Showing 117001 words to 120000 words out of 139687 words

Chapter 40 - SHIRYAYYAR ƘADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

da numfashi zaka tabbatar da ba ƙaramin jin jiki take ba har wata muguwar rama tayi iya daren jiya kawai,ba'a da ɗe da fito da ita daga Emergency ward ba,mom na daga zaune gaban bed ɗin hannunta riƙe da hannun kainart ɗin da babu komai a jikinshi,da ka kalli fuskarta zaka fahimci ba ƙaramin ku ka tasha ba,
laatifa na daga kana sofa fuskar nan tayi jawur idanunta sun kumbura,time to time take sa hankey ta goge hawayen da tun jiya su ka gagara tsaya mata,wani irin mugun tausayin ƴar uwarta take ji,ba komai ta tunawa zuciyarta ke sake karya ba sai irin farin ciki data shiga ciki lokacin da fawar ya tabbatar mata tana da ciki,data tuna sai hawaye sun wanke fuskarta,dady da Abbah na daga tsaye gefen bed ɗin,dady ya goya hannayensa a baya yayinda Abba ke riƙe da sandarshi babu yanda ba suyi da shi ba akan ya zauna amma yace A'a,kowannan su kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar damuwar dake shimfiɗe a fuskarshi.
Zaabith na daga can bakin ƙofa ya rakuɓe kamar maraya kallon ɗaya zaka mashi shima ka hango tsantsar tashin hankali da ruɗun da yake ciki hatta rigar jallabiyar dake jikinshi a baibai take,har wata yar rama yayi dare ɗaya kawai,da ka kalli idonshi tsantsar nadamace kwance a cikin su,tunda ya shigo ɗakin ya toge a nan,wani mugun shakkar kowa yake da tsoron matakin da za su ɗauka akan shi.
ƙofar ward ɗin ce aka turo gaba ɗaya su ka kai dubansu ga ƙofar dan ganin waye zai shigo,wani faɗuwar gaba ne ya riske su a lokacin da su ka sauke idonsu akan waƴanda ke shigowa, zaabith zuciyarshi kusa tsayawa da aiki tayi,kallon juna Abbah da dady su kayi,da kalli fuskar su kasan suna cikin tsantsar tashin hankali,mom tayi tunani su yumnah ne su ka dawo,ba kowa bane face uncle mustafa,yana daga gaba mom Maryam da su Ammar na bayanshi,da gudu Ammar da Aman su ka nufo bakin bed ɗin suna kuka,mom Maryam ma ku ka take kamar ƙaramar yarinya,tashi mom tayi ta nufeta,kamo hannunta tayi tana lallashinta,bakin bed ɗin ya ƙarasa ba tare da ya kalli kowa dake cikin ɗakin ba,bazaka iya gane actuall halin da yake ciki ba fuskarshi ita ba a ɗaure ba ita ba a sake ba.
Inda mom ta tashi ya zo ya zauna,hannun kainart ɗin dake kan bed ya kamo cikin nashi ganin haka ne yasa zaabith lallaɓawa ya fice daga ɗakin a tunaninshi babu wanda ya ganshi, direct parking lot ɗin hospital ɗin ya nufa,motar shi dake wurin ya nufa,buɗe driver seat yayi da nufin zai shiga,ɗaga ƙafar da zaiyi yaji an toshe mashi baki ta baya,kokawa ya shiga yi da wanda rufe mashi baki,baiyi aune ba yaji an shaƙa mashi wani abu,baya yayi zai faɗi,da saurin wasu jibga jibgan ƙatti dake sanye da baƙaƙen kaya, fuskokinsu rufe da mask,sama su ka ɗagashi,booth motar dake kusa da tashi su ka buɗe su ka saka shi,babu wanda ya gansu kasancewar parking lot ɗin a ƙasan ginin hospital ɗin yake kuma haka nan ya fito ba tare da securitys ba,a tamanin su ka fice daga hospital ɗin gaba ɗaya.
su Aman na daga ɗayan side ɗin,kuka su ke suna kiran sunan mahaifiyar ta su wallahi dole su baka tausayi.
