Showing 3001 words to 6000 words out of 17203 words

Chapter 2 - HAUWA KULU WOMEN LEADER book 1 HAUSA NOVEL

22 Sep 2024

1686

in shanye mai kafa ɗaya allon kafaɗa shi wancan wanda ya zo daga baya in kwashe mai ya'yan hanji....,




Hannu jabiru ya ɗora akai ya saki ihu ga futsari da ya saki wani irin gumi ke karyo mai ba rayuwa ba kenan in ta kwashe mai ya'yan hanji cikin kuka yace



"Goje Umaru je baku zakuyi kuka ba....nizan yi dan girman Allah ke temake ni nasan kina jina bansan kin kwan'ta ba nazo da wallahi na sani ba dalilin da zai sa in taka ƙashin ki me daraja.....,





Wata dariya ta bushe da ita abin ka da kauye gidaje ba a haɗe suke ba tuni ta shiga amsa kuwa curewa gu ɗaya sukai tace



"Wato ku bil'adama Allah yayi muku kunnan ƙashi......kuna jina ina ihu sakamakon ballamin kashin ƙwaƙwalwa da kukai amma ko a jikin ku tun dazu kun hanani sakat na gayyato kawayena domin party cikar shekara'ta dari takwas da haihuwa kun dame su da warin wiiiiiwiii to yau zaku ci kaniyar ku bara ɗan tsitaka yazo ya kaddamar muku.........,



Dan girman Allah da manzonsa ki hakuri haka suka haɗa baki suka ce ɗib suka ji ba sai can suka ji tace





"To inna ta ban hakuri amma zan kafa muku doka ko wannan ku ya tafi gida da rarrafe sannan kar wanda ya sake ya ƙara yin dare a waje haɗa baki suka ce to suka fara jan kafa sai da'taga sun yi nisa tafito tana kyalkyala dariya yau zuciyar'ta kyal tayi maganin shegu



kofar gidan su taja ta tsaya sakamakon ganin malam yana zaune da radiyo a gaban'sa cije lips ɗin'ta tayi ta fara sanda domin bacci yace har takai kofar gida taji yace




"Ja'ira zo.....nan ke nake jira juyowa tayi ta ɗurkuwa ƙasa tace




"Malam gani...,





Tashi zaune yayi ya kalle'ta ya girgiza kan'sa yace


"Hauwa'u Hauwa'u Hauwa'u rashin ji wallahi ba inda zai kaiki ki mace ce ba namiji ba namji ma inyayi ba riba yake ci ba balle ke kina mace ki tausaya wa maraicinki ki gyara halinki Hauwa'u mahaifiyar ki mutuniyar kirkice wallahi dube ni duk narame kullum cikin jawo min magana kike ɗazu haka musa yayi min tass duk keki ka jawo min kina biyewa gwaggo Allah ya shirye-ki ya gyara min ke ni bazan miki baki ba ,




Tashi tayi ta karkaɗe jikin'ta tace




"Amin malam amma wallahi duk wanda kaga nayi wa yimin yayi kahu musa kuwa gwaggo ce tasani nayi ta yammun...,





Shiru yayi mata ya kashe radio ya nannaɗe tabarmar ya bi bayan ta ɓagaran'sa ya shiga ita kuma ta shiga bayan gida jabiru ne ya shigo dai-dai fitowar ta cikin daga murya tace



"Innalillahi inna baba lami iya hansai babar su hamza kahu hamisu kahu musa malam......gwaggo ku fito yau jabiru yasha wacce tafi ƙarfin'sa yayi tumu tumu a ƙasa rarrafe yake ma....,




Kowa fitowa yayi wani kukan takaici jabiru ya fashe dashi yau yana ganin darasi cin naka ne kunama ce be sani ba shine yaji an zabga mai wani uban cizo a gwuiwa ba abin ya tashi ya duba ba aljani ɗan tsitaka ya kwashe mai ya'yan hanji tambayar'sa aka shi ga yi kallon su kawai yake yana girgiza kai yana kuka kahu hamisu ne yazo zai ɗaga shi da sauri yace





"Dan girman Allah ku barni kar ta kwashe min ya'yan hanji tsaki jidda ta saki ta ajiye bota tace



"Kuma ku barsa yasha wacce tafi karfin kansa ne cikin saui gwaggo tace




"Aikuwa dan daga gani daga kun yan iskan yaran nan yake kai dai Allah ya shirye ka jikalle zo mu shiga inda ta ajiye naman'ta taje ta dauka suka shiga ɗaki ta baje musu suka fara ci gwaggo tace




