Showing 141001 words to 144000 words out of 182239 words

Chapter 48 - Baqar inuwa Hausa Novel

24 Nov 2024

5294

tsaye bai fito ya ambaci sunan kowa ba. Babban fatansu kawai susan wanene wannan mai turo saƙo. Hakan yasa ganin wannan hand writing da yay dai-dai dana Raudha yay matuƙar ɗaure kansu.

    “Wannan ya sake tabbatar min yarinyar nan Alheri ce kuma akwai dalilin zuwanta garemu”. Bappi ya faɗa lokacin da suke ganawa da Ramadhan a office.

   Cikin sauke numfashi Ramadhan yace, “Tabbas akwai abinda bamu saniba kuma ita take ɓoye mana. Abin ɗaure kan anan kawai shine a gaba ɗaya tarihin yarinyar dana bibiya babu wani alamun alaƙarta da wani sai danginta ko anan cikin Bingo. Sai dai sister ɗin mom nata tanada alaƙa da matar forma president, a yanzu kuma matace ga Alhaji Yaro glass Vice ɗina, dama kuma sun taɓa zaman aure ta fita. Bappi inhar hasashena yana kan dai-dai akwai boyayyar manufa tsakaninka da abokan nan naka gaskiya”.

   Murmushi Bappi yayi yana ɗan jinjina kai. “Komai zai iya faruwa musamman idan akai la'akari da abubuwa masu yawa. Sai dai bana so zargin sunan kowa anan har sai muntabbar. Shawarata gareka anan lkawai ka cigaba da jan yarinyarnan Ameenatu a jiki, zaka iya jin fiye da abinda muke buƙata daga gareta. Amma tabbas ka shaida naji ƙarin ƙaunarta a raina da kimarta fiye da zaton mai zato. Dan zuciyata bata gayamin an haɗa kai da itane dan a cutar damu”.

   A hankali Ramadhan ya sauke numfashi wani abu mai sanyi na sauka masa a cikin zuciya. Jiyake kamarma ya buɗe ido ya ganta gabansa. Jin yau ɗin yake daban da kullum a rayuwarsa. Sai dai me, yana zuwa gidan ya iske ɓacin ran su Lubnah da har takaisa ga marin Lubnah ɗin. A kuma daren yasa driver maidata gida. Sai dai abun ƙarin takaici washe gari Maah tasa aka maidota.

   Wannan haushin ya sakashi tunda ya fita gida da safe bai dawoba sai dare. Washe gari kuma tafiya ta taso masa zuwa ƙasar faransa babu wani walwala tattare da shi sukai sallama da Raudha da ayanzu ta sake nutsuwa akan makaranta dan harta fara jin daɗin lectures din saboda taimakon da su Basma ke bata.

  Ta ɗan shiga damuwa da canjawar tashi, sai dai daga baya ta watsar da komai dan indai dan abinda su Lubnah sukai matane ita ya wuce a gareta basa ma gabanta. Fatanta dai ALLAH ya bata kariya daga cutar da waninsu.



   A washe garin daya wuce ta tashi da ciwon mara. Tasha azaba sauƙintama yasa Bilkisu dawowa gidan saboda ya fahimci suna ɗasawa da Raudha ɗin. Sai dai sunsha gargaɗi kamar babu gobe akan abubuwa da yawa. Hakama su Muneera sunsha nasu, dama tun marin da Lubnah tasha suka koma shiru-shiru a gidan dan sun san hali. Yanzu ko daya tafi sun ɗau alwashi kala-kala akan Raudha sai akai rashin sa'a Bilkisu ta dawo kusa da ita.  

   Bilkisu ce ta sanar masa halin da Raudha ke ciki ta hanyar massege. Hankalinsa ya tashi lokacin daya lura ta text ɗin. Sai kuma a lokacin ya tuna da zancen Dr Hauwa'u a wancan lokacin. Bai samu magana da Bilkisu ba sai dare bayan ya samu nutsuwa. Ta kwantar masa da hankali akan da sauƙi, dan Anne ta kira shine ta turo musu Maman Jabeer (Dr Hauwa) tazo ta dubata. Ta tabbatar masa tayi faɗa sosai akan ƙin zuwan Raudha ɗin bayan tun wancan karon tace taje bayan ta warke.

