Showing 15001 words to 18000 words out of 24075 words

Chapter 6 - MAI FARAR ƘAFA COMPLETE HAUSA NOVEL

22 Sep 2024

2676

mai girman gaske ga kyau kamar ma ba a Nigeri'a ba. Can wani ɓangare ya nufa da su ya buɗe ɓangaren ya kai su wani babban falo ya ce su zauna zai je ya ce su shiga zai je ya sanar da Daddynsa, da to Mama kawai ta amsa suka shiga ɓangaren suna ta ƙarewa wajen kallo.



Bayan sun zauna Mama ta kalli Safiyya da ta yi nisa cikin tunani pos ɗinta a kan cinyarta ta ce

"Safiyya kar kike saka damuwa a ranki komai ya same ki a rayuwa ki zama mai fawwala wa ubangiji domin shi ne majiɓancin dukkanin al'amura. Yana sane da dukkan abubuwan da suke faruwa da ke dan haka ki ɗauki hakan a matsayin jarabawa sai dai ki yi fatan Allah ya baki ikon cinye wa. Shi kuma yaron nan dama Allah ne ya baki kuma yanzu ya karɓi kayansa, dan haka ki saka a ranki dama can Allah bai rubuta shi cikin wanda za su shaƙi iskar duniya ba , kuma ko da a a ce ya rayu tsawon lokaci yo akwai ranar fa ubangiji zai karɓi ransa domin alƙawarin Allah ne sai kowace rai ta ɗanɗani mutuwa kowa zaman jiranta yake wanda ya tafi bai yi gagggawa ba wanda ya yi jinkiri shi ma ranar ƙarewar kwanakinsa tana nan zuwa sai dai mu yi fatan cika wa da imani" Mama ta faɗa tana kallon Safiyya da zuwa lokacin hawaye ne suke ta zirya a fuskarta saboda sai ta ji tamkar Mama ta tsokano mata inda yake mata ƙaiƙayi.


"Ba komai Mama dama bawa ba ya wuce ƙaddararsa, sai dai sakin da Baba ya miki ne a dalilina ban ji daɗi ba dom...

"Haba Safiyya yanzu a ringa maimaita magana dai sakin nan fa ba wai laifinki bane kuma ki sani ba ke ce sila ba shi aure da kika ji da gani rai gareshi tamkar mutum shi ma akwai ranar da kwanakinsa za su ƙare dama can Allah ya rubuta cewa yau ne ranar da aurena da mahaifinki zai mutu kuma ko da a ce baki zo gidan ba tun da Allah ya ƙadarta zai sake ni a yau to dole sai ya sakie ni! Shi ya sa a rayuwa za ko ga ma'aurata suna zaune tsawon lokaci kuma suna samun saɓani wata rana ma saɓanin ya zama mai yawa kuma mai rikitarwa, wanda rikitarwasa da kuma ɓacin ran da aka fuskanta sai ki ɗauka a ranar auren nan zai mutu to amma kuma tun da Allah bai ƙaddara mutuwarsa a ranar ba sai ki ga duk girman laifin sun manta sun daidata sun cigaba da zama dama mata da miji sai Allah. Amma wani lokacin kuma sai ki ga wani abu ya gifta wanda bai taka kara ya karya ba, wanda bai kai ya kawo ba amma sai ki ga an kasa haƙuri an kasa jurewa sai ki ga abu ƙalilan ne ya kashe auren wanda an yi ta gumurzu a zaman sama da wanda ya yi sanadin mutuwar auren amma auren bai mutu ba sai a kan abu kalilan wanda za a yi ta cewa a kan abu kaza ya sake ta, to ba haka bane dama ranar Allah ya ƙaddara auren zai mutu dan haka ki daina ɗora wa kan ki laifin mutuwar aurena" Mama ta kai ƙarshen maganar idanunta kafe a kan ƴar tata ganin duk jikin Safiyyar ya yi sanyi.


