Showing 1 words to 3000 words out of 22968 words
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/I8iDBWAiJUS6qX9VZqRrlQ
# SQUAD 2024
A WANI COMPANY
BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
Page 2,
Washegari tun wuri ya tashi shiryawa yayi cikin cuz Black masu matuƙar kyau da shaƙi, hannunsa riƙe da yar ƙaramar back ya fito yana tafiya cikin isa da ƙasaita ya nayin yadda yake tafiya sai ka ɗauka ta zame masa dole ne. security ne suka rufa masa baya motoci uku suka yi combai jeri suke tafiya har suka isa cikin katafaren Company mai matiƙar kyau da girma suna isa ya ɓale murfin motar ya fito left ya hau zuwa bene na biyar in da office ɗinsa yake a hankali ya murda handle ya shiga, wow shikansa office ɗin abun kallone Office ne mai matiƙar kyau zama yayi ya na cire riga dake saman kayan
Zaune ya ke cikin Office talphone pole dage gefansa ya janyo wasu Numbobi ya danna da basu shige biyar ba "turomin Suhail" ya faɗa ya na aje wayar ɗago kansa yayi Masha Allah babban mutum ne wanda a ƙalla zai kai shekaru (60) haka farine tass ya ɗaure gashinsa da wani ɗan ƙaramin ribom. Nocking aka yi duban ƙofar yayi, da sauri kuma ya miƙe yana rungumar wanda ya shigo cikin office ɗin da kansa ya zaunar da shi shima ya samu waje ya zauna kallon Suhail yayi wande idansa ke lumshe wannan ɗabi'a ce ta Suhail koda yaushe zaka ga idanunsa a lumshe kamar wanda kejin bacci Suhail a salin kyakyawane kuma ɗan gayu irin dai mutanan nane da ake wa laƙabi da classic aje'butter ya na da pink leps sai ƙwayar idanunsa da ta kasance brown, gashinsa ya sauka har baya.
Miƙa masa takarda dake hannusa yayi duk da yasan haka bamai yuwa bane dan yana da tabbacin tun da suhail yace ba inda zasa to bafa zaije ɗin ba murmushi yayi yana karɓar takarda sai da yagama karantawa tass kafin ya ɗaga kai yana kallon datinjon wanda ya kasance mahaifi agaresa "yanzu dad da gaske sai na tafi wance garin? da ku ka turani kadai san babu wanda nasani acen kuma ban taɓa zuwa ba why dad mai yasa?" shiru mahaifinasa yayi yana kallonsa dan ya rasa me zaiyi tasowa yayi daga inda ya ke ya zo dab da ɗan nasa yana dafa kafaɗarsa "kayi haƙuri son wannan tafiyar dole ce kai ya kamata kaje ka cigaba da kulamana da wancen Company dake nigeria banaso abun da yafaru abaya ya sake faruwa" "shikenan dad naji na kuma amince zanje mudum hakan zai faranta maka rai" wani irin yalwa tacen murmushi yayi yana sake rungume sa "Thank y my son Thank you" "Never mind dad" ya faɗa yana fita daga Office ɗin shifa harga Allah baya son zuwa ko ina ya amsa ne kawai dan farin cikin mahaifinsa wanda ya kasance gatansa.
"Ayrah" "Ayrah" shine abun da Mama ke faɗa tana tsaye a jikin ƙofar ɗakin fitowa tayi tana turo baki ita ala dole an takuramata sanye take cikin atamfa maroon mai adon ganye green "ni zan fita ba daɗewa zanba kinji" "Tom Mama Allah ya tsaremin ke" tafaɗa tana shiga ɗakin murmushi Mama tayi tana fita abunta sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta isa gidan alh hadi wanda ke nesa da anguwar su tana shiga ta isa part ɗin hajiyar, da karamawa ta tarbeta suka gaisa dan hajiya sarai matace mai matiƙar kirki da karamci abunta ko kaɗan bai rufemata idoba ta na matuƙar tausayin su Ayrah don yawanci ma anan suke samun abinci da zasuci.
