Showing 150001 words to 153000 words out of 182239 words

Chapter 51 - Baqar inuwa Hausa Novel

24 Nov 2024

5261

Bayan sallar isha'i suna falo zaune Raudha nata dauriya Anne ta fito daga ɗaki tai kiranta, da ƙyar ta iya dauriyar ganin ta saita tafiyarta amma hakan ya gagara. Har suka shiga ciki Anne batace mata komai ba, sai da ta zauna tana gaisheta ta haɗe fuska dan bata son Raudha tai mata gardama. Murya a dake tace, “Ameenatu faɗamin mike damunki tunda kukazo gidan nan naga baki da walwala kuma idonki ya nuna kinyi kuka?”.
        Da sauri ta girgiza kai tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata na zugin da take ji tace, “Ba komai ALLAH Anne. Kawai dai banajin daɗi ne”.
      Shiru Anne tai cike da nazarinta. Sai kuma ta miƙe batare da tace komaiba ta nufi toilet ɗinta. Ruwa mai zafi ta haɗa yanda tasan zai taimaki Raudhan. Sannan ta fito ta kama hanunta suka shiga ciki. Duk yanda Raudha ke wani zame-zame ga kunya kamar zata halakata Anne bata saurareta ba. Babban towel ta bata ta ɗaura ta lulluɓa da gyalenta sannan ta sakata shiga cikin ruwan. Wani kuka maiban tausayi Raudha ta sanya har numfashinta na fisga kamar zata shiɗe. Ga kunyar Anne ga azaba, jikinta har wani karkarwa yake. Anne ta gama fahimtar matsalar Raudha amma mamaki ya hanata gaskatawa.
      Haka ta sake canja mata wani ruwan har sau uku, sai ga Raudha taji wata irin nutsuwa na saukar mata. Anne ta fito tana bata umarnin tayi wanka da ruwan ɗumi kafin ta fito.

       Ramadhan da tun shigar Raudha ruwan farko ya nufo ɗakin Annen ya tsaya cak jin ƙarar da Raudha ta ɗan saki sanda ruwan ya ratsata, ya dafe kai da riƙe ƙugu a fili yake faɗin, “Ameenatu kin kasheni, miyasa kikaƙi yarda na tainaka miki gashi nan kin gama tonemin asiri wajen tsohuwarnan da darunta baya karewa”.
     Duk da Anne kakace renon uwa tai masa ba kaka ba. Hakan kuma baya hanashi yin wasa da ita wani lokacin. Dole ya fasa shiga ɗakin dan yasan rikicin Anne yanzu saita sauke masa na cikinta. Tun ɗazu itace a ransa. Duk abinda yakeyi hankalinsa na kanta, sai dai kuma haushin yanda ma ta wani sharesa na cinsa, dama sanda ya gansu da Bilkisu yaga kamar tafiyarta ba dai-dai ba, sai dai bai samu damar gama ƙare mata kallo ba suka shige. Falon ya koma dole wajen Bappi suka cigaba da hirarsu har Pa. Dama zai kira Anne ɗinne kamar yanda Bappi ya sakashi, koda ya dawo sai ya ce masa bai gantaba amma yaji ƙarar ruwa a bayi....

       Babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya a jajjere, Anne dake kallonta cike da tausayi ta nuna mata bakin gado tana miƙa mata shayi data saka aka haɗo mata, sai gasashshen nama da akaima haɗi na musamman dan zuwa yanzu ta tabbatar da abinda ke faruwa. Kokwanton da ranta keta mata yasata kiran Dr Hauwa tunda itace ta duba Raudha a wancan likacin da sukai zargin cikine da ita da kuma zubewar cikin. Dr Hauwa da take ɗaukar Anne matsayin uwa ta faɗa mata gaskiyar lamari akan kowancan karon ciwon marane kawai irin na period, hakama lokacin da akace tayi ɓari maganin zubda ciki tasha batare data sani ba, amma Ramadhan yace suyi shiru dan zaiyi bincike akan wanda ya aikata zuba maganin da Raudha tasha., kuma bayan shi Raudha ta karayi har sau biyu tama dubata akan hakan, itace kuma ta sanarma Ramadhan mafitar da zai iya dakatar da Raudha daga azababben ciwon marar da take fama dashi a kowanne period.
     Godiya Anne tai mata ta yanke wayar, shiyyasa kafin ma Raudha ta fito Anne tasa aka kawo mata wannan abincin da tasan zai taimaka mata. “Maza kici kafin a samo miki magani”.
     Yunwar takeji, amma sam bata son cin abincin. Sai ma wani irin barci dake fisgar idanunta. Haka ta daure taci abinda zata iya tace ta ƙoshi. A kusan tare Ramadhan da Anne suka shigo ɗakin. Sanye yake cikin kananun kaya da tun ɗazun ya canja. Anne ce kawai ta amsa masa sallamar da yayi cikin tsuke fuska. Raudha kam dake fama da kunyarsa dama bata yarda ta motsa ba, ba kuma ta ɗago ba.
        Zama yay a ɗaya daga sofa's ɗin. Idanunsa akan matarsa da yakeji kamar yaje ya rungumeta, sai dai ya daure ya fuske dan tunda yaga yanayin Anne yasan fushi take da shi. Yanzun ma maimakon ta kirashi da wayarta Bappi tasa ya kirashi yana sashensa yana ƙullawa da kwancewa akan yanda zaizo ya tafi da Raudha can.
        A hankali ya janye idanun nasa a kanta yana jingina kansa jikin kujera ya lumshe su. Cikin ɗan furzar da numfashi yace, “Anne gani”.
     Shiru kamar bazata kulashi ba, tanata ƙoƙarin sakama Raudha safa mai kauri a ƙafa bayan ta mulke ƙafar da wani mai da ita tasan amfaninsa. Sai da ta gama tsaf ta kamo hannayen Raudha suma ta shafa mata man ta saka mata safar hannu sannan tai magana batare data dubesaba tana rufe man. “Magani nake buƙata da zata sha”.
      Idanunsa ya buɗe tare da ɗagowa. Sai ya saukesu akan Raudha da sam taƙi kallon ko inda yake har yanzu. Kafin cikin ƙanƙan da murya yace, “Waye baida lafiya?”.
        Wani shegen kallo Anne ta zubo masa cike da harara kai kace idonta ne zai faɗo. Daƙƙuwa ta watsa masa a zafafe tace, “Ramadhan ungo wannan.”
       Tattausan murmushi ya saki mai sanyi yana lumshe idanu ya sake buɗewa a lokaci guda. Fuska ya ɓata sosai cike da marairaicewa kamar ba shugaban ƙasa Ramadhan ba. “Waini Anne kamarma fa kinajin haushi na..”
    Harara ta sake dalla masa tana janyo burner ɗin turare kamar zata jeho masa. “Oh saima yanzu ka fahimci haushin naka nakeji ashe....” ta ƙare maganar dayin kamar zata jeho masa har abin yaso bama Raudha dake kallonsu ta wutsiyar ido dariya. Amma saita gimtse yana sake kauda kanta dake mata tsananin ciwo gefe...
