Showing 6001 words to 9000 words out of 17203 words

Chapter 3 - HAUWA KULU WOMEN LEADER book 1 HAUSA NOVEL

22 Sep 2024

1691

kofar da zata sada shi da floor mahaifinsa cire takalmin sa yayi ya shiga baƙinsa dauke da sallama ya shiga





Samin sa yayi yana kishin giɗe gaban sa kayan marmari ne ga ƙira'ar al'kur'ani ɗaukan remote yayi ya kashe cikin fara'a yace



"Sannun ka da zuwa uban masu gida...,




zama yayi cikin ladabi yace







"Barka da war haka abba da fatan ka tashi lafiya....,




Tashi yayi zaune yace



"Lafiya qalau asharaf ya iyalin naka....?,




Ƙasa yayi da idanuwan'sa dan ƙaramanin aikin mahaifinsa ne ya iya gano wanne hali yake ciki yace



"Alhamdullahi na same ku lafiya..,



Tufa mahaifinsa ya gutsura yace




"Lafiya qalau ɗauko waccan jakar.....,



Tashi yayi ya dauko ta ya ajiye a gaban mahaifin nasa





Abba buɗewa yayi wani daɗaddan photo ya dauko miƙawa asharaf yayi





Amsa yayi ya duba gabansa ne ya waɗi na hannun dama ya tabbata mahaifin'sa ne na hannun hagu kuwa kamar su ɗaya sak yawa an zana shi lokacin yana yaro





Dauko wani kaya yayi na sojoji lumshe idanuwansa yayi tuni kwallar da ta cika kurmin idon'nasa damar zubowa cikin kiɗima Ansh ya ɗauko tissue ya miƙawa mahaifin nasa ƙin amsa yayi yace




"Muhammad gwara ka barni nayi kukan da najima ina so inyi Muhammad wannan na gefen nawa shine mahaifinka bani na haife ka ba..,





Cikin kuɗi ma ya juyo ya kalli mahaifin nasa buɗa baki yayi zai magana abba ya daga mai hannu yace





"Dalilin da kuwa yasa na fada maka nasan zuwa yanzu ka mallaki hankalin kan ka in zaka tuna lokaci kana yaro har zuwa girman ka bana barin karaɓe kowa ciki kuwa harda matana babban tashin hankali da na shiga lokacin da ka kawo min fadeela a matsayin matar da zaka aura har istahara nayi.... naga ba makawa sai anyi wannan auran shiyasa na haƙura ka aure'ta....,





Ɗan nisawa yayi ya cije lips ɗinsa yace



Shekara arba'in da biyar bayan




Muhammad Yusuf Maɓaya shine asalin sunan mahaifinka ɗan asalin karamar hukumar maɓaya ne dake GEZA aiki ya kawo mahaifinsa GEZA BUZUNU ne inda ni kuma mahaifana barebari ne



aminina ne na kut da kut haka muka taso cikin so da kaunar juna haka ma mahaifan mu aminai ne sai an faɗa maka sannan zaka gane cewa mu ba yan uwa bane




Da muka gama secondary ni na zaɓi low inda na tafi jami'ar ibadan dake Nigeria naje na karanci low shi kuma ya zaɓi zama soja sai da aka kai ruwa rana tukunna aka kyale sa tare da binsa da addu'a




Cikin hukuncin Allah muka fito da sakamakon me kyau bayan mun gama ni na sami aiki a koton musilci dake garin geza



Inda shi koma suka tura shi barikin sojoji ta Afrika ta Kudu badan iyayan mu sun so ba haka suka haƙura ya tafi





Ni kuma ba dadi nayi aure ba amma shi Muhammad ba zancan aure a rayuwarsa dan ko waya muke na ce mai yau she xai aure sai yace sai Allah ya nufa har matata saudat ta sami ciki





Muhammad be dawo ba




Ko sau daya be taba bani labarin takurawar da shugaban ninsa suke mai ba akan roƙon gaskiya da amana





Cikin saudatu ya girma wata rana Litinin ta haihu amma dan barai ko da jin haka sai Muhammad ya dawo





Duk wannan kyan nasa yayi baƙi ya rame na yi tambayar duniya ya faɗa min meke damun sai sai yace tension din aiki ne





Kwansa biyu yaje maɓaya tare dani mun zaga ɗanginsa ana haka ya hado da khadiya ba adade na akai auran su ya dauke'ta suka tafi in da yake aiki