Adu'a ya shiga karantowa yana tofama Kainart ɗin
gaba ɗaya ɗakin zuba mashi ido su ka yi suna kallon shi har ya kammala yi mata Adu'a, kissing forehead ɗin ta da hannunta dake cikin nashi yayi kafin ya miƙe ya nufi ƙofar fita ya fice,babu wanda bai sha jinin jikinshi da wannan reaction ɗin na uncle mustafa ba,musamman dady da Abbah da ba su san waye ya sanar da shi ba.
wurin daya tashi mom Maryam ta nufa ta zauna, hawaye dake idonta ta goge,forehead ɗin kainart ɗin tayi kissing kafin ta ɗaga idonta ta kalli dady da Abbah gaishe da su tayi girmamawa tana tambayar su ya mai jiki da Alhmdllh su ka amsa mata,maida dubanta tayi akan fuskar kainart ɗin,dady ne ya kama hannun Ammar da Aman haɗa su yayi duka yayi hugging,ɗan bubbuga bayan su ya shiga yi yana lallashin su har su ka yi shiru.
ɗan gyaran murya Abbah yayi yana sauke ajiyar zuciya,bakin gadon ya matso,kallon seconds 10 yayi ma kainart ɗin kafin yayi mata Adu'a,kallon mom da mom Maryam yayi “ni zan koma gida, Allah ubangiji ya bata lafiya” da Ameen su ka amsa gaba ɗayan su, laatifa dake zaune kan sofa dady ya nufa,su Ammar yace su zauna kusa da ita “kukan ya isa haka laatifa in sha Allah zata samu sauƙi,ki lallashe su suma kinji”
“to dady” ta faɗa tana jansu zuwa jinkinta ta rungume su,a hankali take hitting bayan su,dady tare su ka fice da Abbah domin yayi mashi rakiya,a bakin ƙofar ward ɗin su ka samu securitys ɗin Abbah da drivern shi,cike da girmamawa suke tambaya ya mai jiki da Alhmdllh su ka amsa masu.
tun daga corridor da zai sada su da reception su ke jiyo hayaniya haɗe da koke koke,suna ƙarasowa reception ɗin uncle mutallab na shigowa ɗauke da Noor,Kamar bata numfashi bakinta sai fitar da kumfa yake,nureses na biye da shi da stretcher sun yi sun yi ya bari su ɗauki Noor ɗin yaƙi,mom Fatilah na bayan su sai ihu take kamar wacce uwarta ko ubanta su ka rasu gaba ɗaya ta cika reception ɗin da kuka,a hanzarce su ka ƙarasa cikin reception ɗin suna ambatar innalillahi wa Innah ilaihi raji'un...
Dr's biyu ne su ka nufo Uncle mutallab ɗin,babu wanda ya kalla a cikin su,Direct Emergency ward ya nufa da ita,mara mashi baya su ka yi harda wasu nurses,a bakin ƙofar dady da Abbah su ka tsaya hankalin su a tashe,ga kukan da mom fatilah ke yi duk wanda ya ganta sai yayi tunanin mutuwa aka mata.
lallashinta Abbah da dady su ke amma kamar ƙara tunzurata suke,abun nata kamar mai taɓin hankali.
a saman Electrical bed ɗin dake ɗakin ya kwantar da ita,da sauri ɗaya daga cikin nurses ɗin ta miƙa mashi surgical gown dake hannunta,Nurses ɗin da Dr's ɗin da su ka biyo shi suma gown ɗin su ka shiga zurawa a jikin su,ba komai yasa su ka kawo ido su ka zuba ma uncle mutallab ba sai he's being their colleague and bugu da ƙari hospital ɗin na su ne.
Emergency treatment su ka shiga ba ma Noor,sun shafe kusan two hours suna abu ɗaya da ƙyar su ka samu tafarfaɗo ta hanyar defibrillator,kwata kwata Bata cikin hayyacinta banda kiran sunan Irfan babu abunda take shima sai ka kai bakinka saitin kunnenta sosai tukun zaka iya ji.
allurar bacci uncle mutallab yayi mata saboda wannan motsa baki zai iya haifar mata da matsala,ba ƙaramin raunata tayi ba ta shiga halin rayuwa ko mutuwa,yayi mamakin ma yarda har take iya furta sunan irfan.
