Showing 1 words to 3000 words out of 17203 words

Chapter 1 - HAUWA KULU WOMEN LEADER book 1 HAUSA NOVEL

22 Sep 2024

1684


*HAUWA KULU WOMEN LEADER*

Oum yasmeen




Da sunan Allah me Rahman mejinkai

Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfanar da al'umma





*Perfectly pen's*

*King and queen writing chamber*



Story and writing

*Oum yasmeen*


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

Domin samun cigaba kuyi following din channel dina


Book 1

page 1 🔞



Ji tayi an buge'ta da sauri ta dago zata zuba uwar tijara sai kuma taga baraka tace



"Baraka ina zuwa haka...da tsakar ranar nan..?,


ke kai zan tambaya ina zaki ai ni kinsan inda nake zuwa



Haɗa rai tayi tace



"Baraka kin san halina sarai bana son rashin arziƙi ina tambayar ki kina tambaya ta...,


dariya tasa tace



"Maida hukar gidan gwamnati zani....,

washe baki hauwa tayi tace


"Dan Allah aikuwa nima gobe in zaki zani..,

Tsalle baraka ta daka tace

"Dan Allah gwaggo ta barki...?,



guntun tsaki taja tace




"Ai ita gwaggo bata da matsala inhar ina so to itama tana so kahu hamisu ne matsalata amma shima a sannu zan maganin sa..,





kai baraka ta jinjina tace



"Wallahi hauwa in kika shiga gidan gwamnati zaki iya da ko wanne shege barin shegun woman leader ɗin nan da basu da mutunci....


turo daurin ta gaba tayi tace




"Ke nima ai woman leader zan zama...,



dafa kafaɗar mara tayi tace


"Uhmmm kin san kuwa zaki iya...,

dariya ta sheƙe da ita baka ganin dariyar hauwa in ba mugun'ta ba zata yi ba tace




"Dan Allah ai kuwa kaf garin geza sai an san da zamana ke har fadar shugaban kasa sai naje...... siyasa sanadi..,



Jinjina kai Baraka tayi tace





"Allah ya nufa kin ga tafiya ta...,


To sai kin dawo ai zanzo kai kurun baraka ta gyada mata tayi gaba itama ta ci gaba da tafiya har ta isa gun me kayan miya washe baƙi yayi yace


"A'a rabebe arnan daji kece yau a gun nawa...,



haɗa rai tayi ta miƙo mai hamsin tace





"Bani attaruhu......na hamsin..,





da rawar jiki ya amsa saurin ja da baya tayi ta ya mutsa fuska tace




"haba jolu ka dinga tsabta gaka warin da kake kaga bani kuɗina in kara gaba in siya...,



ransane ya ɓaci yace


"To yar hau in baki ba ai ace bake bace shegiyar jikar masifaffiyar tsohuwa.......ai kafin ya ƙarasa ta daddage ta zabga mai kasa baki diɓar attaruhun'ta tayi ta fita a guje


kasa haɗe baƙin sa yayi


ya shiga tofar da yahu haɗe da kasa ya bita a guje da gudu ta shiga cikin gidan su ta rufo kofar langa langa dafe gwuiwoyin'ta tayi tana mai da numfashi tasan tun da tazo gida ta tsira zuwa gobe kuma zata ƙara shammatar sa ta rama zagin da ya yiwa gwaggon'ta yar aljanna tana jin irin zagin da yake yi


nan zuciyarta ta har zuƙa ta shiga gida ajiye attarun da ta siyo tayi yafi na dari......
ta shiga ɗakin da mage yake ajiye karan..... farautar mage



ta kunto da yake sun saba da karan in ya kace yabi mutum binsa yake duk inda ya shiga sai ya bi wan da kanuna mai buɗe kofar tayi ai jolo yana ganin karan a guje ya fita bama takai da sakin sa ba dariya ta sheƙe da ita ta kamosa


mai dashi ma'ajiyar'sa tayi



gurin kahu musa ta nufa buɗe wajan da yake kiwon zaɓin'sa tayi ta kamu uwar garken'sa ta mai da ta kulle jikake tana kuyat kuyat kuyat


Da saurin kama baƙin zabuwar nan tayi ta salallaɓa ta fito sai ta kanta tayi a rariya zata ta yanka saita kan tayi ta yanka ta murɗe kanta a fuka fuki ta ƙari burburwar'ta


