Showing 126001 words to 129000 words out of 139687 words
har motarshi ta fice daga masallacin,ya so ya tambaye shi ko Zaabith na tare da shi dan tun jiya rabonshi da shi ga wayar shi da yake kira baya samu,ganin reaction ɗinshi ne yasa kawai yayi shiru,motocin shi ya nufa,suma barin masallacin su ka yi direct hospital su ka nufa.
Irfan tunda su ka shigo mota yayi shiru idanun sa na akan side road,kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar farin cikin da yake ciki,jin abun yake kamar mafarki wai yau shi da Noor ɗin shi sun zama mata da miji,mafarkin da su ka daɗe suna yi ya zama gaskiya,kallon shi Waseef yayi ya na sakin murmushi “Ango kasha ƙamshi,tunanin mi ka ke?” ya faɗa yana kallonshi, murmushi kawai Irfan ɗin yayi ba tare da ya ce mashi komai ba
“yanzu dai ba sauran tashin hankali da ɓacin rai,finally dai burinku ya cika,Irfan angon Nurjahan,gaskiya nayi farin ciki bro,Allah ya baku zaman lafiya,har na ƙosa Noor ta samu sauƙi musha shagali” murmushi Irfan ya saki yana girgiza kai.
A jere motocin su suka shiga cikin hospital ɗin,a compound su ka yi parking,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga fitowa daga motocin suna nufar cikin hospital ɗin,ɗakin da aka kwantar da kainart su ka fara zuwa Laatifa da yumnah sai fa'iza kawai su ka samu mom da mom Maryam sunje ward ɗin da aka kai Noor,a jiya aka canza mata ɗaki,tunda aka kawota ba su samu damar zuwa ba sai yanzu da aka fito da ita daga Emergency ward,har yanzu Kainart a kwance take,data farka nurses ke sake mata Allurar bacci a bisa umarnin Dr Lelarh.
gaban gadon su ka ƙarasa Adu'a su ka shiga yi mata su yumnah na amsa masu da Ameen sun ɗan jima a ɗakin kafin su ka fice zuwa ward ɗin da aka kai Noor ɗin babu nisa daga nan, Irfan gaba ɗaya ya ƙosa ya yi ido biyu da Amaryar tasa dan zaman da su kayi a ɗakin da kainart take daurewa kawai yake dan ji yake kamar ana tsirarshi,ya so ace wurin Noor ɗin su ka fara zuwa.
A bakin ward ɗin su ka tsaya,su mom ne su ka fito,tunda su ka fito idonta ke kan Irfan shima kallonta yake rabon da su sa juna a ido tun ranar Friday.
Abbah da su dady ne su ka shiga,sai dai su dunga shiga ɗaya bayan ɗaya saboda sun yi yawa.
Ƙara sowa su mom su ka yi wurin,cike da girmamawa su ka shaga gaishe da su suna amsa masu da kulawa,zama su ka yi akan waiting chairs ɗin dake wurin banda Irfan da duk a ƙagare ya ke su Abbah su fito.
kamo hannunshi mom tayi tana kiran sunanshi ba ƙaramin kewarshi tayi ba,ta san fushi yake da ita amma yanzu ta san komai ya wuce tunda ya samu abunda yake so,faɗawa yayi jikinta yana hugging ɗinta “am sorry mom,kiyi haƙuri idan na ɓata ranki dan Allah ki yafe man nayi kuskure bazan sake ba” ya faɗa a hankali,murmushi mom ta saki tana shafa bayan shi “karka damu Irfan komai ya wuce,fatan Allah ya ba Noor lafiya” tana jin saukar hawayenshi a bayanta wanda ba na komai ba ne sai na farin ciki
“Ameen nagode Sosai mom, Allah ya ƙara girma ya kare gabanki da bayan ki,Allah ya haskaka maki mom,Allah ya bamu ikon faranta maki kamar yanda ki ke faranta mana,kin sani farin ciki mara misaltuwa,nagode sosai mom” jikin su ya Naeem ne yayi sanyi da jin irin Adu'ar da Irfan yake mata kai ka san yana cikin farin ciki,ya Naeem duk sai yaji wani iri lokacin da ya tuna ranar da su ka tasa Irfan ɗin a gaba akan sai ya rabu da Noor,bai san cewa har haka yake sonta ba.
