Showing 6001 words to 9000 words out of 30501 words
yayi hijira ya koma Madinah inda ya samu sababbin masoya, suka karbeshi karbar da ahalinsa basu yi masa ba, sannan ne ya zauna lafiya. Ki duba tarihin Hijirar manzon Alah SAW zuwa Madinah.
Banda wauta irin taki wai har bayan jin abin da Zakari ya aikata wa mahaifinki kina marmarin ci gaba da zaman Kanon inda yake zaune taki kadan zuwa dan agundi, yo ni ai ko don in raba ki da dan Zakari haihata-haihata na tafi Ghana, kurwata kur da iyalin Zakari da shi kansa. Zakari abin neman tsari ne.
Malam Bilyaminu kam ya sha mamakin Jamilu a kan Hauwa, wai yana son auren Hauwa, koda yake tuntuni ya san halin Jamilu na kirki duk cikin ‘ya’yan Zakari shine kadai in ya hadu da shi a hanya yake gaida shi, sai ya rage mamakinsa ya ce,
"ki mata a hankali, lallashinta za kiyi, sabo ne, amma Ghana dole mu tafi ba makawa muddin muka kai kwana uku a raye, komai na rayuwata ya koma can, sannan ba zan kara rayuwa a inda Zakari yake ba, na barshi da Allah, na bar shi da fitowar rana da faduwarta.
Amma tafiyarmu zuwa Kumassi (Ghana) ita ce mafi alkhairi a garemu, ko yaya ka gani Likita Sarhamu?"
Dr. Sarham wanda tunda ya dukar da kai yana sauraron su bai ce komai ba, amma bai taba jin tashin hankali irin wanda yake ji a zuciyarsa yanzu ba, musamman da Hauwa take wani irin kuka kamar na fitar rai tana fadin bazata bar BADALA zuwa GHANA ba, tace gara abarta ita kadai ta zauna zata iya rayuwa a gidan su ko babu dan jagora.
Malam Bilyaminu wanda shi ma kukan Hauwa ya rikita shi, kalamanta kuma sun hautsina shi, amma bukatarta na ya cigaba da zaman Kano ba mai yuwuwa bace, ya ce,
"Haba Hauwa-Kulun-Majadun, ‘ya daya tamkar da dubu!
Shin ke ba kya fatan yin aure ne kamar kowacce mace, sai fatan dauwama a cikin Badala ko a gaban Innarta?
Ai ke yar gidan wasu ce Hauwa'u, don haka barinki Kano zuwa Ghana ba komai bane, don idan ban da lalurar nan da na same ki a ciki, tuni na bada auren ki ga Salisu dan wajen Alhaji Munkaila, to a yanzu na san ba lallai ya yarda da zabin mahaifinsa ba, in ya kasance sun ji kin daina gani, ba kowa zai yarda ya auri marar ido ba sai mai soyayyar gaskiya, don haka na bar wa Allah ya zaba miki abin da ya fi zama alkhairi ga rayuwar ki, amma hakika nafi so kiyi aure".
Inna ta yi sauri tace, "Mafi alkhairi ya fi a ce yaro mai nakasar ido yana tare da uwa da ubansa a gefensa? Suna zama garkuwarsa da karfinsa a lokacin duk da yake bukatar su a tare? Ka taimaki kanka Mallam, ka kuma bai wa kanka zaman lafiya ta hanyar cire wa ranka batun son aurar da ita ga dan uwangidanka da kowa ma.
Yau da a ce Hauwa da idanunta biyu, sai na fi kowa son ta yi aure a wannan matakin na girma data shiga a rayuwarta. Amma da ya kasance haka Allah ya zaba mata rayuwa barin maganar yi mata aure da kowa shi ya fi alkhairi Baban Hauwa".
“Kina wasa ne kema, lalura ce zata hana aure sunnar Annabi SAW?”
Kamar daga sama kawai sai suka ji Sarham ya ce (cikin rawar murya ta tangardar harshe), rudani da rawar murya,
"Har da ni Inna? Ina nufin ko nine na nemi auren nata? Har ni ma idan na bukaci hannun Maijiddah zuwa aure ba za ki bani ba?"
Ya kuma tsareta da ido yaki dauke idanunsa da suka rine da damuwa da tausayin kukan HAUWA daga kan Inna, sosai yake casa zuciyar Inna da kaifin kwayar idanunsa, masu haske da wata nasaba ta musamman da ba duk Maza keda ita cikin idanunsa ba.
Yanayin kallon da yake mata, irin kallon nan ne na hana ta kawo kowanne irin uzuri ko togaciya ko rashin yarda ne, a kan bukatarsa.