Wanke hukar tayi ta wanke gun


daman kafin ta dawo gwaggo ta dora ruwa fige'ta tayi tsab ta sa gashin a baƙar leda duk bidirin nan da take ba wanda ya sani a gidan





hakan kuwa baƙaramin dadi yayi mata ba dan haka ta cikin sauri take komai gwaggo tane gefe tana jajjage tace





"Amma wannan attaruhu yayi araha...,



ta gefen ido ta kalli gwaggo tace





"In ana cin ɓaure ba'a tone tone...kawai ki ci gaba da daka,





banza tayi mata har ta gama ta kwashe ta koma ɗaki



tafasa zabuwar nan tayi sannan soya zabuwar nan tayi sannan ta soya attaruhun nan tayi tare albasa yaji kayan kamshi saka ta tayi a cikin soyayyan attaruhun nan ta juja'ta nan fa kamshi ya baza ko ina





gafaran ku dai masu gida gaban jidda ne ya waɗi sai ta dake ta washe baki tace







"Kahu musa barka da dawo wa..,



mamaki ne ya kama shi to jidda hankali tayi ne ......har tana mai barka da zuwa in kana da rai zaka sha kallo ya raya a zuciyarsa yace





"yauwa kululu me kike dafawa haka...kamshi ya ƙaraɗe ko ina..na garin ɗurma..,


Sosa keya tayi tace



"yauwa kahu zo kai ma ka kwashi rabon ka biyan bashi akai min da kaza shine nace mun dade bamu motsa baki ba bara nayi mana dabgee muciiii...yau kowa ya mai da mugun yahu....,





tattare malin malin ɗin'sa yayi zuciyarsa tayi fari kal yau zai washe baki....da jajjaja..an dade ba ahaɗuba ƙaraso kujera ya samu ya zauna







dariya ce ta kusab kubbucewa jidda gashi dai yana giwo amma ba wanda ya isa yaci shima ba ci yake ba sai dai su mutu ba wanda ya isa yaci aikuwa yau tasan ladan kowa na gidan nan domin sai sun tauna kashin uwar garken kahu musa tace



"Kahu lafiya naga kayi hurjajan da kai kaga fuskar ka kuwa...? yawa kwan lantarki duk ta motsi...,



haɗa rai yayi kome ta tuna sai kuma ya saki yace


"Am kululu bara in samo kwano ki zuba min nawa naga kamar ya dahu...,





Da sauri gwaggo ta fito tace


"Wallahi baka isa ba ko ni ban ciba sai kai daga zuwan ka da kafa yawa katafila kana cewa a zuba maka da sai miƙe huya kake yawa murriƙen lema...anya kuwa musa kana so kaga annabi...?,





me jidda zata yi inba dariya ba haɗa rai yayi ya kasa magana saukewa tayi ta zubawa gwaggo nata sannan ta zuba nata ta miƙowa haku tukunya da huya da kafafuwa zaman dirshan yayi yana ci yace



"Amma kululu wallahi baki da kirki jibi wanda kika bani me maƙon ki raba dai-dai ni da gwaggo ki dau karami shine kika nuna wariyar launin fata ko....?,





Kut gwaggo ta haɗe naman bakin ta taci



"Kululu dauko min tukunyar nan tun da bashi da godiyar Allah....duk wanda be godewa Allah ba zai godewa azabarsa..,




saurin jan tukunyar yayi ya zuge huya yace



"Haba gwaggo agaban yarinyar nan kike min haka..,





gyara zama tayi tace



"Wato jidda anya akwai tsuntsuwar da takai zabo dadi...?,


kasa haɗiye yar tsokar da ya cira yayi besan lokacin da ya zunduma ihu ba yace





"Wayyo Allah na shiga uku gwaggo me kike faɗa..,



saurin tashi kululu tayi ta sheƙe da dariya tana kallon kahun nata sai zare ido yake yawa wanda ya yiwa sarki karya ga dalalal da yahu da yake ya kasa haɗiyewa tace


"Wayyo Allah gwaggo kahu musa bashi da lafiya abin mahaukata yake....mu gudu...kar ya murɗe mana huya kamar yarda ya murɗewa zabuwar....sa,