    Yaji babu daɗi sosai, dan kuwa akwai sakacinsa tunda shine bai nuna maida hankali akai ba matsayinsa na wadda take a ƙarƙashinsa. Bai ce a haɗashi da Raudha ɗin ba, sai dai ya tabbatar ma Bilkisu tayi ƙoƙari idan Raudha ta samu lafiya suje asibitin Maman Jabeer ɗin.



    Haka kuwa akai, bayan kwana biyu ta koma ragas kamar ba'ita ba. Dan haka sukaje asibitin da dare gudun idon mutane. Sai dai tana tare da dogaranta duk da hakan. 

   Sosai Dr Hauwa tai mata gwaje-gwaje na musamman yanda ya kamata. Cikin amincin ALLAH kuma ta gano matsalolin dake tare da Raudha ɗin harda imfection. Magunguna ta bata tare da wani bayanai a rubuce tace ta bama Ramadhan ba nata bane. 

     Kamar yanda akace shi ɗin zata bamawa kuwa bata buɗaba ta ajiye ta cigaba da sabgar gabanta. Tayi fes da ita, da alama kuma makaranta ta fara buɗe mata idanu da wasu abubuwan. Gashi bata wasa sam da karatu sosai take nuna ƙwazo dake bama su Basma dama class mate ɗin nata mamaki. Gashi taƙi yarda kowa yasan ita wacece, koda yaushe fuska a ƙunshe da niƙab. Bata shiga harkar kowa sai su Basma. Wasu na mata kallon girman kai wasu kuma tana ɗan birgesu duk da basu san wacece ita ba. Suma su Basma kuma sun kame bakinsu saboda gargaɗin Ramadhan da Anne. 



    ★Kasancewar yau juma'a da wuri ta dawo school. Ta zube a falo Bilkisu na mata dariya. “Aunty ahaka za'ai karatun kuwa?”.

   Dariya itama Raudha tayi tana ajiye ruwan data sha sosai. “Wlhy bazaki ganeba Aunty. Abunfa babu sauƙi sam. Dan masifa yau text har biyu mukayi ga submitting Assignment ɗin masifaffen malamin nan da nake gaya miki”.

    Cikin dariya Bily tace, “Haka ake shan yaƙi ai Aunty har a cimma nasara. Fatanmu dai ki fito da first class duniya tasan firt lady ɗinmu bata wasa bace”. 

  Dariya Raudha tai tana miƙewa. “Uhhm Aunty Rabani da wata first lady. bara na watsa ruwa nazo naci abinci ko breakfast banyiba yau”. 



   Bayan tayo wankan anan suka baje a falon bilkisu na sake nuna mata aikin yau da mata ƙarin bayani. Salla kawai ke tadasu har magrib. Sam Raudha batasan yau shugaban ƙasa zai dawo ba dan tunda ta shigo gidan basu buɗe tv ba. Bayan sallar isha'i taɗan sake watsa ruwa. Fitowarta kenan a toilet ɗin ta samu wayarta na ringing. Cike da zumuɗi ta ɗaga ganin Fatima. Tun jiya suka sanar mata yau zasuje Hutawa duba Abba (Dauda) da baida lafiya. Taso zuwa amma babu dama har kuka tayi. Sai dai ta ƙudiri niyyar idan Ramadhan ya dawo zata roƙesa alfarmar zuwa itama. Bayan sun gaisa dasu Fatima har dasu Inna Fatisa ke sanar mata ga ƙawarta Zubaida da tazo duba Abban su gaisa.

   Cike da mamaki tace “Zubaida fa? Dama bata mance ina duniya ba?”.