        Hannu ya ɗaga mata alamar surrender. “Kinga yi haƙuri ajiye burner ɗin. Ina arziƙi ranar Monday a ganni da fasashen kai azata matata ce ta fasamin”.
     “Oh to bara na fasa ɗin ai gara sumayi zaton hakane koba komai ta rage zafin muguntarka”.
      Tasowa yay daga kujerar murmushinsa na sake faɗaɗa. Ya zauna kusa da Raudha a gefen gadon yana mai ruƙo hanun Anne ya amshe burner ɗin. “Yi haƙuri tagaba goshin Bappi yanzu mi akeso nayi?”. Yay maganar da juyawa yana ɗaura hanunsa a goshin Raudha da kunya ta dabaibaye kamar ta nutse saboda yanda ya zauna gab da ita sosai duk da baya taɓa jikinta dai.
        Mikewa Anne tai tana mita ta fice. Ka tambayeta abinda ke damunta kasa a nemo mata magani kafin na dawo kuma ku tattara ku barmin ɗaki barci zanzo nayi”.
     Gwalo ya ma bayan Anne, kafin ya maido dubansa ga Raudha. Jawota kawai yay jikinsa ya rungumeta baki ɗaya. Rawa jikinta ya farayi kaɗan-ƙaɗan har yana iya jin gudun da zuciyarta keyi. Ga zafin da jikinta ya ɗauka sosai na ratsa shi.
    “I'm sorry Ustazah”.
  Ya faɗa a hankali cike da tausayinta. Ita dai babu bakin magana, sai ma lafewa da tai duk da tsoron dake tattare da ita nashi. Kusan mintuna uku suna a haka kafin ya ɗagota daga jikinsa, hannu yasa ya share mata hawayen dake sakko mata a kumatu. “Yi haƙuri kukan ya isa haka Sweetheart, amma miyasa ɗazun baki shiga ruwan dana haɗa miki ba”.
       A hankali yake maganar cike da nutsuwa. Da ƙyar Raudha ta iya buɗe baki tace, “Akwai zafi ne”.
       “Ai zafin shine zai taimaka miki Ameenatu, gashi ƙinyin haka ya saka miki zazzaɓi har kin tone mana asiri wajen Anne dama duk mai hankali da zai lura da tafiyarki a gidan nan ɗazun”.
      A ɗan tsoroce ta ɗago manyan idanunta a karon farko ta kallesa. “Ya Ramadhan kowa ya sani kenan?”. Tai maganar cikin rawar murya wasu hawayen na rige-rigen sakkowa. Dariya da tausayi ta bashi lokaci guda. Maimakon ya bata amsa sai ya sake rungumeta. Kusan minti biyu ya sake ɗagota. “Kinga tashi muje kisha magani dan tun ɗazu nasa aka kawo miki. Ga shi Anne dama ta koremu duk da nasan itama ba iya kwana zatai anan ba sai a bayan Bappi. Shiyyasa kema takeso kije jikin mijinki ki kwanta ki more..”
     Hannunsa ta turo dan yanda yay maganar da abinda hanunsa ke mata sai kunya ta sake lulluɓeta. “Ni ALLAH ka bari”.
       “Uhhm iyayi, nasan dai kinana daɗi ya rufeki bazaki kwana batare da mijinki ba.”
     “Innalillahi... ALLAH Ya Ramadhan ka iya sheri”.
             “Su Yaya anji jiki, wane Yayane zaiyi bidirin da nai a daren jiy.....”
   Hannu tasa ta toshe masa baki da sauri kafinma ya ƙarasa. Da ƙyar ya iya danne dariyarsa yana janye hanunta. “To shikeman nayi shiru”.
       Yasan ya kora su Basma tun ɗazu, Anne kuma tana sashen Bappi, sai kawai ya duƙa wai Raudha ta hau ya goyata. Ƙin yarda tayi itakam. Ganin zata cigaba da ɓata lokacinsa ya ɗauketa cak suka fice tanata mutsu-mutsu da roƙon ya sauketa bai saurareta ba. Dole tai saurin saƙalo hannayenta a wuyansa jin kamar zata faɗi. Ta lumshe idanunta da hawaye ke zaryar fitowa kunya kamar zata halakata, fatanta suje lafiya inda zasu batare da wani ya gansu ba..........✍


