Showing 6001 words to 9000 words out of 9074 words
manne a idonsa yana duban shi sannan yace.
"Dama kaine mijin nata to masha Allah dama wasu 'yan 'tambayoyine zan maka idan bazaka damu ba kwanaki inaiwa Baba amma taki sanar dani takamaiman abinda yake damun Hauwa'u saboda akwai sila mudai a iya bincikenmu na likitoci mun gano abinda ya haddasa mata ciwon sai dai ƙarin bayanin da muke san ji daga gare ka ina sauraronka".
Cikin kiɗima da fargabar ta ina zai soma yace a ransa ranar wanka ba'a boye cibi yau itace rana ta ƙarshe da zan bayyana maƙasudun ciwon Hauwa'u saboda aga *Laifin Waye* a ciki".
Inji Umar.
*AISHA YAHYA TANKO*
*LAIFIN WAYE*
*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*
*BY AISHA YAHAYA TANKO*
*PAGE 13*
_Ga masu buƙatar talla su tun tu ɓemu ta wannan Number kamar haka 08173846034_
Wani irin kallo yake masa me ɗauke da tuhuma gyaran murya kafin yace wani abu ya ɗan numfasa yace.
"To Malam Umar kai nake sauraro nasan kasan dalilin da yasa nake san ganinka amma ka gaza cewa komai".
Ya ɗago kansa yace.
"Ina maraba da duk tambayoyin da zakai min nima in sha Allah zan sanar dakai komai game da rayuwar mu da Hauwa'u".
Dr Yayi murmushi me ɗauke da nuna jin dadi.
Umar ya fara magana kamar haka.
"Ni dai tunda na buɗi ido naga Hauwa'u a gidan mu nasan nayi matar aure daga wannan lokacin na ɗau san duniya na ɗora mata duk da lokacin kowa zai ɗauka ƙauna ce kawai ta wa da ƙanwa nake mata saboda duk abinda take buƙata nina ke mata shi, ko take san ci ni zanyi ƙoƙari naga na siyo na bata a haka har tai girman da zata fahimci soyayyar gaskiya nake mata daga nan ta fara jan baya dani ta kuma guji duk abinda zai fito daga hannuna tun ina ganin abun wasa ne har ya zama gaskiya,ni kuma kullum ƙaunarta ƙara shiga raina take ga samari a waje suna tururuwa a kanta a duk lokacin dana ga Hauwa'u da wani ji nake kamar na fille kansa na huta, abokaina suka bani shawara ko tana so ko bata so nasan yadda zai ai na aureta da zarar anyi auren zata fara sona naji daɗin shawararsu nabi duk hanyar da zanbi don naga na mallaketa nasami goyan bayan Baba Sa'a tai ruwa tayi tsaki hatta Babana dan kallo ya zama bayan anyi bikin mu ne sai matsala ta ƙara kunno kai Hauwa'u kwatata taki bani haɗin kai ni kuma abin yana damuna narasa wanda zan faɗawa kawai sai na yanke shawarar sanar da Baba Sa'a nan take ita ta nuna ɓacin rai a fili ta zo gida ta iske Hauwa'u tai mata nasiha ta tafi bayan ta tafi ne Hauwa'u ta nuna ita wannan nasihar bata shiga zuciyarta ba, ni kuma gashi nasha magani ƙarfin dana ke jina kamar matashin doki da shigata dakin na iske baccin ya fara ɗaukarta banyi wata-wata ba na haikefa wanda tun tana motsin yadda zata ƙwaci kanta har ƙarfinta ya fara karewa ni kwa ji nake kamar ana ƙara min wani sabon ƙarfin ajikina nan take naga jini ya fara tsattuwa ajikinta daga nan hankalina ya dawo jikina gabana yai mummunan faduwar ganin bata motsi ga jini be dena zuba ba na ɗauketa a suma na kawo ta wannan Asibitin naku na komagida na sanar da Baba Sa'a halin da ake ciki, itama hankalinta yayi mutukar tashi".
Daga nan na tsorata na fara dana sanin abinda na akaita mata.
Dr Nasir yace.
"To ga irinta nan ka haddasa mata cutuka idan an sami sauki anan sai kuma wani abun ya ɓullo,har yanzu kana san zama da ita idan ta sami sauƙi?,ko yaya amma inaso ka gane itafa rayuwar aure sai anbi ahankali balle a wajen yara dudu shekarun Hauwa'u nawa da har zaka gwada mata karfi inaso ka sani cewa kaine sila ba kowa ba".
