Showing 18001 words to 21000 words out of 24075 words

Chapter 7 - MAI FARAR ƘAFA COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Sep 2024

2670

takamaiman dalilin yin kallon.

*BAYAN SATI BIYU*

Duk yadda Mama da Safiyya suka so su bar gidan amma Daddy ya hana su dan shi Annur ma daga Mama ta fara masa maganar barin gidan sai ya faɗa wa Daddy, haka Daddy zai yi ta musu nasiha yana jan hankalinsu a kan kar su damu ko su saka wani abu a ransu domin nan gidan babu wani abu da za a musu shamaki za su rayu ne a cikinsa tamkar dama a nan suke tun asali. Ganin hakan sai su Mama suka saki jiki suka zauna suke sabgoginsu ko rayuwarsu ta baya basa tunawa ga komai nan na buƙata babu abin da suka nema suja rasa dan ko aiyuka akwai masu yi da mai girki Baba Dudu dan ko Mama ta ce za ta tayata girkin bata yarda sai ta ce ta sha zamanta ta huta. Kwanci tashi asarar mai rai a haka har Safiyya ta zubar da wanka. Sun yi ƙiba abinsu sun yi kyau sosai jin daɗi da kwanciyar hankali ya bayyana a jikinsu. A haka har Mama ta kammala iddarta.

Zaune yake a mota ya sako ƙafafunsa waje fa yake ƙofar a buɗe take. Ya yi nisa wajen kallon hoton Safiyya wanda ya ɗauketa ba tare da ta sani ba, suna zaune da Mama suna hira ya shiga gaishe da Mama bayan Safiyyar ta gaishe da shi ya amsa yana ɗan danna waya a haka ya saita fuskarta ya ɗauki hoton ba tare da Safiyyar da Mamar sun fahimci ya ɗauka ba. Ya kafe hoton da ido yana zooming kyakkyawar fuskarta ma'abociyar kyau wacce a koyaushe ba ya gajiya da kallonta har kullum ganin Safiyya yake tamkar sabuwar halitta a idanunsa duk da wani lokacin yana ta tunanin ina dangi da ƴan uwansu suke. Duk da cewar har yau Safiyyar bata wani saki jiki da shi ba iyakarsu gaisuwa ko zuwa ya yi ya tarar suna hira da Mama ko da Baba Dudu daga lokacin da ya shigo ɗakin za ta saka wa bakinta linzami ta rufe ruf tamkar ɗakin da aka kulle da ɗankwaɗo. Haka za ta yita sunkuyar da kai idan ma ta ga sun fiya haɗa ido da shi sai ta tashi ta shige ɗaki ta barshi da Mama a falon.

"Ranka ya daɗe ga kukar kaɗin an samo kuma wallahi tana da kyau sosai" Cewar Ibra direban gidan su Annur.

Ɗago kai ya yi daga kallon wayar da yake na ganin hoton Safiyya tare da sauke wata ajiyar zuciya ya kalli Ibra ya ce

"Ka shiga da ita gida ka ce a mini ɗanwaken amma ka faɗa wa Baba Dudu Safiyya ce za ta mini ɗanwaken" Ya faɗa yana kallon Ibra da ya ɗan rissina cikin girmama wa dama ɗanwake ya ce a masa sai Baba Dudu ta ce babu kukar da za a yi shi ne ya aika direban ya siyo a kasuwa.

"To ranka ya daɗe an gama" Cewar Ibra yana juya wa ya shige cikin gidan.




Can kicin ya nufa inda ya san zai samu Baba Dudu. Zaune ya same su da wata wacce bai ga fuskarta ba dan ta bashi baya ne.