Baba lami ce ta fito tana lasati tace



"Malam ban ga uwar garken ka ba...kuma kamar kwai zata fara Allah isa ɓarayi ne suka shigo ba...,





da hannun'sa ya shiga nuna su kululu yama rasa bakin magana





Karab jidda tayi tace





"Kar ka doramin jakar tsaba kaji su dinga bina biyan bashi akai min na zabuwa...,



malin malin ɗinsa ya cire yayo kan jidda a zafafe gwaggo ta jawo shi tace



"Wallahi ka taɓa ta zan ɓatar maka jidda ce tace tana son cin dabgee shine ni kuma bani da kuɗi nace ta zaɓo mana me tsoka da maiƙo a cikin zabin ka muci tun da nasan kai in na tambaye ka ba bani zakai ba shi kuma maraya ba a hanashi a bu...,



wani irin tukuƙi zuciyar kahu musa take kai ya gyaɗa yawa kadangare ya dauki malin malin ɗinsa bal yayi da tukunyar cikin daga murya gwaggo tace




"Kayi ball da ɗuwawun Rabi'u...,





tsalle jidda tayi ta dinga dariya ran baba lamine ya ɓaci ta bar gurin .....



fakar idon gwaggo yayi ya dauki kwanon jidda ya tafi


ihu jidda tayi tana ta zauna a kasa tana rusar kuka kai kace mahafin'ta da ya rage mata shine ya mutu



tsaki gwaggo tayi tace



"Na dawo gareki shine kika zuba naki yafi nawa Allah shiƙara da ya dauke miki..,







dakata wa tayi da kukan ta zaro manya manyan idanuwanta.....,







********


Cikin sauri ta ballo magani ta watsa a bakin ta ta dauki glass cup ɗin dake kan table ta sha daga shi sai trouser milk colour sai singlet ya shigo saurin boye



raguwar maganin tayi da sauri ya ƙarasa cikin haɗa rai yace



"Bani abin da kike sha...,



gaban tane ya waɗi kut ta haɗiye wani yahu duk rashin kunyar'ta tana tsoron mijin'ta saidai komai zai yi yayi bazata iya daukar ciki ba a wannan shekarun nata da yarinyar ta ta tsofa ya ga wata ya auro mata jikinta a sanyaye ta miƙo masa kara family planning da sauri ya dago fuskarsa har ja take saboda ɓacin rai yace




"Nadeeya daman ke kike hana kanki haihuwa me isa zaki min haka kinsan kuwa yarda nake son yara....?,


tashi tayi ta tushe kunnu wanta tace




"Please ash ka saurare ni ban yi haka ba sai dai da na tsaya nayi tunani a gaskiya bazan iya haihuwa ba sa da kananun shekaruna zan tsofa da huri ne bazan iya rainon yara ba a inzo cikin dare in kula da kai ga aikina bani da lokacin kai na balle naka sai in kara shigo da yara cikin lissafin mu....,





ai ba ta ƙarasa ba ya wanke ta da mari dafa kuncin ta tayi tace





"Asharaf yau nika mara...?,





A fusace yace




"Nadeeya ban san baki da tunani sai yau ashe daman ke kike hanani samin muradina...wallahi zan dau kwakkwaran mataki a kan ki..,


cikin kuka tace




"Wallahi yau a gidan mu zan kwana hulakancin naka har ya kai haka...,




Ransa in ya kai dubu ya ɓaci fita yayi cikin sassarfa yake tafiya har ya isa part ɗinsa murɗa handle ɗin yayi ya buda kofar kan royal sofa ya hau ya dafe kan'sa dake tsakanin sara mai





Allah ya jarab beshi da wata irin mata fadeela auran soyayya sukai amma a komai nuna mai gazawar ta take musamman ɓangaran auratayyah bata iya jure buƙatunsa

a kullum cikin korafi take Allah yayi mai son yaya dole ta dau kwakkwaran mataki a kan'ta bashi da burin auran mata biyu da a yau ba sai gobe ma ya daura aure




wayar sa ce tayi ruri be kula da ita ba har ta kusan katsaiwa sannan ya daga haɗe da yin sallama




cikin dadtako mutumin ya amsa sallamar yace




"Asharaf gobe ka biyo geza akwai Magana da zamu yi....,



Cikin ladabi yace







"Barka da dare to insha Allah zanzo...,





yauwa Ashraf ya harkar siyasar zaɓe na ƙaratowa..ko





Asharaf yace







"Eh wallahi abba...,





to Allah ya bada narasa da sa'a





Amin ya amsa



Abban nasa yace





"Ya iyalin naka...,



Ajiyar zuciya ya saki me nauyi har mahaifin nasa yana iya jiyowa shi mutum ne da ba'a gane inda ya dosa ga zurfin ciki yace