_AISHA YAHYA TANKO✍️_
*LAIFIN WAYE*
*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*
*BY AISHA YAHAYA TANKO*
_KASHI NA BIYU_
*PAGE 14*
A can gida kuwa Dr Zahra ce ta gama ƙulluwa ganin irin kiran da takewa Dr Nasir amma baya ɗagawa ta kwanta akan doguwar kujera ta yanke shawarar idan har yana ganin kiranta be daga ba kuma be biyo kiran ba tasan me za tai masa saboda ya fahimci abinda take nufi yake shareta be san ita wace ba, shi yasa yake mata haka ta miƙe tsaye ta nufin toilet tayo alwala ta zo ta gabatar da sallah tare da yin addu'ar neman nasara akan Dr Nasir tashi wayarta tai ƙara da sauri ta ɗauki wayar ba tare da ta duba sunan ba muryar ƙawar Humaira taji akan wayar cikin karfin hali take bata amsa.
"Haba Dr ina kika shiga ne kwana biyu gashi kuma yanzu naji muryar ki kamar baki da lafiya gaskiya akwai matsala.
Wata irin dariya ta ƙaƙaro me ɗauke da sigar damuwa.
"Wallahi Humaira kawai gajiya ce kinsan aikin namu sai a hankali fa, kedai Allah yasa mu dace".
a haka sukai sallama ta ajiye wayar tana bin ta da kallo.
A can office kuwa Dr ne zaune shi da Umar suna ci gaba da tattaunawa akan ciwon Hauwa'u Umar yace.
"Naga tun ɗazu anata waya baka dagawa gwanda ka daga kaji ko lafiya".
Ya dube shi yana murmushi yace.
"Ba ruwanka da ko kira nawa za ai min ni dai fatana ka sanar dani tambayar dana ke ma akan Hauwa'u shin kana ganin zaman ku da ita ya ƙare ko zaka ƙara zama da ita idan taji sauƙi sosai ko yaya?".
Yana maganar ne cikin tsare shi da ido daya yi.
"A gaskiya ina mutukar ƙaunar ta amma bana jin da sauran zaman mu a gaba na gama yanke shawarar tana samun sauki zan sawaƙe mata amma ba'a san raina ba kawai ina ganin hakan shine zaman lafiyar mu".
Inji Umar.
Wata ajiyar zuciya yayi Dr Nasir yayi yace.
"To shikenan Allah yasa hakane ya fi zama alkairi baki ɗaya ina ga tun da mun gama ni zan tafi gida sai kuma gobe in sha Allah nagode bisa haɗin kan daka bani yanzu mun gane _LAIFIN WAYE_.
"Nawa ne ina fatan nan gaba zan ƙara irin wannan kuskuren da a baya ba".
inji Umar.
Suka Miƙe a tare suka fice daga office ɗin Dr Nasir yana gaba Umar yana biye dashi Dr ya nufin wajen ajiye motoci ya fara ƙoƙarin buɗe tasa kenan wayarsa tai ƙara hannu yasa ya ɗauka ya dubi sunan Dr Zahra yayi murmushi sannan ya ƙara a kunnesa yayi sallama cikin natsuwa yace.
"Kiyi haƙuri Dr Zahra inata ganin kiranki amma ba damar ɗagawa na saboda wani dalili yanzu kin ganni sai yanzu nake shiga mota ina ƙarasawa gida zaki ji kirana nagode sai kin jini".
ya kashe wayar yana dariya yace Dr Zahra rigima yana shiga motar ya tayar ya nufi get ɗin fita waje.
Sallama Umar yayi acikin ɗakin jinya ya kalli inda Baba Sa'a take zaune yace.
"Sannu Baba ya jikin nata naga kamar ta koma baccin koh naje na fayyace wa Dr komai game da halin da Hauwa'u take ciki kuma nasan LAIFI NA NE yai min nasihohi waɗanda suka shiga jikina daga ƙarshe na yanke shawara akan Hauwa'u idan Allah ya bata lafiya".
Inji Umar.
"Ɗan nan wacce irin shawarace Allah ya sa ta saki ce,dan ni a yanzu shine burina zan bata dama ta zaɓi irin mijin data ke so ba san raina ba".
Inji Baba Sa'a.
"Hakane dama kuskure ne kuma anyi shi da kuma ƙaddara saboda kowa na duniya akwai irin tasa".