"Hajiya Dudu an buga an barki"

Dariya ta yi tana kallon Ibra ta ce

"Aikuwa dai sai dai a barnin"

"Ga wannan in ji yallaɓi ƙarami ya ce amma Safiyya ce za ta masa ɗanwaken"

"To sannunka da ƙoƙari Safiyya lambarki ta fito" Cewar Baba tana dariya ta miƙa wa Safiyya ledar kukar da Ibra ya miƙo mata. Ita Safiyya rasa bakin magana ma ta yi sai kawai ta miƙa hannu biyu ta karɓa tana sakin murmushin yaƙe. Ibra da ke ta son ganin fuskar Safiyya sai kuwa aka yi sa'a ta ɗan juyo a nan ya yi gamdakatar na ganin fuskarta saboda bai san fa zamanta a gidan ba dan ya ɗan yi jinya ne ya daɗe ba ya zuwa aiki.

"Safiyya!" Ya faɗa da mamaki. Juyo wa ta yi gabaɗaya sai ta sauke idanunta a kan fuskar Ibra. Cikin fargaba ta ce

"Na, na, na'am" Har tana inda-inda dan ganin Ibra ya mugun tasar mata da hankali dan ta san shikenan yanzu sai ya yi sanadin barinsu gidan fa suke ganin sun samu kwanciyar hankali har suna mantawa ma da wani abu wai shi ɓacin rai ko baƙinciki na jifansu da magana da jama' a dan tun da suna samun komai na buƙata babu inda suke zuwa ko nan da can bare Safiyya dama bata da yawo ko da na gidan ƙawaye ne bare kuma da mutane suka canfa cewar ita MAI FARAR ƘAFA ce sai kowa yake gudunta ita ma kuwa sai ta daina zuwa wajen kowa bare ma har a wulaƙantata.

"To iko sai lillahi! Wato dama a nan gidan kike ake ta raɗe-raɗin...

"Ibra dakata dan Allah! Ni fa ban tambayeka koma mene ne ba dan haka duk wasu maganganunka ka riƙe kayanka" Safiyya ta faɗa tana ɗaukan ledar kukar ta tafi cikin kicin ɗin dan yin ɗan waken dan ta san Ibra tauraruwa mai wutsiya ne ganinsa ba alkairi bane.

"Baba Dudu wai ko dalilinki ta zo gidan nan? Shin ta daɗe ne a nan gidan ko yanzu ta zo har na ji yallaɓi Annur na cewa a bata ta masa ɗanwake, ko dai ita ma aiki aka ɗauketa" Ya faɗa yana wani ɗaga wuya dan ya hango Safiyya da ta shige kicin yana wani waiwaye-waiwaye kamar marar gaskiya.

"Ibra ka je ka tambayi masu gidan ni ma dai ai ka san aiki nake a gidan nan tun da kana buƙatar a maka ƙarin bayani sai ka tuntuɓi masu gida tun da dai ka san babu zai shiga gidan mutum ba tare da mai gidan ya sani ba" Baba ta faɗa tana ɗaure fuska dan dama ta san Ibra da shegen gulmar tsiya kuma tun da dai har ta ga Safiyya ta ɗaure fuska kuma ta nuna bata buƙatar yin magana da shi to tabbas akwai wata gulmar da yake son aiwatarwa duk da ita bata ga wani aibi a kan Safiyyar da mahaifiyarta ba , amma ɗan adam tara yake bai cika goma ba.

Ganin Baba ta yi banza da shi ya juya yana waiwaye har yana yin tuntuɓen da ya nemi faɗuwa.

*SAFIYYA*

Tun da ta yi ido huɗu da Ibra gabanta yake faɗuwa dan ta san idan har Ibra ya yi wa masu gidan bayanin wacece ita to tabbas za a kore su daga gidan kuma bata san inda za su je ba. Dan Ibra unguwarsu ɗaya da shi babu abin da bai sani a kanta ba game da jifanta da ake na cewar ita MAI FARAR ƘAFA ce. A haka ta yi ɗanwaken cikin sanyin jiki fa saƙe-saƙe har ta gama ta sanya masa a foodflaks ta masa miyar jajjage dan da miya yake ci ba ya ci da yaji. A kicin ɗin ta bar masa dan ta san Baba za ta saka a kai masa part ɗinsa, fitowa ta yi daga kicin ɗin amma sai ta tarar Baba Dudu ta tashi daga wajen tunaninta ko ta tafi ɗakinta ne dan a gidan take kwacakam da zama tana aiki.

