Showing 15001 words to 15735 words out of 15735 words
ɗora santaleliyar ƙafarsa me cike da gargasan gashi baƙi siɗik akan ƙaramin carpet ɗin dake shimfiɗe bakin ƙofar bathroom ɗin. kafin ya Ida fitowa gaba ɗaya ya a nutse ya fara taka sawayensa cike da nutsuwa take ɗakin ya gauraye da ƙamshin shower jal ɗin da yayi wanka dashi.
Ahankali ya nufi gaban dressing mirror yana ɗaure da towel navy blue iya ƙugunsa da yama wani irin loko lokon ɗauri, sai wani milk saman wuyansa yana goge ruwan jikinsa dake yarara lafiyayyar tsayayyen jijinsa me jini a jika sai faman walainiya take tamkar woni beby sabuwan haihuwa.
Wannan fuskar da cikar kamala mai nuna barazana wa maƙiyinsa dole ne ya yarda yaci wannan suna na jarumi kuma ingarman namiji me ji tashen samartaka wanta jinin mulki ya gama ginashi, zuciyar nan nasa samm babu daɗi baƙar zuciya ta ɗan motsa da dukkan alamu kenan yau don a matuƙar haɗe take.
Ba kuma komai ne ya fusatar dashi ba sai zancen matar shi da Oum ta masa a daren jiy!, wani ɗan numfashi ya sauƙe a karo na farko tare da ware lumsassun idanunsa yana me sauƙe ganinsa saman Abubuwansa da yake da tabbacin Zaid ne ya kawo mishi.
Komai yake yi cikin tacin zuciya yake tsafff ya gama shirya kansa cikin wasu haɗaɗɗun egyptanian riga da wando ya sanya sky blue, pcarp nashi ya zira inda farar lafayayyar cutie face nashi ta ƙara fidda ainihin taswirar kyawu da kuma zatinsa. A natse ya isa gaban Iphone nashi inda sautin karatun ke fita take karatun kuma ya tsaya sakamakon shigowan ƙira ɗan lumshe Ido yayi ya kuma sake buɗewa ya kalli agogon dake manne jikin bango, red lips nashi ya ɗan ciza bada yawa ba yana ɗaukan phone in dama yasan ƙiran bazai wuce Oum nashi bace, ba tare daya ɗauka wayan ba ya nufi hanyan fita,
kamar yadda yana yinsa na rashin fara'a yake haka yafito daga cikin ɗakin hannunsa riƙe da key nashi na Keken da yake son hawansa yau. Drectly Sassanta ya fara nufa tana zaune akan wata royal sofa ruwan zuma, tayi crossing ƙafafunta wanda da duk alamu a wurintane Ak namu yayi gado aha.
A nutse ya shigo cikin nutsuwarsa da deep voice ɗin nan tasa ya furta
"Assalamu Alaikum!"
"Wa'alaikas salam habeebty"
Zama yayi daga gefen ƙafafunta yana me ɗora kansa saman ƙafafunta cike da cunkushewar zuciya ya furta, "Barka da safiya Oummuna"
Gashin kansa ta ɗan shafa kasancewar ya zame pcarp ɗin, kafin a tausashe ta amsa shi cike da kulawa. Apple ya ɗauka daga jerin fruit ɗin dake shaƙe a gabanta. Babu jimawa saiga zaid shima wata harara ya cillama Ak ɗin yana ɗauke kai daga kallonsa, shima yi yayi tamkar be ganshi ba ya zauna aka fara break ɗin dashi. Shigowan jesrah kenan ko zama bata samu ikon yiba oum ta furta, "Maza je kizo min da zauj Al-maleek!"
Rassssss gabansa ya bada sautin bugu yana tsayawa daga shan coffee ɗin da yake a tsime, babu jimawa sai gata ta dawo zama tayi gefe da Ak tana faɗin. "Oum bacci ta koma mebi ta gaji ne kinsan yau ita kaɗaine tayi duka dinner ɗin nan" kai kawai ta ta ɗaga mata suna ci gaba dacin kayan karinsu.Ak kuwa wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana ci gaba da shan coffee ɗin da ya masa daɗi sosai, bayan da suka kammala yin dinner ɗin jesra ta fita cikin sauriri domin yau ta kusa yin late nema.
Zaid ne ya ɗan dubi oum a shogoɓe yana karyar da wuyansa gefe cikin ɗan tura baki kaɗan ya furta "Oum ni yaushe zaki min auren ne tunda kimma biyuna?"
Wata daƙuwa oum tama zaid ɗin tare da ranƙwashin kansa da samm baya saka hula ko wacce iri, sake tura bakin gaba yayi yana me sake faɗin.
"Kinga dama gobe birthday na don haka saiki shirya min suprise mata a maimakon kyautan da zaki min really?"
Yana faɗin haka ya kwasa da ɗan gudu gudun kada yanzu kuma yasha dundu, saman lafiyayyan gadonsa ya faɗa tare da ciro wayansa yana buɗe datan wayan domin tunawa duk wani clips nasu cewar gobene fa birthday nashi..........
To ai shikenan saimu gimtse anan kawai
Sai munzo taya murnan birthday koda kuwa a gayyar soɗi ne aha koba haka ba my FAN'S???
*BY AMMEYLAYLERH*