Showing 165001 words to 168000 words out of 182239 words

Chapter 56 - Baqar inuwa Hausa Novel

24 Nov 2024

5289

shi da su basu sani ba. Zata tayashi da addu'a koma minene ALLAH ya yaye masa shi.
 
     Kamar wasa sai ga karamar magana ta zama babba, dan kuwa dai ciwo sosai Raudha ta kwanta washe gari ko makaranta bata iya leƙawa ba ma. Kusan kwananta uku a halin jiyya kafin ta warware ta cigaba da harkokinta. Sai dai fa a yanzu babu wanda take tsananin tsoron haduwa da shi a duniya sama da Ramadhan. Ko maganarsa taji a tv sai gabanta ya faɗi. A haka rayuwa ta sake turawa suka sake cinye sati huɗu, sati kusan na bakwai kenan da shiga halin da suke ciki. Zuwa yanzu kuma har an kai kuɗin auren Aynah saboda birkicewar da Ramadhan yay musu.
       Tuni Pa ya fahimci akwai sihiri tattare da yaronsa. Amma ya zaɓi barinsa a hakan dan yanaji a ransa dole sai Adda Asmah ta shayar da gimbiya Su'adah zumar mamaki sannan zata san ANNABI ya faku. Koda su Bappi ma suka fara irin wannan zargin Pa ɗinne ya gusar musu da zargin ta hanyar nuna musu babu wani sihiri uwarsa ke zugasa. Yayi hakane dan baya son suce zasu tashi tsaye akan Ramadhan ɗin, yafi son sai uwarsa taji a jikinta sannan. Amma kuma bai gaza da masa addu'ar kariya ba.
      Abinda hankalinsu kuma ya gagara kaiwa akai su duka basuyi tunanin ko abin ya shafi Raudha ba. Dan ita dai ko sau ɗaya bata kawo wa kowa ƙararsa ba. Ta kuma hana Bilkisu faɗa duk da itama Bilkisun ba komai ta sani ba har yanzun. Kullum kuma Anne ta tambayi su Basma sukance Raudha na lafiya harma tana gaishesu tunda kullum dai suna tare a makaranta. Hakanne ya ɗan basu nutsuwa suke ganin shi kaɗai abin ke dawainiya dashi kenan.