"Allah yayi miki albarka in kika auri iliya kululu mun gama hutawa wallahi ke fadaman ta gaban mota ce wallahi...,




ɓata rai tayi tace




"Gwaggo in aure iliya kuma tab.....ai wallahi sai na zama woman leader ke fa makkan nan wallahi sai kikaga na kai ki...,





Washe baki tayi tace





"Dan Allah...,





Gyara zama tayi tace




"Wallahi....,



To bayan sun gama ci ta wanko bakin'ta lokacin ba kowa a tsakar gidan sun watsai ana jiran gobe tayi a kira me ruƙiya ta kwanta



Asuba ta gari





*******



Karfe 2:30 na dare





GEZA Government house





Sa'eed mai garo ne zaune yana girgiza kafa ɗaya abin duniya ya ishe shi sai da yaja fasali sannan yace


"Kwana arba'in ya rage ayi zaɓe abubuwa matsowa suke bana so in rasa kujerar shugaban ƙasa alamun da nagani al'umma sun fi son Asharaf imam geza amma zan maganin shi....,




Dariya ɗaga daga ciki yayi yace




"Allah ya jada ran ka ai wannan abin kabar min shi ahannu na sufa talakawa da han watsa musu tsaba shikkenan za su ta caccaka kaga mun kauda musu da hankali mu ci gaba da kwasar dukiya.....,





🤔 🤔




Yusuf jirga yace





"His excellency ai wannan abin ba abin da muwa bane saboda mu muke da yan jagaliya muke da yan daba ga woman leaders muna da su ban da shugaban nin local government kana ganin shi kansa matawalle zai barsa ne ya zama shugaban ƙasa bayan ba biyayya zai masa ba shi talakawa ne a ransa a tsarin ƙasar nan duk me tausayin takala bazai mulki ba wallahi......,





Dariya suka sheƙe da ita Mustapha Umar jiran lokaci yace




"Zan sa sojojin baka su ruɗashi da yan media sai ya gagari bacci sannan za muje gub boka ya hana shi sakat har sai ya janye.....,





Yusuf jirga yace





"A'a ai bama so ya janye kawai ya waɗi zaɓe shikkenan ...,





daga nan taro ya watsai his excellency ya shigo cikin gida da sauri Hajiya adabiya ta ƙaraso tace




"Your welcome his excellency daga gun daga mata hannu yayi yace




"Hajiya adabiya na gaji inna huta kyamin bayani.....,




Kai ta gyaɗa tace





"Ka huta lafiya....,




ta huce ta bar part ɗin nasa....



floor ta ta koma ta zauna najuwa ce zaune tana daddana waya zama tayi a kujerar da take kusa da ita tace




"Najuwa yau shene komawar ki Jerusalem.....?,




Ajiye wayar hannun ta tayi tace



"End of this month..,



Tunani Hajiya adabiya tayi kana tace




"Yauwa sai ki tafi da yasir da basma saboda gab zaɓen mahaifin ku ba zaku zauna anan ba nika daga baya zan biyo ku sai mu huce America ke kuma ki zauna a can....,



Tashi tayi tace



"Okay ta shiga bedroom ɗin'ta key tasa ta kulle akan luxury bed ɗin'ta wayar ta ce tayi ruri da sauri ta daga ganin me kiran tace




"Hello annuwar ka samo number tasa....?,




ɗan jim yayi yace




"Najuwa wallahi ban samu ba duk yadda kike tunanin mutumin nan ya huce haka nayi bincike akan sa amma abin da nasamo bazai miki dad'i ba shine abokin karawar his excellency sannan kuma yana da mata nadeeya.....,



Bata san lokacin da tayi jifa da pillow ba hakan kenan yana nufin bazata sami burin'ta ba komai saita nutsuwar'ta tayi tace



"Hakan ba damuwata bace wallahi tun da na ɗora ido akansa naji ina ba'in son sa abu ɗaya ne matsala'ta matar'sa.,



Matar'sa ba ita bace matsalal his excellency shine matsal kinsan kuwa ba wanda his excellency ya tsana sama da kowa a duniyar nan face Ansh Imam geza shine mutum na farko da yake kokarin dakyile tauraruwa his excellency shine mutum na farko da yake wayarwa da al'umma kai game da mulkin damakwaraɗiya har suke ƙoƙarin fito na fito da his excellency Najuwa daman zaki hakuri ko da daddy ki yayarda tofa shi bazai yarda ba duba da irin haɗuwar da kukai mutum ne me addini dan boko kinsan wane mahaifinsa kuwa a GEZA babban malamin nan kuma alkali a kotun musulunci IMAM NASIR Muhammad geza kinsan kuwa zuri'ar gidan tarbiyya ruƙo da addini ga son juna akwai yar tsama tsakanin mahaifinki da ya Sheikh dan haka ina me baki shawara tun huri ki janye batun nan a ranki....



