Showing 6001 words to 9000 words out of 15735 words
salman bane wanda shiba bansan waye mijin nawa ba.
Wurin sauran matan sarkin ta rakani muka sake gaggaisawa duk da kuwa cewar mun gaisa dasu washe garin ranar da nazo, daga nan kai tsaye fada aka rakani wurin sarki suraj anan na ɗan jima sosae domin wasu dunkulallun kuramen maganganu daya ringa bani a baybay.
Sha ɗaya da rabi na safe duk wanda ya kamata ya fito domin min rakiya ya hallara a compound na fadar. Bisa jagorancin ZAYD SURAJ SUNUSU SHUREIM da kuma jagorancin NAFISA WADA (Fulani) zamu tafi. Haka suka mana rakomu suna me binmu da fatan sauƙa lafiya, Sanyen nake cikin wani shegen almurun golding less. Me shegen tsada wanda kuɗaɗen da suka lasa suke a bayyane.
Wata kafurar yellow'n Alkyabba me ratsin fari wacca aka ƙayawatata da brawn ɗin duwatsu ita kanta abar a kallace alkyabbar. ga nose mark ɗin da Fulani ta bani na sanya sai ɓakin glass ɗin dana toshe ido dashi ni kaɗai a raina sai mita nake (Wata sabuwa kenan ko duk wannan ɗin na miye?)
Haka na shiya furtawa a raina har xuwa laƙacin da muka kai airpot a cikin wasu mayan ƙerarrun mktoci na musamman , a vip/section muka zauna loƙacin da muka shiga wani irin lumshe idanuna nayi kirjina namin wani irin lugudan da bansan ko na miye ba.
Haka jirginmu ya keta hazo muna lulawa sararin samaniya wasu adda'oi na shiga karantawa a zuciyana ko zan samu abinda nake ji na lugudan da akemin a ƙirjina ko zai ragu, "Ya Salam" na furta a bayyane loƙacin da jirginmu ya gama daidaita a sararin samaniya tun ina iya lissafa loƙuta harna koma awanni daga haka har wani bacci yazo yayi awon gaba dani har bansan loƙacin da muka ɗauka ba. Sai idan loƙacin sallah yayi a tasheni nayi na sake komawa ga wani irin kaina da yake sara min kamar ya rabu da jikina. Sha biyun dare muka sauƙa a babban airpot ɗin kasar inda hasken streetling ya haskaka ko ina na harabar airpot ɗin wata dunkulallar farar mota ce tazo ɗaukar mu sai ɗaya kuma data kasance ta security ce.
Da taimakon fulani na samu fitowa domin zuwa yanzu kaina kusan zan iyace muku ma a juye yake dan bana gane komi ga komi ɗin da nake gani bibbiyu. Ita ta shigar dani har cikin motar kafin kai tsaye mu lula cikin masarautar EMAAR's.
Tafiya bame zurfi bace ta kawomu katon ginin masarautar wanda kallo ɗaya nama ginin kaina ya idasa rikicewa bawai na kyayun ginin ba sai kawai na yadda kaina ya sara da wani irin masifar ƙarfi ƙirjina ya wani irin buga. Take wani mayen zazzafan zzazzabi ya kawo min farmaki. Daidai da loƙacin da muke shiga ginin masarautar daidai wata iriyar Guguwar iska ce na turniƙe sararin samaniya masarautar ta shiga juyamin ilahirin compound ɗin yayi baƙiƙirin tamkar ruwan sama na daf da sauɗa. domin ba sautin da ke tashi sai gunjin fitar iska wanda guguwar ta ke kaɗawa da mugun ƙarfi gami da tashin duk abin da taci karo da shi zuwa sararin samaniya, abin mamaki har da ƙananun duwatsu iskan sama ta ke yi da su tamkar ledoji. ƙara gami da rugugi kawai ke tashi.
A Kuma daidai wannan loƙacin MOH JIDDOH ta farka a firgice dafe da ƙirjinta dake barazana wa rayuwarta, wata irin zufa na wanko ilahirin jikinta ba ita kaɗai ba duk wani me alhaki akan haka haka ya tashi a furgicen haɗi da bugawar zuciya data ruhi. Wanj irinhaskene kuma ya gilma shuuuu tamkar ƙiftawar ido.