ɗan bubbuga bayan shi tayi “godiyar ta isa haka Irfan,nauyi ne a kaina na faranta ma ku,ya isa haka kaji Allah ya sanya Albarka a cikin Auren ku ya ba ku zaman lafiya” da Ameen ya amsa,raba jikin su tayi, murmushi tayi tana kallon fuskarshi yayinda take goge mashi hawayen da ke fuskarshi,su mom Maryam sai sakin murmushi su ke,wurin su ya Naeem ya matsa ɗaya bayan ɗaya ya shiga ba su haƙuri musamman ya Naeem, murmushi kawai su ka mashi suna masu Allah yasa Alkairi da fatan zaman lafiya.
wurin Kainart su mom su ka koma,su dady sun ɗan jima tukun su ka fito daga ɗakin,tashi su ya Naeem su ka yi su ka shiga Irfan na bayan su,da sallama su ka shiga,a zaune su ka hango uncle mutallab gaban gadon da Noor ɗin take kwance, sallamar da su ka yi uncle mutallab ya amsa masu yana kallon Irfan,har gaban gadon su ka ƙaraso Banda Irfan da ya toge a bakin ƙofa,tunda ya sauke idonshi akan Noor ɗin da idanunta ke a lumshe ya kasa ko da motsi mai ƙarfi,wani mugun tausayinta da kewarta ne haɗe da ƙaunarta ke shigar shi a lokaci guda.
ya mai jiki su ya Naeem su ka shiga yi ma uncle mutallab ɗin bayan sun gaisa,da Alhmdllh ya ke amsa masu,ba su wani jimaba su ka fice,kallo Irfan da har lokacin yana bakin ƙofar tsaye uncle mutallab ɗin yayi “Irfan!”ya kira sunanshi,kallonshi Irfan ɗin yayi
“ƙaraso mana” uncle mutallab ɗin ya faɗa,sai a lokacin ya ƙaraso gaban gadon,da ladabi yace “ina wuni uncle,ya mai jiki” da Alhmdllh ya amsa mashi “ina ka shiga jiya nake ta kiran ka Irfan?” sadda kai ƙasa Irfan ɗin yayi ba tare da yace mashi komai ba “ka yi shiru?”
“bana tare da wayar ne uncle” jin jina mashi kai yayi “ok,matsa ga Noor ɗin can, kwana tayi tana kiran sunanka,nayita nemanka ne saboda halin da take ciki,banji daɗin hukuncin daka yake ba Irfan,a dalilin guje matan da kayi yasa ta shiga wannan halin?”
“kayi haƙuri uncle,nayi hakan ne saboda hukuncin da mom ta yanke a lokacin,amma kayi haƙuri ban san hakan zai sa ta aikatama kanta haka ba”
“shikenan ai Irfan,komai yanzu ya wuce,zo ka zauna” ya faɗa yana tashi daga saman chair da yake zaune,matsawa Irfan ɗin yayi ya zauna kan chair,kallon Waseef dake tsaye gefen gadon uncle yayi yana faɗin“waseef tunda kun zo bari naje gida na dawo,ban samu na koma ba tunda jiya”
“to shikenan uncle ba komai,nima tafiya zanyi Irfan ɗin ma ya isa ya kula da ita kafin ka dawo”
“to shikenan,Irfan sai na dawo” da to Irfan ɗin ya amsa,Waseef ma ce mashi yayi sai ya dawo,ficewa su ka yi daga ward ɗin.
ba komai yasa uncle mutallab tafiya ba sai dan ya ba su damar kasancewa da juna ko hakan zai taimaka Noor ɗin,Waseef ma dalilin tafiyarshi kenan dan ya san idan suna wurin Irfan ɗin bazai samu sakewar da zai ba Noor ɗin kulawar data kamata ba.
tunda ya zauna ya kafeta da ido yana kallon kyakkyawar fuskarta da duk ta faɗa ga wani irin haske da tayi,ya kai tsawan 5 minutes ƙalla baice ba,ɗan ajiyar zuciya ya sauke yana kamo hannunta cikin nashi,a hankali ya kira sunanta yana kai ɗayan hannunshi saman fuskarta,shafa gefen fuskarta ya shiga yi yana sake kiran sunanta,slowly ta shiga buɗe idanunta da su kayi mata nauyi ta sauke akan fuskarshi,tunda aka kawota hospital ɗin wannan ne karon farko data buɗe idanunta duk zuwan da ake gaishe da ita idonta a rufe yake.