Mahaifiyarta bata son auran saboda kankantar shekarun ta saidai Allah ya nufa matar sa ce





Tafiya ta nisa tun muna samunsa a waya har abu ya faskara mahaifin nabeela shima sojane dan haka yau naji ance yazo na wanke kafafuwana





Na tafi unguwar ɗan burmu sallama nayi a kofar gidan su shiru ƙara sallama nayi huru huru na shiga yi domin inne mo yaron da zai shiga yayi min sallama da shi gabana ne ya waɗi lokacin da kunne na suka jiye min bakin labari




Mahaifin nabeela ne ya fito yana waya yace



"Oga ya tura kanal Muhammad Yusuf maɓaya yaƙin tsibirin birni nanɗi amma da biyu ya tura shi in ya je can bazai dawo ba za'a kashe shi shi zai jagoranci yaƙin tsibirin birni nanɗi...,





Bansan me aka ce mai ba naji ya bushe da wata mahaukaciyar dariya da baya da baya ba juya ban zame a ko ina ba sai a tashar mota





Wacce zata kaini Nigeria kwanana hudu ina tafiya tukun na na isa Afrika ta Kudu



Da yake lokacin da akai bikin naje nasan gidan sallama nayi Khadijah ta fito da tsohon ciki ta buɗe min har ƙasa ta gaishe ni na amsa nace









"Lafiya kwana biyu bama samin wayar me gidan ki....,







Hawayan da take riƙe wa suka sami damar kwaranyo wa tace


"Yau wata guda kenan da tafiyar sa birnin nanɗi...nima tun ina bugawa ina samu ba'a dagawa har ta dena shiga...,



Innalilahi wa'inna'laihir raji'un kalmar da nadin ga faɗa kenan


Wata baƙar mota ce ta tsaya a gaban gidan nasa yayin da wasu suka fito dashi ruƙe da cikin sa yayi wani irin fari kal suka ce




"Sun tsince shi a ƙabar tekun sindi sun duba jikin'sa suka ga information ɗin'sa godiya mukai musu suka tafi......inda suka ajiye mana wannan kwatin da take gaban ka



Tashin hankali da dimuwa yasa mahaifiyar ka atake anan ta fara kaƙuda da maƙoncin su da matar sa tare muka kai Muhammad asibiti kallon ana haihuwar ka aka kawo ka gunsa.....








Duk halin irin na ciwon da yake ciki hakan be hanashi daukan ka ba ya samaka albarka...naga baƙar rana guna dawo min da kai yayi ya damkamin amanar ka da ta Khadijah da kuma jakar da ya dawo da ita ya cika da kalmar shahada..




Iya firgici na shiga haka Khadijah itamana tana ji ya mutu ta bishi haka mu ka kawo gawarsa gida su nanne sun shiga tashin hankali domin iya shi suka mallaka binciken likitoci bayan harbinsa da akai har wata guba an bashi a hankali take mamaye jiki sai dai kawai aga mutum ya mutu




haka na dauki ragamar komai ta rayuwar ka domin ban bawa su nanne kai ba ni na ke kula da kai ba ruwan saudatu da kai.....akwai lokacin da har sakin'ta nayi sakamakon ture ka da tayi ka waɗi shine sanadiyyar ɗingishin nan da kake



Kabi a hankali Asharaf bance lallai sai ka faɗa min abin da ke faruwa da iyalanka ba amma jikina ya bani akwai wata munufa da yasa mahaifin nadeeya ya baka yar'sa bayan baya son mahaifin ka da haɗin bakin sa aka kashe da wasu manyan ƙasar nan na fara bincike abun ya faskara direct daga aka aikomin da takarda daga fadar shugaban kasa cewa in janya hannuna daga batun kisan kanal Muhammad maɓaya ba daddara ba na ci gaba sai da sukai min barazana da kai sannan na haƙura



Mutanan gidan nan ma ba abin yarda bane saboda ko su nasan suka sami dama wallahi sai sun aikaka lahira ASHARAF wata irin sarkakiya ke tare da banso Ka shiga siyasar nan ba Asharaf saidai na fahimci burin kane



Iɗagowa yayi idon'sa yayi ja jijiyoyin ƙansa sun fito rada rada da kyar ya iya buɗa baki yace



"Abba jininsa bazai taɓa tsulwan'ta a banza ba insha Allah sai duniya tasan wayan da suka kashe shi ƙasar nan an gina tubalinta a rashin gaskiya duk wanda zai gaskiya ɓatar da shi ake.....,