Wani irin ƙasataccen murmushi fulani ta saki cike da nishaɗin ganin yarda al'amura suka soma haske tun a farkon tafiyar. Kallonta ta mayar kan merrah wacce kamar ma bata a cikin nutsuwarta.
Gani tayi fatar jikinta yayi wani kalan hasken kyawu gami da jan hankalin duk wanda ya yi arba da arba dasu ga wani irin kwarjinin daya lulluɓe ta nan take. Shafo fuskanta tayi da hannun dama idanunta lumshe sumar idanunta na ɗigar da ruwan hawayen dake bin saman kuncinta. Kirari ta shiga jerama mahalicci tare da ambato a bayyane ta furta.
"Ga Haske nan tafe a cikin masarautar EMAAR's me maganin duhu har abada zakara shi kaɗaine sarki. Masu rufaffun ido su farka haka nan game buɗaɗɗen na ainihin nan a gabanku! Makamin yaƙin ga bayyana!"
To ai shikenan saimu gimtse haka nan ko?😊😁😀
# Shin me kalaman Waɗannan mutane suke nufi ne kam wai?#
_SHIN WACECE JADDERN ASHAAN?_
_SHIN WACCE GASKIYAR BIYUNIN MAHAIFIN SU AK SUKE GUDUN SU AK ƊIN SU SANI?_
_SHIN MIYE HAƊIN MERRAH DA MASARAUTAR EMAAR's ?_
# Shin wanne kalan wasane za'a buga tsakanin AK da kuma Al-hussein (DA'DA)?#
Duk ku biyo ni *AMMIEY LAYLERH* don warware muku zare da abawar dake cikin wannan littafi na *MIKIYA*
Wanda koda kuɗinka saida rabonka Hajiya idan kin shirya jin kitumurmurar dake cikin wannan littafin saiki biyo *AMMEY LAYLERH* da ɗarinki biyar domin ayi tafiyar manya dake Hajjaju🙅🙌. Kibar tagumi😱 nibance kowa yayi tagumi tsakaninki da Allah idan har kinsan halin ɗari biyar ɗinne baki da to nayi haƙuri ki turim ɗarinki Huɗu nikuwa na antayaki *PAID GROUP* namu da muke posting kullum Insha Allah.....
*Idan kin shirya saya saiki min magana a wannan number'n*
08104493215
*Idan kuma kai tsaye account naw kike da buƙatan shima ganan*
3206656358
Maryam Nasiru
Fisrt Bank
*Sayen na gari maida kuɗi gida koba haka ba😟😵😰 Dob Allah karmu ɓatama juna loƙaci idan baki shirya sayaba karkimin magana, Masu zagina harda ma masu kiran ai ance marubuciyar MIKIYA ta rasu ku sani Allah ne me kashewa da rayawa. Wata ma data tambayeni nace mata paid ne kai tsaye cewa tayi shikenan tama samu*
_Kunsan dana tambayeta inda ta samu me tace min? Kai tsaye cemin tai a wurin ƙawarta, ni kuma sai nace mata saidai kuma banma fara rubutun part Two ɗin so dan allah a faɗi alkhairi ko ayi shiru😯_
[07/11 9:07 pm] ★~AMMEY LAYLERH🤫: *🦅 MIKIYA 🦅*
_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________
*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
BOOK Two…………………………✍
5&6
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
# The changer game's
# Romance scene
# His bloved_friend Meerah
# His love towards
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
A daidai wannan loƙacin na'urorin dake jone da jikin me martaba sarki Hassan Al-hassan suka ɗauki wani irin kururuwar daya farkar da duk wani makusancin dake jikin ɓangarensa.
AK shine mutum na farko daya fara bayyana ta cikin wata shegiyar ɓoyayyar hanyar da ko su Oum basu san da ita ba. Shigansa ɗakin daidai da gilmawar inuwar mutum ɗin da yayi wanda kai tsaye bazai tantance ko mace bane ko namiji. Wurin Paah ɗinsa ya nufa domin dama tunda ya dawo kasar baccin kirki bayayi, kullum yana cikin tsoron mahaifinsa da yake a tsakiyar damisai masu farautarsa.