Ɓangarensu ra nufa dama ta fito wajen Babar ne dan ta ɗan huta da zaman ɗakin sai ta bar Mama tana kallo. Da sallama ta shiga falon Mama ta amsa mata da kallo Mama ke binta ganin ta sauya jikinta sanyi ƙalaw ba kamar lokacin da ta fita ba.

"Safiyya lafiya dai na ganki haka?" Mama ta jefa mata tambayar. Shiru ta ɗan yi da ba za ta faɗa wa Mama ba dan kar hankalinta ya tashi sai kuma ta yi tunanin gwara dai ta faɗa mata dan idan ta san da maganar ko da an kore su abin ba zai ɗaga hankalinta ba duk da ta san mahaifiyarta jarumar uwa ce tana tunkarar matsalar da ta tunkarota a koyaushe.

"Ki faɗa mini mana kar ki manta baki da wacce ta fini a rayuwa ni ma kuma haka to mai za ki ɓoye mini Safiyya"

"Mama Ibra ne ya ganni a gidan nan"

"To sai aka yi yaya?"

"Mama ina ga fa aiki yake a gidan nan kuma kin san shi da gulma saboda shi faɗi ba a tambayeka bane, yanzu na san dakyar ne in bai faɗa wa masu gidan cewar ni MAI FARAR ƘAFA bace"

"To mene ne na damuwa? Kowane lamari fa Allah ake miƙa wa, kuma nan ɗin ma ba yin kanmu bane Allah ne ya sa masu gidan suka amincw da mu har suka yarda muka zauna musu a gida to haka in suka koremu Allah ba zai hana mu wani wajen da za mu zauna ba dan mutum komai yake ya saka Allah to kuwa Allah zai zame masa jagora!"



"Haka ne Mama"

"To ki kwantar da hankalinki komai muƙaddari ne daga Allah, ko yanzu aka zo aka ce mu tafi kar ko ɗaga hankalinki ai duniya da faɗi maye ba ya ci kansa ba"

"To Allah iya mana"

"Amin Safiyyata"

Murmushi kawai Safiyyar ta yi.


*IBRA*

Ƙafafunsa har wani wani rawa-rawa suke tsabar sauri da yake yana son ya je ya barbaɗa wa Annur gulmar wacece Safiyya dan ya san duk wanda ya san cewa ita MAI FARAR ƘAFA ce ba zai bari ta raɓe shi ba.

"Taɓ MAI FARAR ƘAFA a gidan SARKIN SHANU yo wannan kwana kaɗan ya rage duk wannan ɗinbin dukiyar da kuka tara sunanta ƘURMUS dan duk inda MAI FARAR ƘAFA ta raɓa sai komai ya lalace"Cewar Ibra a ransa bakinsa har wani mutsu-mutsu yake na son faɗin gulma da ɗumi-ɗumi.


Yana fitowa sai ya ga Annur a kan mota a zaune amma lokacin ba wai waya yake latswa ba carbinsa na dannawa yake dannawa.

"Ranka ya daɗe an isar da saƙon" Cewar Ibra yana ɗab rusunawa idanunsa kafe a kan fuskar Annur ɗin dan yana so ya ga fuskar da zai faɗa masa abin da ke ci masa tuwo a ƙwarya wanda ya gani yanzu, dan yana ganin idan har ya ɓoye kamar bai riƙe alƙawari ba ya ci amanar zaman tare. Ganin Annur ɗin ya tsare gida dan ko maganar ma bai amsa masa ba kawai hannu ya ɗaga masa.

"To fa! Yallaɓai sarautar ta motsa ya wani haɗe rai gashi ni kuma ina son faɗa masa akwai MAI FARAR ƘAFA a cikin gidansu.

"Am,um ranka ya daɗe dama akwai magana da nake son faɗa maka" Cewar Ibra a ɗan ɗarare yana kallonsa.