Inji Umar.
Dama gida zan koma idan ta tashi kice ina dubata kafin na dawo gobe.
✍️
*LAIFIN WAYE*
*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*
*BY AISHA YAHAYA TANKO.*
*PAGE 15*
Wata irin harara ta zuba masa me ɗauke da tuhuma tace.
"A'a kai zamanka ba sai ka dawo ba mun yafe".
haka ya fice daga ɗakin cikin sanyin jiki.
Iskar sa ke da wuya cikin gidan ya buɗe ɗakin ya cikin gajiya wa ya kwanta akan doguwar kujerar dake falon ya zare glas ɗin dake manne a fuskarsa ya lumshe ido yana tunanin abubuwan da suka wakana tsakanin sa da Umar daya tuno Umar yace.
_zai sawaƙewa Hauwa'u yaji wani irin daɗi_ sannan ya mike tsaye ya nufi firij inda ya zaro ruwa me sanyi ya buɗe ya fara sha kenan wayarsa tai ƙara sai da ya gama shan ruwan ya dawo inda wayar take ajiye sunan Dr Zahra ya gani akan fuskar wayar yasa hannu ya ɗaga yace.
"Sannu Dr ya kike yanzu nake shirin cewa sai na gama abinda nake zan kiraki ban jima da shigowa gidan ba ki dan kara haƙuri nan da lokaci kaɗan zan kiraki kinji ya kashe wayar yana ƙoƙarin sake kwanciya saboda irin gajiyar da yai cikin lokaci ƙalilan bacci yai awon gaba dashi be farka ba sai wajen 2: 00 na dare.
Washe gari kuwa haka Dr ya tashi cikin ƙarfin hali yake shirya wa saboda gajiyar data gallabeshi ya gama shirya wa tsaf ya nufo wajen motarsa ya shiga ya tayar tafiya yake a hankali kamar ba'a kan titi yake ba har ya ƙaraso asibitin ya wuce office ɗinshi.
A can ɗakin da Hauwa'u take kwance kuwa Baba Sa'a ce tana zaune a ƙasan gado tana jan carbi taji motsin Hauwa'u ta Baba Sa'a ta dubi inda take tace har kin farka ne sannu.
Daga kai tai alamar Eh tai mata nuni data gyara mata kwanciyar Baba Sa'a ta tashi cikin sauri tana kicikici taji shigowar Dr Zahra.
"Ki dai gyara mata a hankali karfi fama mata ciwonta".
*AISHA YAHYA TANKO*
*LAIFIN WAYE*
*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*
*BY AISHA YAHAYA TANKO*
*PAGE 16*
Ta gyara mata kwanciya ta koma ta zauna tana sauraron abinda Dr Zahra zata ce game da Hauwa'u
Ta gama yan dube_dubenta ta dubi Baba Sa'a tace.
"Masha Allah jikin Hauwa'u yayi kyau sosai muna sa rai nan da lokaci kaɗan zamu sallameku".
inji Dr Zahra.
Wata irin dariya Baba Sa'a tai tare da yiwa Allah godiya tace.
"A gaskiya naji daɗi sosai burina ya cika kuma Allah ya saka muku da Alkairi yasa ku gama aikinku lafiya nagode sosai".
Dr Zahra ta fice daga ɗakin tana murmushi
Baba Sa'a ta kalli Hauwa'u tace sannu Yarinyar kirki.
Acan office kuwa Dr Nasir ne yake duba files din dake gabansa yaji shigowar Dr Zahra ya kada da abinda yake yi yace.
"Barka da zuwa Dr ashe har kin shigo".
ya umarce ta data zauna.
Taja ta zauna a kujerar data ke dab dashi tana murmushi tace.
"Ai na jima da shigowa har naje na duba Hauwa'u kuma naga wajen ya fara kamewa masan nan da lokaci ƙalilan zata iya dawo normal kaga daga nan ma iya sallamarsu su koma gida taci gaba da shiga ruwan zafi".
"Ƙwarai kuwa dama ranar da muke jira tazo kenan ɗazu naje can dakin naga wata me shigen matsalar ta itama inaso muje tare muga ta ina zamu fara da ita".
Inji Dr Nasir.
Dr Zahra tace to ba damuwa Allah ya bamu ikon sauke nauyin da yake kanmu,jiya bayan na barka a nan naga kayi busy daka koma gida ma haka.
"Wallahi kinsan aikin namu ne sai a hankali Allah dai ya shiga lamarin".