# *OUMYASMEEN.........✍️*



*Kar ki bari ayi tafiyar book 2 bake only 🔞 please*




*HAUWA KULU WOMEN LEADER*



🔞



*Gargaɗi banyarda wani ko wata su maida min littafina document ba ko audio kunyi yarda kuka gadama a destiny love Wallahi wannan karon bazan yarda ba*





https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



Book 1





Tashi tsaye tayi ta kalli dressing mirro tace



"Wallahi in har kaga ban aure shi ba to ba na doron ƙasa ......ban taɓa neman abu narasa ba..,



Annuwar yace





"To shikkenan Allah ya bada sa'a,



Amin tace ta kashe wayar kwanciya tayi rub da ciki yayi da wanda yafi kowa sata ya lallabo yayi a wan gaba da ita




********


Da asubar fari ta sheƙa wanka wani material tasa blue da adon fari yayi mutuƙar amsar jikin'ta daurin nan tayi ture kaga tsiya ta rayata mayafi ta nemi guri ta zauna jira take gari yayi haske ta fita gidan su Baraka ...




Kallon tsanaki gwaggo take nata zama tayi ta ajiye kofin kokon da ta shigo da shi ta ci gaba da taunar goron ta yar karamar wayar tace tayi ƙara da sauri ta buɗe jaka ta dauko washe baki tayi ta daga tace




"Baraka gani ai tun safe na shirya ashe tafiyar ma ta asuba ce...,




Ehwllh ki sauri da sauri tatashi tace




"Gwaggo ai min addu'a na tafi Allah isa in shiga harkar nan asa'a...,




amin kululu ki fita tayi kamar daga sama taji ance




"Dan uwar....ki ina zaki,







Bata juyo ba tace




"Gidan tsohuwa me sai da yaɗiya nan zani...,



Tana faɗa haka tasa kai ta fita da sauri ya bi bayan'ta da katawa yayi sakamaƙon ganin ɗan isiya dan daba da baraka baraka CE ta fara hawa gaba sannan sai jidda


cizon yatsa sameer yayi ya juya a guje ɗan isiya ya fisge mashin ɗin





Sun yi tafiya me nesa tukunna suka iso




*GEZA Government House*




Suna zuwa ka buɗe musu gate ɗin farko sauka sukai dan isiya ya juya wara ido jidda tayi sosai tayi tana kallon kwawacaccan gidan me kyau da tsari gaban hani hol suka tsaya cike yake damƙam da mutane maza da mata da sauri ta dubi baraka tace




"Baraka badai mun makara ba...?,



Samin guri tayi ta zauna tace



"Ga shi kuwa kina gani in bada Allah ya hadani da dan isiya da sai an gama zamu zo..,



wata tsohuwa ce ta fito taci man kwallin ga bulal hanci ta ƙwama wani tabkeken glasses a fuskar'ta cikin fara'a tace



"Kawata sannun ki....,



da sauri ta daga tace


"Yauwa aunty Barka da safiya...,



Yauwa baraka yau wallahi akwai tashin hankali a gidan nan Joseph ne ya cinye mana kuɗin da jiya muka fita wallahi yau sai dai a yi waje da ni amma sai na ci ubansa



Ai bake kaɗe ba hajja ta madina billahillazi mu mun fi sheɗan iya iskanci taɓa ta shaƙa ta fesar taci gaba da cewa in banda hulakanci har mu kwana mu tashi ba muga kuɗin mu ba mu mun mai kama da wayan da zai cinyewa kuɗi yau sai naci bura......ubansa yau sai yafi fulawa laushi wankin babban bargo za muyi mai



Sakar baki hauwa tayi tana kallon su inda ranka zaka sha kallo su wayan nan su waye wa kuma zasu jibga Baraka tace



"Ai gwara da ya taɓo ku mu ba ya raina mu ba wallahi ku yi mai rashin arziki shege arnan banza...,