*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*







*_Episode 52_*


..........Sai dai addu'ar tata bataci ba. Dan suna shigowa falon daya raba sashensa da nasu Anne sukai kiciɓus. Sai dai Ramadhan ya ɗauke kai kamar baiga Anne ba dan shima dai kunyar yaji. Ɗan murmushi Anne tai tana binsu da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya da numfashi tana mai binsu da addu'oin zaman lafiya da samun zuri'a masu albarka.
       Har ya isa ƙayataccen bedroom ɗinsa da komai na ciki yake kalar royal blue and golden bata yarda ta buɗe idanunta ba. Ya direta a saman lallausan gadonsa da yaji shimfiɗu masu inganci, anan ma da runfa ta net white color mai kwalliyar blue kaɗan-kaɗan.
      “ALLAH nauyine dake Ustazah, wannan ai sai kisa na rame”. Ya faɗa cikin kunenta tare da sumbatar kuncinta na haggu. Ita dai bata motsa ba balle ta buɗe ido, sai da ta ɓata fuska da tura baki yace tana da nauyi. Murmushi yayi da ɗallin lips ɗin a hankali.
       “ALLAH da zafi Ya Ramadhan”.
“Ai dama dan kiji zafin nayi. Idan kuma wannan yayan bai fita bakinki ba ALLAH sai nazo na darje ciwon na banbanta miki tazarar dake tsakanin Yaya da ni”.
      “Toni mizance dan ALLAH?”.
“Oho ya rage naki tashi kisha magani kisa kayan barci kar wannan towel ɗin yasa mura kamaki”.

        Da ƙyar ya iya sakata tashin tasha magungunan da tun bayan sallar magrib aka kawo masa su. Dan tun da yaga yanda take tafiya ya yanke shawarar nemansu. Kayan barci ya ajiye mata ya shige toilet, hakan ya bata damar sakawa da sauri-sauri tai amfani da designers turarurrukansa masu ɗan karen ƙamshi ta haye gadon da sauri tai kwanciyar kai da kafafu tare da yin addu'a kafinma ya fito taja bargo har saman kanta. Dan tasan kaɗan daga aikinsa ya fito da towel babu kunya a gabanta.
          Ilai kuwa hakan ya fito kansa tsaye, ya ƙaraso har gaban gadon saboda wayarsa dake ring. Kasancewar ata gefen can ɓangaren Raudha ta kwanta shi kuma sai ya zauna a gefen gadon ta ɓangaren data bari domin shi. Yana goge ruwan fuskarsa da jikinsa yana wayar da A.J dake kula masa da business ɗinsa a can America yanzun. Cikin harshen turanci suke maganar cike da ƙwarewa, dan haka Raudha ta shagala a saurarensa dan yanda harshensa ya karye bama zakace yasan wani yaren Africa ba. Wayar taɗan jashi lokaci dan harya miƙe ya koma gaban mirror. Yana gyara jikinsa yana cigaba da wayar harya shirya cikin tausasan kayan barci, kafin taji ya sake zama a gefen nata. Kaɗan ta ɗaga bargon ta leƙashi, sai tagansa da kofin tea daketa turiri sai kuma lap-top da yake ƙoƙarin kunnawa har sannan wayar na maƙale a kunensa. Shagala tai a kallonsa ƙasan zuciyarta na godema ALLAH daya azurtata da samunsa matsayin miji. Banda ƙaddara ita tasan ko a ƴar aiki bazata ishi Ramadhan kallo ba. Sai dai UBANGIJI shi mai rahamane mai kuma jinƙai. Sannan mai ƙaddara abinda yaso ga waɗanda yaso koda akwai tazarar nisa ta rayuwa ko yare ko addini ko yanki a tsakanin bayinsa.
       Yaja lokaci yana aikin sai dai ya ajiye wayar tuni, har barci barawo yay tashiri kan Raudha saboda maganin data sha.