         ALLAH sarki Raudha, sai dai kuma abinda ba'a sani ita kaɗai tasan halin da take ciki, ga yanzu kullum da zazzaɓi take kwana. Ga kasala da batasan kota minene ba. Komai da ƙarfin hali take yinsa hatta karatun. Ita Bilkisu tana ɗaukar yanayin natane kawai da tunanin maganar auren Ramadhan ɗin. Dan haka ta maida hankali wajen bata shawarwari da nasiha.
      Bazatace auren Ramadhan baya damuntaba, dan tasan wacece Aynah tasan kuma burinta akanta, dan tunda Ramadhan ya fara birkice mata Aynah da Addah Asmah suka kirata sukai mata zagin ƙare dangi saboda fahimtar ita sihirinsu bai kamataba. A tunaninsu itama bin malaman take shiyyasata ta tsira. Basu san ALLAH ne bai ƙaddara mata shan zoɓon waccan ranar ba kawai. Ranar taci kuka matuƙa dan zagine da cin mutunci da bazai taba goguwa a zuciyaba kai tsaye. A kalamansu kuma ta fahimci lallai akwai ƙullin dake kan mijinta da alama kuma sunada alaƙa da shi. Bata da abin faɗa, dan koba komai dai ƴan uwansa ne. Adda Asmah ma na amsa sunan uwane a garesa tunda yayar mahaifiyarsa ce da itama zata iya kiranta da uwa. Haka ta cigaba da masa addu'a da ita kanta abun na damunta.
      Sai dai halin da take ciki na rashin jin daɗin jiki yafi kwashe kaso mafi yawa na damuwarta. Ko mahaifiyarta batasan halin da take a ciki ba. Sai dai a duk sanda sukai waya takance Mummy kimin addu'a. Idan asabe ta nuna damuwarta cikin tashin hankalin furicin Raudhan sai ta dinga kwantar mata da hankali akan babu komaifa saboda karatu take cewa hakan.
     Ita dai Asabe hankalinta ba wani ya kwanta bane. Amma sai ta dage da bin ɗiyarta da addu'ar fatan alkairi. Itama kuma Raudha bata wasa. sosai take a kan ƙafafunta tana gayama ALLAH damuwarta akowanne dare. Wani lokacin ma tana salla tana rawar sanyin zazzaɓi, haka ta dage da azumin alhamis da litinin. Ta kuma dage da saka har Abba (M. Dauda) turama kuɗi akan ya bada sadaka yasa a mata addu'a ita da Ramadhan. Da yake shi kan babu notika ɗaurarru maimakon ya fahimci akwai matsala sai ya kama dariya yana yana faɗin.
        “Ƴar nema taji daɗin gidan gwamnati bata son suyi shekara biyar kawai. Indai addu'a ce kin tara kin samu, yau kaf almajiran dake garin hutawa saina bisu kowacce tsangaya na tattare da malamansu sun saka rokon ALLAH, dan nima inason ku koma hawa na biyun ai. Amma Raudha ya kamata kima mijinki magana ko ministan bada kuɗin fansho ya bani mana. Zamannan ya isheni haka kinga wannan sarautar ba wani kuɗi ake samu ba sai uban fama da rawani da zazzare ido a fada. Ni badan ma kar hakimi yace na raina karamcinsa ba da wlhy tuni na ajiye. Ni kuma yan kuɗina kullum kasa suke, dan ma ALLAH ya taimakeni wanda Ƴaƴan Larai suka sata an ganosu ai da yanzu hawan jini ya shanye muku ni.
     Murmushi Raudha tayi tana share hawaye. “Karka damu Abbah insha ALLAH zan san abinyi. Amma nidai gara kayi haƙuri ka cigaba da zuwa gidan hakimin”.
     “To ai duk yanda kikace haka za'ai uwata farar haihuwa farar aniya your excellency. Insha ALLAH sai kunyi goma indai mulkin NAYA ne”.
    Dariya ta ƙyalƙyale da shi babu shiri dan ya bata dariya sosai. Da ga haka sukai sallama ta ajiye wayar. Bargo ta kara ja har kanta dan wani irin sanyi mai ratsa ƙashi takeji. Ga ƙasusuwan ta kamar ana mata daka a kansu. Saboda zazzaɓin yau ko lecture ɗin karshe bata zaunaba ta gudo gida. Sai dai ta iske Bilkisu bata dawo ba. Haka shima mai gayya mai aikin da rabon dama ta sakasa a ido tun randa yay mata murzar ƴan bori. Dan ko zaune take a falo da taji shigowar motocinsa take shigewa. Ta katange duk wani abinda zai haɗasu a inuwa ɗaya saboda kare mutuncinta da nashi. Tun kusan satin baya take tunanin yanda zata fara masa addu'oin warware sihiri, idan ma shine tare da shi sai dai bata san ta hanyar da zata bashi yasha ba tunda baicin abincin gidan yanzu sai yaso. Hakan yasa ta haƙura ta barma ALLAH komai ya kawo musu mafita.
     Barcine ya ɗan figeta da sam bama daɗi yake mata ba. Dan har a cikinsa tanajin ciwon dake nukurkusarta. Bude ƙofar ya sakata farkawa aɗan razane...........✍
     


