Showing 3001 words to 6000 words out of 9074 words

Chapter 2 - LAIFIN WAYE by A'isha yahaya tanko

07 Aug 2024

1543

kazan take".

Hauwa'u tasa hannu ta rufe fuskarta.


zan miki allura yanzu guda biyu sannan zan sa miki jini roba daya kuma daga yanzu wake zaki dinga ci da ganye har tsawon wata guda.


ta mai da dubanta ga Baba Sa'a dama kece Mamanta koh to ki kara lura da lafiyarta tana gama fada ta gabatar da aikin daya kawota dakin ta juyawarta ta koma office.



Malam yai sallama dasu, Baba Sa'a ta zauna a gefan gadon tana Jan carbi Lokaci-lokaci tana kallon yadda jinin yake tafiya har bacci ya dauketa ahaka cikin bacci taji Hauwa'u tana kwalla mata kira akan ta kirowa Nurse su zare mata robar tunda ya kare.

Mikewa Baba Sa'a tai a gigice har tana kokarin faduwa kasa.








*AISHA YAHYA TANKO* ✍️


*LAIFIN WAYE*



*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantarw da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~



*NA MARUBUCIYA*
*AISHA YAHYA TANKO ✍🏻*



*PAGE* 6

*__________📖 washe gari Baba Sa'a ta gyara Hauwa'u tsaf ta zaunar da ita jikin gadon, ta koma gefe d'aya ta zauna tana Jan carbi.


Likita ne ya shigo cikin d'akin yana sanye cikin k'ananan kaya fuskarsa cike da murmushi ya dubi Baba Sa'a cikin girmamawa yace.

"sannu ya me jikin?".

"Jiki kam akwai sauki ai dole a godewa likitoci irin k'ok'arin da kukeyi wajen ceton ran mutane".

Inji Baba Sa'a.

ya mai da dubansa wajen Hauwa'u sannu yarinya Allah ya baki lafiya kamar kowa inji likita.


"wallahi likita ta uzzira sai anyi sallama mun koma gida saboda ta gaji da zaman asibitin nama rasa yadda zanyi dare yanayi take cikan kunne da kuka".



Likita ya zare glas d'in dake fuskarsa ya matsa dab da gadon HAUWA'U yace.

"haba ke kuwa kin kwa san matsalar da kike ciki da kin sani da har zaki zabi komawarki gida, ki sani cewa lafiyarki itace me amfani idan kin daure kamar yau ne zaku koma gida ai duk wanda Kika gani anan ba dadi ne ya kawo shi ba yazo ne kawai don neman sauki da mafita".

Ta turo baki tana matse ido kamar me shirin kuka.


"Dama baki k'arasa bani labarinta ba ya kamata kizo muje office ki k'arasa bani labari".

yana gama fad'a ya fice daga cikin d'akin cikin sauri.

Baba sa'a ta amsa masa to gani nan zuwa tafara kici-kicin gyara hijabinta.


"Nifa yunwa nake ji amma shine kike k'ok'arin fita ki barnini kadai' koh" .

Hauwa'u ke fad'ar haka.

Ko kallonta bata yiba balle ta bata amsa.

Acan office kuma Dr Nasir yana zaune akan kujerarsa yana sa hannu a farar takardar dake gabansa, yaji an murd'a k'ofar office ana k'ok'arin shigowa ciki d'aga kansa yayi yana duban me shigowa.


Baba Sa'a ce ta shigo ta rabe jikinta a bangon office d'in.

Dr Nasir yai mata nuni da hannu data zauna akan kujera, nan-da nan ta zauna dama jira take.

Likita ya dakata da aikinsa ya numfasa ya fuskanci Baba Sa'a kafin yace uffan sannan yayi gyaran murya yace.


"Ina fatan dai kinzo da shirin zama saboda kici gaba da bani labarin marar lafiyarki".

Baba Sa'a ta gyara zama tace.


"To Likita ai labarin Hauwa'u yana da tsawo nasan ko kwana zamuyi ina baka baze kare ba, amma kaima ka k'ara bud'e kunnenka kaji sannan ka shirya shirin kuka nasan kafin na k'are sai ka zubar da hawaye sannan kuma zaka tsaneni".

Numfasawa tayi sannan taci gaba da cewa.

"zaka kaso nabar wannan asibitin dan nasan zai iya zama rana ta k'arshe wadda zaka kyamaceni, bazaka so ka k'ara jin muryata ba saboda irin gudunmawar dana bayar wajen haddasa ciwon Hauwa'u" .

Dr Nasir ya dafe kirji idanuwansa suka fiffito ya mike tsaye yana goge gumin dake tsatstsafowa a fuskarsa.



"Yace...........





*Aisha Yahya Tanko* ✍️.
*LAIFIN WAYE*








*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~



*NA MARUBUCIYA AISHA YAHYA TANKO ✍🏻*



*PAGE 7*

*__________📖 cikin Mamaki yake dubanta yace "kina tsammanin abinda kunnuwana suka ji gaskiya ne ko yaya?, amma idan haka zanso kiyi saurin k'arasa min labarin nan".


inji Dr.


Baba Sa'a idanuwanta suka kawo kwalla tasa hannu tana matsewa.

