Showing 3001 words to 6000 words out of 24075 words
da ke zancen zuci yana tuƙi. A dai dai lokacin da ya ƙaraso ƙofar gidan da yake son ganin wacce yake fata da burin sanyata a idaniyarsa a kullum.
Tun da yake a rayuwarsa sai biyu ya taɓa ganinta kuma a ƙofar gidan da take tsaye tana zubar da hawaye.
"Allah ka karɓi addu'ata ka ƙara haɗa ni da ita ba tare da na bi ta hanyar wani ba" Ya faɗa a dai dai lokacin da zuciyarsa ta buga da uban ƙarfi sanadin idanunsa da ya sauke a kan kyakkyawar fuskarta wacce take zubar da hawaye kamar yadda ya taɓa gani sau biyu yau ma hakan ce ta faru sai yanzu ya tuna cewar gabaɗaya ganin da ya mata sau biyu lokacin ma tana riƙe da akwati a hannunta sai dai gabaɗaya akwatinan mabanbanta ne kamar yadda ya lura domin kuwa babu wani abu duk ƙanƙantarsa da zai manta a game da ita. Da sauri ya take birki wanda ƙaran ya sanya Safiyya da ke tsaye har lokacin bata shiga gidan ba ta juyo da sauri domin ƙaran motar ya dawo da ita daga tunanin da take na yadda za ta shiga gidan nasu da kuma abin da zai faru. Hannu ya sanya ya shafe fuskarsa tare da murza idanunsa domin tabbatar da abin da idanunsa ke masa tozali da shi, domin yana son bambance tsakanin aya da tsakuwa yana son tabbatarwa cewar ba ƙarya idanunsa ke masa ba, kuma ba gizo bane sannan ba mafarki bane kamar yadda yake yi a kullum ita ɗin ce a zahiri, sabo da tsabar farincikin da ya samu kansa ciki ko lura bai yi da tirtsetsen cikin jikinta ba.
Safiyya kuwa dawowarta cikin hayyacinta daga tunani sai ta yanke shawarar shigewa cikin gidan. Annur kuwa da mugun sauri ya buɗe motarsa dan yana so ya cim mata amma yana sako ƙafarsa hakan ya yi dai dai da jan akwatin da Safiyya ta yi ta shige cikin gidan. Ko ƙofar bai tsaya rufewa ba dan so yake ya mata magana cikin gudu-gudu sauri-sauri ya tunkaro wurin sai dai cikin rashin sa'a Safiyya har ta shige dan ita bayan motar babu wani da ta gani dan gilashin motar yana da yalwar baƙi baka ganin na ciki bare ma tana cikin yanayin da ba za ta iya lura da ko waye a motar ba dan dama yana daga cikin halinta ƙin shiga sabgar mutane da shiga abin da babu ruwanta.
A dai dai ƙofar ya tsaya daga ɗan baya-baya idanunsa kafe a jikin ƙofar zuciyarsa tana ta zillo tana kaiwa da komowa dan ganin wacce duk bugun da zuciyar za ta yi tare da ita yake bugawa duk da bai san sunanta ba. Hannayensa duka biyu ya saka a cikin kwantacciyar sumar kansa yana murzawa tare da yamutsawa idanunsa na kawo ƙwallar da bai san dalili ba sai dai hakan ya san ba ya rasa nasaba da halin da ya ga wacce yake muradin gani cikin halin damuwa na zubar da hawaye. Ya fi minti uku tsaye a wurin yana kallon ƙofar daga bisani ya juya cikin rashin ƙarfin jiki ya nufi motar tasa.