sake kiran sunanta yayi yana faɗin“ya jikin na ki?” ɗan lumshe ido tayi tukun ta buɗesu tana sake kallon fuskarshi
“da sauƙi?” ya sake jefa mata tambaya,hawaye ne su ka taru a idonta,sake shafa fuskarta yayi da hannunshi dake saman fuskar yana girgiza mata kai alamar kar tayi,gyaɗa mashi kai ta shiga yi tana ƙoƙarin tashi zaune,sakin hannunta dake cikin nashi yayi yana miƙewa tsaye,taimaka mata yayi ta tashi zaune,zama yayi gefen bed ɗin yana sake kamo hannuwanta,a hankali ya fara magana“why Noor,mi yasa za ki yi haka,dubi halin da ki ka jefa kanki,kin kuwa san halin da zan shiga idan na rasaki?” zuba mashi ido kawai tayi “ko dana daina kiranki ba wai hakan na nufin na rabu dake ba ne ko na daina sonki,Noor bazan taɓa iya daina sonki ba,kuma ki sani babu wata mace a rayuwar nan da zata maye man gurbinki,bazan iya rayuwa da wata ba bayan ke,mi yasa ba kiyi tunanin halin da zan shiga ba lokacin da zaki sha poison,ke ɗin wani ɓangare ce ta rayuwata Noor,rasaki abu ne wanda ruhina bazai iya ɗauka ba,karki sake maimaita kuskure irin wannan kinji”
kallonshi kawai take yayinda hawaye ke sake taruwa a idanunta “please Noor kiyi man magana,ina so naji muryarki” ya faɗa yana kissing hannunta dake cikin nashi.
hawayen da su ka taru a idanunta ne su ka shiga zubowa,lallashinta ya shiga yi yana goge mata hawayen
“kiyi haƙuri idan maganganuna ne su ka ɓata ranki,ban maki faɗa dan na saki kuka ba kawai banji daɗin abunda ki ka yi ba ne amma yanzu komai ya wuce” lallashinta ya shiga yi har ya samu ta daina kuka,murza hannunta dake cikin nashi ya shiga yi yana faɗin
“ban sani ba ko uncle ya sanar dake mom ta janye furincinta akan Auren mu,komai ya wuce Noor daga ƙarshe dai burinmu ya cika,a yau mu ɗin mallakin juna ne,daga yau na tashi daga matsayin saurayinki na dawo mijinki,Noor yanzu ke matatace ba budurwata ba,ban san mi yasa su ka fasa ɗaura Auren mu bayan sallah kamar yanda Abbah yace ba,amma na san hakan bazai wuce yana da nasaba da halin da ki ke ciki ba,Noor su dady yau sun sani farin ciki mara misaltuwa,jina nake kamar an sauke man wani ƙaton dutse daga saman kaina,ina fatan kema kina jin abun da nake ji” zame hannuwanta dake cikin nashi,motsi ta shiga yi da bakinta tana mashi alama da ya zo gareta,a hankali ya matsa sosai kusa da ita,jawota yayi zuwa jikinshi,tightly yayi hugging ɗinta,saukar hawayenta yaji saman shoulder ɗin shi.
hitting bayanta ya shiga yi a hankali yana faɗin “please ki daina kukan nan it's paining me” shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya,sun ɗan jima a haka kafin a hankali ta kai bakinta saitin kunnen shi,magana ta shiga yi mashi,da ƙyar take furta kalmomi,baza ka iya jin mi take faɗa mashi ba saboda muryarta da tayi ƙasa sosai,shi kanshi sai yayi da gaske yake gane abunda take furtawa,saurin ɗago da kanta yayi daga jikinshi jin furucin da tayi.
Cike da tashin hankalin furucin da tayi ya shiga bin fuskarta da ido,kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar damuwar da yake ciki
“mi yasa zaki faɗi haka Noor, ciwo ba mutuwa bane, Adu'a ya kamata kiyi kinji” girgiza mashi kai tayi hawaye na bin fuskarta,ƙarfin hali tayi wurin furta “ka yafe man ya Irfan,ni kaɗai na san halin da nake ciki” girgiza mata kai ya shiga yi
“tunda har baki mutu lokacin da ki ka sha guba ba yanzu ma ba zaki mutu ba,babu abunda zai sameki Noor,in sha Allah zaki samu sauƙi,think about me mana, idan ki ka tafi ya ki ke so nayi da rayuwata,baki tunanin halin da zan shiga?” ya faɗa yana share mata hawayen dake zarya daga fuskarta
“Noor we are husband and wife now,think about our unborn babies kin ji,ki daina faɗan mutuwa in sha Allah we will fulfill all our dreams soon,Allah zai baki lafiya,ko kin manta irin rayuwar da muke fatan muyi bayan Auren mu?” hawayen dake zuba daga idanunta ne su ka ƙarfin gudu,girgiza mashi kai ta shiga yi,ita kaɗai ta san halin da take ciki,duk bayanin da zata ma Irfan ba wai zai fahimceta bane.