"Haka ne Mama ba zan ƙara tunanin hakan ba na yarda haka Allah ya ƙaddara"

"Yawwa Safiyyata kar ki damu Allah zai baki miji na gari mai ƙaunarki wanda ba zai taɓa ƙyamatarki ba. Wanda zai yi sanadiyyar shigarki aljanna, saboda kullum na kai goshina ƙasa a matsayina na mahaifiyarki ba na ɗagowa har sai na roƙa miki miji na gari wanda zai riƙe ki amana wanda ba zai taɓa wulaƙanta ki ba tun kina ƙarama nake miki addu'a kuma kin san addu'ar mahaifiya tana da tasiri ƙwarai a kan ƴaƴanta bakin mahaifiya yana da kaifi shi ya sa ake so a koyaushe ya zamana abu mai kyau ne zai fito daga bakin mahaifiya ya zamana addu'ar alkairi ce ga ƴaƴanta ba wai sai a sallah uwa take yi wa ƴaƴanta addu'a ba ko aiki suka mata ko aikensu ta yi sai ta musu fatan alkairi ta musu addu'ar dacewa duniya da lahira. Ta nema musu tsari da mugayen abokai da mugayen ƙawaye ta musu fatan haɗuwa da mutanen kirki wanda za su zame musu farinciki ba wanda za su gurɓata musu tarbiya da rayuwarsu ba ta nema musu samun ilimi mai albarka ke hatta ƙoƙari uwa ce take yi wa ƴaƴanta addu'ar fin sauran ɗaliban ajinsu ƙoƙari da gane karatu hatta position uwa take yi wa ƴaƴanta addu'ar su zo su ne na ɗaya a cikin ajin islamiya da boko.



Dan haka na jajirce wajen miki addu'a tun baki san inda yake miki ciwo ba ke tun kina ƙarama idan na ga kin zo ta biyu a ajinku to na kan ƙara zage dantse wajen dagewa da addu'a har sai na ga kin doke kowa kin zo ta ɗaya kina kawo kyaututtuka gida sannan hankalina yake kwanciya bare ɓangaren addu'ar samun abokin rayuwa na ƙwarai tun kina ƙaramarki mitsitsiya nake miki addu'ar hakan har girmanki dai dai da rana ɗaya ban taɓa fashin faɗa wa ubangiji hakan ba ke ko da ina al'ada (Fashin sallah) Nake to kuwa na kan yi alwala in hau sallaya in yi addu'o ina dan kar wannan rana ta wuce ban faɗa wa ubangiji buƙata ta ba. Ko aiki nake a zuciyata ina miki addu'a da kaina baki ɗaya dan haka ko da na ga kin yi auren farko baki dace ba kin fito ban damu ba haka aurenki na biyu ma, har kawo na uku duk na san jarabawa ce ko damuwar da nake shiga a sanadin mutuwar aurenki ina yi ne saboda damuwar da kike samun kan ki a ciki da kuma kalmar da mutane suke jifanki da ita ta MAI FARAR ƘAFA. Sai dai na san akwai lokaci, lokaci zai zo wanda komai zai zama tarihi lokaci zai zo wanda komai zai zama kamar ba a yi ba dan na san iya tsawon rayuwa na miki addu'a kuma na san Allah maji roƙon bayinsa ne sannan a duk lokacin da ɗan adam ya roƙi Allah wata buƙata to kuwa Allah ba ya maido wa bawansa addu'a face ya amsa masa ita ko dai ya samu jinkirin amsuwarta ko kuma addu'ar tashi ta tsaya a sama tana kokawa da wata musiba da za ta afka masa ma'ana addu'arsa tana tare wani abu marar kyau da zai same shi. Dan haka na san ko aure goma za ki yi to akwai wanda za ki aura wata wanda burina zai cika ki samu kwanciyar hankali dan haka ke ma ki kasance cikin yi wa ƴaƴanki addu'a da ke kan ki ma" Mama ta kai ƙarshen maganar tana kallon Safiyya.