   “Ni na isa first lady ɗinmu. Ranki ya daɗe kin wuce a manta dake ai a ƙasar NAYA ”.

  Zubaida data amsa wayar ta faɗa.

“Mara kirki bazaki canjaba dai?”.

Cewar Raudha cikin dariya.

   Dariya itama Zubaida ɗin tayi, kafin su gaisa a mutunce. Zubaida ƙawartace ta islamiyya. Itama yarinyace mai ƙwazo da sanyin hali kamar Raudha. So da yawama akance halinsu yazo ɗaya ne shiyyasa suke abota. Duk da abotar tasu bawai takai mai tsanani bace da har suka san sirrikan juna musamman ma Raudha da ba'a jin cikinta. cikin tsokana Zubaida ke faɗin, “Halan kin kusa sauke mana babynmu ranki ya daɗe”.

    Raudha tai dariya tana ɗakko kayan da zatasa a Wadrobe. “Aiko gashi ma har yana motsi a ciki, ina fatan kun shirya zuwa suna”.

  Dariya sosai Zubaida keyi. Itama Raudha haka. “Uhm matsoraciya keda rakin nan naki ace cikin ya tsufa za'aji muryarki haka ragal”.

   “Tabɗi mi kika ɗaukeni. Ki shirya zuwa Bingo kiga yanda nake daram kuma ga ƙaton cikin ƴan biyunku tare dani. K cikinfa ba wani wahala kwantar da hankalinki ke huɗu zaki samo mana lokaci guda......”

    “Idan ita bata samoba ke zaki samoshi yau ɗin nan”. A mugun firgice Raudha ta juyo har towel ɗinta na ƙoƙarin kwancewa jin muryar wanda batai zatoba balle tsammani. Sanye yake cikin kananun kaya tausasa gaba ɗaya baƙaƙe. Ya ƙara wani fresh abinsa harda ɗan tumbi alamar hankalinsa kwance yake. Ga sumarsa data sake samun kulawa na gyara. Sam batasan ya dawo gidan ba balle shigowa ɗakin dan ko shigowar motocinsa yau batajiba sam kokuwa hankalintane bai a wajen, ta diririce da rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi ganin ita yake nufowa. Har yazo gab da ita bata samu mafitar kare kanta da ko saka hijjab ba. Ta cikuykuyo wasu kaya zata yafa a jikinta ya riƙe yana mai zagayawa ta bayanta ya rungumota jikinsa.

    Wayar ya zare da kallon screen ɗin, tuni dama ta yanke kiran, sai dai hakan bai hanashi ganin da Fatima tai wayar ba. “Ai bansan kina bukatar ƴan uku ba Ustazah da tuni na ajiye ƙawancenmu gefe na baki ajiyarsu”.

   Innalillahi ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Ya sake kanainaiyeta jikinsa da kai hannun kan ɗaurin towel ɗinta zai kamar zai kwance. Da wani irin zafin nama ta wulƙito ta rungumesa jikinta na rawa sai ambaton “Innalillahi...” take har ƙarshe. Shiko mizaiyi inba dariya ba. Sai dai yay dauriyar gimtsewa abinsa ya sake kama towel ɗin data ƙanƙanme cikin hannu ta gaba ɗaya. “Dan ALLAH ka rufamin asiri karka cire Ya Ramadhan. Inba hakaba zan iya rasa numfashina”.

    “Sai in baki nawa mu rayu tare ai”.

Ya faɗa cikin raɗa da wata irin murya mai wahalar fassara ga Raudha.

   Raudha ta sake ƙanƙamesa saboda yanda zuciyarta ke masifar gudu cikin ƙirjinta. Tunda suke bai taɓa mata kalar abun nan ba. Iyakarsa taɓa hanunta fuskarta ya dan sumbata ko laɓɓanta. Amma bai taɓa gwada ɗora hanunsa a wani sashe na jikinta ba sai yau. Dan kuwa a bazata taji saukar hanunsa kan ƙirjinta. 