zama yayi gaban bed ɗin da take kwance,zuba mata ido yayi yana kallonta cike da tausayawa,yayi taikici da baƙin cikin halin data shiga saboda ta rasa abunda take so,wani irin tsanar kanshi yake ji na gaza yi mata abunda take so gashi har tana neman ɗaukar rayuwarta,wasu irin hawaye ne su ka taru a idonshi,wata irin wutar tausayinta ce ke ci a zuciyar shi,duk yanda yake daurewa sai da ya zubar mata da ƙwalla,ƙarasowa Dr's ɗin su ka yi inda yake,ganin yanda ya kama hannun Noor ɗin ya riƙe gashi da alama kuka yake yi, hakan yasa likitocin su ka shiga kwantar mashi da hankali in sha Allah zata samu sauƙin,jinjina masu kai kawai yayi,jinin Noor ɗin da su ka ɗiba ɗaya daga cikin nureses ɗin ta ɗauka ta nufi lab ɗin su,tana fita Abbah da dady su ka nufota suna tambayar lafiya haka ma mom fatilah
“Abbah ku kwantar da hankalin ku,in sha Allah zata samu sauƙi” ta faɗa tana nufar lab ɗin,ɗaya daga cikin Dr's ɗin ne ya fito,da sauri ya nufi su Abbah “Lelarh mike damunta ne?” dady ya faɗa
“she's poisoning her self” har haɗa baki su ke waurin furta innalillahi wa Innah ilaihi raji'un,wani sabon kuka mom fatilah ta sake fashewa da shi
“amma yanzu a wane hali take ciki?”
“to da sauƙi zamu ce,dan gaskiya she is on life support”
“innalillahi wa Innah ilaihi raji'un,amma wane irin poison ne tasha”
“abunda muke bincike kenan,poison ɗin ya mata illa gaskiya,ban san ya akayi ba har aka yi sakacen data aikata ma kanta haka ba” ya faɗa yana kallon mom fatilah dake ta aikin tsiyayar da hawaye
“zamu iya shiga ciki mu dubata?”
“She is in a critical condition gaskiya,ku yi haƙuri zuwa lokacin da zamu kammala binciken,in sha Allah zata samu sauƙi”
“to shikenan ba damuwa,ina mutallab ɗin yake?”
“yana ciki” ya basu amsa yana kallo mom fatilah da dole ta baka tausayi
“please ma'am ki daina wannan kukan, Adu'a ya kamata kiyi mata”
jinjina mashi kai tayi ba tare da ta daina hawayen ba gaba ɗaya gani take laifinta ne da ace ta amince da Aurenta da Irfan da duk hakan bata faru ba,wani irin mugun dana sanin abunda ta aikata take,tayi data sanin abunda taje tayi ma mom har gida,gashi yanzu ta dalili wani dalili nata mara tushe zata kashe ƴarta da kanta.
dady ma kwata kwata baiji dadi abun ya zo a haka ba,a ganin shi duk laifin mom ne da bata nuna ma Abbah bata son Auren da duk hakan bata faru da Noor ba.
“zan shiga lab ɗin naga halin da ake ciki kan binciken” Dr Lelarh ya faɗa “to shikenan dr” Abbah ya faɗa,anan tsaye ya barsu waiting chair dake kusa da su mom fatilah ta nufa ta zauna.
“Abbah ya kamata ka tafi gida ka huta tun asuba ka ke nan” dady ya faɗa yana kallon Abbah “Tahir da dai ka bari sun gama binciken sai na tafi”
“A'a Abbah gama binciken su ba yanzu ba,ka tafi kawai in sha Allah duk abunda ake ciki zan sanar da kai”
“to shikenan”Abbah ya faɗa,sauka su ka yi zuwa parking lot dake ƙasan ginin hospital ɗin,securitys ɗin shi da drivern shi na biye da su a baya,har gaban motar shi ya raka shi,da kanshi ya buɗema Abbah back seat ya shiga,shiga driver yayi securitys ɗin ma su ka shiga motocin su,key su ka yima motocin su ka nufi gate hospital ɗin,har sai da yaga ficewarsu daga hospital ɗin tukun ya juya da nufin komawa ciki idanunshi ne su ka sauka akan motar zaabith,
da mamaki yake kallon motar ganin driver seat a buɗe dama zaabith ɗin bai tafi ba kenan ya faɗa a zuciyarshi,nufar motar yayi,abun ya ɗan ɗaure mashi kai ganin motar a buɗe babu kowa a ciki,waige waige ya shiga yi amma bai ga kowa ba kasancewar parking lot a ƙasan ginin hospital ɗin yake ko compound ɗin asibitin ba'a gani,tunani ya fara ko tashin hankalin abunda ya faru ne yasa ya manta da ƙofar a buɗe,maida mashi marfin yayi ya rufe,yana shirin barin parking lot ɗin wata mota ta shigo, kallon motar yayi har su ka yi parking,buɗe door ɗin motar aka yi,mamy ce ta fito daga driver seat yayin da mom halima ta fito ta ɗayan side ɗin,back seat aka buɗe,hajiya zainab ce ta fito ƙanawar mom fatilah,cikin hospital ɗin su ka nufa kwata kwata ma ba su lura da dady dake tsaye ba, tsantsar tashin hankali ne kwance a saman fuskokin su,gaba ɗaya a kiɗime su ke,shima ciki ya nufa.