lallashinta ya shiga yi “ki daina kukan nan dan Allah kina karyaman zuciya,ko nima kina son ganin nawa hawayen ne?” girgiza mashi kai tayi “to dan Allah ki dai na kinji,in sha Allah zaki samu sauƙi” hannunshi dake saman fuskarta ta kama ta kai kan surgical cap ɗin dake kanta,cike da kulawa yace “ya aka yi,ciwo kan yake maki ne??” girgiza mashi kai tayi a hankali ta furta “ka cire man”
“hulan?” ya faɗa da sigar tambaya,ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ohk ya faɗa yana zame mata hular,kitson zane ne guda huɗu akan ta ɗan tufke ƙarshen kitson,ba laifin Noor akwai yalwar suma Masha Allah,kitson ya ɗan zamo saboda santsin da kanta yake da shi,kallon kitson yake da mamaki dan ya kasa fahimtar abunda take nufi da hakan
“me kitson yayi,yana maki ƙaiƙayine?” ya faɗa cike da kulawa, girgiza mashi kai tayi tana kai hannunta saman kitson,a hankali ta shiga cusa fingers ɗinta cikin kitson kamar mai shirin zaro wani abu,saurin riƙe hannunta yayi
“mi yasa ki ke son warware kitson,yana damunki ne?” a hankali ta furta “wani abu nake so na baka” da mamaki ya furta
“wani abu,a cikin kitson??”
“eh” ta bashi amsa
“ohk bari na ciro da kaina” ya faɗa yana kai hannunshi saman kitson,lumshe ido tayi tana ɗan kwantar da kan saman chest ɗin shi yanda zaiji daɗin ciro abunda take son bashin.
a hankali ya shiga ɗaga tsoran kitson yana mai mamakin miye ta ɓoye a cikin kitson,mamaki ne ya kamashi lokacin da ya ciro ɗan madaidaicin flash daga tsakiyar kitson dake kanta
“Noor ma ye wannan ɗin?” ya faɗa yayinda yake ɗago da kanta daga saman chest ɗin shi
“flash ne yaya” ta bashi amsa
“na san Flash ne,amma na minene?” ya faɗa cike da son jin ƙarin bayani daga gareta
“zai taimaka maka a duk lokacin da kaji kewata”
“ban gane mi ki ke nufi ba,wai Noor mi yasa ki ke faɗan haka,baki son yin rayuwa da ni ne yanzu?”
“ba haka bane ya Irfan,a duniyan nan bana jin akwai wata ƴa mace da zata so yin rayuwa da kai kamar yanda na so,kayi haƙuri ba a san raina nake faɗa maka haka ba amma ya zama dole ne,rayuwata ba mai tsayi bace,Allah bai ƙaddara za mu rayu da juna a matsayin ma'aurata ba,kayi haƙuri da rashina a rayuwarka” tunda ta fara magana ya zuba mata ido yana kallo,ya rasa mai zai faɗa mata ta fahimci ƙunar da kalamanta ke ma zuciyarshi,kamo hannunshi da ya riƙe Flash ɗin tayi tana cigaba da faɗin
“nasan ba lallai ka iya jurewa ba,amma karka damu wannan Flash ɗin a cike yake da abunda zai baka ƙwarin gwiwa da juriyar rashina,
ka man alƙawari bayan ba raina zaka cika man burina,duk wata alfarma dana nema a gareka zaka yi man ita,na maka zaɓi wanda nake ganin Alkairi a rayuwar ka,kayi haƙuri in sha Allah ina da tabbacin zaka so zaɓina”
zuba mata ido kawai yayi
“ka yafe man duk wani laifi da na maka,sannan ina neman Alfarma no matter what a rayuwar da za kayi ba tare da ni ba karka manta da ni ya Irfan dan Allah” ta faɗa yayinda wa su zafafan hawaye ke yar tseren fitowa daga idanunta,saurin manneta yayi da jikinshi yana jin wani iri a zuciyarshi,he can't imagine life without her,mi yasa sai da burin su ya cika Noor zata kasa jurewa,wace irin ƙaddarace wannan ke yawo da rayuwar su,mi yasa Noor ba tayi tunanin halin da zata jefa rayuwarshi lokacin da zata sha poison ɗin ba.