*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*







*_Episode 58_*


..........A hankali ta saki numfashi tare da nannauyar ajiyar zuciya ganin Bilkisu ce ba wanda take fargabar haɗuwar da shi ba ko'a hanya bare a cikin ɗaki da ga ita sai shi. Zama Bilkisu tai kusa da ita tana kai hannu a goshinta. “Aunty Lafiya kuwa kika dawo da w....”
     Maganar tata ta maƙale jin jikin Raudha da zafi. “Ya salam baki da lafiya yauma ko? Dan ALLAH ki yarda muje ko cikin clinic ɗin gidan nanne inma bazamu je wajan Mommyn Jabeer ɗin ba. Aunty wai zaki cigaba da cutar da kankine akan Yaya Ramadhan ne? Kin hana na faɗama kosu Anne halin da kuke ciki, ni kaina ɓoyemin abubuwa da yawa kikeyi wlhy. Harga ALLAH nidai na gaji da shurun nan da kika dabaibayeni da haɗani da ALLAH akan nayi”.
       Murmushi Raudha tayi tana haɗiye hawayen dake son zubo mata. Ta tashi zaune cike da ƙarfin hali ta kamo hanun Bilkisu cikin nata. “Aunty B kiyi haƙuri dan ALLAH, ban hanaki gayama su Anne bane sai dan yanda kike kallon matsalar ba haka take ba. Aiki ne kawai yay masa yawa, sannan ni babu wani abu na rashin daɗi dake tsakanina da shi, kawai dan ba zaman gidan yake kamar da ba saboda ayyuka yasa kike ganin akwai matsalane. Kinga babu dalilin kai ƙara akan laifin da babu shi aunty. Nasan kina ganin kamar auren nan nasane cutarwa a gareni shiyyasa. Dan ALLAH kibar damuwa ALLAH ni banajin komai akan hakan duk da nasan dole ne naji kishi matsayina na matarsa. Amma karki manta Aunty ALLAH ya bashi damar yayi huɗu, a addinance ma da biyu aka fara, sannan uku, sannan huɗu. Sannan a yanayin da Ya Ramadhan ke ciki dama ya kamata ace yanada mace mai ilimi da zata jagoranci wasu abubuwa na mulkinsa bawai irina da iyakata secondary ba kuma mai ƙarancin shekaru. Karki manta aunty yanzufa nake shekara ta shatara kawai a duniya, koba komai kuwa Aynah nada kusan ashirin da tara ko talatin da ɗaya ko fin hakan ma, sannan tayi ilimi mai zurfi daga ƙasar NAYA har wajenta. Tako ina ta cancanci zama matarsa koda nauyin al'umma dake a kansa”.
      “Humm Raudha sam ban gamsu da wannan bayanin naki ba. Babu ruwan hankali da ƙarancin shekaru, hakama babu ruwan sanin yakamata da ilimi. Mutane nawane a zamanin da basuyi ilimin boko ba amma sunada basirar tsara abinda ko professor na yanzu bai iya tsarawa ba. Kai har a wannan zamanin akwai wanda basuyi ilimin boko ba amma wlhy idan sukai miki wani abun sai kinsha mamaki. Hakama shekaru, shekaru baga kowa suke taka rawar hankali ba ga mai su. Zakiga mutum da shekarun manya amma idan yana tafka miki baranɓarama ke kyace ɗan goma sha ne. Kuma kiga karamin yaro na gyara masa. So ni a tawa mahangar banga ta inda Aynah zata taimaki Brother ba wlhy. Ƴar uwatace ita kuma jinina, amma bazan ɓoye miki cewar inaji a raina akwai manufa acinkin wannan al'amarin ba Raudha. kuma insha ALLAH bazan gajiyaba wajen ganin na daƙile hakan sai dai in ƙaddararsa ce zama da ita”.
   Tana gama faɗa ta mike ta fita hawaye na sakko mata a fuska. Da kallo kawai Raudha ta bita sai itama ta fashe da kuka. Sai da tayi mai isarta sannan ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta....

(ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawa a duk yanda tazo mana🙏🏻😭).