Shiga motar ya yi ya zauna jiki babu ƙwari, goshinsa ya ɗora a kan sitiyarin motar yana jin wani abu na ratsa dukkanin ƙofofin jikinsa ya daɗe yana so ya ganta ko da daga nesa ne tsawon lokaci bai ganta ba amma kuma yau ya samu ganinta sai ya ji yana so ya mata magana, so yake ga ganshi tare da ita ya tambayeta damuwarta ta faɗa masa domin yana so duk runtsi ya yi maganin damuwar tata dan ba ya ƙaunar ganinta cikin ƙunci ya fi so ya ga murmushi shimfiɗe a kan fuskarta duk da bai taɓa ganin murmushin nata ba amma dai zai fi kyau a ce murmushin ne ya maye gurbin kukan dan ya san dai babu yadda za a yi kuka ya fi yi wa mutum kyau sama da dariya. Sai dai kash! Hakan bai samu ba. Ya jima zaune a cikin motar amma bai ga ta fito ba kuma bai ga wani ya shiga gidan ba duk da ya ɗaukawa kansa alƙwarin ba zai taɓa neman wani ya haɗa shi da ita ba ya fi so shi sa kansa ya samu wannan damar. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗagowa daga kan sitiyarin ya sanya hannu ya rufo ƙofar yana jin babu daɗi a ransa dan har wani ciwo-ciwo ya ji kansa yana yi masa. Motar ya kunna ya bar wajen yana rayawa a ransa cewar zai dawo ko Allah zai sa ya ƙara ganinta.
Safiyya kuwa shigarta cikin gidan muryarta har rawa take yi wajen yin sallama, Mama Majida da fitowarta daga kicin riƙe da kofi ta ji sautin yin sallama amma muryar mai sallamar ta mata kama da ta wacce ta sha kuka ta ƙoshi dan haka wajen hanyar ƙofar ta kalla aikuwa idanunta suka sauka a kan Safiyya da ke ƙara yin sallama a karo na biyu da ƙarfi gaban Mama Majida ya bada wani sautin rass sabo da tsabar kaɗuwar da ta ziyarce ta a lokacin da idanunta suka sauka a kan akwatin ƴar tata.
"Innalillahi wa inna ialaihir raji'un" Shi ne abin da take ra maimaitawa a zuciyarta. Duk da ta san aure rai ne da shi kuma babu wanda ya isa ya canja ƙaddarar ubangiji, sannan ba wai ta gaji da kasancewar ƴar tata ɗaya tilo bane da ba za ta so dawowarta gida ba duk da buri kowane iyaye a kan ƴaƴansu bai wuce su gansu zaune ɗakin mijinsu suna zaune lafiya da kuma kwanciyar hankali ba, babu wasu iyaye da za su so mutuwar auren ƴaƴansu sai dai idan haka Allah ya ƙaddaro sai dai ta san muddin auren Safiyya ya mutu to wani sabon tashin hankalin ne domin kuwa abokiyar zamanta da kuma sauran mutane ba za su bar ta ta rayu cikin farinciki ba sun ringa jifanta da maganganu da kuma kiranta da MAI FARAR ƘAFA.
Ganin Safiyyar ta tsaya riƙe da akwatin ta kasa gaba ta kasa baya sai Mamar ta sunkuya ta ajiye kofin hannunta cikih sauri ta nufi wajen ƴartata zuciyarta na mata wani irin rauni da bashi da misali ko kwatankwaci tana zuwa suka rungume juna domin Mama ba sai an mata bayani ba yanayin da ta ga Safiyya a ciki yanayi ne da take ganinta a ciki a koyaushe idan rabuwar aure ta gifta mata, bare kuma akwatin fa ta gani shi zai ƙara tabbatar mata da hakan. Tun da suka rumgumi juna Mamar ke ta faman bubbuga mata bayanta alamar lallashi sabo da Mamar ta kasa furta komai harshe da laɓɓanta sun mata nauyi.