tun kafin su ƙarasa hajiya zainab ta fashe da ku ka ganin ƴar uwar ta ta ,mamy ma da mom Maryam ƙwalla su ke matsewa “garin yaya haka ta faru Aunty fatilah?” hajiya zainab ta faɗa cikin muryar kuka “zainab nima ban sani ba,mai aiki na ke sanar da ni wai taje ɗakin Noor ta sameta a kwance bakinta sai fitar da kumfa yake,lokacin da zan fito har mahaifinta ya fito da ita”
“amma waye zai bata guba,gida da ga ke sai mahaifinta?” mom halimatu ta faɗa “sai mai aikin su ba” a cewar mamy
“nima ban sani ba,amma ko waye ya cutar dani,bazan taɓa yafe mashi ba” mom fatilah ta faɗa tana goge hawayen dake zuba daga fuskarta.
dady ko da ya shigo bai dawo Emergency ward ɗin ba,VIP ward ya nufa in da aka kwantar da kainart,a bakin ƙofa ya tsaya yana ciro wayarshi daga cikin aljihu, Number uncle Mustafa yayi dialing dan gaba ɗaya hankalin shi bai kwanta da yanayin shi na ɗazu ba.
har kiran ya katse baiyi picking ba,nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke yana maida wayar cikin aljihun shi,tura ƙofar ward ɗin yayi ya shiga,kamar dai yanda ya barsu ɗazu a haka ya same su, Ammar da Aman tuni bacci ya ɗauke su a jikin Laatifa.
tunda ya shiga ya sauke idon shi akan mom dake zaune ɗayan side ɗin bed ɗin ta zabga uban tagumi,da wani irin kallon mai wuyar fassarawa ya ke binta,daga yanayin fuskarshi ta fahimci akwai matsala,dan damuwar data hango a fuskar shi ta wuce ta halin da kainart ke ciki, gaba ɗaya tasha jinin jikinta ganin irin kallon da yake jefa mata,kallon two to three minute yayi mata kafin ya sauke ajiyar zuciya,juyawa yayi ya nufi ƙofa ya fita,da mamaki take kallon shi har ya fice,tashi tayi tabi bayan shi a saman waiting chairs dake bakin ward ɗin ta same shi zaune,ƙarasawa tayi gaban shi tana faɗin “yallaɓai Lafiya?” ɗago da kanshi yayi, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai,zama tayi kusa da shi “yallaɓai magana nake,me ke damunka ne?” da buɗar bakin shi sai cewa yayi “mi yasa ki ka sauya Zulaihart,da ba haka ki ke ba?” da mamaki mom ke kallonshi “Janar nayi wani abu ne da yasa kace haka?” ɗan nisawa yayi kafin yace ”a da ke ɗin mai haƙuri ce, a da ke ɗin mai tausayi ce,a da ke ɗin mai tsoron cutar da bayin Allah ce, amma lokaci ɗaya kin sauya,baki ɗaya ɗabi'unki sun sauya” tunda dady ya fara magana mom ke bin shi da ido,idanunta sun kaɗa jawur,mijinta abun alfaharinta kullum ya buɗe baki Alkairinta yake faɗa yau an wayi gari da bakin shi yake faɗin ta sauya,tsintar kanta tayi a wani irin yanayi na karyewar zuciya “dan Allah yallaɓai kayi haƙuri ka faɗa man mi na aikata ka ke ganin na sauya,wa na cutar?”
murmushin takaici dady ya saki “a dalilin sauyin da ki ka yi kin cutar da yarinyar da ba taji ba ba ta gani ba Zulaihart” faɗuwa gaban mom yayi jin abun da dady yace,tuni hawayen da su ka taru idonta suka shiga zubowa “ka sani a duhu,dan Allah ka faɗa man mi na aikata?”
