Showing 6001 words to 9000 words out of 24075 words

Chapter 3 - MAI FARAR ƘAFA COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Sep 2024

2671

zuciyarsa ta yanke masa cewar ya dawo ya samu inuwa ya faka motar daga nan zuwa dare ba zai fidda ran ganinta ba dan haka a take ya juyo da kan motar ya dawo dan yana ganin wannan ce kaɗai hanya mafi sauƙin da zai sake ganinta a yau dan idan ya tafi ba ya fidda tsammanin wataƙila ya ɗauki dogon zango kafin idanunsa su sake yin tozali da ita. Yana shawo kwanar idanunsa suka sauka a kan wacce ya dawo domin ya ganta sai dai duk da cewa daga ɗan nesa ya hango ta hakan bai hana shi ganin wata riƙe da ita ba.

"Ikon Allah mai kuma ya same ta, ko dama bata da lafiya? To ko dai kukan da nake ganin tana yi dama bata da lafiya, ko dai tana da matsala a ƙwaƙwalwarta? Shin ina za a kaita? Mene ne dalilin da ya sa ba za ta yi tafiya ita kaɗai ba sai an riƙe ta?" Zuciyarsa da ke ta faman bugawa da ƙarfi take masa saƙe-saƙen tambayoyin da shi a karan kansa bashi da amsar su. A sukwane ya ƙaraso ƙofar gidan sai da ya ɗan gota ƙofar sannan ya tsaya, a ɗan tsorace ya kafe su da ido yana son gano ainihin amsar tambayarsa. Aikuwa ya samu amsar domin idanunsa ne suka sauka a kan tirtsetsen cikinta wanda ɗazu so ya masa shamaki da ganinsa. Gabansa ne ya bada wani saurin duuuuum har wani zaro idanu ya yi sai kace wanda aka ce idan ya ƙifta idanun zai ga abin da bai yi zato ba.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, kenan dama matar aure ce?" Wani sashin na zuciyarsa ya jefa masa tambayar.

"Ko dai cikin shege ne ta yi shi ya sa kullum take kuka?" Wani sashen zuciyarsa ya wurga masa tambayar da ta kusa barazanar tarwatsa masa tunninsa a lokaci guda kansa ya ɗauki wani ciwo.

"Ƙarya neeeeee ba cikin shege bane" Ya faɗa a fili yana dafe kansa da hannu biyu yana jin wani tashin hankali marar misaltuwa yana mamaye dukkan ilahirin zuciyarsa.
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)

NA

MAMAN AFRAH

FCW
GAJERAN LABARI

FREE BOOK🥳

Page 7️⃣➡️8️⃣

Wani sarawa kan nasa ke masa wanda yake jin tamkar ana soka masa kibiya a tsakiyar kan, har lokacin yana dafe da kan nasa sai ambaton Allah da yake jerowa a cikin zuciyarsa yana son ya samu sassauci game da sabon yanayin da ya far masa lokaci guda. Mama kuwa riƙe da Safiyya suka zo suka gota motar da yake ciki suna takawa a hankali dan dakyar Safiyyar ke iya tafiya Mama kuwa ganin halin da ƴarta ke ciki ya mantar da ita wanzuwar kowace damuwa da ke cikin zuciyarta yanzu burinta bai wuce a ce Safiyya ta haihu lafiya ba domin ta san duk wata mace da take cikin halin naƙuda to kuwa ba a ƙaramin siraɗi take ba siraɗi ne da yake kan rayuwa ko mutuwa.

"Sannu Safiyya Allah ya raba ku lafiya kin ji bari mu damu abin hawa mu je asibitin" Cewar Mama tana jin tausayin halin da ƴar tata ke ciki.



Safiyya babu abin da ta iya furtawa mahaifiyarta, dan yanzu haƙoranta na sama ta saka ta danne leɓenta na ƙasa sabo da tsananin azaba da take ji na ciwon naƙudar tana raya wa a ranta cewa ita dai haihuwa har kullum sabuwa take dal a leda ba a sabo da ita bare mutum ya ce ya yi ya sake.