            Ramadhan da idanunsa ke faman raɗaɗin barci, ya kai hannu bisa goshinsa ya murza da furzar da iska mai nauyi. Ya gaji matuƙa, gashi abinda yakeyin mai muhimmanci ne. Dan kayan da zasu fitarne a sabuwar shekara A.J ɗin keson ya duba abinda baiyiba su ajiyesa gefe wanda yayi su fara packaging ɗinsa yanda ya dace da mikashi ga yan talla kafin a fitar.
       A hankali ya rufe lap-top ɗin bayan ya kashe yana ɗan danna gefen wuyansa alamar riƙewa. kofin daya sha lipton da lap-top ɗin ya sauke kasa. kafin ya koma toilet ya ɗauro alwalar barci sanna ya hawo gadon da danna wani abu net ɗin ta buɗe gaba ɗaya ta lulluɓesu. Sai ɗan hasken fitilar cikin gadon daya kunna ya kashe ta ɗakin gaba ɗaya. Bargon da Raudha take ƙudundune a ciki ya ɗage, sai yaga ashe kai da ƙafa take kwance. Kansa ya ɗan girgiza kawai, yasan tadata yanzu wani aikinne kuma, sai kawai ya kwashi piilos ɗin shima ya maida inda tasa kanta dan bazai iya yarda da kwanciyar kai da ƙafa ba shida matarsa. Gara ace ɗaki suka raba ko gadon. Dan lokaci Amnah ko faɗa sukai da ita bai yarda da raba ɗaki ba. Dole ta kwana tare da shi ko zata kwana masa kukan baƙin cikin daya tusa mata. Inma itace tai masa laifin duk zafin da yakeji a ransa ya gwammaci su kwana waje guda ɗin, shi kuma yasan a inda zai fanshe haushinsa ai (🤣😂mugu ɗan masa🙊).

        Sai da ya janye bargo gaba ɗaya ya karemata kallon yanda kayan barcin sukai mata ƙyau kafin ya saki wani ɗan guntun murmushi da iya laɓɓa ya tsaya masa. jikin nata ya taɓa yaji zazzaɓin ya sauka, sai kaɗan da bai ida hucewa ba dai. Filon da take kai shima ya ɗaura kansa suna fuskantar juna. Ya sumbaci goshinta da laɓɓanta sannan yay musu addu'a yaja bargo tare da rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.

        Da asuba ya rigata farkawa, sai dai yana motsawa itama ta farka. Gaba ɗayanta a jikinsa take lafe da alama hakan ya mata matuƙar daɗi, sai dai suna haɗa ido tai saurin ƙoƙarin janye jikin nata kunya kamar zata nutse. Riƙota yay ya hanata damar juyawar. Cikin ɗan daburcewa take ƙoƙarin faɗin, “Kayi haƙuri ni ALLAH ban san ma....”
      Ruf ya rufe mata baki da nashi batare daya bari ta ƙarasa faɗa ba (😜ƙazanta ko brush babu🤕🙄). Duk yanda taso kwatar kanta bata samu damar hakanba. Dole ta nutsu ta barshi ya gama yamutsata san ransa tsoro kamar ya kasheta. Dan a tunaninta za'a tafi next level ne😖. Da ƙyar ya iya yakar ƙansa ya barta jin an sake kiran salla na biyu, ya sauka a gadon da ɗan zafin nama ya faɗa toilet. Ruwa mai ɗumi ya sakarma kansa yana mai sauke nannauyan numfashi da rumtse idanu. Sunan ALLAH ya dinga ambata dan yasan lallai akwai matsalolima ba matsalaba. Gashi da alama Raudha tamkar Amnah take itama zatai shegen raki duk da ita daba sickler ɗin ba. Dole ya haɗa harda wankan lada. Koda ya fito yay mata maganar ta tashi bata motsaba dan kunya harya zura jallabiya yasa turare ya fice. Sai dai ya gargaɗeta karya dawo ya sameta a kwance bata tashi tayi salla ba, ta kuma sake shiga ruwan zafi inba hakaba ya dawo da kansa zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login