"Dama Maman Ayrah abunda yasa nace a kiraki wani alkhairi naji shine nace zan faɗamiki ko Allah zai sa a dace" murmushi Mama tayi tana duban hajiya sarai "Wollah kinga ɗazu ne alh ke faɗamin wai Company da suke aiki ana bukatar ma'aikata nayi matukar jin daɗin haka na ce masa kuma in Allah ya yarda zan kiraki na faɗamiki idan mun gama magana sai a samawa Ayarh ko ya kika gani?" farin ciki mara misaltuwa ne ya rufe Mama tama rasa mai zata ce murmushi kawai take tabbas wannan abun farin cikine agaresu "Nagode sosai tabbas keɗin ta dabance kuma ke mai son muce nagode sosai" Mama ta faɗa tana hawaye "haba Aminatu menene abun kuka anan shin dan nayiwa Ayrah abu shine sai kin tamin godiya karki manta Ayrah fa tamkar ya take a wajena " "Hakane hajiya tabbas Ayrah yar'kice"
A hankali ya ke ɗagawa mutane da suka rakosa airport ɗin hannu har ya yi gaba ya dawo da gudu yana rungume mahaifin nasa tabbas ya san zaiyi kewa zai yi kewar Daddyn'sa "I really miss you dad" "Miss you too son ka kula da kanka kaji" ya faɗa shima yana share hawayen dake zubo masa
Austiralia to Nigeria sai dai muce Allah ya sauke ka lafiya Suhail...
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/I8iDBWAiJUS6qX9VZqRrlQ
# SQUAD 2024
A WANI COMPANY
BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT
MARUBUCIYAR
A'ISHA LABIBA.
AND NOW
A WANI COMPANY.
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
*"Wannan labarin mallakin mai shine kawai ban yarda wani ko wata ya sauya min labari ta kowace sigaba idan kuma hakan ta faru bazan kyale ba"*
*BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
*Duk kan yabo da godiya sun ta* *bata ga Allah Subhanahu wata'ala* *mamalakin sammai da ƙasai*
*Allah kai daɗin tsira a bisa shugaban mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama tsira da aminci su tabata a garesa da Ahalinsa da sahabbansa dama wainda suka bisa a tafarki mai kyau daga yanzu har izuwa ranar alƙiyama
Ep one.
Yau ta kama Ranar lahadi a yau kuma duk kanin wasu ma'aikata ke hutawa a gidajensu
Hadarine Sosai ya haɗo
Garin yayi baƙi wata irin iskace ke kaɗawa mai haɗe da ledoji da ƙura mai baɗe idanun mutane. Gajimare ta yi wani irin baƙi tsawa ake mai haɗe da walƙiya yanayin yadda garin yayi duhu na iya tabbatar maka dacewa ruwa na iya sauka a kowane irin lokaci.
tsugune ta ke a jikin bishiya ta kifa kanta a kan gwiwarta duk da wannan hadarin da ya haɗo hakan bai sa taji tsoro ba
wani bawan Allah ne yayo gurin, da sauri ya karasa ya na tambayarta lafiya?
Ɗago kai ta yi ta kallesa da rinanin idanunta wanda suka yi wani mugun ja daga gani kasan ba ƙaramin kuka ta yi ba
Woww Masha Allah tsarki ya tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da yayi Wannan halita farace tass gashinta ya kwanta har gadan bayanta gawani saje da ya kwanta a gefe-gefe n fuskarta tana da ɗan ƙaramin baki sai hancinta dogo mai tsini masha Allah yarinya ta haɗu matuƙa ta na da tsayi sosai ga wani uban Sharpe da ya fita a jikinta. Tashi ta yi bata ce masa komai ba ta fara tafiya jijiga kansa kawai yayi yai gaba abinsa ya na tinanin ko me yasa yarinya kamar wannan tafito tsakiyar layi tana kuka duk da wannan uban hadarin da ya haɗo wanda a koda yaushe ruwa zai iya zuba..