"Ba dan babu kyau mutum ya toƙarwa kansa mutuwa ba da na roƙi na ar duniya a cikin wannan yanayin sai dai sabo da jarabawar ƙaddarorin da Allah ke jarabta ta da su ba zan biye wa faɗar mutane ba zan yi a addu'ar Allah ya kawo mini mafita domin yana ji yana kuma gani" Cewar Safiyya a zuciyarta.

"Ya Allah ka bamu ikon cin jarabawar da kake mana ni da mahaifiyata, ka fitar da ni daga cikin ƙangin jifan da mutane suke mini a kan cewa ni MAI FARAR ƘAFA ce ni nake talautar da mutane daga arziƙin da ka musu bayan babu mai talautarwa sai kai babu mai bayarwa sai kai tabbas suna magana da JAHILCI amma ni bani da yadda zan yi na fahimtar da su ya rabbi kana amsar addu'ar mai naƙuda a lokacin da take naƙuda, Allah ka amshi addu'ata ka kawo mini ƙarshen ƙunci da nake ciki ka bani miji wanda zai zauna da ni ba tare da zargin duk abin da ya rasa ni ce sila ba"


"Wayyo kin ga wannan ɗan sahun ma mutane ne a ciki Allah ka kawo mana ɗauki kar yarinyar nan ta haihu a titi" Ta jiyo muryar Mama na katse mata zancen zucin da take.

*Annur*

Idanunsa da suka masa nauyi wanda har yake wani ƙaƙance su sabo da yadda ya ji suna neman gagararsa ya yi kallon da su, a hankali ya juya ƙofar gidan da ya gan su a tsaye sai dai wayam ya hangi wurin, aikuwa da sauri ya saka hannu ya mari gefen fuskarsa dan duk tunaninsa mafarki ne ko kuma kawai ganinsu ya yi a idon zuciyarsa ba a zahiri bane ya yi hakan yana fatan Allah sa dai mafarkin yake dan ba ya son ko kaɗan yarinyar sa yake kwana da ita yake tashi da ita a cikin zuciyarsa yake tsara komai na rayuwarsa tare da ita ba ya taɓa yin mintina ba tare da ya tuna da ita ba ta zama wani ɓangare a zuciyarsa amma a wayi gari cewar ita ɗin mallakin wani ce tabbas ya san ba ƙaramin ƙunci da tashin hankali zai shiga ba. Sai dai yana maida kallonsa gaban inda hancin motarsa yake kallon tarrr ma'adanar ganinsa suka sauka a kan su, kamar yadda ya gansu ɗazu a ƙofar gidan ana riƙe da ita yanzun ma hakan ne sai dai wacce ke riƙe da ita yanzu ta shiga tsakanin kafaɗarsa saɓanin ɗazu da take riƙe da ƙugu da hannunta.

"A gaske ne Annur ba mafarki kake ba ita ce dai ɗauke da cikin haihuwa" Ya ji wani sashe na zuciyarsa ya kai masa amsar tambayarsa ta ɗazu. Idanunsa ya kafe a kansu yana jin bugun zuciyarsa na tsananta a yadda yake ji yanzu ya kasa gane haushinta yake ji ko tausayin halin da take ciki. Laimar da ya ji ta sauka a kan fuskarsa ita ya tilasta shi ɗakko hannayensa da ke dafe da kansa ya shafa fuskar da su aikuwa ya tabbatar da danshin hawayen da ke waricinsu a kan kumatunsa. Da sauri ya sanya hannayen ya share hawayen yana saka haƙoransa ya danne laɓɓansa da su idanun ya runtse da ƙarfi domin yana so ya aro jarumta domin ya samu ƙarfin gwiwar tunkararsu domin ya taimaka musu dan ya ga suna da buƙatar taimakon.