   “Na shiga uku”.

 “Baki shiga uku ba. Ai maganar kunya kuma ta kare insha ALLAH yau zamu neman ƴan huɗu............✍


End of book
Leave a comment

Post

Comments

104835043420935222197
Masha Allah muah😍🤗🤗

16 minutes ago


Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: arewabookspublishers@gmail.com

Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram


Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

BAKAR INUWA...!!
Chapter: 49

Share:





Report

BAKAR INUWA...!!
View: 8

Words: 3.3K



Chapter 49
49

.........Gaba ɗaya ya gama sabauta mata tunani da lafiyar jiki. Dan kuwa cak ya ɗauketa a karon farko na tarihi, bai direta ko inaba sai saman gado. Bai damu da rawar da jikinta keyiba da roƙon da take masa ya zame towel ɗin da taketa faman riƙo kai kace igiyar neman tsira ce. Batama san ta daka tsalle ta ruƙunƙumesa ba. Atare suka faɗa saman gadon. 

    “Haba hajjaju ki bini a hankali mana ai zanyi”.

  Yay maganar yana danne dariya da ƙyar. Itako kuka ta fashe masa da shi da sake ƙanƙamesa. Burinta bai wuce karya kallar mata jiki ba. Tausayi ta bashi dan yasan wannan wani sabon al'amarine daga gareta. Yajawo bargo da hanu ya lulluɓesu yalwataccen murmushi shimfiɗe a fuskarsa. Jin bil haƙƙi kukan take kuma taƙi barinsa yay ko motsi ya sashi lalubar bakinta ya manne nashi. Cikin salon tsantsar zalama da yanayin da yake ciki ya fara binta da salon da batasan zai iya aikatawa ba.

    A wannan lokacin tsabar firgici zamu iya cewa Asthma ɗin Raudha ma motsawa ta nemayi. Dan da gaske numfashin ta a take ya fara fita a rarrabe har tana sarƙewa. Bai barta ba sai da ya fahimci yana neman kama wani layin saɓanin wanda yay niyyar bi kawai. 

   Shiru yay bayan barinta yana sauraren yanda hawayenta ke sauka a ƙirjinsa har yana huda riga yana ratsasa. Yay tattausan murmushi hanunsa saman kanta da akai ma kitson da baisan anyi ba. Sai da numfashinsu ya gama dai-daita ya kai bakinsa kan kunenta yana magana cikin muryar da batasan ya mallaka ba. “Cutie! Yaufa babu fashi sai anje duniyar samo ƴan huɗun nan bazan iya ɗaga ƙafa ba”.

   Sake ƙanƙamesa tai jikinta na rawa dan harga ALLAH tsoro ma yake bata. Kalamansa sake firgita rayuwarta takeyi. Shine na farko daya taɓa mata abinda wani namiji a duniya bai taɓa mata ba. Shine na farko daya taɓa ɗora hanunsa akan abinda wani mahaluki bai taɓa taɓawa ba. Shine na farko daya ganta a yanda wani bai taɓa gani ba sai yau, yau ɗin ma yanzun nan duk da bata da tabbacin ya kalleta ɗin...

   Ring ɗin da wayarsa tai a jikinsa ya sashi furzar da numfashi mai ƙarfi. Sosai idanunsa suka canja launi hakama fuskarsa tayi ja abinka da fari. Yasan Maah! ce, ya kuma san abinda take buƙata. Dan ta tabbatar masa tana son ganinsa daya dawo akan zancen aurensa da Aina'u. Da ƙyar ya iya saita kansa yakai wayar kunensa bayan ya ɗaga. Da sauri Raudha dake duƙunƙune a jikinsa tai saurin barin jikjnsa ta dire saman gadon. Bai hanata ba harta sake duƙunƙunewa cikin bargon daya rufa musu. Murmushi yay ganin yanda ta yayesa ita kuma ta nannaɗe a ciki kamar an nannaɗe gawa a likafani. Sosai ya tashi zaune ko zai sake samu muryarsa ta saisaitu.