"In sha Allahu Mama na gode ƙwarai kuma ina alfahri da kasancewarki mahaifiya a gare ni, kuma uwa ta gari domin kowace uwa mahaifiya ce ce amma ba kowace uwa bace ta gari, uwa ta gari da ban take"
Mama murmushi kawai ta yi sai ta ce



"Ki kira Rabi'u a waya ki sanar masa cewa kin haihu amma ɗan bai zo da rai ba"

"Mama ba lallai ya ɗauki wayata ba saboda da zan taho har gargaɗi ya mini cewar ko kaya za a je ɗauka kar na je masa gida...

"To ai yanzu ba gidansa za ki je ba a waya za ki faɗa masa kin ga kar a binne ɗan bai sani ba kuma daga baya a zo ana A'i ina indo dan zai iya yin ƙaranki ma ya ce ki fito masa da ɗansa ko ya ce kashe masa ɗan kika yi da gangan"

"Yo Mama ai ina da hujjar da zan kare kaina tun da ba a gida na haihu ba a asibiti na haihu ko masu asibitin za su shaideni"

"Haka ne amma dai gwara ki kira shi yanzu maganin kar a yi kar a soma"

"To" Cewar Safiyya tana fito da wayar daga pos ɗinta.



*ANNUR*

Tun da ya kai su Mama ya ajiye ledojin hannunsa ya fito part ɗin Daddy ya nufa yana jin wani nishaɗi a ransa ganin irin tarin baiwar da Allah ya masa a yau na kawo masoyiyarsa abar ƙaunarsa har cikij gidansu lallai yau rana ce da ba zai taɓa mantawa ba a cikin tarihin rayuwarsa domin ko a mafarki bai taɓa kawo hakan ba, kai bai ma taɓa tunanin a kwana kusa zai haɗu da ita ba amma sai gashi cikin hikimar ubangiji komai ya zo masa da sauƙi ko da ya same ta a matsayin matar aure sakakkiya sai ga shi cikin awanni ƙalilan idda ta fita daga kanta.

"Assalamu alaikum" Ya faɗa yana daga bakin ƙofar falon mahaifin nasa yana jiran ya amsa masa kuma ya bashi damar shiga domin koyarwar mahaifiyarsa ce tun yana yaro ƙarami in zai shiga wuri sai ya yi sallama sannan idan aka amsa aka masa iso sai ya shiga.

"Wa alaikumus salam wa rahmatullah, shigo" Ya tsinkayo muryar Daddy daga cikin falon.

A hankali ya ɗaga labule ya kutsa kai cikin falon mahaifin nasa wanda ya ƙawatu ƙwarai da kayan alatu na more rayuwa. Ƙamshin freshner da sanyin AC ya haɗe falon. Zaune Daddyn yake a kan lallausan capet ya ringisa a kan tuntu sanye yake da yadin kufta wanda aka yi wa aikin hannu sai alkyabba marar nauyi wacce ta sha aiki na lafarma carbi ne ɗan dannawa (Counter) Maƙale a yatsan hannunsa na dama sai kuma hoton matarsa abin faharinsa a gefensa a jingine domin a duk lokacin da hoton yake kusa da shi ya kan ji tamkar ita ce a kusa da shi hakan yana rage masa kewar rashinta a tare da shi duk da ganin hoton ba ya rage masa raɗaɗin rashinta a zuciyarsa amma dai ya fi so hoton ya kasance a kusa da shi sai ya ringa jin tamkar dai ita ce domin a lokacin tana raye bata yin nesa da shi ta kan zauna su yi ta hira abinsu cikin so da ƙaunar juna tamkar sabbin amaren da suka tare a satin farko.


Cikin nutsuwa ya ƙarasa wajen mahaifin nasa ya zauna tare da naɗe ƙafafunsa.

"Daddy...