Baraka wace wannan kallon jidda tayi tace


"Hauwa kulu arabebe arnan daji itama harkar nan zata fara....,


Sheƙewa sukai har da tafi suka ce



"Muna yi miki barka da zuwa gidan shege da shegiya dan banza da na kirki duk wanda kika gani buƙatar kansa ce ta kawo shi...,




Zaro ido tayi tace



"Ai kuwa ya sami dai-dai da shi ni warki ce dai-dai ƙugun ko wanne ɗan iska sai na gyarawa ko wanne shege zama...ni hauwa kulu woman leader GEZA ban fito sai da na shirya....,



Hannu suka bata suka tafa luba tace




"Zaki iya ai daga ganin idon ki zaki aikata wannan fagen yafi son mara kunya....,



Dariya tasa tace



"Tun da Allah ya haɗani da ku nasami dai-dai da ajina....,


Hajja ta madina tace



"Bara in gabatar dake gun barɗe ka shuka tsiya ka gama lafiya.....,


Zaro ido tayi tace




"Badai shugaban yan bakan Radio ba....,




Luba taja taba tafesar tace




"Shifa zo muje kafin muci bura...ubansa la'ada waje...,



Bin su tayi suka bar baraka ta shige cikin hol ɗin


Gaban wani kwatatcan lambu suka tsaya waya luba ta fito da ita tayi dan danne danne ta kara a kunne tace



"Shegen gari kana ina ne....?,


Daga can ɓangaran yace



"Ina cikin lambu...,



Tsai wayar tayi tace



"Zo mu shiga to tace ta bisu samun sa sukai a zaune ya ɗora kafa daya kan ɗaya yana busa yahaƙi jan kujera sukai suka zauna nima ganin tsayuwa ba zata kai ni ba na zauna cikin sanyin murya nace


"Ina kwana....,



Cire glasses ɗin'sa yayi yace



"Lafiya qalau luba yar jila ina kika samu wannan....?,



Far tayi da idanuwan'ta tace



"Sabuwar yar gwagwarmayar siyasa muka samu me jini a jika....,




Dariya ya sheƙe da ita yace




"Daman honourable Mustapha Umar jiran lokaci ya sani in samo sojojin baka wayan da zasu yaƙi waccan gurgun magen to zaki iya.....,



Dan jim tayi tace




"Yi min bayani yadda abin yake....,



ajiye tabar hannun'sa yayi yace





"Bani abu bane me huya zaki shiga gidan Radio GEZA zan rubuta miki komai zaki karanta tare ma zamu yau za ayi hirar Insha Allahu muka ga aikin ki yayi kyau tofa zamu yi tafiyar nan dake...,



Jikin'ta a sannayaye tace




"To...,



Tashi sukai suka bar luba yar shila a gun suka ci gaba da busa taba yawa ba gobe



# *oum Yasmeen*



*HAUWA KULU WOMEN LEADER*



*Ban yarda wani ko wata su mai damin da littafina Document ba ko audio wallahi kun yi min yarda kuka ga dama a DESTINY LOVE wannan karon bazan yarda ba kar wanda ya samin shi a website ba tare da sani ba*


*Masu yimim fantan alkairi ina godiya my lovely fan's my real fan's masu yimin aka sin haka ma ina godiya daman shi ɗan adam ba'a iya mai 🤗😏*




https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



Book 1

🔞



Lumahe idanuwan'sa yayi kansa ke masa wani irin ciwo abubuwa sun mai yawa wayar'sa ce tayi ƙara share'ta yayi ganin me kiran yana ƙara nema ya tunzura ciwon kan'sa ya ɗaga cikin muryar shagwaɓa tace



"Honey kazo gida in anjima mu tafi.... wallahi nayi kewar ka..,




Wani takaici ne ya tukare mai huya yace




"Bada sa hannuna ba kika tafi dan haka kar ki ƙara kirana akan wannan maganar wallahi nadeeya in har bazaki sauya ra'ayi ba tofa kina gab da rasani ta har a bada sanin kankine bana son yin mata biyu amma kiyi ƙoƙarin kaini bango me al'umma zasu ɗauke ni nakasa riƙe gidana ina neman ƙarin nauyin al'umma da dama...,




cikin ɗaga murya tace





"Sai me Asharaf kafito fili kace min aure kake nema kadeba kwana kwana wallahi in har ina numfashi asharaf bakai ba wata mace wacce mace zata zauna dakai bayan nima zaman hakuri nake dakai....,