Hankali tashe yayi kan me martaba wanda daidai da shigowar shaƙiƙansa suma hankalin tashe. Kai tsaye hakan ke musu nuni da an sake _poisoning_ Sarki Hassan kenan?
"La haula fi sha'atullah!"
Shine kawai abinda OUM ta furta wani irin jiri na kwasarta.
Da sauri zaid ya tare da tana faɗuwa a jikinsa zuciyarsa na wani irin mugun bugu. "Yau mun shiga Innalillah wa'inna ilaihir raji'un"
Moh jiddoh ta faɗi tana yin kan me martaba, Wani mugun kallon da Ak ya watsa mata ne ya sanya ta jan birki jikinta ɗan rawa. RAZEERNERH (MAH) kuwa wani irin rumtse idanu tayi tare da cizar lips ɗinta da ƙasan hakorinta tanajin zuciyarta na mata bala'in bugun da tunda take bata taɓa jin irinsa ba sai akan mutum ɗaya.
Kai tsaye Ak yama me martaba ɗaukar jarirai yana barin donpor room ɗin dashi, domin kai tsaye kulawan paah ɗinsa yake son yake son ta dawo hannunsa.
"Kai jinin masu ɓakin jini ina zaka kaimin _ƊANA?_ bayan ga dr shazra ajaan nan na zuwa duba shi"
"Daga yau na dakatar da duk wani likita dubamin mahaifina, a yanzun kulawansa yana ƙarƙashin iko nane kai tsaye idan kuma dame ja bismillah hanyar a buɗe take right?"
Yana faɗar hakan ko inda suke bai sake kalla ba saida yakai hanyar fita kana murya a kausashe ya furta. "Ka biyoni da Habeebty _Ashaan Clinic resoom_ "
Kai tsaye zaid daya san dashi yake ya rufa masa baya wannan ba loƙacin tashin hankali bane dan haka sauran jama'ar ɗakin suka rufa musu baya.
★★★
Da wani irin mugun speed yaja motar yana ficewa daga baki ɗaya passes ɗin mahaifinsa.
Kai tsaye motar ambulance ɗin Masarautar ce ta ɗauki Oum A harabar building ɗin clinic ɗin Manyan Mercedes Benz black biyu na bayan ambulance ɗin ko kyakkyawan parking basuyiba sukai saurin fitowa Babu Wanda hankalinsa ba'a tashe ba sabo da tsananin tashin hankalin dake cikin zukatansu na ganin yadda AK ya shigada me martaba yayinda jigogin jikinsa suke jin rayuwarsu baya iya kwatanta rayuwa babushi ba, yayinda wasu ɓoyayyun zukatan suke jin Allah yasa nesace tazo kusa Ashshe ta gaida umma bi ma'ana ya mutu kenan.
Mutuwar data kasance rigar kowa ko kayi fata ko karka fata dole dole dolen dole dole kasan zaka mutu kuma fa ita mutuwar nan ɗaya ce in akayita ba'a taɓa dawowa har gaban abada abadan, don me kuma zaka ma wanin ka fatan ya mutu.
Arikice suka ƙaraso jikin ambulance ɗin da Oum ke ciki daidai loƙacin da nurses na cikin masarautar mata tareda doctors kusan biyar sukayo kan motar aka fito da ita. Cikin gaggawa akayi ciki da ita itama tun a hanya ake ɗaura mata ruwa dama tun acikin ambulance an ɗaura mata cannula tare da fara mata injections. Wani irin yarfar da hannuwansa zaid yayi yana jingina da jikin motan tare da kulle idonsa kansa na wani irin sara masa.
Cikin wani irin tashin hankali likitoci da nurses ɗin asibitin suka rufa su Ak baya ganin Me martaba sarkinsu me adalci cikin wannan mummunan yanayin. Bayansu suke bi hankali tashe har zuwa cikin private aminity emergency suka shige, Da hannu yama sauran dactor's nuni da suje waje kafin cikin fusgar magana ya furta musu.
"Oummuna! Habeebty itama tana da buƙatarku"
Da kanshi ya shiga bama me martaba taimakon gaggawa bayan wasu dogon aune aune daya masa, wata iriyar ajiyar zuciya ya kawo a sadda me martaba ya kawo wani gauron numfashi.