"To fa! Na dawo in ji ɗan yawon duniya, baƙon jiya ne ya ƙara dawowa? Allah suturu buƙwi in ji kishiyar mai doro, taɓɗi! Ai dama banza ba ta kai zomo kasuwa tun da abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma dukansa ake. Ai sai ko dangana dan babu mai iya zama da ƴarki MAI FARAR ƘAFA! Haka kawai talauci ya baibaiye shi bai ji ba bai gani ba wannan shi ne aure na uku da ƙananan shekarunta kowane gidan biyu ta haihu wannan na ukun kuma an ƙoro miki ita da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe kai a yanzu ma naƙuda za ta iya tashi mata, ai abin da ya dace kawai ku samu dajin Allah ta'ala ku kafa bukka ku zauna ku rungumi ƙaddararku, kun ga kun keɓe kan ku daga jama'a babu wanda wata masifa za ta samu tun da kun nisanta da mutane dan kin san dai ko gidan nan ta zauna samun Malam raguwa yake a toh gwara ta fidda rai daga zaman aure dan ko aure ɗari Safiyya za ta yi sai an sako ta!" Muryar Umma Asiya ta karaɗe kunnuwan Mama da Safiya da ke rungume da juna sun yi mutuwar tsaye duk da sun saba jin maganganu sama da haka ma amma na yau sai suka fi na kullum zafi wai su koma daji su gina bukka su zauna su kaɗai wato ma sun zama annoba, har da faɗar ko aure ɗari ta yi sai an sake ta.
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE )
NA
MAMAN AFRAH
FCW
GAJERAN
LABARI
FREE BOOK🥳
Page 5️⃣➡️6️⃣
Cikin rashin kuzari Mama ta saki Safiyya daga rungumar da ta mata ta juyo tana kallon Umma Asiya da ke tsaye ƙofar ɗakinta tana wani hura hanci da ɗaga kai.
"Wai hayaniyar mai nake ji ne? " Cewar Malam da ya fito daga ɗakinsa yana wani baza babbar riga.
"A'a Malam gani ai ya kori ji, gata nan dai wannan mai ƙashin tsiyar ce wacce bata da ƙashin arziƙi mijin nata ya ga ba haza ya mata abin da ta saba ji da gani wato ya warware igiyar aurensa daga kanta, domin ya ga ba zai iya fuskantar raɗaɗin babun talauci ba shi ne nake cewa tun da ta ƙara kaso auren nata ta taho gida bayan ƙannenta duk suna gidan aurensu amma ita ta gwammace ta zo take haɗa kafaɗa da mu duk da dama kuma auren nata ma kasada ce yo kasada mana auren da baka da tabbas ɗin zamansa kullum kana jiran tsammani" Ta faɗa tana wani taɓa hannuwa tare da maida ɗaya hannun haɓarta. Mama kuwa kawai kallonta take idanunta cike da ƙwalla dan ta san makirci irin na sobar zaman nata shi kuwa Malam Sadiq dama duk abin da ta faɗa masa tamkar ta yi zane ne a kan dutse dan ba ya ji ba kuma ya gani.
"Ke! Safiyya wato dai auren naki ne kika ƙara kashewa a karo na uku? To tun da ke bakya son zaman aure sai dai zawarci to ki san da saninki cewar na gama ɗaukan ɗawainiyarki dan yanzu kin kai munzalin da za a ce mijinki ne zai ɗauki ɗawainiyarki to tun da bakya son zaman aure ni babu akuyar da zan siyar ta dawo tana ci mini danga, dan haka ki kwana da sanin ke ce ci da shanki da kuma suturarki a cikin gidan nan. Tun da babu Allah a ranku daga ke har uwarki kullum aikin ku biye-biyen Malamai kuna tsotsewa mazan da suka aure ki samun su da kuma arziƙin da suka mallaka" Cewar Malam yana aikawa Mama da Safiyya wata uwar harara mai tattare sa tsabagen jin haushinsu.