"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ni'imal maula wa ni'imal nasir, ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagis, aslihli sha'ani kullahu wala takilni ila nafsi ɗarfata ayn" Ya faɗa a fili yana buɗe idanunsa da ya runtse a hankali ya ji nutsuwa na ziyarta ruhi da gaɓoɓin jikinsa wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke key ya yi wa motar ya fara tuƙa wa cikin nutsuwa da ƙwarewa ya nufi wurinsu a lokacin da yake hango wacce ke riƙe da ita ɗin tana ta ɗaga wa wani ɗan sahu hannu wanda ya wuce bai tsaya ba. Sai da ya ɗan gota su kaɗan ya tsaya sannan ya iyo baya kaɗan har sai da ya zo saitinsu, cikin sauri ya fito ya gewaya sashen da suke tsaye da yake ba daga ɓangaren ƙofar da ya fito suke ba, a kan kyakkyawar fuskarta ya sauke idanunsa wanda ganin fuskar a saka shi jin wani maganaɗisu ya masa dirar mikiya dan bai taɓa yin kusanci da fuskarta haka ba yana hangota ne a kullun daga nesa, kafin ya sauke idanun nasa kan haƙoranta da ta danne laɓɓanta da su wanda ke jere rerasa tamkar masara a jikin sosuwarta. Da sauri ya ɗauke idanunsa daga kanta wanda duka wannan kallon ya yi sa ne a tsakanin sakanni, ya mayar da kallons kan matar da take riƙe da ita da yake yanzu a tsaye suke ba tafiya suke ba ya lura kamar dai ta kasa cigaba da tafiya ne shi ne suka ɗan dakata ta huta. Yana sauke idanunsa a kan matar ya mayar da su kan ƴar mamaki yake kamanninsu ɗaya sak banbanci kawai ita wacce ta riƙe ta, ta manyanta saɓanin wacce aka riƙe da yarintarta, a take ƙwaƙwalwarsa ta shaida masa cewa mahaifiyarta ce.

"Dan Allah idan ba damuwa ku shiga na kai ku inda za ku je" Ya faɗa da ɗan sauri tamkar wanda yake da in'inna. Mama da dama take neman abin hawa kamar ruwa a jallo jin zai taimaka musu babu wani tunanin komai ta ce

"To babu damuwa mun gode" Ta faɗa duk da muryarta akwai ɓurɓushin damuwa amma kallo ɗaya za ka mata ka san ta ji daɗin furucinsa, dan dama ta matsu ta gansu a asibiti ko dan ƴarta ta haihu a hannun likitoci ba a wannan tangararan titin ba dan bata san iya lokacin da za su ɗauka suna neman abin hawa ba da yake unguwar tasu tana a can cikin lungu ne. Kuma yau ko dan tana cikin halin son samun abin hawan ne duk sai ta ga babu abin hawan.


Ita kam Safiyya ko a bata ce ba sabo da ita yadda take ji yanzu za ta iya hawa ko da amalanken shanu ne dan ya rage mata wannan tafiyar da take yi tana jin tamkar ciwon ake ƙara mata. Annur kuwa da sauri ya buɗe ƙofar bayan yana riƙe da murfin har mahaifiyarta ta saka ta ciki da sauri ta koma ɗaya ɓangaren ta shiga domin ita ƴar da ta zauna ta kasa matsawa sabo da tsananin ciwo, Annur ɗin ne ya rufe ƙofar ɓangaren Safiyyar yana jin wani tausayinta na mamaye masa zuciya ganin ta kifa kanta a jikin kujera tana ta faman ambaton "Wash Allah na, Alhumma ajirni fi musibati waklifni kairan minha"

Duk da yana hana zuciyarsa ganin ita ɗin mallakin wani ce amma sai da ya ji tamkar ya je yake lallashinta. Cikin hanzari ya buɗe mazaunin direba ya shiga ya tada motar ya haura titi. Yana tuƙi yana ta saƙar jaki.

"Ashe fa bata sanni ba, yadda nake jin ta a zuciyata duk zatona ita ma hakan ne, duk a tunanina ita ma zuciyarta ta san da zaman tawa zuciyar, mafarkinta da nake a kowane bacci da zai ziyarci maganaina ashe ita abin ba haka bane" Har ya karya kwanar da za ta sada shi da wata unguwa mai suna GUSAU.