“please Noor ki daina faɗan haka,kina ƙona man zuciya da kalamanki,in sha Allah baza ki mutu ba,za mu rayu da juna kamar yanda mu ka yi fata,zanyi magana da dady na fitar dake outside of the country,in sha Allah zaki samu lafiya kinji” kwantar mata hankali ya shiga yi duk da shima yana buƙatar mai kwantar mashi da hankalin,dan gaba ɗaya ta gama jefashi a cikin wani hali da kalamanta.
Uncle mutallab sai around 6 na yamma ya dawo tare da mom fatilah,ba komai ya sa su ka zo tare ba sai kukan data tasashi gaba tana mashi kan ƙin barinta da yayi taga Noor ɗin,kamar yanda uncle mutallab ɗin ya bar Irfan haka ya same shi Noor ɗin har ta koma bacci,tunda ya samu lallasheta ta daina ku ka yake faɗa mata kalamai masu daɗi da sake kwantar mata da hankali,ya kuma yi mata alƙawarin in sha Allah gobe ko zuwa jibi zai fita da ita waje danta sake samu kulawa daga wasu likitocin duk da nan ma ba wai basa da kayan aiki mai inganci ba ne,kawai yana ganin kamar zata fi samu kulawa dai dai da yanda yake so duk da nan ɗin ma suna iya bakin ƙoƙarin su a kanta.
ko da ya sanar da uncle mutallab hukuncin da ya yanke na son fita da ita,sosai uncle mutallab yayi farin ciki da jin hukuncin da Irfan ɗin ya yanke,hakan ya sake tabbatar mashi da Noor zata samu kyakkyawar kulawa daga gare shi,ya kuma sake alfahari da kasancewar shi miji ga Noor ɗin
“nima nayi wannan tunanin Irfan,Amma ganin nan ɗinma akwai kayan aiki ma su inganci kuma likitocin mu na da ƙwarewa sosai akan aikin su”
“haka ne uncle,Amma halin da take ciki za'a duba,kamar canjin zai taimaka mata,amma duk yanda kace ba bu damuwa uncle” ya kai ƙarshen maganar a hankali alamar dai hankalin shi sai yafi kwanciya idan aka fitar da ita ɗin.
“bana da ta cewa Irfan,matarka ce kanada ikon fitar da ita ba tare da ma kayi shawara da kowa a cikin mu ba dama shawarace kawai na bada,amma naga kamar kafi son ka fitar da ita ɗin?”
ɗan sadda kai ƙasa Irfan ɗin yayi yana sakin murmushi
“ba haka bane uncle” murmushi shima uncle ɗin yayi,mom fatilah dai na jin su ƙala ba tace ba.
“karka damu,nayi matuƙar farin ciki da ganin irin kulawar da ka ke bata,na sake tabbatar da cewa zaka kula man da Noor yanda ya kamata,shikenan amma kafin komai ka fara sanar da ya Tahir da barrister tukun”
“eh uncle zan sanar da su,amma passport ɗin Noor ɗin?”
“karka damu,ka bar komai a hannuna yanzu dai ka fara sanar da su kawai”
“to shikenan uncle,muna godiya” murmushi kawai uncle mutallab ɗin ya sakar mashi.
Bayan sallar magrib Irfan ɗin yayi ma uncle mutallab sallama ya tafi gidan dan ya sanar da dady hukuncin da ya yanke,mom kuma tunda tana nan sai ya dawo dan yana da tabbacin baza tace komai ba haka ma dady,sallama yayi ma uncle ɗin akan zai sake dawowa zuwa anjima dan anan yake so ya kwana.
sai da ya tsaya a masallacin Estate ɗin yayi sallar isha tukun ya ƙarasa gidan,ko da yaje bai samu dady ba yana gidan Abbah,direct part ɗin shi dake gidan ya nufa dan yana buƙatar ya watsa ruwa ya canza kayan jikinshi,bayan nan yana buƙatar