Showing 30001 words to 30501 words out of 30501 words

Chapter 11 - HAUWA KULU 3 BY TAKORI

TAKORI   

29 Jun 2024

4271

gaira babu dalili.
To hakan ce tsakanin Mama da Madina. Koda bata taba nuna mata Hakan ba. Balle dama Madina wadda tun asali tana da fenti a idon Mama na wulakancin da mahaifinta ya yi musu duk da cewa (eventually) ya yi (repenting), ita kam har gobe in ta tuna sai da ya fara bada ta ga maikudi irin su, ya rasa shi, sannan ya nemo Sarham ya manna masa abin yana ragewa Madina tagomashi a idanunta.
Musamman data san cewa auren da Madina tayi bai rage komai daga soyayyar da Sarham ke mata ba.
Maganar auren Sarham da Hauwa kuwa, Mama ta dade da sakawa a ranta, watarana zai faru. Duk da Sarham ya yi ittifakin ba son Hauwa yake ba a gabanta, amma ita ta dade da sanin akwai babbar kaddara a tsakaninsu. Tana biye da al’amarinsu tun daga ranar da ya yi wa Hauwa aikin ido, har zuwa yau.
Mama ta yarda ta zama uwar Hauwa, tunda har Sarham ya rabo ta da uwa da ubanta, alhalin babu idanu a tare da ita. Tana lura da cewa, tun tafiyarsa bai kara kiran Hauwa a waya ba, sai dai ita in ya kira ta ya ce a gaida masa Maijidda.
Wannan abu yana yi mata ba dadi, ita kuma ba ta taba ce masa don me ba ya kiran Hauwa ‘direct’ tunda yana da lambarta ba? Ko musuluci bai yarda da wannan ba, kuma hakan tauye ‘yanci ne. Ta kwana da sanin Sarham ba zai iya kiran wata mace alhalin yana tare da Madinah ba.
Abin da ba za ta taba kira tsoro ba, don a policy din Sarham ba shi da tsoro ba shi da shakka tun yana dan karamin sa, don haka ba ta san dalilinsa na kin kiran Hauwa ba, bata masa fatan soyayyar da yake yi wa Madina ta kai ga matakin tsoro, tunda ai yana fita, zai iya kiranta in ya fita in ma idon matarsa yake gudu, bata fatan soyayyarsa da Madinah ta yi yawan da za ta saka shi zabar tashi ranar lahira da shanyayyen barin jiki na tauyewa Hauwa hakki.
A karshe ta gode wa Abba Prof. da bai bari Sarham ya tafi da Hauwa Jiddah ba, hakika da ta ga rainin wayo, da rashin adalci, amma ai ba za'a dauwama a haka ba tunda Hauwa-Kulu, ko da ta ke makauniya, aurenta ake kamar yadda ake auren kowa.
Lokaci Mama ta bashi don ganin kamun ludayinsa a kan auren Hauwa, don ba zai yiwu ya auri ‘yar mutane a gaban shaidu ya bata sadaki sanan ya maida ita kanwarsa ta jini Sumayyah ba.
(Da a ce Mama ta san halin da Sarham ke ciki tun bayan komawarsa Jiddah hakika da ta tausaya wa masa, data ji tausayin tilon dan nata namiji daya tamkar da maza dubu, wato (Likita SARHAM)!!!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login