Showing 12001 words to 15000 words out of 30501 words

Chapter 5 - HAUWA KULU 3 BY TAKORI

TAKORI   

29 Jun 2024

4277

san bata so, ko kadan duk son tada aure hankalin ta ba’a kan Sarham yake ba. Har tafi son ace da Jamilu ne.
Wannan kuma shi ake kira ‘power of persuation’. Jamilu ya iya zama ya kalallame Hauwa da alkawarurruka da kalaman soyayya masu nauyi shiyasa kullum hankalin ta da kyakkyawan zatonta na kansa, tsinkayenta na gaya mata da shi ne kawai bazata samu matsalar zaman aure ba saboda tsakani da Allah yake sonta so kuma na soyayya mai zafi, in ka dauke matsalar Babansa.
Yanzu Sarham a wajen su Waheedah yake kashe lokacinsa gaba daya, guiltness ya sakalo wuyansa ya hana shi nisa da Madinah, amma ya rasa ta inda zai fito mata da maganar wai zai kara aure a washegarin gobe, ko yayi kokarin yin jarumta ya fada mata in yaga yadda taketa haba-haba dashi, da kulawa da abincin data san yanaso, duk da take jego a gidansu ma bata fasa yi masa girkinsa shi kadai ba kuma na musamman, duk sai yaji ya kasa furtamata me yake ciki, Annabi SAW yace zuciya na son mai kyautata mata, inda Allah ya taimake shi gobe ne za ta cika arbain da haihuwa, don har sun gama yi mata shirin komawa Jeddah. Ya soma tunanin yabkyaleta ta koma in yaso ya gaya mata ta waya. Kai! Hakan kuma ba dabara bace gara duk halin da zata shiga ta shiga a gabansa
Fargaba mai cakude da shakka-shakka ba wai tsoro ba, irin wadda ko da ace a can baya babu ita a tare da namiji, komai yawan jarumtakar sa, irin wannan shakkar sau tari namiji na gamuwa da ita ne a yayin fadawa uwargida zai kara aure, irin tace ta bi ta addabi Dr. Sarham. Yaji yana matukar shakkar Madinah da gudun bacin ranta.
Madina ta fito daga dakin Haj. Laila (kakarta) ta tadda shi a babban falon gidan. Ta ce, "Dr na, Baban Waheedah yaya dai? Jikin ko garin? Irin wannan daure fuska haka? Ni fa har na sa Yaya Usman ya yi min booking zan koma Jeddah gobe, don na ga kamar kai kam baka da alamar barin garin Kano nan kusa, ka shantake abinka. You are enjoying Kano all the way. Ni kuma kaga inada sabgogina da zan koma inyi. Akwai wani ‘marriage coach program’ da zan gabatar dana koma.
Kodayake ban san tsayin hutun naka ba, amma yaso yayi yawa".
Sarham da yake namijin duniya ne kuma dukinda namiji yake dan rainin hankali ne sai ya ce, "wai ni Madindin, saurin me ki ke da ba za ki bari mu koma tare ba?"
Ta ce, "na gaya maka inada muhimmin program, kuma Daddy zai yi birthday dinsa @70 ina son a yi tare da ni da Waheedah.
Inyaso in ka gama sai ka taho dagabaya, babu komai, I will manage to miss you for a while”.
Duk yadda Sarham ya so ya gaya mata gobe za a daura masa aure da watanta kasawa yayi, musamman data hade bakinsu wuri guda tana manna masa wata soft-kiss mai fidda sauti da kashe jikinsa, sumbar bankwana indeed! Tunda har zuwa lokacin jego take yi, mai nuna yadda zatayi kewarsa har cikin idonta zaka ga hakan. Don haka har suka gama soyayyarsu ya baro gidan, ya shiga mota ya kunna, ya kashe ya sake komawa gidan, amma bai shiga ciki ba, ya sa maigadi ya kira masa ita.
A babban soron gidan Alkalin Alkalai Justice Habibu Sorondinki Madina ta cimma Sarham again, a dan kidime take da kiran da yayi mata din yaki shigowa kamar wani bako. Ta same shi ya harde hannuwa a baya kamar saurayin da ya zo zance wajen sabuwar budurwarsa, amma damuwar da ke kan kyakkyawar fuskarsa wannan karon ta fadar da gaban Madinah.
"Wai ni don Allah Baban Waheedah lafiya ka ke kuwa yau? Tunda ka zo na kasa gane kanka, kai ba damuwa ba kai ba farin ciki ba, mun yi sallama ka tafi, kuma ka sake aikawa a kira ni, kada ka sa in kasa tafiya, wallahi kasa gabana faduwa yake yi, musamman in na kalli yanayin damuwar da ka ke ciki". Ta kama hannunsa ta dora a saman kirjinta, "ji yadda kasa gabana ke faduwa, kirjina ke bugawa".
