Showing 3001 words to 6000 words out of 19751 words
SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
3⃣
Dakin taron ya cika fal da jama’a, tawagar Aisar da shigowar su ke nan, na su 6angaran na shugaban k’asa su ka zauna. Haka ma hakiman Sa’ayra da Fabarusa, Agadez, Diffa da sauran Hakiman yanki da sassa na jamhuriyar Nijar wajan su na musammam su ka zauna. Haka kuma yankin Sarakuna wanda Sarkin Sa’ayrasa mai gayya mai taro ya hakimce, kusa da shi kuma Sarkin Fabarusa ne zaune cikin aminci. Hakan ba k’aramin farantawa jama’a rai yayi ba, wai ashe dai akwai ranar k’arshen gaba tsakanin Sa’ayrasa da Fabarusa? Shin dama akwai rana irin ta yau da za a ga Sarakunan wanga yanki zaune cikin aminci?
Busa na alkgaita ke tashi daga waje, jama’ar Sa’ayrasa kwan su da kwarkwatar su sun yi dandazo cikin d’akin taro, murna gun su ba a cewa komai domin kuwa a yau yunwa zai kau a k’asar su. Ganin shigowar su Yarima Barde tuni dogarai su ka hau yiwa ango kirari. Shi kuwa Yarima Barde sam ba cikin hayyacin sa ya ke ba, amma in aka d’auke Yarima Jafar da Khalil wanda dama sun san halin da abokin na su ya ke ciki babu wanda zai kalle shi ya ce ya na cikin wani hali, sai dai ma ayi tsammanin tsabar sarauta da miskilanci ne yake d’ibar sa.
Sai kuma Mai martaba Sarki Abdulmalik na Fabarusa, wanda kallo d’aya ya yiwa d’an na sa Yarima Barde bayan ya kai gaisuwar sa ga Mai martaba Sarki Sule na Sa’ayrasa, ya gane halin da ya ke ciki, kasancewar wajan mahaifin na shi ya yo gadan kafiya, cijewa da kuma yin burus kamar be san abun da ke faruwa da shi ba, amma in aka tona cikin zuciyar su, Allah kad’ai ya san tafasar da ta ke. Murmushi Mahaifin na sa yayi, cikin ran sa kuwa yacewa ya yi
"d’an mu Abubakar, alkhairi ne mu ka kulla ma ka ba sharri ba, nan gaba za ka gode ma na kwaran gwaske’’
Ganin Yarima Barde durk'ushe gaban Sarki Sule, haka ma abokan na sa biyu, hannun su na dama dunkule suna mai jinjina ga Sarki Sule, fadawan Sa'ayrasa su ka amsa ma su da
"Jinjine dama lafiya alher, gaishe ka Yarima Badde, an gaishe ku samari"
Sarkin Sa’ayrasa kuwa cikin nuna ya amsa gaisuwar ta su shi ma ya dan daga na shi hannun daman a dunk'ule. Yarima Barde ya shiga ran sa saboda kamala da kwarji na sa, ji ya ke ina ma ina ma, ina sirikin na sa ne na gaske, da ya san haka Sarkin Fabarusa zai aikata, da ya bayar da d’iyar sa ko da kuwa ba a san ran ta ba ne.
Ko da Yarima Barde ya had’a ido da Mahaifin na sa, sai ya yi saurin saukar da na sa idanun. Duk wannan abun da ke faruwa a kan idanun yayan Barde, wato Yarima Sadauki na Fabarusa wanda tun da ya ji abun da mahaifin na su ya aikata bisa ga auran da ya d'aura ya k'ara jin tsanar Barde ya dad'u a kirjin sa. Domin kuwa shi ya kamata Sarki ya d'aurawa aure shi da ya ke babban d'an sa ba k'anin sa, hakan da yayi shi ya nuna k'arara Sarki Abdulraman ya fi kaunar Barde, ya kuma fi fifita shi akan Sadauki. Hakan ne kuma Yarima Sadauki ba zai lamun ta, dan ya san ba k'aramin girma aka zubar ma sa ba a idanun jama'a, dole kuma ya d'au Mataki. Idanun sa kan Barde, cike da tsana ya ke duban sa yayin da aka yiwa su Barde nuni ga na su wajan zaman, wato kusa da Yarima Sadauki da abokan sa su ka zauna.