Bayan sun gama tattaunawa ne suka fara ƙoƙarin zuwa duba mara lafiyar.
Acan ɗakin kuwa tuni farin ciki ya baibaye Hauwa'u lokacin data ji Baba Sa'a ta sanar da ita abinda Dr Zahra tace game da ita har ta sami karfin gwiwar cin abinci sosai tana magana.
Suka ji shigowar Umar hannunsa riƙe da ledoji ya ajiye su kusa Da Baba Sa'a yana gaisheta Hauwa'u tuni ta haɗe rai kamar me shirin kuka yace.
"Dan Allah ki saki ranki Hauwa'u ƙaddara ce ta riga ta faru Allah dai ya kiyaye gaba".
Baba Sa'a tace hakane abu dai ya faru ni dai fatana ranar da muka fita daga Asibiti ka bata takardar saki shine abinda nake nema awajenka.
*LAIFIN WAYE*
*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*
*BY AISHA YAHAYA TANKO*
*PAGE 17*
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah Hauwa'u dai ta sami sauƙi har an salamesu daga Asibiti sun dawo gida
Tun ranar da Dr Nasir ya buɗe yaga ba Hauwa'u a cikin asibiti komai ya dagule masa ya rasa inda zai sa kansa Dr Zahra ta rasa gane inda ya dosa har ta fara sawa zuciyarta haƙuri amma ba dan san ranta ba.
Wata rana Hauwa'u tana zaune a tsakar gida kan tabarma tayi jigum tana tunanin rayuwarta a asibiti ne taji maganar BaBa Sa'a tana cewa.
"ke kuwa Hauwa'u me kikeyi ne haka tun ɗazu na barki anan amma ba abinda kikai sai zaman tunani bayan kuma yanzu ba abinda ya rage miki sai fatan Allah ya kawo miki miji na ba irin Umar ba nazo miki da wani babban albishir amma sai kin min alkawari zaki dena wannan tunanin".
Nan da nan Hauwa'u ta ɗago kai tana dariya ta nuna alamar zaƙuwar taji ko menene.
Baba Sa'a ta zauna kusa da ita tace.
"Umar dai ya sake ki".
Wata irin ƙara da murna Hauwa'u tayi tace.
"Dama wannnan ranar nake jira Baba Allah na gode ma daka bani lafiya ka kuma rabani da mutumin da yake kamar bakin maciji gareni ganinsa ya zame mun masifa".
Kafin su ƙarasa magana suka ji sallama gaba ɗaya suka bi kofar da kallo cikin mamaki suka miƙe a tare Dr Nasir kaine agidan namu .Baba Sa'a sannu da zuwa nabban bako nasan wannan zuwan na Hauwa'u ne ƙaraso mana nan ma gidan ku ne.
Hauwa'u ta kasa cewa komai ta kalli wannan ta kalli wannan shine kawai abinda take yi .
Dr Nasir ya zauna bakinsa ya ƙi rufuwa ganin irin karɓar da akai masa.
Baba Sa'a ta koma daki ta kirawo Malam suka gaisa.
Ta bar Hauwa'u da Dr Nasir zaune a tsakar gida.
"Tun zuwa na baki ce komai ba kuma ina ji Baba tace wannan zuwan naki ne ko nayi laifi inaso ki sani tun lokacin da aka kawo miki asibitin mu naji kin kwanta min ta nan ne na fara neman inda kuke zaune kuma gashi ban sha wahalar da mun gidan ba".
Hauwa'u tace.
"Nagode sosai bisa ƙoƙarin da kai akaina Allah ya saka da Alkairi".
"Nazo da ƙoƙan barata ina fatan zaki bani dan Allah ina so ki bani dama idan kin gama idda muyi aure in sha Allah zan baki kulawar da baki samo ba".
Inji Dr Nasir.
"A'a ba zan taɓa amincewa dakai ba har abada na dauke ka Yayanah wanda zaka tsaya min a matsalata".
"Kin san kwa me kike fada Hauwa'u ni bazan cutar dake ba nine mijin daya dace ki aura inaso ki bani hadin kai ki karbi tayin da nai miki nasan zaki ji dadin zama dani yana gama faɗa ya Miƙe tsaye ya zaro kudi acikin Aljihunsa ya ajiye mata ya fita cikin sauri daga gidan ba tare da ya jira amsar ta ba.
ta zubawa kudin ido ganin yawansu BaBa Sa'a ta fito daga ɗakin tace.