Sarham ya daga kai idanu sun yi ja, ya dubi Madinah cikin kwantar da ‘eye-lashes’ dinsa, sai ya ji kamar an kara masa sonta, ya hau tambayar kansa shi kuwa me yake nema a mace bayan tarin baiwarwakin da Allah ya yi wa Madinarsa?
Me ya gani a Hauwa-Kulu wanda ya kamo na Madinah? Banda yana so ya tallafi rayuwarta yayi matsalolonta dana iyayenta? Ya kuma kawo maslaha akan soyayyarta datake yiwa Jamilu???
Bari kawai ya daure ya gayawa Madina gaskiya tunda ba zai iya komawa ya ce da Malam Bilyaminu ya fasa auren Hauwa ba, don a zahiri matarsa kadai zuciyarsa ke yi wa so na soyayya. Tsakaninsa da Hauwa har gobe bai gama tantance matsayinta ba. Ya san dai, da so ko babu so ya zama tilas zai auri Hauwa-Kulu, tunda dalilai da hujjoji kwarara duka sun sallada masa hujjar aurenta.
Madina gani ta yi Sarham ya tafi tunani kuma, ya manta ma tana tareda shi, ta kara tsurewa, sai ta matsa ta rungumeshi tsam-tsam da hannu bibbiyu ta ce,
“Baban Waheedah, baka da lafiya ne?"
Sarham ya samu kansa da rike Madina gam-gam cikin jikinsa shima, ya ce, "Madinah lafiyata kalu, I am sorry, aure zan kara".
Madina ta ce, "Auren namu wani abu ya yi da za a sake daura shi?"
Gaba daya ta rude kamar yadda shi ma ya rikice, azancin harshe na shirya zance ko lallashi ya kwace masa, ya ce,
"Madina ki fahimce ni da kunnen basira, wata matar zan kara aure. Gobe insha Allahu daurin auren".
Madinah ta san a lokuta da dama idan ta yi ‘losing control’ na ‘temper’ dinta tana iya aikata komai, ciki harda jiwa kanta ciwo wadanda ta kan buga su a jikin bango, don haka ta janye hannayenta daga cikin jikin Sarham a hankali, ta soma ja da baya tmkar jikin yana shocking dinta. Ganin haka shikuma ya soma takowa yana biyo ta, yana cewa,
“Saurare ni Madinah, ban so zan fada miki ba, amma wallahi auren jihadi zan yi ba auren so ba....".
Madinah ta ce cikin rufe ido da girgiza kai, hadi da toshe kunnuwanta hagu da dama da dan alinta "sannu MUJAHID!".
Daga haka sai kawai ta juya ta runtuma da wani irin gudu zuwa cikin gidan Kakanta.
Sarham ya dade cikin wani hali na rashin sanin abinda ya kamata ya yi, ya bita cikin gidan ne ya ganar da ita babu wata mace mai irin nata matsayin a zuciyar sa? Ya ga ko me zai ce yanzu bazata saurare shi ba, kuma bazata yi masa uzuri da shi ba, idan ma ta fahimta din kenan, kafin ya ga babu sarki sai Allah ya ja motarsa ya wuce gida, don maigadin ya ce masa, Madina ta ce don Allah kada ya sake ya aika shi kiranta. Shi kuma yau ya samu kansa da maida kansa bako, ya kasa shiga gidan su Madinah kai tsaye ba tareda ya aika din ba. Ji yake laifin duniya ya gama yi musu.
Bai so suka yi irin wannan sallamar da Madinah ba, ko da ya koma gida ya gwada kiran wayarta ya fi sau shurin masaki tana kallonta tana ringing ba ta daga ba.
A lokacin tana hada kayanta ne babu ko kyallin hawaye a tare da ita, illa kawai ta saka wa ranta idan har Sarham da gaske yake aure zai kara, to karshen zamanta da shi kenan daga nan gidan kakanninta gidan iyayenta za ta nufa a Birnin Jeddah.
Idan kuma wasa yake yi, to sai ya gwammace bai kara yi mata irin wannan mahaukacin wasan ba wanda zai iya buga mata zuciya farat daya.
Asubahin fari direban Hajiya Lailah ya dauki Madinah da Waheedah da aka nannade cikin fararen kayan sanyi sai filin jirgi, da yake jirgin karfe bakwai na safe za ta bi da ma. Ba wanda ta yi wa zancen da Sarham ya yi mata, suna sauka a Jeddah ta kira Usman wato Yayanta da take bi, kan ya zo ya dauke ta a Matar (airport) din na Jeddah.