"Malam ko da bin Malamai sauran abin fa a jikinta yake baka ga ƴaƴana da suke da ƙashin arziƙi ba su suna can lafiya limi a ɗakin mazansu ba kullum arziƙin mazansu yana haɓɓaka ba, ai kawai in ka ga ba za ka iya ba ka hankaɗa keyarta daga gidanka ta nemi ko gidan haya ne ta tare dan ba zai iyu ake zaginka a gari ana cewa ka hana ƴarka zaman AURE ba basu san FARAR ƘAFARTA bace silar komai tun da dai ka san mu ma idan ta zauna a gidan nan ba tundun tsira muka hau ba samunka raguwa yake abinci ma yana neman gagararka samu" Umma ta faɗa cikin wat murya mai ɗauke da amon kissa da kisisina, har da wani karkata kai gefe dan maganganunta su ratsa majiyar sautin Malam ɗin da kyau kar fa a samu tangarɗa duk da ta san hakan mai wahala ne a samu.
"Safiyya ki je ki kama hayar gidan da za ki zauna dan ni ba zan cigaba da zama da ke ba tun da kin ƙi zama a ɗakin miji, tun da ƙaddararki ce zama ba aure sai ki ware daga mutane dan kar FARAR ƘAFAR da kike da ita yake shafar jama'a" Sautin muryar Malam ya karaɗe majiyar sautin Safiyya wacce dama ta kwana da sanin faruwar haka sai dai bata yu zaton abun har zai yi tsamari haka ba. Wani duhu ta fara gani yana mamaye ma'adanar ganinta domin maganganun Malam da na Umma har wani amsa kuwwa suke mata musamman wurin da Malam ya ce wai ta nemi gidan haya ta zauna kenan abin har ya kai mahaifin da ya haifeta ya koreta daga gidansa, shin idan har wani ya mata abu za ta ji haushi ko ciwon hakan bayan wanda shi ne silar wanzuwarta a duniya ya ƙyamaci ta raɓe shi.
"Gaskiya ka faɗa ai gwara ka faɗi gaskiya kar ka ƙwari kan ka, tun da ka dai gani duk auren da ta yi sai ta yi kashi kamar fara" Cewar Umma tana kallon Malam.
"Bangane sai ta yi kashi ba?" Ya tambaya da alamar tambaya a fuskarsa.
"Yo duk auren da ta yi sai ta haihu mana haihuwa kamar kaza shikenan ita haka za ta yi ta barbaɗen ƴaƴa ta haihu a can ta tafi can ta haihu"
"To ai yanzu komai ya zo ƙarshe tun da ni dai na faɗa mata ta kama haya kin ga ko nan gaba ta samu mai kwasarta (Mai aurenta) Ta san idan ta ƙunso cikinta ma ta fito daga gidan mijin ita za ta ɗau ɗawainiyar yaron to za ta hankalta ta zauna a gidan aurenta" Cewar Malam yana gyara zaman hularsa a kansa.
"Haba Malam Safiyya fa ƴarka ce ko wani ya faɗi magana a kanta ko ya gujeta bai kamata a ce kai ka kasance cikin masu aibatata da kuma gudun taɓarta ba ko kuma ƙin ɗaukan ɗawainiyarta ai ita macece da idan aka koreta daga gida aka ce ta ɗauki ɗawainiyar kanta tamkar an bata lasisin shiga gurɓatacciyar rayuwa ce ta karuwanci ko wani abu makamancin haka bai...
"Majida ya isheki wato har rainin ya kai ban isa in yanke hukunci ba sai kin tsaya gatse-gatse a gabana kina min bita da ƙulli dukan kabarin kishiya, wato ni ban san abin da ya dace da wanda ya kamata ba sai ke, to ki sani ni dai na ce ta je ta nemi wajen zama in ta ga za ta kyautata rayuwarta wannan ruwanta, in kuma za ta munana ta shiga wata bauɗaɗɗiyar hanya shi ma duk ɗaya wai an ce da karuwa hayo gado, idan kuma kin ga za ki bita to hanya a buɗe take amma ki sani zan daddatse igiyar aurena daga kanki"
Wannan furucib na Malam shi ne ya sanya Safiyya jin wani irin hautsinawa mararta ta yi tare da wani murɗawa
mata a take ta fara jin gabaɗaya duniyar na juya mata, hannu ta sanya ta dafe mararta.Mama da ta lura da halin da ɗiƴar tata take ciki a hanzarce ta yi saurin riƙo ta tana cewa
"Safiyya mene ne?"