Tun shigowar su Yarima Barde idanun Yarima Nuhu ke kan sa, ji yake kamar ya je ya sheda ma sa wacece Bintu in ya so kowa ma ya rasa. Haka ma Aisar wanda ya san burin Bintu na ganin Yarima Barde ko da sau d’aya ne a rayuwar ta, wai ta rasa wanda za ta kira mai kyawun duniya sai wanga buzu! Cewar Aisar cikin ran sa yayinda wani bakin kishi ya ta so ya mamaye ran sa, shi dai fatan sa Allah ya sa ya sami damar ganin Bintu tin ka a tafi da ita cikin bayin da za su raka gimbiya Binta Fabarusa, ko dan Yarima Barde dole ya d’auke ta, sam jinin su be had’u ba, dan haka Bintun shi ba za ta yiwa matar Barde bauta ba, ko da kuwa duka dukiyar sa za a buk’ata domin mallaka ma sa Bintu, a shirye ya ke ya rasa komai.
Bayan an sami nutsuwa ne aka bud’e taro da addua’a, sannan aka shiga abun da ya tara su a wajan. Su Yarima Jafar sun so su nemi izinin tafiya, amma hakan be samu ba, sai hakura su ka yi su ka zauna kamar gumaka, ba um ba um um, ga abokan Yarima Sadauki da shi kan shi Yarima Sadauki sai harbin iska su ke. Barde kam duk be san ana yi ba.
Sarkin fabarusa ne ya fara jawabi, ya mai nuna farin cikin sa na kulla aminta da auratayya wacce ta kawo k’arshen gaba tsakanin Masarautar ta su biyu. Bayan haka ya gabatar da takardar shedar sun bayar da bashin da masarautar Sa’ayrasa su ka buk’ata, ya kuma ce tun da an zama d’aya, sa iya biya a tsanake sannu a hankali ba tare da tashin hankali ba.
Nan waje ya kaure da ihu da sowa na jama’a, kowa na nuna jin dad’in sa da kuma alfahari da halin girma irin na sarkin Fabarusa. Dogarawan Fabarusa su ka shiga jera kirari ga Sarkin Su, fad'i su ke
"Lafiya Sarkin yakin Sarkin musulmi
Lafiya maida garin wani kango
Lafiya Barden mahadi
Lafiya Sukukun bakaka
Lafiya Darzaza amalen sarakuna
Lafiya ba hau da wani ba sauke wani
Lafiya hana kangara
Lafiya Sakaka babban bako
Lafiya Bango madafar bayi
Lafiya hadarin kasa maganin mai kabido
Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Lafiya adali, lafiya salamun, salamun salamun"
Jikin sarkin Sa’ayrasa ba k’aramin sanyi yayi ba. Sai da waje ya lafa sannan Sarki Abdulraman ya k’are jawabin na sa da adduar zaman lafiya tsakanin Masarautar da kuma fatan Allah ya bawa shugaban k’asa lafiya.
Sai da sarkin Sa’ayrasa ya sa hannu a takardar ta hanyar amfani da hatimin masarautar ta sa, yayi na sa jawabin na nuna farin ciki da godiya ga masarautar Fabarusa, sannan kuma ya yaba da halin dattako na Sarki Abdulrahman dan har ga Allah ya bashi mamaki matuk’a. ya k’are jawabin na sa tare da fatan alkhairi tsakanin Masarautar biyu. Cikin ran sa ya na alhinin aurar da d’iyar bayin da yayi maimakon d’iyar sa, maimakon ya kawo k’arshen gaba, gudunmawar dad’a k’arfafa gaba yayi muddin sarkin Fabarusa ya fahimci yanda ya haince shi saboda san zuciya.
Daga tawagar shugaban k’asa Kwaminishinan da yayi jawabi ne ya mik’a gaisuwar shugaban k’asa tare da gudunmawar sa na buhuhunan hatsi, shinkafa da dabino ga masarautar ta Sa’ayrsa, wanda sam kyautar ta shi ba burge su ta yi ba, a fad’ar su sai da yunwa ta ci ta cinye su har su ka kai ga neman taimako gun abokan gaba sannan zai wani kawo musu gudunmawar sa na bogi. Kafin kwaminishna ya k’are jawabin sa, wayar Junaidu ta d’au k’ara, ko da ya amsa kiran tuni fuskar sa ta canza, cikin dabara ba tare da ya bari an san halin da ake ciki ba ya ja Aisar su ka yi waje.