"Tana lafiya...,





sallama yayi mai ya kashe wayar tashi yayi yana zirga-zirga ya kai ya komo dole fa in har yana son farin cikin sa ta dore sai Nadeeya ta gyara halin'ta





inba ta gyara fa shashin zuciyarsa ya cillo mai wannan tambayar limshe idanuwansa yayi hakan na nufin zai dawwama ba farin ciki kenan ya cillowa kan'sa wannan tambayar cije lips ɗinsa yayi ya sami gu ya zauna system ɗin'sa ya dauko aiki ya fara saurin kallon tamfatsaitsan agogon dake manne abango karfe 10:00 cikin takaici ya girgiza kai





Yanzu Nadeela bazata gyara halinta ba yau shekarar su tara da aure amma bata sati biyar batare da tayi yaji ba akan ɗan karamin dalili wannan wacce irin mata ce bata san ta rufe sirrin ta ba sai daita bankada shi

kasa aikin yayi ya rufe system ɗin yayi ya tashi tunani yayiwa ƙwaƙwalwarsa yawa ga na yan uwansa





tabbas dole ya nemo mafita inhar fadeela ba zata gyara halinta ba bata son shiga dangin'sa ko wanne taro in za'ai ba ruwan'ta ga ƙazan'ta kwanon da taci abinci anan zata barshi saidai yan aiki su ɗauke shi mutum ne babba be daci a gan'sa a restaurant ba dole saidai kullum yana aikin order musamman ma yanzu da yake neman takarar shugaban ƙasar GEZA wayar sa ce tayi ruru sai da takusan kasaiwa sannan ya dauka yace



"Innalillahi an kona ofishin jam'iya..,





kashe wayar yayi batare da ya tsaya jin me za'a ci gaba da ce mai zaman dirshan yayi daman haka siyasa take ko kuma shi kade akewa haka ba me bashi amsar nan lulawa duniyar tunani yayi......


*****

Yi min shiru shasha sha wallahi ki guji ranar da asharaf zai gaji da halin ki wannan wanne irin sakarci ne Nadeela...asharaf ya manyan'ta dole yanzu yana bukatar ya'ya da kwanciyar hankali amma kin gaza samar mai ya fita waje a cazo mai kai ke kixo ki chazamai kai dame zai ji... wallahi tun huri ki dena biyewa shawarar ummi...





Fab ta buge baƙin'ta to ta uwar...ubanki zata ji... wallahi mubeena ki fita a idona nawa fadeela take da har zata iya wata haihuwa





girgiza kai tayi ta fita tana kukan baƙin ciki bawai dukan bakin ta da tayi bane ya ɓata mata rai aa saidan ta'kaicin halin mahaifiyar tasu duk abin da nadeela tayi to wallahi ummi ce tasa'ta ga bin masu tsubbu ko ina in taji taje





Kwantar da hankalinki yar lele yanzu na fadawa hajiya saratu zata nemo mana mafita yaron ne a kwai taurin kai da yaya aka samu ya aure ki







Tagumi ta zare tace







"Wallahi ummi kullum har wasiwasi nake anya kuwa malaman nan suna yin aiki kuwa karkarin sa kwana uku daga nan zan rasa control ɗin ASH zai ƙara juyemin bai bai,



dafata tayi tace




"Kar ki damu zamuje gun malam me kankat aikin sa yawa yankan huka....,





Tsalle ta duka tace




"Saini uwar gida kuma amarya a gidan Asharaf imam geza A.I.G ,





tashi ummi tayi ta sa dariya tace




"Faɗi dawai ki ƙara da ihu inde ina raye ke kaɗece matar Asharaf...,





🤔 🤔



Wani irin juyi tayi gami da rausaya tace



"Shiyasa nake son ki ummi na..,





dariya ta sheƙe da'ta......✍️




*HAUWA KULU WOMAN LEADER*


🤣🤣🤣🤣



Yawan sharing din Ku yawan read more



# *HAUWA KULU WOMEN LEADER*




🔞




Book 1


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



Gashshan malango ta gutsura yana tururi tace



"Gaskiya iliya ka iya gashi...,




Washe baki yayi ya gyara hutar tsiransa yace





"Allah ko jidda....,





sakamakon tana tauna gyaɗamai kai kawai tayi komawa gefe yayi ya sarke hannuwansa yace