Tafiya take a hankali kasan cewar ita ba ma'abociyar sauri bace wata tsawa da akayi yasa tai saurin rintse idanunta tana toshe kunnanta sunan Allah ta ke ambata cikin yar ƙaramar Muryarta wadda idan ba kana kusa ba bazaka taɓa jin abun da ta ke faɗa ba,ta kai kusan 5 minute a haka kafin a hankali ta buɗe idanun na ta kamar mai tsoron wani abu
Ruwane ya fara zuba kamar da bakin ƙwarya yayin da ruwan ke zuba tare da wata tsawa da ke tashi cigaba da tafiya ta yi a hankali duk da ta'taka abu a ƙafarta hakan baisa ta tsaya ba harta ƙarasa cikin ɗan ƙaramin gidan nasu dake anguwar lokogoma.
Da sauri ta ƙarasa cikin ɗakin tana haki faɗawa kan wata yar taɓarma tayi dake shimfiɗe a tsakar ɗakin a hankali kuma jikinta ya fara wani irin rawa tana fitar da wani irin wahalala numfashi
Gaba ɗaya ta fita hayyacinta babu abin da take ambata sai Mamah Mamah washh Allah na mutuwa zanyi shine kaɗai abun dake fita daga bakinta
Fitowarta kenan daga cikin bayin buɗe ɗan yalolon mayafin dake ƙofar tayi gabanta ne yayi wani mugun faɗuwa dan-danan zufa ta shiga keto'mata duk da ruwan saman da ake ƙarasa shiga cikin ɗakin tayi da sauri jawota tayi jikinta ta rungume wasu zafafa hawaye ne ke fita daga fusakarta da sauri kuma kamar wadda aka tsikara ta tashi ta nufi cikin ɗakin wata yar ƙaramar leda ta ɗako ta nufi yar randar dake ɗakin ta ɗibo ruwa tsayawa tayi tana nazari shin taya zata bata magani bayan tin safe ruwa ne kaɗai a cikinsu? hawayene ya ƙara gangaro mata. daga hanayanta sama tayi gaba ɗaya ta kasa furta komai sai hawaye dake ambaliya akan fuskart
Ƙarasowa wajan tayi a hankali ta ɗagota tana bata maganin, Kwantar da ita tayi a saman cinyarta ta na shafa sumar kanta a haka har bacci ya ɗauke su
Washegari.
A hankali take buɗe idanunta wanda suka mata wani irin nauyi kwance ta ganta kan cinyar Mamah da ke zaune ta jingina da bango kenan a haka Mamanta ta kwana tafaɗa tana jin wani irin tausayi mahaifiyartata da sauri ta ƙarasa jikinta ta rungume ta murmushi Maama tayi dama ta daɗe da tashi batason ta yi motsine ta tada yar'tata "yanzu Mama a haka kika kwana? meyasa baki tasheni ba?" ta faɗa idanunta na kawo ruwa "da ban tasheki ba ai gashi yanzu kin tashiko Maza tashi kije ki ɗauro alwala muyi sallah" tashi tayi a hankali dan har yanzu jikinta na mata wani irin ciwo
Austaraliya
Afusace ya ke maganar wanda kana gani kasan ransa ya ɓaci sosai da sauri kuma kamar wanda aka tsikara ya miƙe yana gyara zaman cuz din dake jikinsa fita yayi cikin sauri security dake wajan suka rufa masa baya daga musu hannu yayi dan baya buƙatar kowa yanzu a kusa da shi wani haɗaɗan ɗaki ya shiga mai tsananin kyau cire rigar dake jikinsa yayi ya kwanta a kan katafaran royal bed ɗin dake shimfiɗe a ɗakin gaba ɗaya kansa ya ɗau zafi ya ma rasa me ya kamata yayi shin idan haka ta kasance menene makomarsa kenan? anya zai yarda ya tafi wani guri No ya faɗa yana girgiza kansa gaba ɗaya ɗimuwa da tashin hankali sun wanzu akan fuskarsa
Da sauri ya tashi yana nufar badroom, ya na shiga ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi dan-danan kuma wata nutsuwa tafara saukar masa, lumshe idanunsa yayi a hankali ya na sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ
# SQUAD 2024
A WANI COMPANY
BY
HAUWAU OMAR
...CUTIE MEEYRAT