***** ****** ****
MR&MRS SHANONO
(KARO NA BIYU)
Karfe goma na safiyar ranar asabar din da Madinah ta tashi zuwa Saudiyyah, iyaye da waliyyai da makwabtan malam Bilyaminu da mai unguwar Kofar Na'isa na lokacin, suka daura auren Hauwa'u Bilyaminu da Dr. Sarham Abbas Shanono, akan sadaki mai albarka wato mafi kankanta, daurin auren bai ja mutane da yawa ba, don ba su sanar ba sai a daren ranar.
A daren ranar, wato jajibiren daurin auren, bayan tafiyar Babansu Sarham. Malam Bilyaminu ya isa gidan makwabcinsa Malam Isah ya gaya masa komai, shi kuma Malam Isa cikin matsanancin farin ciki ya karasa ya fada wa sauran makwabtansu da Mai unguwa. Aka daura auren mai ban mamaki da karfe goma na safiyar ranar. Auren da ya janyo magana sosai a cikin Badalarsu Hauwa bayan daurin auren, kowa so yake ya san waye ya auri Hauwa-Kulu alhalin ta samu laluran da ake kira "mutuwar tsaye". Shi kuma Sarham a lokacin yana gida yana fama da tsokanar Sumayyah data saka shi gaba, ko na minti daya ba ta bar shi ya huta ba da shagube. "Yau dai Allah ya rubuta mai abu ya dauki abunsa kowa ya huta!".
Ta kara da cewa cikin rufe baki da boye dariya “shikenan daga yanzu babu sauran korafi a kan Hauwa-Kulu na zance a soro da saurayinta Jamilu, ni ka me zance da wanan Jamilun banda godiya? Tunda shi yasaka yin hobbasa ka ceci kanka?” Sarham ya yi fuska sosai yace “Sumayyah zan sabar miki, ni sa’an wasan ki ne wai?”
A lokacin ya gama shiryawa cikin wata (grey excellency) shaddah mai karkar kamar ansa mata starch, ya karya ruwan tokar hula zanna a kansa, shiri yayi zai tafi kofar Na'isa din, don an tabbatar masa daga Sorondinki cewa Madina ta tashi tun safe zuwa Jeddah.
Ya ce da Sumayyah “in ta gama yimasa shaguben ta wuce su je su gaida su Inna”. Duk dai don ya hana ta surutun da ta ke faman masa kamar an bude famfo.
Da murna Sumayyah ta je daki ta dauko abayarta ta rufa masa baya suka dauki hanyar Badala.
A hanya Sumayyah ta yi wa Bhaiyanta congratulations, da felicitations ya fi a kirga, amma a aurensa da Madina ai bai manta tsiyatakun da ta yi masa ba, alhalin Madina ba ta yi mata laifin komai ba. Sumayyah kenan.
Nan ya saka wa ransa sai ya tashi tsaye a kan mu'amalar matansa biyu da kannensa biyu, don ba ya son bangaranci irin wanda tun ba a je ko'ina ba Sumayyah ta soma nunawa. Surayyah ma ta soma irin nata na taya kawarta Madina kishi don ya lura ta daina kula shi. Abin mamaki ga idonta ga nasa sai tayi kamar bata gannshi ba. Ya kuma fahimci hakan ne zai kasance ta bangaren Sumayyah ma in bai yi da gaske ba. Wato itama ta taya Hauwa kishi da Madina. Mamakinsa daya ne, yaushe har Sumayyah ta yi wa Hauwa farin sanin da ta ke sonta har haka? Duka-duka ya san sau daya ya taba hada su suka gaisa a gidan su Hauwan.
Sumayyah ta tuno wani abu sai ta hau hadiye dariya. Da gefen ido Sarham ya kalle ta yana ci gaba da tukinsa cikin wata irin nutsuwa da bai taba ji a tare dashi ba.
Yau ji yake ya fi kowa nutsuwa, ya fi kowa kwanciyar hankali da ya auri Hauwa-Kulu, da ba zai ce don soyayyarta ya samu wannan kwanciyar hankalin ba sai don Hauwa ta zame masa wani 'mission' mai muhimmancin da dole ya cika shi a rayuwa in yana son kwanciyar hankalinsa ya dore dari bisa dari.
Sumayyah ta ce, "Bhaiya!"
Sai ya juyo kadan suka hada Ido taga ya kara mata kyau da kwarjini, har da kyallin angonci akan goshinsa da suka hada ido sai ta hango wani boyayyen ‘contentment’ a kwance kan kyakkyawar fuskarsa, ai kuwa Sumayyah ta fashe da dariya ta ce,
"Yanzu Bhaiya, duk inda ka ga kare yana sunsunar takalmi ka yarda dauka zai yi ko?"
Shikam ya gaji da shegantakar Sumayyah Harararta ya yi, ya ci gaba da tukinsa, amma da da ne tabbas da ta sha Mari yatsu goma. Sumayyah bata daddara ba ta sake cewa, "Wato Bhaiya, soyayyarka da Hauwa na lura wata irin special soyayya ce boyayya a zukata, wadda Allah kadai ya san ta yadda ya tsara ta. tunda Hauwa dai bata taba ganinka ba.