Be jira me zaka ƙara cemai ba ya kashe wayar dole zai tauna aya ɗan tsakuwa taji tsoro amma wazai aura wace zata iya riƙe mai sirrin sa wacce mace ce zata yi dai-dai da ra'ayin'sa turo kofa akai aka shigo da sauri ya dawo hayyacin'sa yace




"Wa'alaikas salam jafar...,


Zama yayi yace





"Abokina lafiya ka lula duniyar tunani ko dai har nauyin ƙasa ya fara hawa kan ka...?,





ɗan murmushi yayi jafar baya rabo da abin dariya yace




"Ina file ɗin....?,



Miƙo mai yayi buɗewa yayi yace





"Wayan nan sunayan mene amfanin su....?,



Shugaban jam'iya ne ya bani yace sunan wayan da zaka bawa kwangilane in Allah ya bamu nasara sun yi hidima da jam'iya....,




Tsaki yayi ya ajiye yace




"Wacce hidima ba cancanta za a duba ba ina cewa Sani me dala shi ne wanda efcc ta kama tana zarginsa da amsar kuɗade batare da yayi aikin da aka sa shi ba tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta NBB ne ya dawo tafiyar nan saboda sun ƙi bashi wasu kuɗaɗe....,



dafa kai jafar yayi yace





"Wannan haka yake wai me isa a yan kwanakin nan bara gurbi suke yawan shigowa jam'iyyar nan anya ba kura bace da fatar akuya.....


Wata kila kasan haka suke in suka ga mulki yana yane neman ƙarewa sai su koma jam'iyya me ci nidai wallahi cancanta zanbi duk wanda na bincika ya taɓa sama da dukiyar al'umma bazan yi tafiyar nan da shi ba saidai suyi abin da za suyi ace duk azzalumai suka taro suke mulki ba me son al'umma ...,




Hakane Allah ya datar da mu yanzu kenan bazaka sa hannu ba ..?



dafa kansa yayi yace



"Jafar kamar bada hausa nayi maka wannan bayanin ba kace mai na ajiye zan duba shi....,



To yace mai ya tashi ya fita ɗaukan mukullin motar'sa yayi tare da brief case ɗinsa ya fito cikin nutsuwa yake takawa wanda be sani ba zato zaiyi ɗan ɗin gisa ƙafar da yake gayo ne duk inda me kyau yake ya kai




cikar haiba da kalama suka bi suka mai da shi wani irin nagartatcan mutum ilimi hutu jin dadi fatar sa yawa kafasa jini ya fito




ba macan da zata gansa ta ɗauke idon'ta akansa shiyasa mata da yawa suke ɗilmiya cikin kogin'son sa kallo ɗaya zakai mai kasan a cikin maza ma sunan sa mazaje





Da sauri John ya karɓe jakar hannunsa buɗe mai kofar mota yayi gurin me zaman banza ya shiga zaka yowa yayi ya shiga ya fara tuƙi a hankali yake tafiya har yabar katafaran asibitin nasa





Kai tsaye hanyar GEZA suka nufa jaridar**CIKI DA GASKIYA DAILY NEWS**



ya ɗauka gabansa ne ya waɗi da sauri ya ɓan ƙaɗa shafin Farko inda ake cewa





Asifiya yau ne Jidda ita da Barde Tsula tsiyar ka ka gama lafiya suka cakcaki ɗan takarar shugaban kasa Inda suke bayyana al'umma cewa Asibitin koyarwa na jami'ar A.I.GEZA Teaching general hospital ya daɗe yana kashe rayuwa kan al'umma sakamakon ma'aikatan sa ba ƙararro bane




Sauri rufewa yayi be karasa karantawa ba wacce wannan jidda woman leader dole ya nemo ko ita wacce ɗaukan waya yayi cikin sauri ya shiga nemo number ɗin hamisu bugu ɗaya ya dauka cikin girmamawa yake gaishe shi


Amsawa yayi yace





"Hamisu ka duba jaridar ***CIKI DA GASKIYA*** abu na biyu ka binciko min wacce wacce sukai hira da Barde a ina take zan dau komai amma banda sharri da taɓa martabar iyayena da addini na




Cikin ladabi yace


"To katsai wayar yayi dai dai isowarsa gaban wani tabkeken gida daga gani kasan me gidan baƙaramin attajiri bane a kofar gidan yayi parking fitowa yayi ya shiga cikin gidan cikin taƙunnan nasa na kasaita yake tafiya har ya isa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login