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
fallow my account Arewabooks
Arewabooks@hauwauomar05
Page 4,
"Ayrah" "Ayrah wai me kike har yanzu baki fito ba kin san dai ba tsayawa jiranki za'a yi ba ko" da sauri ta fito daga ɗakin tana gyara zaman zumbulele hijjab ɗin ta da ya sauka har ƙasa tayi matiƙar kyau. "Mazaki wuce kije gidan alh hadi yana cen yana jiranki tun ɗazu" da sauri ta kama hanya ta tafi har tayi gaba ta dawa tana kiss ɗin Mamanta akumatu murmushi Mama tayi tana ɗaga mata hannu "Allah ya tsaremin ke dear" "ameen Mamana"
Tafiya take cikin sauri duk da ba wani sauri ta'iya ba tayi tafiya sosai kafin ta karasa gidan tana shiga taga habib da'alama shima fita zai yi da sauri ya karaso wajanta yana murmushi "a yau Ayrah ce a gidan na mu?" "eh wllh ya habib kwana biyu" "kin guje muba" ya faɗa yana dariya murmushi tayi tana sun kuyar da kanta ƙasa "ki maza ki shiga ciki dad yanan yana jiranki tin ɗazu" da sauri ta nufi cikin falon tana shiga tagasu zaune kan kujerin falon tsugunawa tayi har ƙasa tana gaidasu amasawa suka yi da fara'a "sai mu wuce ko kar muyi late dan yanzu Mdee da aka sauya baya da sauƙi kwata-kwata"
Kama hanya sukayi zuwa wajan parking space shiga cikin motar yayi hajiya da kanta ta buɗewa Ayarh motar ta shiga..
Suna isa ta tsaya tana karanta sunan Company
* JULIUE BERGER NIGERIA PLC*
Company Juliue Berger Nigeria Plc yana hedikwata a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Company ya kasan ce wani kamfanin gine-gine da ke aiki a fannoni daban-daban na gine-gine, musamman a fannin gine-ginen tituna,
Akwai kamfanoni da dama a Najeriya da ke da alaka da kamfanoni a kasashen waje, ciki har da kamfanin Juliue Berger Nigeria Plc. Kamfanin ya kasance yana aiki tare da kamfanoni daban-daban a duniya, ciki har da na Austiralia, don gudanar da ayyukan gine-gine da kuma bayar da kayayyaki.
Sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su isa left zaro ido tayi tana kallon alh hadi dan ita tun da uwarta ta haifeta bata taɓa ganin irin wannan abun ba murmushi yayi yana nuna mata gurin "shiga muje kinji daughter babu abunda zai miki" shiga tayi a tsorace jin sunyi sama ya sa tayi saurin rintsa idanunta tana ambatar sunan Allah
Dai-dai left na biyar suka isa fita yayi tana biye da shi nocking yayi a jikin wani office mai kyan gaske, asama an rubuta General Mdee Suhail . P.a din dake zaune a Office din farko ce ta basu umarnin shiga shiga suka yi bakinsu dauke da salama zama alh hadi yayi akan kujera da sauri p.a ta miƙe tana gaidasa amsawa yayi cikin sakin fuska wani banza kallo ta watsawa Ayrah duk da bata santa ba amma gani farko taji ta tsani yarinya da sauri Ayrah ta sun kuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta
Tashi yayi yana ruke da hannuta suka shiga cikin katafaren office ɗin wani mugun sanyine ya daketa da sauri ta kan-ƙame jikinta suna shiga ya nuna mata wajen zama da kecen nesa karasawa yayi wajan Suhail da fara'a ya miƙawa masa hannu shima cikin girmamawa ya basa hannu sukai musabaha dan Suhail duk wulaƙancisa yana matukar girmama manya bayan sun gaisa ne yake faɗa masa ga yarinya da yace zai kawo murmushi yayi yana kallon yarinya wani irin faɗiwar gaba yaji da sauri ya kautar da idanunsa daka kanta .