Dakin ya bada wani irin shiru. Daga Inna har Hauwa duk sun firgice da jin abinda likita Sarham ke cewa, Inna ta diririce ta rikice hau kame-kame ta rasa inda za ta sa kanta. Hauwa kuwa idanu ta firfitar waje kamar zasu fado kasa a soya su a cikin mai.
Malam Bilyaminu kuwa murmushin manya ya yi, ya ce. "Da shi ke nan ka raba gardama, ka raba rigima tsakanina da Hauwa, da tsakanina da Innarta mai shirin ajiyeta a kwibinta har karshen duniya. ka Kuma yi Tuwona - Maina, wato dai ta kwana gidan sauqi idan yau aka ce LIKITA YAYAN HAUWA ya dauke abarsa, ya kai ta gidansa na aure ya killace ta sun tara zurri’a mai albarka, in yaso, ki yi ta karata da son Kanon naki, tunda kowa ya shaida ke 'yar Badala ce ba ‘yar Inna ba da ba’a dinga jin kanku ba, babu kuma wanda ya kai ki son zaman cikin ta.
In yaso ni da Inna mu koma Ghana ki yi zaman aure kamar kowa.
Yo kai mai abu maganin a kwabe ka, ai ba sai ka tsaya tambayar Innarta ba, sadaki kawai za ka kawo in har da gaske ka ke, kuma iyayenka sun amince ka auri Hauwa da zuciya daya duk da lalurarta, to nikuma in hakan ta faru, tuwon girma miyarsa nama! Na baka auren Hauwa duniya da lahira.
Ka sani ko aurenta na baka ba tare da na karbi komai naka ba bayan sadaki da Ubangiji yace na karba, tofa ban biyaka ko rabin-rabin abin da ka yi min ba na kulawa da rayuwarsu, da abinda kayi mata ita Hauwa din, tsayin lokacin da na dauka bana nan tare dasu baka bar su sun wulakanta ba sun tozarta ba.
Inna duk ta rude, rudewar ta ta kasa boyuwa fadi ta ke, "A’ah Malam, kada ka biyewa da na Sarhamu, kada yi gaggawa, bi maganar nan a hankali don Allah, na tabbata likita Sarhamu zolayarka yake, kukanta ne ya daga masa hankali, amma babu makamanciyar wannan maganar a tsakaninsa da Hauwa. Na rantse da Allah babu soyayya.
Ai ba yau muke tare ba, ko Sarhamu? Ba ka taba ce min kana rikon auren Hauwa ba koda da subutar baki ne.
Idan muka baka ita alhalin bata da ido, hakika mun kware ka. Kada ka bari tausayi ya rinjayi zuciyarka ka aikata abinda zaka zo kana dana-sani.
Hakika ni uwarka ce da ba zan so ka yi auren wahala ba, kuma ba sai ka auri Hauwa bane zan san kana kaunata, ni shaida ce Allah kuma shaida ne".
Ta soma share hawaye tana cewa,
"Malam ba ka san wasa ba ne? Ya daga wasa zaka Maida allura garma? Daga ganin sarkin fawa sai Miya tayi Zaki mallam???"
Rudewarta da rikicewar ta ya kai intaha. Sarham sai ya mike tsaye yana dan murmushi yana shafar kansa, rikicewar Inna ce ta sa shi dariya, ya san dama za'ayi haka, ta sha fada ta maimaita a gabansa bazata taba yiwa Hauwa aure ba, koda kuwa da dan shugan kasa ne, don ma dai shine, wato don shine ya furta ba wani daban ba, tabbas da an ga dan karamin yakin sunkuru! Idonsa a kan Hauwan da ke ta ta kokarin kai kanta daki tana cuno baki tana zumbure-zumbure wai Inna wulakantata, ta kuma yi mata gorin ido tunda ta ce (ba ta da ido aurenta wahala ne). Cewa ta ke cikin turo baki gaba irinna shagwababbu.
"Ni dai Inna a yi min gorin komai zan jure, amma ban da gorin idanu. In ma makantar ce ai shi ya bani lasisinta don haka don ta kare a kansa ba laifi bace.
Allah ma ya sauwake in auri likitanki Inna, wushe nan inji dan fillo, ya yimin tsufa, bayan yanada matarsa har da goyo. Yo Allah na tuba ba gara min Yaya Jamilun ba yaro danye shar kama na?"
Ai ba ta kai ga rufe baki ba Inna ta mike ta sauke hannunta a bakinta, jikake bumm! Da sauri Sarham ya kauda kai, ganin har ta fasa mata baki, ya hau saka takalmin sa absent-mindedly.
Malam ya ce, "Haba Safiyya, in rai ya baci hankali ke nemo shi, ki rasa abin duka da fiddawa jini sai Hauwa abin Allah sarki wadda ko ganinki ba ta yi da idanunta?"