Safiyya kuwa ta kasa furta wa mahaifiyarta komai, ganin da Mama ta yi naƙuda ce ta taho gadan-gadan sai kawai ta fara tunanin abin yi dan bata son ƴarta ta haihu a gida sabo da gudun matsala.
Safiyya kuwa duk da babu wani sauran kuzari a tattare da ita haka ta yi dibarar janye jikinta daga jikin mahaifiyarta ta juya riƙe da pos ɗinta ɗaya hannun kuma ta saki marar tata ta dafe bango, juya wa ta yi ta ɗaga ƙafarta da niyyar barin gidan nasu dan ta ji dai mahaifinta ya ce ba za ta zauna masa a gida ba sannan kuma ya ce matsawar Mama ta bi ta to zai yanke igiyar aurensu wannan dalilin ne ya sanya ta janye jikinta daga mahaifiyarta domin ta tafi ita kaɗai ta gwammace komai ma ya same ta idan ta tafi ko da kuwa a ce mota ce za ta yi ɗiban karan mahaukaciya da ita a hanyar to tana ganin za ta fi samun sauƙin idan ta koma ga ubangijinta domin tana ɗauke da tsohon ciki a kuma halin naƙuda dan haka zai kasance ta yi mutuwar shahada a kan abubuwan da take fuskanta na daga ƙaddarorin da suke afka mata wanda mutane suka yi wa hakan babbbar fassara ta jahilci suka danganta komai a gareta.
Tafiya ta fara yi tana ɗaga ƙafafunta da take jin tamkar wani gagarumin dutse aka ɗora wa ƙafafun nata a haka ta tunkari ƙofar gidan gadan-gadan. Mama kuwa yadda take jin zuciyarta ta gwammace auren nata ya mutu auren da bashi da wani alfanu a tare da ita bayan cizgunawa da bautar da ita sa ake yi a gidan Malam ba ya jin maganar kowa sai ta Umma ko ƙarya ko gaskiya shi dai duk wani abu da xa ta faɗa ko ta aikata shi ne dai dai duk da cewar ana zargin kamar akwai sammu a al'amarin amma abin ya yi yawa tamkar ba Mama ce uwar gidansa ba.
"Majida tun da kin zaɓi bin ɗiyarki ki j na sawwaqe miki na yanke igiyar aurena guda ɗaya a kan ki" Mama ta jiyo maganar Malam a kunnuwanta, maganar da ta ƙara tsanantawa Safiyya ciwon naƙudar da take ji, domin har lokacin jan ƙafa take bata fita daga gidan ba kuma tana iya jiyo duk maganganun da suke wanzuwa suna wakana a cikin gidan.
"A hayye ayyiriri yiriiiiiiii" Umma ta rangaɗa wata uwar guɗa da sautin ta ya zama tamkar ana bugawa Safiyya guduma a kunne.
"Allah sa haka ahi ne mafi alkairi" Shi ne kaɗai abin da Mama ta iya faɗa ta juya.
"Hehehehe ba haka aka so ba dai ƙanin miji ya fi miji kyau, to Umma ta gaishe da Aisha, Malam dai ya jefar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda" Cewar Umma wani farinciki yana mamaye zuciyarta.
Mama dai bata ƙara ko da waiwayensu ba ta bi bayan ƴarta. A dai dai bakin ƙofar fita ta cim mata, tana dafa bango tana tafiya dan lokacin ma kamar haihuwar ta zo dab.
*ANNUR*
Tun da ya baro ƙofar gidan su Safiyya ya kama hanya amma jinsa yake tamkar ba shi ba gani yake kamar idan ya tafi ba zai sake ganinta ba saƙe-saƙen da yake ta faman yi wanda ya sanya kwanyarsa ke barazanar tashowa jin ya rasa makamar lamarin sai kawai