"Annur wani irin abu ne ya faru da kai wanda ya sauya yanayinka gabaɗaya daga mai damuwa zuwa mai annushuwa tun a sallamarka na fahimci kana cikin farinciki a muryarka, yanayin tafiyarka da ka shigo yanzu fa ma zaman da ka yi duj cikin zumuɗi ne na ƙara fahimtar daɗin da ke lulluɓe ɓoye a cikin ranka ta yadda na ga walwala shinfiɗe a fuskarka ka sai wani walwali take tamkar sabon angon da ya dawo daga wajen ɗaurin aurensa" Daddy ya katse masa maganar cikin nuna tsantar farinciki yana son sanin mene ne ya canja shi lokaci guda Annur ɗin da har shi yake bashi umarnin ya fita ya zaga gari dan kawai ya rage damuwar ransa tun mutuwar mahaifiyarsa lokacin ya dawo daga ƙasar Ingila ya kammala karatunsa har yau bai ƙara ganin farinciki a tare da shi ba ya fahimci yana cikin damuwar da ba mutuwar mahaifiyarsa kaɗai bace damuwar tasa, ya fahimci akwai wani gagarumin abu da yake damunsa a zuciyarsa wanda ya ƙi sanar da shi sai dai a yadd ya fahimta ya yi ƙiyasin kamar dai soyayya ce yake fama da ita sai dai kasancewar Annur ɗin ba ma'abocin kula mata bane babu ruwansa da ƴan mata shi ya sa ya watsar da wannan tunanin a ransa amma kuma ya tabbata koma mene ne a yau ya samu warwarewarsa dan ba haka ya fita ba.



"Daddy za mu yi maganar daga baya yanzu baƙi ne na kawo gidan nan wasu mutane ne masu kirki da karamci kuma suna buƙatar taimako na wurin zama shi ne na kawo su gidan nan"

"Ma sha Allah, Annur hasken rai da zuciyata ai babu wani wanda za ka kawo gidan nan kai ko da a ce dabba ce bare kuma mutum ɗan adam mai cike da karamci da martaba da kuma daraja a ƙi karɓarsa dan haka ka kai su masauki ko da shekara nawa za su yi a gidan nan ba za a ƙyamace su ba kai ko da za su rayu a nan ne tsawon rayuwarsa babu wani abu da za su nema su rasa matsawar ina raye kuma kaima kan numfashi sai inda ƙarfinmu ya ƙare wajen taimakon bayin Allah"

"Godiya nake Daddy" Annur ya faɗa farincikinsa ya kasa ɓoyuwa.

"Babu godiya ai yi wa kai ne kuma aikin lada ne matsawar mutum na taimakon mutane masu buƙatar taimako to tabbas ba zai taɓe ba kuma arziƙinsa ba zai gushe yana ƙaruwa ba domin Allah na taimakon masu taimako"

"Haka ne Daddy"

"Maza ne ko mata, ko kuma maza da mata, sun kai kimanin nawa?"

"Mata ne su biyu ne"

"Ikon Allah mata, Allah sarki ashe ma masu rauni ne ka san mata suna da rauni, kuma ma a she su biyu ne basu da yawa ma Allah bamu ikon kyautata musu"

"Amin ya rabb, amma Daddy uwa da ƴa ne kuma daga asibiti muke yanzu ƴar ce ta haihu dama a hanyarsu ta zuwa asibiti na haɗu da su ƴar tana naƙuda shi ne na kaisu asibiti to yanzu dai ɗan bai zo da rai ba shi ne nake so a masa sutura "

"Allahu akbar kabiran ina alfahri da kai ƙwarai saboda taimakonka ga jama'a"

"Daddy ai a wajenku na koya"

"Mu je yanzu na gansu sai ka fita ka sanar da mutane a waje domin a sallace shi"

"To Daddy"

*SAFIYYA*

Tun da ta fara kiran wayar Rabi'u yake katsewa har ta gaji ta ajiye sai Mama ta ce ta ƙara gwada wa ko Allah zai sa ya ɗauka dan Mama ta fi so a sanar da shi cewar ɗansa bai zo duniya da rai ba tun da dai har ya san ta taho da cikinsa to dole ya san halin da ake ciki. Haka Safiyya ta daure ta ƙara kiran nasa har ya katse bai ɗauka ba sai da ta yi sau huɗu a na biyar ɗin ya ɗaga da wata muguwar tdawa da ta sanya Safiyyar razana bata shirya ba kafin ta dawo daga razanar da ta yi ya kawo wata ashariya ya luƙa tamkar ɗan maguzawa.