Su kuwa waje Wani irin kuka Razeenerh ke rusga tare da sauran mutane tuni wadda basa a wurin ma duk sun bayyana zuwa yanzun kuma. Wani irin rawa Jikin Adeenerh yake ganin yadda jikinta ke rawane ya sanya Jesra matse hannunta cikin nata hannun da ƙarfin daya sanya adeernerh ɗagowa. Jikinta ta faɗa tana me fashewa da wani irin cunkushashshen kukan da tun farko yaƙi zuwar mata...
Dr Abaan Areef ne ya ƙaraso harabar inda duk suke tsaye babu wanda ya iya ko zama a cikinsu, kallon Razeenerh yayi sai kuma yaɗan saki ijiyan zuciya tare da faɗin.
"Sorry ma'am you will have to wait hia and please calm your self insha Allah he'll be fine we'll do our all best just pray for him! And duk ku daina musu kuka Insha Allah komai Fine" Yana faɗin hakan Ya juya ya shige tareda wasu nurses biyu dasuka zo shigewa da gudu zuwa emagency room ɗin da oum take.
Baya jesrah tayi cikin tsananin tashin hankali tareda fashewa da wani sabon kukan ganin yadda likitoci ke gudu suna shiga ɗakin Oum ɗinsu. uzaid dake gefenta ne yayi saurin tarota cikin qarfin hali ya buɗe bakinsa daƙyar shima yasamu iya furta mata.
"Please Uktie just pray for him kinji and kiyi ta musu du'a kuka baya taɓa maganin damuwa okay?"
Wani sabon kukan ta sake saki tareda rintse ido tana me furta.
"Ya Allah ka bama Paah sauƙi tare da oum sauqi da sassaucin wannan masifa! Ya Allah ka zame musu bango majingina a cikin rayuwarsu Rabbi ka hana wani mahaluki damar sake taɓa mana paah ɗinmu! Innalillah Wa'innah ilaihir raji'un wannan ɗin wacce iriyar ƙaddarace Mai wuyar cinyewa.....
Saurin rufe mata baki Mah ta yayi da sauri tana kallonta da idanuwanta dasuka kaɗa sukai jajir tsabar tashin hankalin da suke ciki ga wani mugun bugu da wani irin sanyin da taji yana ratsa mata har cikin jikinta.
Juyawa tayi ahankali ta kalli gefenta daidai isowar Ak arikice ko gani sosai bayayi tsabar tashin hankali yana isowa ya tsaya cak tare dabin kowa na wurin da jajayen idonsa.
Kallo ɗaya zaid yama Ak ya ɗauke kansa wani hawayen da besan sanda suka taruba sun cika jajayen idanuwansa shima nan take yaji gwiwowinsa sun gaza ɗaukarsa ya zube gaban ƙofar roon ɗin dake kusa dashi tareda rufe fuskarsa da tafukan hannayensa hawaye na tsinke masa masu zafi da ciwo... Ɗauke kansa yayi daga kallon zaid ɗin yayi ganin halinda da yashiga zuciyarsa na qara nauyi sosae.
Har hawayen da yake ta ƙoƙarin dannewane na neman gangaro masa loƙacinda ya ɗago kansa ya ɗora idanuwansa kansu Mah tare da jesra da suma kukan suke, kallonsa ya mayar kan Adeenerh tana zaune gefen AYESHER tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Al-hussien kuwa hannuwansa goye da bayansa sai kaiwa da komawa yake ya haɗa wata uban zuba. Moh jiddoh ma tsayen take hankalinta ba a kwance ba domin hankalinta ya rabu kashi biyu ne, neman hanyar da zata sadata da musassin abinda ya farun take,
"Me hakan ke nufi?"
Ta faɗi da tayi zaton a zuciyarta ne, Mahoob dake dab da itane ya furta.
"Me kuwa hakan ke nufi bayan sake poisoning paah da akayi,moh nifa an fara sanja min tunani wllh yanzu zuciyata ta kasa zama wuri guda me waɗan nan jeron gwanon abubuwan suke nufi? Me yasa ake kullum cikin tryn na rayuwar paah ake? Me yasa duk sanda hakan ya faru Oum jesrah ke shiga comma itama?......