"Wallahi ke sakarai ce mara wayo ae duk ina jin abinda kuke fada ki sani cewa Dr Nasir shine mijin daya dace ki aura da zartar kin kammala idda kinsan baxan iya zama dake muna goga kafada ba sai kace uwar gida da amarya ba".
_AISHA YAHYA TANKO_
*LAIFI N WAYE*
*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*
*BY AISHA YAHAYA TANKO*
*PAGE 18*
Ta gama balbalin faɗanta ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba tace.
"kiwa kanki faɗa ki sani a yanzu bani da burin da ya wuce naga Allah yai miki sakayya daga wahalar da kika shiga abaya kullum addu'ar dana ke miki ita ce zaɓin Allah ada na tursasaki akan abinda bakyaso kuma kin bi amma yanzu na gane kurena naga faɗan dana ke miki ba shine mafita ba, na biki a hankali shine kawai dan Allah Hauwa'u ki karbin tayin Dr Nasir kinji".
inji Baba Sa'a.
Hauwa tace.
"Baba kar ki damu zanyi dogon tunanin akan Dr Nasir in sha Allah zan sanar dake nan da kwana biyu".
To shikenan ƴar albarka Allah ya shiga lamarin mu Baba Sa'a tace yawwa dama ina so ki shirya kayanki jibi gobe zamu kauye wajen su Inna Hama saboda suga jikin naki su tabbatar kin ji sauki kuma kinsan Mahaifiyarka tana fama da ciwon ƙafa ko tashi bata iya yi.
Inji Baba Sa'a.
Hauwa cikin zullumi ta miƙe tsaye bakinta
yaƙi rufuwa dan murna tace to Baba bari naje na fara shirya kayan.
"Haba ƴar nan kya dai bari kici abinci kar yai sanyi irin wannan murna haka kamar wadda akai mata albishir da zuwa Makka".
Inji Baba Sa'a.
"Tab Baba ai zuwana ƙauye dole nai murna yaushe rabon da naje yau kusan shekara uku fa ai kinga dole naji daɗi sosai ki bar abincin bana jin yunwa".
A can asibiti kuwa mutane sun cika a kofar office ɗin Dr suna jiran zuwan sa isar sa ke da wuya yayi parking ya fito daga motar fuskarsa babu walwala yana ta saƙe-saƙen acikin zuciyarsa game da Hauwa'u har ya isa bakin office ɗin mamaki ya kama shi ganin yadda aka cika bakin office ɗin ya saki fuska yai musu sallama suka amsa duk suka miƙe tsaye tare da yi masa sannu da zuwa ya Amsa toh aka buɗe masa office ɗin ya shiga ya ganshi tsaf yayi addu'a sannan ya zauna akan kujerar sa ya fara ganin mutanen da suke zaman jiransa a haka duk ya gama da kowa ya ɗan kashingiɗe yaji wani ƙamshi ya bugi hancinsa ɗago yai yaga waye Dr Zahra ce tsaye bakin kofar ta kasa ƙarasowa inda yake yace.
"ki shigo mana Dr ya kika tsaya Anan ko nayi laifi ne.
Inji Dr Nasir.
Dr Zahra tayi murmushi tace "ai kai baka laifi nice dai me laifi da har yanzu na kasa rabuwa dakai zuciyarka bata wajena tana wajen Hauwa'u amma duk da haka nake bibiyarka inaso ka sani duk halin dana shiga kaine silla".
tana gama faɗa ta juya tana tafiya.
Dr Nasir ya mike tsaye yana buga hannu yace "a fili wannan wace irin ƙaddara ce take nufin tunkaroni Allah yai min magani ya dawo ya zauna ya ci gaba da duba files din dake gabansa.
Washe gari da sassafe tuni Hauwa',u tai wanka ta shirya tsaf ta zauna a kan wata tsohuwar kujerar ƙarfe tana jiran fitowar Baba Sa'a tasha kyau kamar bata taɓa aure ba idan ka ganta.
Jim kaɗan Baba tta fito daga cikin dakinta itama ta shirya tsaf ta dubi Hauwa'u tace Allah yasa dai kin gasa jikinki kinsan dai likitoci sunce aci gaba da gasawa har sai kin dena jin ciwon ko yaya kar kilu ta jawo bau kina jina koh".
Hauwa 'u tace haba Baba Sa'a ta ina zanyi wasa da lafiyata ai