*______________★_____________*

          A ɓangaren su Gimbiya Su'adah kuwa shirin biki suke na ƴaƴan gata, dan a wannan gaɓar ko auren Lubnah da Bilkisu bata bama muhimmanci ba kamar na Ramadhan da Ayna'u. Babu abinda zuciyarta ke raya mata sai cewar zata haɗa cikar birinta da maido ɗanta ƙarƙashin umarninta ta kuma rabashi da wadda ta zame mata ƙayar kifi a maƙoshi badan ta taɓa mata wani laifi ba ko kuskure.
      Hatta da Ramadhan yanzu wani gata take masa na fitar hankali ita da su fulani da uwar gayya Addah Asmah. Baya iya jera sati baizo gidan ba a sace. Takai yanzu ko sashen su Anne baya shiga sai dai suji labarin yazo a bakin Basma. Hatta yin waya ya rage dasu, komansa gimbiya Su'adah. Ko abu ya shige masa akan harkar mulki maimakon kiran Bappi da yakeyi ko Anne a da sai ya kira Gimbiya Su'adah yanzun. A mafi yawan lokuta shawarar tata bata haifar da ɗa mai ido a garesa. Dan kuwa dai gadarace kawai da son nuna isa take ɗorasa akai, ALLAH ne kawai ke taimakonsa da in yay maganar da Cos sai yay saurin faɗama Bappi shi kuma ya gyara, wani lokacin idan Bappi ya kirasa yace kar ai kaza ɗin nan kaza ya kamata ayi har haushi yakeji, ya dinga ƙunkuni kenan yana cika yana batsewar fushi. Idan kaga haƙoransa a waje yanzu to tare yake da su gimbiya Su'adah. Aynah kam kamar yanda bokan Adda Asmah ya faɗa mata a ɓoyeta kar Ramadhan ya ganta har sai an kaita gidan gwamnati haka akai, sai suka fake da cewar gyaran jiki ake mata, amma a zahiri umarnin boka suke bi, dan ya tabbatar musu inhar Ramadhan yay ido huɗu da Aynah kafin aure duk wani sihirin jikinsa sai ya warware.
    Game da Raudha kuwa a yanzu basu da lokacinta, dan su tunaninsu sun gama da shafinta lokacin komawarta gidansu kawai suke jira. Shiyyasa ko bibiyar lamarinta basa waniyi gaba ɗayansu.

        Mutane har yanzu basu farga da halin da Ramadhan ɗin ke ciki ba, sai dai yanayinsa na kullum fuska a cunkushe yanzu kansa wasu yin kananun magana. Ƴan adawa kuma suka samu na suka a garesa da sake dawo da furicin nan na mai girman kai garesa.