    “Kiyi haƙuri Maah zanzo ALLAH amma sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Inaga ma anan zamu yi hutun nan na kwana huɗu yanzu kaina na ciwo”.

   Abinda ta faɗa ya sashi sake marairaicewa kamar yana gabanta. “Please maah i promise you bazan saɓa alƙawari ba”.

   “Okay thanks you dear Mammah I love you”.

Wannan kalma ta Ramadhan ta bala'in faranta ran Gimbiya Su'adah. Sai taji gaba ɗaya fushin da takeyi da shi ya kwaranye a zuciyarta. Sai dai hakan baisa taji zata janye maganar auren Aina'u ba, tana akan bakanta duk da suna kan rikici da Pa ne akan hakan ma. Dan kuwa su Bappi sunce su babu ruwansu indai Ramadhan ya amince su masu son hakane ai.

    Mikewa yay yana kallon Raudha dake ƙudundune fuskarsa da murmushi. “Irin wannan nannaɗa haka Ustazah kamar wata shawarma?. Indai nine nayi nan ina jiran abinci da yunwa na dawo cikina kamar anmun sata”.

  Ya ƙare maganar da shafa cikin nasa daya ɗan taso. Shi kansa ya fahimci ya ƙara nauyi, kwana biyun nan baya iya fita training, dole ya dawo kar azo yakai matsayin da ƴar rigimarsa zata kasa ɗaukarsa wata ran. Da wannan tunanin ya fice ya barta bayan ya gwada yayeta ta sake saka masa kuka.



     Kallon-kallo Aina'u da Muneera kema juna ganin yanda Yayan nasu ya fito a ɗakin Raudha fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi da sai dai su hanga yanama wani shi ko su Bappi. Wani irin zafine ya shiga ratsa zuciyar Aina da jin ƙara tsanar Raudha da duk wandama ke tare da ita. jitake zata iya kashe Raudha saboda Ramadhan a yanzu. Dan tun tana shakkar maganar auren nasu a yanzu abin ji take yana ƙara mata tasiri a rai da ɗokin kasancewarta matarsa kodan suma susha romon mulki, dan tasan dai ta auresa yanzu tabbas itace zata zama first lady bawai waccan kazamar yarinyar da ko tsarkin kashi batajin ta gama ƙwarewar yi. Momynta (Adda Asmah) ta gama tabbatar mata indai Ramadhan ne sai ya sota fiye da uwarsa ma a duniya da su Anne, dan zata mallake mata zuciyarsa yanda bazai sake tunawa da kallon wata mace da daraja a duniya ba sai ita. Tabbas tahau ta zauna. Ta kuma yarda. Dan ita shaidace Abbansu a tafin hanun Mom nasu yake. Sai abinda tace yake yi.





(Hummm🚶🏻🤕. ALLAH yasa sanda za'aima wasu hisabi muna aljannah a fadan MANZON ALLAH (S.A.W).



 ★★★



   Da ƙyar Raudha ta iya daurewa ranta ta tashi. Sai dai gaba ɗaya a tsorace take da komai ma. Yau gaba ɗaya Ramadhan ya rikita mata lissafi. Tama rasa wane kalar tunani zatai. Shiryawa tai cikin doguwar rigar abaya baƙa. Komai bata shafa ba sai khurah da turare. Sai dai ta wanko fuskarta saboda kukan datai. Cikin ɗar-ɗar da zuciyarta keyi ta fito domin sama masa abincin daya buƙata. Cikin sa'a ALLAH ya taimaketa tai kiciɓus da Bilkisu a kitchen ɗin sama. Dan ƙamshin da taji da motsine ma yaja hankalinta tunda tasan bamai shiga inba itaba sai mama ladi dake gyarawa.

   Ido taɗan waro kaɗan na mamaki. “La aunty Bilkisu..”