A cikin mota ya ke sheda masa ai jikin Shugaban kasa ya dad’a tashi kiran da aka masa kenan, su za su fara yin gaba in ya so sauran tawagar za biyo su a baya gudun kada a d’aga hankalin jama’a. Aisar ya na ji ya na gani haka su ka bar yankin Sa’ayrasa, ya na mai kudirin dawowa da sun sami kan Shugaban k’asa.
Daga d’akin taro kuwa tawagar shugaban k’asa sai neman su Aisar su ka yi su ka rasa, bayan sun kira su ne su ke sheda mu su ai sun yi gaba saboda wani uziri da ya taso, duk da dai ba du sheda mu su ainihin abun da ke faruwa ba, sai da jikin su yayi sanyi matuk’a.
An kamala taro yayinda aka ci aka sha, dan kuwa yau take salla a masarautar Sa’ayrasa. Yarima Jafar ne ya nemi a kai su ga masaukin su da ke su dama nan Sa’ayrasa za su kwana su da tawagar Yarima Sadauki. Amma bakin ciki da kuma Allah Allah da ya ke ya bud'e ido ya gan sa a Fabarusa domin shedawa Mahaifiyar sa cin fuskar da aka masa ya sa Yarima Sadauki fasa kwana, nan ta ke ya juya shi da tawagar sa ba tare da sun jira Sarki ba. Su Yarima Barde kuwa da wasu dogarawa aka had’a su domin kai su masauki[truncated by WhatsApp]
®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
4⃣
Bayan sarkin Fabarusa ya yiwa Sarkin S’ayrasa bankwana, ya d’au hanya tare da tawagar sa. Haka d’aya bayan d’aya taro ya shiga watsewa. Tawagar shugaban k’asa ma tuni su ka d’auki hanya dan tadda su Aisar.
Sarkin Sa’ayrasa na komawa turakar sa Jakadiya ta zo ma sa da buk’atar iyalan sa na ganawa da shi. Ganin magariba ta gabato ya ce su maza su iso gare shi kada ya rasa sallah.
Hajja Kilishi, Inna Salti, Gimbiya Binta da kuma Gimbiya K’amariyya ne zaune gaban sarki, sai kuma Jakadiya da Bintu can gefe nesa da su. Jikin Bintu har karkarwa yake, fatan ta Allah ya sa Sarki ya duba lamarin ta hanya warware auren masifar da aka d’aura mata.
Ya na mai kallan Gimbiya K’amariyya ya ce
‘’ke mu ke sauraro’’
Maimakon ta bashi amsa sai ta kai kallan ta ga Inna Salti, cikin idanun ta ta na mata magiyar ta taimaka ta shedawa sarki. Inna Salti da ta gane halin da K’amariyyar ke ciki ta ce
‘’Allah shi ja da ran Takawa, batun amren da aka d’aura ne, wanda aka d’aura amren da shi, shi ke neman amren Kamariyya’’
‘’dama akwai wanda ya zo ya same mu da batun amren d’iyar mu? Ba mu san da wanga Magana ba’’
Fad’in Sarki Sule. Inna Salti na mai kame kame ta ce
‘’eh dama ba su zo din ba, kasancewar da akwai rashin jituwa tsakanin Masarautar ta Fabarusa da ta mu, hakan shi ya kawo jinkiri Allah ya taimaki Takawa’’
Sarki Sule na mai gyad’a kai cikin nuna 6acin rai ya ce
‘’ki nufin d’iyar mu ta na sauraran wani ba tare da sanin mu ba?’’