Da kuka da wiwi Hauwa ta ta karasa dakinta tana tafiya tana dafa bango har ta shige daki. Ta rufo kofa ta kifa kai a jikin kofar tana kuka.
Ba kukan dukan da Inna tayi mata a gaban Sarham take yi ba, kukan Malam yace “ita abun Allah sarki ce tunda bata da ido”. Bazata taba karbar kaskanci akan nakasarta ba amma zata karbi kwarin guiwa.
Sarham ya yi musu sallama cikin sanyin jiki zai tafi, bayan ya roki Malam Bilyaminu ya daga komawarsa zuwa Ghana sai sun gana da mahaifinsa tukunna.
Yace zai dawo da daddare ya kai shi gun Abban nasa kamar yadda ya bukata.
Da haka Sarham ya juya ya bar gidansu Hauwa yana jin kansa kamar duk abin da ke faruwa din nan a cikin mafarkiyake gudana. Baban Hauwa ya dawo, har ga shi ya bashi aurenta da kansa. Duk abin da ya tsara wa ransa a kan matakan da zai bi ya auri Hauwa, da yardar Allah za su tafi cikin sauki fiyeda yadda ya zace su tunda mai kankat (Baban Hauwa) yayi amanna nan take, Innar Hauwa dama yake ji kuma ga mai tausa matai ta ya dawo. Sai ya gane har da daukin Ubangiji a cikin al'amarin nasu.
Daga nan gidan su Hauwa, ofishin Abbansa ya wuce cikin makaranta, don ya san a daidai wannan lokacin a can ne kadai zai same shi.
Abba Prof. na shan shayi a kujerar ofishinsa dake cikin tsohuwar jami’ar Bayero, babban dan sa, shalelen Abba (Dr. Sarham) ya yi sallama cikin rashin nutsuwa.
Abba ya bashi izinin shiga idonsa a kansa. Kallo daya ya yi masa ya lura da cewa Sarham duk kwalisar shi wadda bata barinsa ya fito koda falon gidansu ne ba tareda ya dauki wanka na musamman ba ga dukkan alamu yau ko wankan safe bai yi ba ya fito har ofishinsa.
A nitse yake kallonsa har ya zauna a kujerar gabansa, ya ce, "Lelen Abba, what's wrong with you haka? Daga kwanaki bakwai a baya zuwa yau, you are upset? Duk ka canza daga yadda na sanka anya kana auna bp dinka?".
Kai tsaye Sarham ya ce, "BP na lafiya lau Abba. Amma Abba aure nake so ka karba min, nan da kwanaki uku kafin su bar kasar nan.
Abba alfarma nake so ka yi min, irin wadda ba ka taba yi min ba!
Abba ban taba rokon ka wani abu ka hanani ba, amma na san wannan zaka iya hana ni, nikuma bazan iya fasawa ba, sabida dalilai na masu yawa ne Abba. shiyasa ka ganni a haka, ba kuma zan kara nutsuwa ba sai ka yi min auren, Abba na zo neman amincewar ka da taimakon ka da albarkar ka don Allah Abba na, ni na san a komai kana fahimtata Abba”.
"Aure Sarham? Duka-duka yaushe ka yi auren fari?” Abba Prof. ya tambaya cikin tsoro da mamaki. “Wannan karon kuma ina ka debo auren? Namamajo sarkin mata, yau shekarata talatin da biyar da mahaifiyarka ita kadai. Kaji na taba sha’awar karawa?
Ba zan taba hana ka yin aure ba, don ba'a hana namiji aure, don in an hana shi aure baza’a hana shi zin aba, ban san yanayin halittarka ba, amma ka sani ka dauko hanyar saya wa kanka rashin kwanciyar hankali muddin ka hada wa kanka mata biyu da kuruciyar ka to 35 baka kai ba, alhalin kana zamanka lafiya da matarka har ga albarkar haihuwa Allah ya fara ba ku.
To karin auren na mene ne kuma? Ni dai nasan ba sha'awa bace, don nasan kaina kuma nasan ni ka gada, ba kuma rashin gamsuwa da iyalinka bane ya saka wannan rigimar".
Sarham ya yi maza ya ce da Abbansa, "Auren da zan yi yanzu na kwakkwaran dalili ne, wanda idan ka ji shi kuma kanada zuciya a kirjinka Abba zaka mara min baya, bana son zuciya ba ne, bana soyayya bane. Sannan ba sha’awace ta saka ni yin sa ba Abba.
Auren jihadi zan yi Abba wanda dalilai masu yawa suka yi sanadinsa".
Duk ya saka Abba cikin rudu, ganin haka ya gyara zama ya shiga kwancewa Abbansa labarinsa da HAUWA, wato tun daga ranar da ya yi wa Hauwa aikin ido, abubuwan da suka faru bayannan, har zuwa dawowar Malam Bilyaminu jiya.