Tsawar da mahaifinsa ya buga masane ya sanya shi shanye sauran maganarsa ba tare da ya ida ba.
Duk da ƙarancin shekarunta hakan besa ta gane mayucin halin da addarta deenerh take a ciki ba. Tsamm ta miƙe daga jikin mah kuma har yanzun bawai daina zubar hawayen tayi ba Hannuwan Adda deenerh ta riqo cikin nata tare da kwantar da kanta saman sholder na deenerh nan. ɗagowa ta sakeyi A Karo na biyu tana me sake riƙe dukkanin hannuwanta biyu tanata qoqarin ganin ta kwantar Mata da hankali cikin hawaye da tsananin tashin hankali ganin kamar ko bata a hayyacinta ne, Sabo da tunda abin yafaru ko motsin kirki batayiba bare hawaye saidai jajir da idanuwanta sukai Sam ita tafiso taganta tayi kuka yafi sauqi akan wannan halin dataga tashiga, Cikin muryan kuka jesh ta shiga faɗin.
"Yi kuka! Kiyi kuka Adda deenerh paah ɗinmu ne fa baya da lafiya tare da oum, kinga duk nan kuka muke muma kalla ki gani! Kinga can gacan ma kalla _GARGALION'n_ ɗin Oum ma kukan yake hawaye yake zubarwa a karo na farko a rayuwasa tunda ya mallaki hankalin kansa..... Wani irin rumtse idk yayi yana barin wurin da sauri zuciyarsa na ƙoƙarin faso ƙirjinsa ta fito dole Anzo gaɓar da bazai sake be wani mahaluƙi damar sake taɓa may mahaifiba, Wasan yazo ƙarshe captering ɗin ya isa haka nan.
Lumshe idanuwanta dasukai jajir tayi cikin tsananin tausayin _*Abdoul-maleek*_
Tabbas dukkaninsu suna cikin wani hali Amma shi ya fisu dan kuwa shu ƙunci da Sauyin rayuwa tuni ya daɗe da wargaza komai na cikin duniyarsa, ya tsallake yabar ƙasar sa. Yabar kowa nashi duk dan bama maƙiya ƙafa dan kuma ahalinsa su rayu cikin aminci tunda ta fashimci shi ɗin yafi tsole idanu.
_AK_
Ahankali yake jujjuya ƙaramar kwalban dake gabansa wacce ajikinta aka rubuta Carbon Monoxide Poisoning da manyan baƙi, wacce yaci karo da ita a loƙacin da yake dab da barin ɗakin me marta ba.
poison ne mafi matuƙar haɗari wanda kuskuren amfani dashi kan iya lalata sassan jikin mutum yayi damage nasa kai tsaye. Carbon monoxide poisoning itace poison ɗin da ayanzu samunta keda matuƙar wahala saboda haɗari da kuma illar da takeyiwa ɗan Adam kai tsaye. Ya tabbar da wannan cctv footage ɗin da yayi setting da na'urorin ɗakin ne ya toni asirin duk wanda yayi ƙoƙarin harar Mahaifin nasa.
Murza kwalbar yaci gaba dayi ahankali fuskarsa ɗauke da wani irin ɓacin rai da fusatar da zuciyarsa.
Hannunsa ɗaya dake ɗauke da cigarette ya kai bakinsa tare da zuƙan hayaƙin cigarette ɗin ya fesar cike da bacin rai,
Kana ya ɗaura ƙafarsa ɗaya akan ɗaya haɗi da maida idanunsa ya lumshe.
Wuta ne sosai keci azuciyarsa wutar da har yau ta kasa daina ruruwa.
Amma saidai wayanda suka yi yunƙurin ciyar da paah ɗinsa poison ɗin ayanzu wutar ƙiyaayyar dake ci azuciyarsu tafi wanda ke ruruwa acikin tasa zuciyar ya sani, domin suma sun san sunyi kuskure tare da saɓanin lamba tunda harya suka bari ya farka kuwa.
Ko so suke su ɓallo ma kansu hasalin haukarsa. Wanda zallar sarauta da isa da kuma uwa uba miskilancinsa suka bisne hakan. Lallai idan har suka bari allurarsu na sojoji ya motsa masa tabbas za'a ɓarin makauniya dole.
Insha Allah daga rana me irin ta yau har