   Bilkisu dake murmushi tai saurin cewa “Kamar kice komai. Kawai naga Yaya a bazatane shiyyasa na rugo kitchen ɗin tunda ba salla zanyi ba. Mun shagala kwata-kwata bamu buɗe television ba balle muga batun dawowarsa.”

    Ajiyar zuciya Raudha ta sauke. Cikin danne abinda ke taso mata tace, “Wlhy nima nasha mamaki.”

   Ƴar dariya Bilkisu tai. “Uhm ya miki surprise na masoyane kawai”.

   Kunya zancen Bilkisu ya bama Raudah, ta kauda kai kawai tana murmushi. Hannu ta saka suka karasa aikin da aready dama Bilkisun tana gab da kammalawa. Sai da suna haɗa abincin a basket Bilkisu ke faɗin. “Niko idonki kamar wadda tai kuka”.

   Da sauri Raudha tace, “Abune ya faɗamin a ido daƙyar na samu ya fita bayan nata zuba masa ruwa”. 

  Sannu Bilkisun ta mata dan har zuciya ta yarda. Raudha ta ɗauka basket ɗin tana mata godiya da addu'ar ALLAH ya kaisu ran aurenta da yanzu haka ana shirin saka rana kusan su biyar.



     Da ƙyar ta iya kawo kanta ƙofar ɗakin nasa. Ji take kamar bazata iyaba amma ta daure matuƙa. knocking tayi kamar bataso. Tana shirin sake na biyu aka buɗe ƙofar. Bata yarda ta kallesa ba, dan tasan dai shine ɗin. Shiko idonsa a kanta ƙyam yana ƙaremata kallo yanda abayar tai matuƙar mata ƙyau. Matsawa yay ya bata hanya ta shige batare da yace komaiba. Sai da ta gittashi ta shiga ya maida ƙofar ya rufe. Saman kujerar daya tashi ya koma ya zauna tare da ɗaukar Tab.. Da ke a hanunsa kafin shigowarta. Ganin ya basar da ita ya sata daurewa tace, “Ga abincin”.

   “Zuba”

Ya faɗa a taƙaice batare da yabar abinda yakeyi ba. So yake yay dauriyar fasa abinda yay niyyar yi a gareta amma zuciyarsa taƙi amsar lallashin sam. Bai kalleta ba harta zuba masa gasashen naman ragon daketa ƙamshi, yaji haɗi na musamman. Sai kunun madara da Bilkisu tayisa a nutse saboda sanin yanda yake ƙaunarsa. Zata zuba abincin yay saurin dakatar da ita. “No bar nan kawai”.

  Dakatawa tai ta maida kwanon ta rufe da tura table ɗin gabansa yanda zai samu nutsuwar ci. Sai da ya ɓata wasu sakanni ya ajiye tab.. Ɗin, dai-dai da miƙewar Raudha dake fatan samun hanyar guduwa dan yau bazata juri zama da shi a inuwa ɗaya ba. Caraf ya riƙo hanunta ya zaunar a gefensa.

   “Na sallameki ne?”.

Jitai kamar ta fashe masa da kuka kawai, amma ta daure dan kar yaga kamar ta cika rashin wayo. Hankalinsa ya maida ga abincin zuciyarsa na tunanin ta yanda zai ɓullo mata ta saki jikinta. Sai dai ya kai laumar nama baki yake faɗin, “Uhhmm Bestie kinji wani gashi na musamman kamar a birnin sin. K karfa ki zata santi nake naji abunne har cikin kai”.

    Murmushi ne ya suɓucema Raudha. A hankali tace. “Uhhmm!”.

      “Ai bakiji Humm bama sai kinci”. Ya ɗago gareta da tsoka daya ciro jikin dogon tsinken da Bilkisu ta tsiro guda uku. “Buɗe bakin kiji kar ayi babu ke”.

   A kunyace tace, “ALLAH ni na ƙoshi”.

   Fuska ya ɓata yana ɗan hararta. “Keni bansan gulma buɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login