"Ibra ba na son damu ka yi abin da ke gabanka ni ma ina da abin yi"

"Yallaɓai wallahi tallahi maganar tana da matuƙar muhimmanci matuƙar ban faɗa maka ba hankalina ba zai kwanta ba gani nake kamar ma na ci amana ne f...

"Ibra! Ka faɗi abin da ya kawo akwai abin da nake yi ne tun da har ka ji na bafa uzurina amma tun da har ka faɗi hakan ka gaggauta faɗa mini domin in cigaba da abin da ke gabana" Cewar Annur da bai so ya katse azkar ɗin da yake ba domin azkar ne da yake na neman Allah ya bashi ikon furta wa masoyiyarsa Safiyya kalmar so tare da dacewar ya samu ta amsa masa ta karɓi tayin da zuciyarsa za ta yi wa tata zuciyar dan ba ya fatan ta watsa masa ƙasa a ido ta hanyar ƙin karɓar kalmar so daga gare shi idan har haka ta kasance bai san makomar damuwarsa ba zai rayu ne cikin damuwa da ƙuncin zuciya saboda ya yi nisa ya yi nutso a cikin kogin sont d ƙaunarta wanda ba ya jin akwai wata mace da za ta samu kwatankwacin irin ƙaunar da yake yi wa Safiyya daga wani ɗa namijin dan shi ita kaɗai ce a zuciyarsa kuma da ita kaɗai yake fatan kasancewa har iya ƙarshen numfashinsa.

"Ranka ya daɗe wata wuta na hango tana shirin kama wa a gidan nan wacce idan ta kama za ta haifar da gobara wacce ba ƙaramar ɓarna za ta yi ba don...

"Ibra ka dai san ban cika son gutsiri tsoma ba, kuma ka san wannan doguwar Hausar da kake jerowa ba wai ina fahimta bane sanin kn ka ne ban zauna na yi rayuwa a ƙasar Hausa ba na tsawon lokacin da zan ke iya fahimtar wannan murɗaɗɗiyar Hausar gwara ka mini gwari-gwari yadda zan fahimta"


"Ranka ya daɗe wata ƴar unguwarmu na gani a gidan nan mai suna Safiyya to cikin ikon Allah sai ma na ji ka ce ita ce za ta maka ɗanwaken"

"To sai aka yi yaya? Mene ne matsalarka da hakan ni fa ba na son shishshigi in ma wa na ce ya girka mini kai mene ne naka a ciki"

"Ranka ya daɗe ka gane mana, yarinyar nan aurenta uku, aurenta na farko ta auri wani Sani haihuwarta ɗaya suka rabu saboda gabaɗaya samunsa ya ragu sai uban talauci ya baibaye shi aikuwa suna gano FARAR ƘAFA gareta ya rattaba mata saki, ɗan ma mahaifiyarsa ya baiwa dan ba ya so FARAR ƘAFARTA ta shafe shi. Bayan ta fito ta auri wani Salisu shi ma dai hakan ce ta faru ɗan nasu yana wajensa ya ba wa sabuwar matar da ya aura. Ta zo ta auri wani Rabi'u shi ma dai auren bai je ko ina ba ya sako ta da tsohon ciki saboda karayar arziƙin da ya same shi talauci ko ta ina ya masa katutu ba komai bane sila kuma sai FARAR ƘAFAR Safiyya.


Yanzu maganar da nake maka a ranar da ya sake ta ubanta mahaifi ya saki mahaifiyarta ya musu korar kare kuma ba a kan komai ba sai a kan FARAR ƘAFAR Safiyyar dan ba ya son komai nasa ta kassara masa shibya sa ya jefar da ƙallon mangwaro ya huta da ƙuda. Tun daga ranar ba a ƙara jin ɗuriyarsu ba aka rasa ma ta inda suka bar unguwar dan kowa sai ya ce bai gansu ba wannan ya sa mutanen unguwa suka yi ta murnar cewar annoba ta bar wajen su. To fa yanzu ina shiga gidan na yi arangama da tauraruwa mai wutsiya wacce ganinta ba alkairi bane wato Safiyya MAI FARAR ƘAFA. Shi ne na ce ba zan yi ƙasa a gwiwa ba dole in garzayo in faɗa maka domin a ɗauki mataki dan kar a sakankance sai dai ka ga komai na arziƙi yana ja baya komai yana lalacewa ya ɓalɓalce dan da zarar ta ɗauki kwanaki uku a gidan nan to kuwa abin ba zai yi kyan gani ba" Ibra ya kai ƙarshen magana yana kallon Annur da tun da ya fara magana yake kallonsa da baki a sake.