Amma ni dama, ko ka yarda ko kada ka yarda, na dade da sanin a haka za ta kare. Bhaiya Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a mai albarka I am so happy Bhaiya na, nafi kowa murna da faruwar al’amarinnan nikam!".
Sarham ya yi mamaki da ya samu bakinsa da amsa addu’ar Sumayyah da "Ameen" duk da ya san shi ba wata special soyayya tsakaninsa da Hauwa, sannan ba dole aka yi masa ya aure ta ba. A wurinsa aurensa da Hauwa kaddara ne, kuma DALILI MAI GIRMA ne ya yi sanadinsa.
Sai shigo da huhun goro da alewa ake yi ana ajiyewa a falon Inna, bayan ‘yan daurin auren sun watse kenan da waliyyan Sarham da suka zo daga Shanono. Malam Isah shi Baban Hauwa ya bai wa waliccin auren Hauwa-Kulu.
Hauwa ta fito wanka a daidai lokacin ta gefen sallarta a dakinta, ta zuba hijabin sallarta ta tada sallar walha kenan ta jiyo muryar Malam Isah na gayawa Inna daurin aure ya kammala, HAUWA-KULU ta zamo matar SARHAMU, Allah ya kade fitina ya bada zaman lafiya.
Kawai sai ta tada kabbarar sallarta cikin gigicewa da tare sautin kuka da tafin hannunta.
Cikin sujjadarta ta farko taji muryar Sarham ya yi sallama a tsakar gidansu, sai ta ji gabanta ya tsinko daga kirjinta ya fadi kasa ras! Ras!! Ras!!! Har sau uku. Daga nan sai muryar data shaida ta kanwarsa Sumayyah ce ita ma ta karade gidan da sallama, da alama tare suke.
Ta ci gaba da sallahrta amma ta kasa karanta komai daidai har ta idar, lokacin Inna ta rako Sumayya dakin nata, ta ce, “Hauwa, kin idar ne? Sumayya ce suka zo tare da likita".
Sumayyah ta shigo ta zauna a kusa da ita, ta mika mata hannu ta rike nata wato (shake hands), sannan Inna ta ce, in sun gama gaisawa Sumayyah ta zo dakinta su yi magana.
Sarham na falo a lokacin da Inna ta ce ya shiga dakin Hauwa su gaisa, Hauwa ta idar da sallah. Cikin jin nauyi Sarham ya ce, “Inna ashe tun jiya baki yi mata bayani ba? Wannan zuwan ba nawa ba ne ai na Sumayyah ne, ni ai Yayanta ne ba zance nazo ba, na kawo Sumy ne ta gaishe ku ne".
Inna ta yi dariya ta ce, "na san da haka mana, nafi kowa sanin kai Yayanta ne. Amma wanda aure ya dan karawa Yayan matsayi yanzu ya daga darajarsa zuwa ta abokin rayuwa. Na kuma gode da zuwan Sumayya. Amma likita a yi haka? Yaushe rabon ku gaisa da mutuniyar taka idan ka zo?
Daure ka je ka lallashe ta don Allah, don ni dai tun jiya da uban ya zaunar da ita ya gaya mata gobe daurin aurenta da kai ta daina kula ni, ta kuma kwana tana kuka.
Hauwa ta ina za ta gane cewa ba yinmu ba ne mu duka, wannan auren yin Allah ne, alkawarinsa ne tun fil azal ba na kowannenmu ba? Na fi kowa son kada a yi mata aure ka sani".
Idanun Inna suka ciko da kwallah, ta yi shiru don har ta fara jin kewar Hauwa a cikin jikinta, tun ma kafin a yi batun kai ta gidan miji.
Sarham ya sunkuyar da kai kasa yana jin wani iri a ransa da ganin hawayen Inna. Ya san irin shakuwar da ke tsakaninta da Hauwa. He can feel for her, na irin kewar Hauwa da za ta yi, amma hakan ne kadai abin da zai yi ya zama maslaha akan rayuwar HAUWA-KULU da ta iyayenta, hakanne kuma kadai abinda zai dorar da dangantakar su, musamman da aka yi sa'a ya lura Sumayyah na son Hauwa, ya tabbatar za ta taya shi kula da ita, kai dai bar Sumayyah da ra'ayin ta na rikau akan abin da ranta yake so da wanda ba ya so.
Ya ce, Insha Allah Inna ki sa a ranki ko kin koma Ghana Hauwa na hannunku ne, bana jin Mamana, bana kuma jinsu Sumayyah, za ta taya mu kula da Maijidda. Adduarki za ta bi Maijidda duk inda ta ke.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login