‘’ta yi kuskure, ayi mata afuwa’’
Cewar Hajja Kilishi, da ita kad'ai ke iya bawa Sarki hakuri idan ya na cikin yanayin 6acin rai. Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Sarki Sule ya ce
‘’a shedawa wanda d’iyar mu ta ke saurara a bayan idon mu, ya zo nan da kwana biyu dal mu na so mu gana da shi’’
‘’shi ne Yarimar da aka d’aurawa amre da d’iyar bayi Allah ya huci zuciyar babban bijimi’’
Cewar Inna Salti a hankali kamar wacce ke tsoran maganar. Sarki na duban Gimbiya K’amariyya ya dad’a tambayar
‘’ku na nufin Badde na Fabarusa?’’
‘’Badde kuwa Allah ya k’ara ma ka lafiya’’
Ga mamakin su sai gani su ka yi Sarki ya murmusa, kafin ya k’ara da
"shin kin san ita d’iyar bayi a matsayinwa aka d’aura mata Badde?’’
Inna Salti wacce ta fara dana sanin furta maganar ta ce
" a matsayin Binta, Allah ja da ran ka’’
‘’wacece Binta?’’
Tambayar Sarkin Sule da ya sa kowani mahalukin da ke wajan sai da ya sha jinin jikin shi. Da kyar Inna Salti ta yi k’arfin halin furta
‘’d'iyar babban bijimi ce’’
Cike da 6acin rai ya ce
‘’ita Kamariyya da aka amrer da d’iyar bayi a matsayin kaunar ta, kuma ta zo mana da zancen alakarta da wanda aka d'aura din, ya ta ke so mu yi ma ta?’’
Shiru babu wanda ya iya furta komai. Idanun sa bisa silin yace
‘’an bar mu muna jira, ke mu ke sauraro K’amariyya!’’
Murya na rawa ta ce
‘’dama tin da haka abin ya kasance, na ke so a warware matsalar ta hanyar raba amren …….’’
‘’yashasheshshen zance!’’
Sarki Sule ya katse ta ta hanyar daka mata tsawa, tuni jikin K’amariyya da Binta ya hau k’yarma tsabagen firgici, kowa sai da ya sha jinin jikin sa, Jakadiya ta durkusa ta na fad’in
‘’tuba mu ke ran Babban biji ya dad’a, Allah huci zuciyar Babban Biji, lafiya salamun’’
Sarki kuwa be gushe b ya cigaba
‘’mun biye mu ku mun bi san zuciya mun aikata ha’inci, hakik’a Sarki Abdulrahman ya kasanse mai zurfin tunani, mu kuma mun kasance daga cikin ma’abota san zuciya, fatan mu shi ne gyara wanga kuskure da mu ka aikata bisa san zuciya ba tare da 6ata dangantakar arziki da mu ka kulla a wanga rana ta yau ba’’
Kallan sa ya mayar ga Bintu, kana ya ce
‘’ina Kilishi?’’
‘’ran Takawa ya jima, gani kusa gaban ka’’
Cewar Hajja Kilishi.
‘’wagga d’iya ta arziki (yayi nuni ga Bintu) ta ma na abun da jinin mu basu ma na ba, sanadiyar ta yunwa ta kau a masarautar mu, idan ba mu maishe ta d’iya ba, ko shakka babu mu na daga cikin wanada ake kira butulu, wagga d’iya d’iyar mu ce, ni Sule na kira wagga d’iya da d’iya a gare mu, maza a shirya d’iyar arziki, idan an wayi gari ta bi tawagar masarautar Fabarusa dan kuwa jinkirin makwannin biyun ka iya zama barazana a gare mu, da zafi zafi akan bugi karfe…mun gama Magana’’
Ya na dasa aya ya tashi cike da Sarauta yayi shigewar shi daga ciki, ya na jiyo koken Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta amma ya mu su kunne uwar shegu duk da kuwa har ran sa ya ke jin abun.
Ita kan ta Bintu jin gobe gobe za a wuce da ita hankalin ta ya dad'a tashi, ta ma kasa motsawa daga in da ta ke, ta nemi kuka ta rasa.
Gimbiya K’amariyya kuwa wacce har shid’ewa ta ke tsabagen kuka da ya ci karfin ta, tuni ta sake fad’uwa sumammiya a karo na biyu. Nan waje ya sake kaurewa da salatin su Hajja Kilishi da Jakadiya. Dan kok’ari har da Bintu cikin kawo d’oki ta hanyar ciro mayafin ta, ta shiga yiwa Gimbiya K’amariyya fifita, yayin da Inna Salti ke yayyafa mata ruwa.