Fito da wani littafi yayi duk yayi kora yace




"Ungo wannan shine mahimman abu da sa mahaifinka yace abaka wannan akwati in Ka girma kaje kai bincike akai...,


Amsa yayi hannu bibbiyu ya riƙe yace



"Insha Allah komai zai zamo karshe nima akwai wasu ayoyin tambaya da nasawa mahaifin nata da ita kanta saidai duk abin da suke ina lura da su yanzu ainiyin wasan zai fara...,




Kai ya jinjina yace



"Allah yayi maka albarka ka cika ɗa na ƙwarai..,



Amin yace sun ɗan tattauna wasu batutuwa akan takarar sa yayi mai sallama ya fita kai tsaye gurin hajiya sauda ya nufa dan mutuncin abbansa badan halinta ba




Saminta yayi a zaune ta ɗora kafa daya kan ɗaya baƙinsa dauke da sallama ya shiga sauran yaranta suka amsa mai kadaran kada ham suka gaishe shi gaishe'ta yayi cikin mutun tawa




Ɗan yatsuna fuska tayi ta amsa mai

a guje wata sanye da riga da wando ta fito ƙanwar hajiya sauda ce yar autar su cikin so da kauna tace




"Ya ansh barka da warhaka...,




Tashi yayi cikin halin ko in kula yace







"Yauwa ya juya yace na tafi ba wanda ya tamka maganar'sa ya fita shima ko kuwa ko a jikin sa dan adam yasan hali



Komawa gun abba yayi ya dauki akwatin nan





yafita kofar gida yayi tuni ya cika damƙam da mutane da yake duk sanda zai ziyarci mahaifinsa sai sun taro kuɗi ya bawa john yana rarrabawa





Dakyar suka barsa ya huce tafiya me nisa sukai kafin suje inda gidansa yake



Gaban wani tabkeken gida suka tsaya John yayi horn me gadin ya buɗe




Parking space ya shiga inda ya ajiye motar ya fito ya buɗewa uban gidan nasa ya fito cikin izza yake tafiya John biye da shi har izuwa kofar da zata sada shi da shashinsa




Amsar akwatin yayi John ya juya shi kuma ya shiga ciki


*******




Sai yamma liƙis suka dawo gida a kofar gidan su me a napep ya kawo ta sauka tayi ta biyashi kuɗinsa ya ƙara gaba da baraka.....sanadin program ɗin nan da tayi gwamna ya cika mata jaka da kuɗi dan haka yau ji take tana shawagi a sararin samaniya



da yar wakar'ta ta shiga gidan kahu hamisu ta yi kicibus da shi a tsakar gida cikin baƙin ciki ya kalle'ta yace




"Yanzu jidda abin da kikai ya dace to wallahi bazan boye miki ba A.I.GEZA yasa inyi bincike akanki yace zai yarda ba wallahi in yayi miki wane daurin ko su wayan da suka saki basu isa su kunto ki ba....,



Wani takaici ne ya kamata tace





"Kahu wallahi siyasa yanzu na fara faɗuwar gaba a sarar na miji kasani sarai bana jin tsoro wallahi in ya fasa shi ba ɗan halak bane....,




Tau ya dauke'ta da mari da sauri ta kama kuncin'ta tace



"Ni ka mara to wallahi yau kowa na gidan nan bazai kwana cikin kwanciyar hankali ba MUZU BA MUGA NI ( shin KO kinsan me littafin MUZU BA MUGA NI nace kin sani ko kema ambarki a baya....?) tana kaiwa nan ta shiga ɗaki gwaggo ce ta fito cikin kumfar baki tace





"Wallahi hamisu ka fita a idona in rufe kowa na gidan nan ya tsani marainiyar Allah nan..,



Cikin takaici yace





"Gwaggo yarinyar nan siyasa fa tashi ga .....,




Turo daurin ta gaba tayi tace





"To sai mai hamisu karkai ma ka fara yi mata hassada ne dan kaji muryar ta a gidan rediyo tab wallahi ka shiga hankalin ka tun kafin Ubangiji yayi mak kunar baƙin wake dan kaga shi wancan me fubfar kafurawan farko ba shi take ba ta tafi siyasar su tsula tsiya ka gama lafiya yo kululu akwai wayo ba ta tsaya fagen su yan kuci ku bamu ta tafi sama ɗoɗar...,