"Allah mai hikima da baiwa, Allah mafi ji da gani Allah mai yadda ya so da bawansa. Wato ka ce ashe ƴar baiwa ce Safiyyar bamu sani ba"

"Baiwa kuma Ranka ya daɗe, ana ga yaƙi kana ga ƙura, kaska raɓi mai jini ce fa ba wai baiwa gareta ba zama da ita jafa'i ne d...

"Dakata Ibra!!! Ka san mai kake faɗa kuwa, Safiyyar kake jifa da munanan kalamai haka? Shin in banda JAHILCI da rashin imani da cewa Allah ke bayarwa kuma shi ke ƙwacewa a ce wai har ɗan adam yana iya hana alkairi ya samu mutum, ko kuma a ce yana sanya alkairin da mutum yake da shi ya rasa. Shin ina ilimin jama'a yake? Kenan idan har ɗan adam zai iya talauta wa to ina tauhidi yake? Shin ina imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau? Shin bayan faɗin ma'aikin Allah ne cewa mutum ya yi imani da Allah da mala'ikunsa da litattafansa da ranar lahira da kuma imani da ƙadddara, alkairinta da kuma sharrinta.


To in har mutum ya yi imani da waɗannan abubuwan kenan ba zai zargi kowa a kan wani abu da ya same shi ba, duk abinda ya same shi zai fawwala shi ga Allah ne domin duk abinda Allah ya ba wa mutum to ko duniya za ta taru babu mai ƙwace masa haka idan Allah bai bashi ba ko duka duniya za ta taru ba za su bashi ba, saboda haka duk abinda Allah ya bayar shi ya ga dama ya bayar kuma a ko wane lokaci zai iya karɓa. Kuma da kke maganar idan ta yi kwana uku to a wata huɗu kaɗan ne babu a kwanakin da suka yi a gidan nan suna gidan nan daga ita har mahaifiyar tata kuma Alhamdulillahi arziƙinmu na ta haɓaka babu asara ko ta ƙwandala da ta same mu dan ko yanzu bayan shigarka cikin gidan nan an mini waya motocina da na yi odarsu suna nan zuwa na biliyoyi ma kuwa kuma sanin kan ka ne akwai kwangiloli da nake yi wanda kullum sai dai alkairi da samun nasara a cikinsu ba wai faɗuwa ba da a ce JAHILCIN da kuke jifan Safiyyar da shi na FARAR ƘAFA haka ne da tuni ai wata maganar ake ba wannan ba kuma ina so ka sani ko da a ce yau zamu wayi gari a gidan ƙasa da langa-langa wato mun talauce babu cin yau sai an nemo to wannan ba zai sa mu zargi Safiyya ko wani ɗan adam da haka ba dama Allah ne ya bamu kuma shi ya karɓa , dan ya bamu bai mana alkawarin za mu dawwama da arziƙin ba dan haka ka kiyaye idan ka ƙara wani furuci marar kyau a kan Safiyya wallahi!!! Sai ka gwammace kiɗa da karatu idan ku JAHILCI ya muku katutu to ni fa ilimina kuma Alhamdulillahi ina aiki da shi bar wurin nan" Annur ya kai ƙarshen maganar yana aika wa Ibra wata muguwar harara.

"Haka ne, haka ne, haka ne" Shi ne kawai abinda Ibra ke maimaita wa yana tafiya cikin sanyin jiki kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki.

MAMAN AFRAH😍




MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)

NA

MAMAN AFRAH

FCW
GAJERAN LABARI
FREE BOOK

🔚🔚🔚

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login