsu har su ka ƙaraso in