"Bawan Allah General hospital fa za ka kai mu"Muryar Mama ta katse masa tunaninsa.

"Gwara dai a je privet hospital" Ya ba wa Mama amsa hankalinsa na kan tuƙin da yake.

"Ka dai kai mu na gwabnati ba asibitin kuɗi ba wannan asibitin ba ƙaramin kuɗi za a kashe ba idan za a haihu a cikinsa"

"Babu damuwa zan biya mata komai" Ya faɗa cikin sanyin murya yana jin ko wani ne zai iya kashe ko nawa ne a kansa indai a kan lafiya ne ko taimako bare wacce yake ji dalilint ma zai iya bada abin da ya mallaka bare kuma ita da kanta.

"Matar aure ce" Wani sashen na zuciyarsa ya katse shi.

"Allah da iko yake, kai amma mun gode Allah saka da alkairi" Cewar Mama tana jinjina abin alkairin a ranta ɗazun nan suke neman abin hawa da kuɗinsu suka rasa amma ga shi zai kai su kyauta ba tare da su suka nemi taimakon ya kai su ba sannan ma wai asibitin kuɗi kuma zai ɗauki ɗawainiyar lallai hanyar Allah yawa gareta. Mama da ke ta jinjina alkairin da zai musu a ranta take faɗa.

"Amin ya hayyu ya qayyum" Haka kawai ya faɗa.

Safiyya kuwa tana jin duk abin da suke cewa sai dai ciwo ya hana ta magana.



A dai dai get ɗin asibitin mai suna FHARAHA ya tsaya, yana tsayawa Mama ta buɗe ƙofar ta fito ta gewaya ta buɗe wa Safiyya.

"Sannu Safiyya, Allah raba ku lafiya"

"Safiyya kenan sunanta Safiyya" Annur da fitowarsa kenan sunan Safiyya da Mama ta ambata ya yi wa majiyar sautinsa dirar mikiya. Yana ta maimaita sunan a zuciyarsa ya ga Mama ta fito da ita ƙarasa wa ya yi ya mayar da ƙofar ya rufe.

"Mama ba zan iya hawa ba benen ba" Muryar Safiyya da ke cikin tsananin ciwo ta furta a hankali, Annur da ji ya yi tamkar ta masa busa da sarewa a kunne sautin muryarta tamkar wanda aka zuba wa zuma kan daɗi wai a hakan ma tana cikin halin rashin lafiya ne ina ga tana da lafiya ga muryar a hankali.

"Matar aure ce" Wani ɓangaren na zuciyarsa ya katse shi lokacin da suka shiga get ɗin yana biye da su, kuma da yake gabaɗaya asibitin a saman bene yake dan ƙasan shaguna ne a wurin.

"Ki daure ki hau kin ji" Annur da bai san da zaman fitowar maganar ba sai jin ta ya yi ta kufce masa ta fito ba tare da ya shirya ba.

"Eh haka za ki daure ki hau" Muryar Mama ma ta ƙara da faɗin hakan. A hankali a hankali suke tafiya har suka hau saman Annur yana biye da su.

Bayanan faɗa masa duka kuɗin ya biya ita kuma nurses sun shiga da ita labour room Mama tana nan tsaye ta kasa zama kana ganita ka san tana cikin damuwa.

"Innalillahi wa inna ialaihir raji'u, La'ilaha ilallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Muryar Amminsa ta dawo masa a lokacin da take halin naƙuda tana ɗakin haihuwa ita ce magana ta ƙarshe da ta zauna daram a kunnensa maganar da ita ce maganarta ta ƙarshe a duniya haka ta tafi da cikin jikinta bata haihu ba. Wannan tunanin da ya faɗo masa wanda lokacin da abin ya faru suna tsaye a dai dai windown ɗakin haihuwar da mahaifiyarsa take ciki a wani asibiti na kuɗi yanzu kimanin shekara biyu kenan. Da sauri ya juya ya sakko daga saman benan jin hawaye suna neman zubo masa yana zuwa ya buɗe ƙofar motar ya shiga ya zauna ya rufe ya kifa kansa a sitiyarin yana jin ƙunci da damuwa suna yi wa zuciyarsa ƙawanya.