Wani kululun takaicine ya tukare mai ma ƙogaro yace



"Gwaggo ina jiye miki ranan na dama wallahi domin kar jidda ta ɗebo abin da yafi karfin ku...,







Tub aniyar ka ta bika masaharranci ba ruwan ka da ita

Fita yayi domin bazai iya zaman gidan ba shi yanzu besan me zai fadawa oga ba jidda ta cuce shi wallahi





Cikin gida kuwa tana shiga ta cire kayanta zama tayi daga ita sai daurin kirji tana lissafa kuɗin da ta samu dubu hamsin cas gwaggo ce ta shigo ta washe baki tace


"Kululu duk wannan su suka baki....?,


Ajiye su tayi a gefe tace



"Eh wallahi zan ware kuɗin motar tafiya kamfen sannan in baki ke da malam...,



Buɗa tasaki tace



"Ta gaban mota insha Allahu wata ran sai kinyi Kwamishina....,



Cikin farin ciki tace



"Amin gwaggo...gobe ma da huri xan fita zan raka gwamna kamfen...,


Tashi tayi ta fita gun tattabarun'ta ta shiga buɗe su tayi fur suka fito suka tsagaye'ta gero take watsa musu suna ci suna hawa jikin'ta takan shiga farin ciki inhar tana tare da su ji take bata da wata damuwa.....baba lami ce ta fito tace




"A'a woman leader kin dawo...?,



ɗaga gira tayi tace



"Ga shinan kuwa kin gani..,


Ɗan dam baba lami tayi tace




"Kululu yar gidan gwaggo nace ko zan sami rancan dubu wallahi jarina ne ya karye..,





Wani kallon up and down tayi mata baba hansai ce tafi to hannun ta rike da buta da alama makewayi zata shiga Cikin dan habaici tace



"Allah ka kara bamu da haifar ya'yan kuka...,


Yaron'ta ne ya tsala ihu da yake sabuwar haihuwa tayi da sauri ta ajiye botar cikin sauri ta koma dakin'ta


Kallon baba lami jidda tayi ta saki wani banzan murmushi tace



"To jeki zuwa safiya zan baki rance amma Wallahi duk randa na bushi iska baki biyan ba tofa duk abin da nayi miki ke kika jawa kanki....,


Da sauri tace



"A'a zan ma biya ki nagode..,



Banza tayi mata ta ci gaba da watsa musu hatsi Allah Allah take baba lami tabar gun aikuwa ta gaba yan abun da za ta yi ta bargun da sauri jidda ta watsar da hatsin hannun'ta ta shiga ɗaki


Kullun wani abu ta dawo da shi cikin sanda ta buɗe wannan butar ta hansai ta juyai tsidugu tas a cikin ruwan nan kusan rabin leda fara a inda ta ajiye ta sa shi.....ai daman da tasu da mijinta dazu har shi zai mare'ta ya manta da


Wacce jidda woman leader wanka ta shiga fitowar ta kenan hansai na tsaye tana jiran'ta yi tayi kamar bata ganta ba


Ta bangaje ta ta shiga makewayin jidda bata kulaba ta koma ɗaki daman tayi al'wala jira take a kira sallar magariba tayi


Wani irin wahalallan ihu hansai ta saki.........✍️





*Oum yasmeen*




*HAUWA KULU WOMEN LEADER*


*Banyar da wani ko wata ya mai da min wannan book audio ko document ba bazan fitar da document ba kuma ban bawa wani ko wata document na wannan littafin ba*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

🔞book 1



*Typing..................*


Wani irin wahalallan ihu hansai ta saki da sauri kowa na gidan ya fito ban da jidda da take kwance tana dariyar keta

Fitowa tayi tana dafe bango tana tale kafa dafe kirji gwaggo tayi tace



"Na shiga uku badai yaran da suke haurowa gida suna yiwa matan mutane ba sun kamaki hansai ji yadda kike tale kafa yawa wacce akai wa fyade...,




Cikin yanayin azaba tace



"Gwaggo barkono aka zabamin a ruwan da zan shiga bayi da shi....,



Tunu gwaggo ta harbo jirgin me ya faru amma saboda bata ganin laifin jidda tace



"Ke hansai bana son shashancin banza wa zai zuba miki barkono a ruwa...kidai nemi wani abun badai wannan ba,