"Shikenan babu komai ka koma bakin aikinka zan mata inter biyu" godiya ya masa ya nufi ƙofar dan fita tashi tayi da sauri tabi bayansa "kije wacen kujera ki zauna daughter shine zai miki inter biyu" "tom Daddy" ta faɗa tana bin inda ya gaya mata zama tayi akan kujera har lokacin kuma bai dago ya kalleta ba sai da ya gama abun da yake kafin cikin wata sanyayiyar muryasa ya ce ya sunanki
"Fatima Mahir"
ta bashi masa itama a taƙaice
Menene matakin karatunki
Secondary
"It's also an opportunity for job seekers, we are hiring young people here"
Ya faɗa a tsawace sunkuyar da kanta tayi ƙasa dan-danan hawaye ya fara ambaliya a fusakarta
Miƙa hannu yayi ya karɓi takardun hannu nata yana dubawa murmushi yayi abun ba karamin mamaki ya bataba ganin yanzu ya gama mata tsawa amma kuma ya koma murmushi "shikenan zan daukeki aiki amma kin san wane aiki zaki yi?" girgiza kai tayi alamar a'a "coffee" Zaki zama mai kawomin coffee ko da yaushe kuma ban yarda ki kaiwa wani acikin Company coffee ba in bani ba kina jina" ɗaga kai tayi alamar eh ita dai koma me zai bata ya bata in dai zata samu kuɗin da zata na siya musu abinci kuma Mamanta ta daina wankau wata takarda ya ɗauka yayi rubutu "gashinan zuwa gobe sai kizo dan fara aikinki sanan idan kin fita kicewa p.a ɗin dake zaune a Office na farko ta rakaki wajan alh hadi ki kai masa takarda" ɗaga kai tayi tana masa godiya, da sauri kuma ta fita daga Office ɗin
tana fitowa p.a taimata wani irin kallo sun kuyar da kanta ƙasa tayi tana magana "dama cewa yayi kirakani wajan wanda mukazo dashi ɗazu" wani kallon banza tamata kafin tace "ke bana son iskanci da ni na shigo dake da zakice narakaki wawuya kawai" ita dai bata ce mata komai ba kuma bata ɗaga kai ta kalleta ba duk abunda suke yana kallonsu jin telephone ɗin dake kan table din nata yayi kara yasa tayi saurin ɗagawa hlo sir cikin wata irin murya mai amo ya ke bata umarni gaba ɗaya ta rikice dan bata taɓa jinsa da irin murya ba "am sorry sir Insha Allah hakan bazai kara faruwa ba" ajiye wayar yayi yana dora kansa ajikin kujera a hankali kuma ya ke lumshe idanunsa
Fita tayi ita batace mata komai ba da sauri ta bita abaya sai da suka hau left ya kai su bene na 3, in da office din alh hadi yake wanda ya kasance Office ɗin da duk wani taransaction ya ke shiga "Ga office ɗin nan zaki iya shiga" ta faɗa tana juyawa abunta hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tashiga
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/Ilta4xHroxoHpDTtpEW4H9
#SQUAD 2024
A WANI COMPANY
BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS
Fallow my account Arewabooks
Arewabooks@hauwauomar05
Page 3.
A hankali yake sauka daga matata kalar jirgin sanye yake cikin cuz maroon da sauri security suka nufesa gaba ɗaya suka gaidasa ɗaga musu hannu kawai yayi yana miƙa musu back ɗinsa gaba yayi suna binsa a baya har suka ƙarasa wajan motocin