"Shin ita ma kar dai ta je ta mutu" To ina zan sanya rayuwa ta, ko bata mutu ba ta haramta a gareka matar wani ce fa. Ina mijin nata yake mahaifiyarta ce kaɗai za ta kawo ta asibiti haihuwa shi wanda ya mata cikin ina yake ko ba ya muradi da murnar haihuwar da za a masa kamar yadda wasu mazan JAHILCI ke yi wa katutu a kan ba sa son haihuwa? Ko dai ba ɗan sunna bane ɗan gaba da fatiha ne?"

"Noooooooo" Ya faɗa a fili yana ɗago kansa daga kan sitiyarin.



Neman agajin da waya take yi shi ya dakatar da shi yana mamakin ina aka samu waya a mota dan ya san tashi tana aljihunsa. Cigaba da ƙaran wayar a motar ne ya so ya addabi majiyar sautinsa kuma ƙaran yana ƙara masa damuwa da ɓacin ran da yake ciki. A fusace ya juya yana kallon bayan motar aikuwa idanunsa suka sauka a kan wata ƙaramar pos da ke kujerar da Safiyya ta zauna. Ƙaran dai yana katsewa wani kiran ke shigowa, da sauri ua miƙa hannu bayan ya ɗakko wayar lokacin kiran ya ƙara katsewa wani ya shigo.

"Kai ina dalili wannan mai kiran da naci yake ni yanzu su da suke cikin halin nan ma na nufe su da waya?" Cewar wani ɓangare na zuciyarsa.

Kawai ka kashe wayar dan mai kiran ba zai daina kira ba in ya so daga baya ka sanar da su" Wani sashen na zuciyar tasa ya ƙara raya masa hakan.

A ɗan fusace ya kai hannu ya zige zip ɗin, yana zigewa wata takarda ta faɗo wacce ba a linke take ba.

"Na sake ta saki uku" Shi ne abin da idanun Annur suka sauka a ka. Cikin sauri ya ajiye jakar dai ko wayar da ke faman ruri bai fiddo ba, hannunsa har karkarwa yake wajen miƙar da takardar gabansa na bugawa da mugun ƙarfi dan tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin takardar saki ba.

*Ni Rabi'u na saki Safiyya saki uku, ba dan ta min laifin komai ba sai dan tana ɗauke da FARAR ƘAFA da kuma ƙashin tsiya a tattare da ita kullum samuna raguwa yake ba ya ƙaruwa*

Shi ne abin da ke ƙunshe a jikin takardar.

"Safiyya, saki uku"
Su ne kalam da suka fara kai kawo suna safa da marwa a ƙwaƙwalwar Annur.

MAMAN AFREH
09030283375
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)

NA

MAMAN AFRAH

FCW

FREE BOOK🥳

Page 9️⃣➡️1️⃣0️⃣


"Mene ne kuma MAI FARAR ƘAFA? Tana da ƙashin tsiya shin mai waɗannan kalamai ke nufi, amma ai ya ce bata masa komai ba" Cewar wani sashe na zuciyar Annur har lokacin idanunsa kafe a kan takardar kamar wanda aka ce zai gano asalin tambayar fa yake jefawa kansa domin shi bai san ma'anar kalmar FARAR ƘAFA ba bare mai ƙashin tsiya.

"Shin dama kuka take mijinta ya sake ta? Kenan son sa take bata son ya rabu da ita shi ya sa har take yin kuka...

Tun kan ya kai ƙarshen maganar zucin ya ji kishi ya turnuƙe shi, gabaɗaya ransa ya ɓaci tuna wa fa ya yi tana ƙaunar mijinta ashe ma ba shi bane a zuciyarta shi kaɗai yake kiɗansa yake rawarsa.

"Ka manta bata sanka ba, ka manta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login