"Wai uban me zai miki da kika nace da kirana, bayan abin da ya haɗa mu da ke ya raba kuma ko cikin mafarkina bana fatan dake ko haɗa hanya da ke yanzu ma na ɗauka ne dan in miki kashedi a kan kirana da kike to ki sani ni dai na fi ƙarfinki a yanzu domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa kuma ina gama wayar nan da ke zan yi blocking ɗinki ke hatta wayar bayar da ita zan yi gudun kar muryarki ta sa wani abunki na FARAR ƘAFA ya shafe ni ko sim ɗin ma zan cigaba da amfani da shi ne saboda customer na da suke da number...

"Ina son sanar da kai ne na haihu kuma ɗan bai zo da rai ba... Cewar Safiyya da ta katse shi daga munanan kalaman da yake faɗa mata domin zuciyarta zafi takw mata in banda ma Mama ta matsa da babu abin da zai sa ta kira wo shi, dai dai tun kan ta kai aya ya katse ta da faɗin.

"Alhamdulillahi! Allah na gode maka da hakan ta faru shikenan ma na huta da baƙar jaraba don haɗa zuri'a da MAI FARAR ƘAFA ba ƙaramin jafa'i bane gwara ma da ɗan bai zo da rai ba shikenan a ja a je an hana tsohuwa shiga mota, ko suturarsa na yafe ba sai na zo ba ku binne shi Allah sa ya ceceni a lahira amma ba zan zo ba in raɓi inda ahalin masu FARAR ƘAFA suke"

MAMAN AFRAH😍
MAI FARAR ƘAFA
(JAHILCI NE)

NA

MAMAN AFRAH

FCW
GAJERAN LABARI
FREE BOOK

Page 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣

Gabaɗaya jikinta ne ya yi wani irin sanyi zuciyarta ta karaya ta shiga mata wani zugi na maganganun fa yake faɗa mata ta cikin wayar kafin ta samu ƙwarin gwiwar furta komai ya ja wani uban tsaki tare da yanke kiran. Hawaye ne suka shiga malalowa daga idanunta ko wayar ta kasa cire ta daga kunnen nata bare a yi zancen yin magana.


Mama ce ta aro jarumta tare da ƙarfin gwiwa ta ce

"Kar ki damu ai tun da kin faɗa masa kin fita haƙƙinsa, dama ni burina ya san da haihuwar da kuma komawar abin da aka haifar to tun da kin isar da saƙo baki da haƙƙinsa ko a wurin ubangiji kin fita" Cewar Mama tana dake muryarta dan bata so ƴar tata ta fahimci raunin da zuciyarta ta yi na sauraren maganar abin da aka mata ta waya dan akwai volume Mamar tana iya jiyo duk abin da Rabi'un ya ce

"Danne zuciyarta ta yi tare da maida hawayen da ya yi wa idanunta tsinke, ta ce

"Babu komai Mama" Saboda ta ji daɗin yadda mahaifiyarta take kwantar mata da hankali ko ba komai ai soyayya da kulawar mahaifiya sama take da kowa a cikin mutane.

*BAYAN AWANNI BIYU*

Mama, Safiyya, sai kuma Baba Dudu mai aikin gidan SARKIN SHANU su ne zaune a falon lokacin Safiyya har ta yi wanka da ruwan zafin da Baba Dudun ta haɗa mata tana zaune tana cin abincin da Baba Dudu da kuma Mama suka matsa mata. Dan ko Daddy da ya shigo sosai ya yi farinciki da ganinsu domin kana yin tozali da su za ka gane mutane ne masu karamci.

Sannan shi ma Annur ya sake shigowa bayan sun dawo daga maƙabarta ya ƙara jajanta wa Mama tare da yi wa Safiyya sannu da jiki haka ta amsa tana jin kunya saboda kallon da ta lura yana jifanta da shi wanda ta kasa gane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login