"Wallahi jidda duk randa na same ki nayi babbar sa'a...,


kut ta haɗeye naman kallon sama da kasa tayi mai tace




"ILIYA ILIYA......taja karshan sunan tace



Wallahi ka gyara kalaman ka nan da ka ganni wallahi bazan aure ba sai na zama woman leader bara in maka da manyan baki gobe insha Allah gidan gwamnati za ni nida baraka



Shiru yayi ya shiga tunani can kuma yace

"Jidda bakya gudun abin da mutan garin nan zasu faɗa....kinsan fa ita kanta baraka kallon karuwa ake mata sannan kina ji kina gani zaki tsoma kanki kar fa ki zo ki gujeni....,




Wani dogon tsaki ta ja ta tashi ta tufar da yahu tace


"Wallahi iliya baka taɓa batan rai irin yau ba har kasa naman nan da nake ci yayi min ɗaci sanin kan kane ni abin kunya baya na bashi wallahi ,




Ƙasa yayi da murya yace




"Dan girman Allah ki yi hakuri...,



gyara mayafin'ta tayi ta sashi a kafaɗa tasa hannu ta dauki takardar balangon'ta tace



"Okay ni na tafi daman ai yan gidan ku kallon mara mutunci suke min ga saƙo ka faɗawa zulai na rantsai da Allah in har na ganta sai nasa su jagwal sun yanke ta a fuska daman chajimoshin na saba zuwan'ta dan nasan karshen ta a kai ni can ko huni bazan ba zan fito.....,



Da sauri ya kalle'ta cikin sarkewar harshe yace





"Jidda kiyiwa Allah da manzon'sa ki dena abin da kike wallahi ina gudun randa yan gidan mu za suce bazan aure ki ba me zulai tayi miki....,



Hannu ta tafa tace







"Good question kamata yayi tun farko tambayar da zakai min kenan amma ka tsaya dogon jawabi yanxu wanne zan amsa maka a ciki kafin in tafi....,






"Duka..,



Zaro kyawawan idanuwan'ta tayi tace



"Zan amsa maka daya amma yanxu time ya kure..,



Tazarcan rigarsa ya karkaɗi yace




"To sai yau she yanzu...?,



Far tayi da idanuwan'ta tace



"Sai nan da jibi..,


Allah ya kai mu amin tace ta fara tafiya wani uban warin ganye taji tsaki taja ta laɓe a jikin wata ƙatuwar bishiya kasancewar darene ba me ganin'ta dan haka ta daddage ta maƙe murya tace



"Wayyo inna ya takan Kashim kaina..,


da sauri goje ya ja rigar umaruju yace


"Da kata kaji kamar magana naji anayi sama sama karab a kunnan jidda ƙara maimaita tayi aikuwa tuni suka bar bushe bushen da suke duk kuwa da sunyi mankas




Waige-waige suka fara ƙara ɗaga murya tayi ta maƙe'ta tace


"Wayyo inna wannan mataƙi zan dauka a kan su kinga waccan me farar jamfar ya dodana min taba a kwakwalwa...,





Gaban umaruje ne ya waɗi ba shiri ya zura tabar a baki ya taune ta duk kuwa da irin zafin da yake ji zare ido yayi yace



"Mun shiga uku munyi gamo Allah ka zama gatana....,



Jabiru da yazo yana tangaɗi ya zaune yace




"Gayu ya akai naga kunyi likimo bame kwakkwaran motsi a cikin ku....ko kun luluƙa hazo da yawa ne.....?,




Kuka goje yasa fyace majina yayi da hannun rigar'sa yace







"Jabiru yau mun shiga komar aljanu har umaruju ya ɗoɗana mata taba a kashin kwakwalwar'ta....,



Wani uban ihusa yace



"Goje zance kut....ubanka kaga dan bantan uba...me kai yawa lauje ni zaka kawo wa zancan banza wanne irin aljani..buga ƙafafuwan'sa yayi wani irin ihu irin na yan tsaki jadda tayi jikake



"Tsiyau tsiyau inna ga wani can ya take min ƙashin kuguna.....,



Zaro ido umaruju yayi yace




"Shikkenan jabiru ka cuce mu yanzu Allah ne kaɗe yasan abin da zata yi mana wallahi daga yau na dena daba da shayeshaye...tashin hankali ba'a samai rana kamar daga sama su kaji tace





"To inna ɗaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login