“saboda dalilinki mara tushe Noor tayi poisoning kanta, she's on life support!” wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi, da sauri ta dafe saitin zuciyarta kalmar life support ta shiga maimaitawa
“mi ye laifinta dan ta nuna tana son ɗanki,ai duk maso naka masoyinka ne” mom bata san lokacin data fashe da ku ka ba tana ambatar “innalillahi wa Innah ilaihi raji'un,wayyo Allah nah,Allah na tuba ka yafe man, wallahi ban yi haka da nufin cutar da kowa ba sai dan gudun halin da zan shiga Allah shi ne shaidata,dan Allah kayi haƙuri”
ƙalla dady bai ce mata ba sai ma kauda kai da yayi ya kalli gefe,yana jin kukanta amma ya zama dole ya nu na mata baiji daɗin abun da tayi ba
“magana nake kayi shiru, wallahi ba dan na cutar da ita naƙi amincewa ba,ban san har haka take son Irfan ba” still dady bai ce mata komaiba,hannuwanshi ta kamo “dan Allah ka yi haƙuri ka daina wannan fushin,in dai Aurensu ne na amince ko yanzu ku ke son ku ɗaura masu bana da wata matsala,dan Allah kayi haƙuri”
kallonta yayi yana girgiza mata kai “karki damu Zulaihart ni ba fushi nake dake ba,kawai dai banji daɗin abunda ki ka yi ba,a ranar da ki ka nuna baki amince ba kasa jurar rasa ɗanki tayi har hakan ya haddasa tashin ciwanta,da ƙyar da taimakon likitoci ta dawo hayyacinta,na san ganin da gaske ta rasa shi ne ya sa tayi ƙoƙarin kashe kanta” mom bata san ciwan Noor ya tashi ba sai yanzu da dady yake faɗa mata
“tunda har ki ka fahimci yarinyar nan tana son ɗanki kuma shima yana sonta da haƙuri ki ka yi ki ka bisu da Adu'a,ko kin manta wahalar da mu ka sha kafin mu samu peace of mind na zama da juna,ke shaidace akan halin da mutum yake shiga idan yaga za'a rabashi da wanda yake so”
“kayi haƙuri in sha Allah bazan sake maimaita kuskure irin haka ba,kayi haƙuri”
“ba komai ya wuce,Allah ya yafe mana baki ɗaya”
“Ameen,yanzu a wane hali Noor ɗin take ciki”
“har yanzu likitoci ne akanta”
“Allah ya bata lafiya,amma ina son ganin mutallab idan ka amince man,ina so na bashi haƙurin halin dana jefa ƴarsa”
“karki damu,yanzu yana tare da Noor ɗin”
“shikenan” ta faɗa tana gyaɗa mashi kai.
suna a nan zaune sai ga uncle Ahmad tare da mom salima,suna gaba yayinda securitys ɗin su ke take masu baya,banda tsiyayar da hawaye babu abunda mom salima take,tun lokacin da labarin abunda zaabith ɗin ya aikata ya riske su take kuka,shi kanshi uncle Ahmad ya shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa.
kallon ɗaya zaka masu ka shaida rashin kwanciyar hankalin da su ke ciki,har in da su dady su ke suka ƙaraso, gaisawa uncle Ahmad su ka yi dady tukun su ka gaisa da mom,mom salima kuwa kukan da take ma ya ƙi bari ta gaishe da shi,burinta kawai taga a wane kainart ɗin take ciki.
Ward ɗin su ka nufa su ka bar securitys ɗin a waje,dady ne ya tura ƙofar ɗakin ya shiga uncle Ahmad na bayanshi tare da su mom,bakin su ɗauke da sallama su ka shiga,a hanzarce mom salima ta nufi bed ɗin da kainart ɗin take kwance tana fashewa da wani irin kuka ganin halin da kainart ɗin take ciki,lokaci ɗaya ta dawo abunda tausayi.
kallo ɗaya mom Maryam tayi masu ta ɗauke kai,har ya mai jiki uncle Ahmad yayi mata amma ko kallon arziƙi bai samu daga gareta ba,babu wanda yaji daɗin abunda ta yi, girgiza kai kawai uncle Ahmad ɗin yayi dama yasan dole hakan zata faru,tashin hankalin shi ma uncle Mustafa,ya san dole ya ɗauki mummunan mataki akan zaabith wanda bazai so hakan ba.
gaishe da shi laatifa tayi,da kulawa ya amsa mata yana kallon Ammar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login