Wani k’akk’arfar ajiyar zuciya ta saki, alamar ta farfad’o, amma idanun ta lumshe ta kasa bud’e su, hawaye ke gudana bisa kuncin ta. Sai fa a sannan Gimbiya Binta ta ankare da Bintu da ke sunkuye bisa kan Didin na ta, sai fifita ta ke ma ta, ai kuwa ta daddage ji kake tas! Ta sauke yatsun ta biyar bisa kuncin Bintu sai da ta ga wuta a idanun ta. Hannun ta biyu bisa kuncin ta ta ke duban Gimbiya Binta, hakan ne ya dad’a k'ular da ita, ta sake d’aga hannu da niyar kai mata wani marin caraf Inna Salti ta ruke hannun ta, ta na mai fad’in
‘’kul kar ki kuskura ki sake! Kin san kuwa matar Yeriman Fabarusa ki ka d’aga hannu ki mara? Ina hankalin ki ya tafi?’’
Jin haka Gimbiya Binta kamar ta yi hauka, fad’i ta ke
‘’d’iyar bayi na mara, d’iyar bayi wacce na saba takawa ita na mara, babu wata matar Yariman Fabarusa da ta wuce Didi, duk makirci da munahunci wanga wulak’antacciyar Baiwa arudu ya k’are bisa kan ta! Ku ma mu zuba ni da ke ina mai tabbatar mi ki alkiyamar ki ta zo dan kuwa da ki tafi zuwa Fabarusa a gurbin Didi gwamma ki je ki kashe kan ki, dan kuwa masifa da balak’I ya na nan an tanadar mi ki, kuma shi za ki riska, sai dai uwar ki ta haifi wani…..’’
Ta juya fuuuu ta fice gudun kar Bintu ta ga hawayen ta, dan kuwa su ke sauka d’aya bayan d’aya tsabagen bakin ciki da takaici. Hajja Kilishi shi ce ta ja Bintu zuwa turakar ta dan neman yanda za a yi idanun Bintu da ya kumbura da shatin yatsun Gimbiya Binta ya baje, bayan Inna Salti ta bata baki bisa ga lamarin Gimbiya Binta da kuma mata alk’awarin irin haka ba mai sake faruwa ba ne. Nan su ka bar Inna Salti ta na rarrashin Gimbiya K’amariyya, domin kuwa bakin alk’alami ya bushe[truncated by WhatsApp]
®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
5⃣
Da daddare bayan an idda sallar isha’i, Yarima Jafar da Yarima Barde zaune a falo sun yi jigum kamar wanda aka yiwa mutuwa, Khalil na daga d’aka ya na waya da matar sa.
Babban falo ne mai d'auke da k'ayataccun kujeru na sarauta, masauki ne da dama a ka tanada na musammam domin saukar bak'i na alfarma irin su Barde.
Tun da su ka isa ga masauki Barde ke zaune nan falon, sallah kad'ai ke iya sawa ya motsa. Shigar sa na d'aurin aure ke jikin sa, sai dai ya cire babbar riga da rawani, sumar kan sa kwance lub lub bisa kan sa.
'Daya daga cikin dogarawa da ke ciran kofa ne ya shigo ya zube gaban Yerima Barde, kana ya ce
‘’ran Yarima ya dad’e, Gimbiya K’amariyar d’iyar Mai martaba Sarki Sule na S’ayrasa ce me neman iso gare ka’’
Jin sunan K’amariyya tuni kafad’a Barde ta tasa, yayinda jijiyoyin wuyar sa su ka bayyana. Amma ya kasa furta komai. Yarima Jafar ne ya ce
‘’ka iso da ita gare shi’’
Dogari na mai fad’in
‘’an gama ran Yarima Ja’afar ya dad’e’’
Ya tashi da sauri ya fice. Yarima Ja’afar ma tashi yayi, ya d’an dafa kafad’ar Yarima Barde sa’annan ya shige ciki. Shigar sa ke da wuya Dogari ya shigo biye da shi Gimbiya K’amariyya ce. Sai da ya kawo ta gaban Yarima Barde sannan ya juya ya koma waje in da bayan Gimbiya