Matakin da Inna ta dauka a kan Hauwa, da yadda ya ce shi a ba shi aurenta zai iya zama da ita da lalurar tata. Kai hatta rayuwar dasu Hauwa sukayi a baya ta sayarda abinci a Tasha Bai boyewa Abbansa komai ba.
Abba Prof, sai ya dan zakuda kadan a cikin kujerarsa, sau tari kana haifar Da har ya girma ya fika halin kwarai, in baka yi wasa bama sai ya riga ka shiga aljannah.
Yana alfahari da Sarham akan halin kwarai da nagartarsa wajen darajja al'ummar Annabi, amma rayuwar Tashar nan da su Hauwa sukayi in ya tuna sai yaji ransa baya so, ace dansa ya auri ‘yar mai abinci a tasha, sai hya kada baki ya ce,
"Lelen Abba na dade ina jiran ranar da za ka zo min da wannan bayanin akan Hauwa dinnan ai, na kuma san dama da wuya in ba karshen alewa kasa ba.
Ni ban yarda wai ba son Hauwan nan ka ke yi ba, ka cire maganar wani JIHADI da ka ke fakewa da shi, don jihadi kala-kala ne in shine akwai wanda yafi wannan lada ma, amma ka sani ni ba yaro ba ne kamar ka. Da zan tsaya yaudarar kaina da kaina.
Ka saka sa a ranka kawai tuntuni, ko recently, ka fara son yarinyar nan ka fara developing interest a kan ta yanzu, ko ba yanzu ba.
Well, ba ni da hujjar hana ka, amma ka shirya daukar dala babu gammo daga matarka, wai makauniya da auren nesa.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na yarda wadannan mutanen suna cikin kaddararka, don haka ba ni da ja cikin abin da Allah ya hukunta. Kawai dai bana so ka gurbata zaman lafiyan gidanka da auren rainon tasha. Ka san rayuwar sayarda abinci a Tashar mota kuwa? Da kallon da akewa mai yin ta? Hummm.
Amma tunda ka ga za ka iya ka kuma yarda da tarbiyyarta ni shawara ce kawai tsakaninmu.
Zan tura insha Allahu a karba maka auren kafin iyayen nata su koma Ghanan.
Ko babu komai ni ma ban san yaya karshen rayuwar nawa 'ya'ya matan zai kasance watarana ba, ba wanda aka gama yiwa halitta sai ranar da ya koma ga mahaliccinsa".
Wani irin relief ya sauka a zuciyar Dr. Sarham. Tunda har ya samu hadin kan Abba ya san na Mama Maishari’ah ma ba zai zamo mai wahala ba. Mai wahalar da ma Innar Hauwa ce, ita kuma ya gane ba ra'ayinta daya da maigidanta akan Hauwa ba don haka nata ra’ayin ba zai yi tasiri ba, yana da tabbacin malam Bilyaminu din zai iya janyo masa ra'ayinta. Kenan matsalar in ma zai sameta to zata fi karfi daga matarsa uwar 'yar sa Dr. Madinah ne. Madinah zata fahimci komai amma banda lamarin kishiya ya sani. Inda shine babban weakness dinta.
Kamar Sarham ya sani kuwa, don kuwa Malam Bilyaminu yau wuni ya yi yana ganar da Inna, yana fadakar da ita don Hauwa ta rasa ido ba yana nufin bata da feeling ba, don Hauwa bata da ido baya nufin bazata so daukar yaran data haifa ba, ya kuma ce Allah ya halatta mata yin aure wanda sunnar kowanne musulmi ne don kare kansa daga dattin zina.
Bata da hujja har a wurin Allah na cewa bazatayi aure ba, tunda yarinyar nan duk da lalurar ba ta rasa ma su son aurenta jajirtattun mazaje irin haka ba.
Yace idan ma ta hana Sarham to shi zai baiwa Salisu.
Bata yadda zaayi ya aje Hauwa a gabansa ba aure in ta kai shekaru 20 wai don kawai bata gani. In ita bata gani su sun ganta sun ce tayi musu. Duk yadda Inna ta so ta ganar da shi abin da ta ke hangowa wato wulakanci da tozarci take gujewa Hauwa Malam Bilyaminu ya ko ki sauraronta, cewa yake.
“Ba ki isa ki katange ta daga duk wata rubutacciyar kaddararta ba. Mai lafiya ma yana shan wahala a gidan aure yana fuskantar kalubale kala-kala ba sai mai nakasa kadai ba.
Aure ibadah ne dama ai, ba gidan jin dadi da kashe ahu bane.
Ni dai fatana da addu’ata Allah ya ba Hauwa dacewa a cikinsa, dama kowacce irin rayuwar aure ta samu kanta. Na yi amanna ibadah ce. Zan roki Allah