Kahu hamisu ne ya shigo yace



"Lafiya nagan ku anan kunyi cirko cirko..,



Tsaki gwaggo tayi tace




"Wannan alimar matar ka ta tara mu inban da iskanci ta zuba barkono a buta tace zuba mata akai wata kila wata shegiyar ce zata ce maganin gyaran gaba ne..... saboda ita tazama me kan dosa ta dauka dan kaji zam-zam ai gashi ita taji a jikin'ta....,



Ƙasa yayi da kansaa yace




"Hansai shige mu shiga....,


Cikin takaici tace




"Wallahi jidda ce tayi min wannan aikin ba ɗazu ka mare ta ba....,



Da sauri jidda ta ɗaga labulan ɗankin'su tace




"Innalillahi wa'ina ilaihir raji'u ni kuma kiji tsoron Allah kuka tasa harda shashsheƙa tace



Yanzu gwaggo kina gani ana cin zarafina dan anga bani da uwa wallahi yau bazan kwana a gidan nan ba gun inna ta gabas zani



Kamo jidda tayi ta rungumi tasa kuka tace




"Wallahi Allah zai saka mana yanzu dan rashin mutunci a gabana kuke cin zarafin yarinyar nan kai sokon banza kana tsaye kana jin baka ɓarar mata da haƙoraba ta rasa na zawarcii...,



Ransa ne yayi matsifar ɓaci yace





"Inna Dan Allah kiyi haƙuri.....,



Kahu musa ne ya shigo yace




"Jidda gani na dawo zo ki bani kaso na duk inda nayi a garin nan cewa ake kinyi kuɗi nima figa min nawa kason....,



Turus yayi ganin abin da yake faruwa yace




"Lami me yake faruwa....?,



Ina zan sani me gida hansai ce da wani abu wai jidda tasa mata barkono shine gwaggo take kuka


Ai kafin ta ƙarasa wani zancan ta suka wasai sakamakon karurnuƙan mage da suka shigo da alama ya dawo ga yawan nasa


Ihu ya saki yace



"Dawa dai malam sai Ni uban mafarautan garin nan sai Ni wan kulu annuba cau cau cau an ja dani an barni..,



Jidda ce ta fito ta saki buɗa tace



"Duk wanda yace zai ja damu tofa karshan sa yazo....mukan hana mutum bacci..cau cau Ni RABEBE ARNAN DAJI...,



Da sauri kahu musa ya fito har yana harɗewa da rigarsa yace





"RABE anya kuwa kana da hankali..? kullum kana girma kana ƙara shiga dawa yau kwanan ka nawa rabon ka da ga gidan nan...wallahi Rabi'u dole in gyara maka zama a gidan nan..,


Muciji ne ya fito ya tsaya ya saita kahu Musa mage yace




"Kahu Allah yayi maka tambaya to kai bashi amsa danni bani da lokacin ka.....,



Zare idanu ya shiga yi yana waige waige yace



"Dan girman Allah jidda mage ku yi min rai....,








Dariya jidda ta sheƙe da ita tace



"Kahu yanzu zan dauke maka shi amma gum ba ruwanka da shiga sha'anin da ba'a saka ba...,


Da sauri ya ɗaga kai yace



"Na yarda kululu yar gidan gwaggo...,


Danna remote control ɗin mucijin yayi na ruwaba ne ai kuwa tuni ya dawo kusa da shi ya hau jikin'sa da sauri kahu musa ya bar gun dariya jidda ta shiga yi tace



"Ya mage ina ka samu wannan mucijin roba me kama da na gaske....,




Dariya ya sheƙe da ita yace





"Kar inji abakin wani kiyi shiru yau mutan gidan nan sun shiga uku a tsakar gida zan ajiye shi duk wanda ya fito yayi farin gani....,




Kai ta gyaɗa mai kasancewar an kira sallar magarib duk abin jidda tana da roƙon ibada da sauri ta shiga ɗaki tace



"Ya mage tafi masallaci an kira sallah...,



Idanuwan'sa ya zaro da yasha kwalli yace


"To tasallah in nayi lokacin da na gadama kar ki amsa..,


Girgiza kai tayi ta shaga ɗaki



*******




Tafiya yake cikin natsuwa sai ka kula zaka san yana motsa baƙin'sa tasbihi yake ga ubangiji madaukakin sarki ɗan taƙi kallan yayi ya zo gida


Da yake tsakaninsu da masallacin ba nisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login