      Pa da duk abinda ake a gidan ya saka ido badan baya cikin damuwa da halin da ɗansa yake a ciki ba. Ya barine kawai azo gaɓar da gimbiya Su'adah zata gane kurenta. Sai dai a yanzu bita da ƙullin daya shirya musu akan shirin da suke gagarumi na auren ne. Dan ko events an haɗa yakai kala goma, sanin Taura family ba'a wannan almabazaranci sai suka fake da cewar duk a gidansu amarya aka ɗauki komai. Lokacin da gimbiya Su'adah tazoma Pa da zancen dariya sosai abin ya bashi. Amma sai ya gimtse kayarsa yace ALLAH ya bada sa'a.
     Daɗine ya kama gimbiya Su'adah, dan gani take yanzu fa kamar ta fara samun kan Pa ɗin a dalilin turaren da Adda Asmah ta kawo mata tace tai amfani da shi a duk sanda zataje gareta. Dukan wata bukatarta sai ya amsa babu musu sai ma shakkarta da zai dingayi. Murmushi tai tana ficewa cike da tafiyar takama. A ranta kuwa sakama Addah Asmah albarka take da yaba mata. Dan ta tabbatar wannan turare shike taimaka mata wajen hawa kan Pa ɗin yanzu a yanda takeso. Amma da tasan bata isaba indai wannan uban kafiyar ne da taurin kai.
    Bayan ficewarta nannauyan numfashi ya sauke da girgiza kansa, sai kuma ya saki murmushi tausayin ɗansa na ƙara ratsa masa zuciya. Mikewa yay ya fice sashen mahaifansa. Acan ya samu har su Yafendo suna hirarsu cike da farin ciki kamar yanda suka saba.
     Bappi dake shan fura ya ɗan tsura masa idanu cike da nazarin ɗan nasa. Sai kuma ya ɗauke kansa. Ita kanta Anne idanun nata a kansa suke, dan tun shigowarsa ta fahimci akwai damuwa tattare da shi. Bayan ya gaishesu Inna ke faɗin, “Bashari lafiya kuwa na ganka kamar mai damuwa?”.
     Ɗan murmushi yay mata yana furzar da huci. Sai kuma ya gyara zamansa sosai yana fuskantarsu. “Lafiya lau Inna, kawai nazo nayi magana da ku ne in ba damuwa”.
    Yafendo tace, “Faɗi kanka tsaye Bashari mike faruwa?”.
     Jin Anne da Bappi basuce komai ba ya sashi dubansu, sai dai yanda suka maida hankalinsu garesa suma ya sashi sauke ajiyar zuya. “Ba komai bane dama akan Ramadhan ne da wannan auren nasa.”
       “Ba mun wuce wannan babin ba mi kuma ya faru?”.
Bappi ya faɗa yana kallonsa fuska a tsuke.
      “Kayi haƙuri Bappah, bawai na dawo da hanun agogo baya baneba. Kawai ina son muyi wani abune dan ALLAH saboda wani nazari dana zauna nayi.” batare da ya jira cewarsa ba ya cigaba da faɗin. “Ni da ku duk munsan waye Ramadhan da kuma kammu, amma jama'ar gari da Ramadhan ke mulka har yanzu basu gama sanin waye shi ba. Auren Ramadhan da yarinyar nan Ameenatu dududu watanni na bakwai muke a ciki yanzu, ko shekara bamuyiba. Aurene da yasha soke-soke da kace nace a idanun mutane da bakunansu dalilin tazarar da su suke hange da mu babu ita a zukatanmu. Shin ya kuke tunani idan akace yanzu an fiddo maganar ƙara auren Ramadhan wa duniya, kuma da ɗiya irinsa mai irin matsayinsa kuma ƴar uwarsa sannan mai dukkan kishiyar abinda akai cece kuce Ameenatu bata da shi a baya?. Dama ance munyi haɗin auren Ameenatune da Ramadhan saboda mu gyara masa siyasarsa ace yana son talaka gashi harya auri ɗiyar cikinsu. To yanzu wannan auren nasa da har yanzu bamu gama sanin kansaba ake masa shiri na tashin hankali bama tunanin cikkakkiyar amsace ga ƴan ƙasa da abokan hamayya?. Ba ina fargar damu bane dan tunanin kar Ramadhan ya rasa kujera a zaɓe nagaba. Ina fargar damune domun kare mutuncin kammu dana Ameenatu yarinyar kirki da batajiba bata ganiba, hakama ina kare kunyar da zamu daurama bayin ALLAH da suka goya da bayanmu suka kuma tabbatar da tsarkake abinda mukayin badan sakamakon mu a hanunsu yake ba, sai dan bana son mu cire hope ɗin mutane akan mulkin Ramadhan. A yanzu Su'adah tazomin da wannan invitation card ɗin” ya ajiye iv ɗin gaban Bappi. “Bappah ka dubafa ka gani, events kusan goma ne anan aka shirya wanda ake fatan duniya ta gani ta shaida za'ama Ramadhan auren gata bama ƙasar NAYA kaɗai ba. Bayan kuma mu a wannan gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login