"idan zaka tuna tun farko nace ma bani na haifeta ba,yarinyar k'anwatace sannan ba'a san ranta ba na aura mata Umar a haka dai rayuwarta ta kasance cikin bak'in ciki da k'unci a gidan mijinta
Kowa yana bak'anta ran d'an uwansa gaba d'ayan su idan ka gansu a wannan lokacin zaka tabbatar suna cikin matsala, amma ba wanda yasan meye matsalar tunda sunk'i bayyanawa lokaci-lokaci nakan lekabsu don naga lafiyarsu haka zan tai mata dabarun mu na manya ko da zanji ta sanar dani halin da take ciki amma ina bata iya furtan komai haka zan futo daga gidan ina wasi-wasi".


Baba Sa'a ta d'anyi shiru na lokaci kad'an kafin ta kara magana.



Dr ya koma ya zauna akan kujerarsa yana ci gaba da sauraronta.


Acan d'aki kuma Hauwa'u ce kwance kan gado ta daga kai sama tana cije baki sakamakon rad'ad'in daya taso mata.


Likitace ta shigo cikin d'akin ta tsaya a kanta tare dayin magana.

"Lafiya Hauwa'u na ganki haka ko har yanzu tunanin gidan kike, ki tausayawa kanki irin halin da kika shiga kinsan fa dole sai anbi a hankali sannan za'a cimma buried, ina Maman taki take?".


cikin karfin hali ta d'an yunkura maganar ta bata iya fita saboda ciwo tace.

" tana wajen Dr wallahi yau wajen zafi yake min ji nake kamar ana barkono ake zuba min".


Subhanallahi inji Likita me ya kawo haka ko kin sosa ne kinsan ba'a san tab'a wajen.

"Aa kawai dai yanzu naji yana min zafi.

A can office kuwa Likita ne yaci gaba da sauraron Baba Sa'a, wayarsa tai k'ara yasa hannu ya dauka ya kara a kunnensa yace.


" eh gata tana office d'ina to bari muzo yanzu".


ya mike a gigice yana laluben glas dinsa.



itama ta mike tsaye tana dubansa me ya faru lafiya naga duk ka rud'e ?inji Baba Sa'a.






*AISHA YAHYA TANKO*✍️

*TSANANIN RAYUWA*






*PAGE 8*





*By AISHA YAHAYA TANKO ✍️👭😨*




*INA ƘARA MIƘA TA'AZIYYATA GA IYALAN AMINU S BONO DA RASHINSA DA MUKAI LALLAI MUN YI BABBAN RASHI ACIKIN WANNAN MASANA'ANTAR TAMU😭😭*



"Abban Walida ina ka samo waɗannan mutanen me zasu yi a gidan nan kuma?".

Inji Amina.

Dakatar da ita yayi tare da daka mata tsawa yace.

"Ki iya bakinki, ki kuma sani nan gidana ne dan haka zan iya kawo kowa kar na sake jin bakinki ya furta wata magana game da su inaso ki bamu wajen zama ki kuma basu abincin da zasu ci su koshi nan zasu ci gaba da zama har sai ranar da Allah ya kawo tafiyarsu baki san irin ladan da zamu samo a wajen Allah ba, shi yasa kike haka ko kin manta *WANNAN TSANANIN RAYUWAR* da ake ciki a yanzu".

Inji Yusuf.

Tunda ake wannan maganganu Hama ta rakube ajikin mahaifiyarta tana tsoro.

Nan dai Amina tayi dukkan abinda ya buƙata saboda ba yan da zata iya ta gyara musu sashen baƙi ta kaisu ta kuma dawo wajen Yusuf ta iske shi yana wasa dasu Walida tace aranta.
``` ko wannan mutumin kamar ba shine ɗazu yake ta faman yi mata faɗa kamar zai cinyeta```

Yusuf ya dubeta yace.

"Sannu da ƙoƙari har kin kammala da baƙin kenan".
Nan ya kwashe labarin ƙarya da gaskiya ya faɗa mata har sai da Amina ta fidda kwalla dan tausayi.

A can ɓangaren Musa kuwa tun shigar sa cikin gida tunani ya addabeshi ya kasa zaune ya kasa tsaye ina tunanin irin badakalar da Abokinsa yake yi,Khadija ce ta iske shi a wannan halin ta tsaya tana dubansa kafin tace uffan,sannan tayi gyaran murya ta ƙaraso inda yake hannu tasa ta dafa shi tace.

"Haba me gida na lura tunda kuka rabu da abokinka ka shiga cikin tunani shin meye? matsalarka,inaso ka sanar dani ko akwai shawarar da zan iya taimaka maka da ita amma rashin sanar dani baze zamar maka mafita ba sai dai ma ya ƙara maka, karuwa ni dai ina me rokonka daka sanar dani pls me gidana".

Musa yaji daɗin kalamanta ya saki ransa ya zauna akan kujerar nan ya bata labarin duk abinda ya haɗu da Yusuf ya ƙara da cewa.

" Nikam bazan iya zama inuwa ɗaya dashi ba, tunda baya jin shawara ko banyo tunani duk abinda yayi zai iya faruwa akan Walida tunda itama mace ce".

"Hakane amma dai rabuwa dashi baze zamar maka mafita ba, ka daure kaci gaba da zama dashi har lokacin da Allah zai ganar dashi kasan fa irin su Yusuf basa jin kira tunda sunyi nisa addu'a kawai itace mafita dakuma ƙara tunatar dasu amma saurin fishi ba naka bane, tunda kowa ya sanka dashi haƙuri kawai zaka ci gaba da yi bari na kawo maka abinci kaci kayi wanka ko zuciyarka zatai sanyi".

Inji Khadija.

Nan ta mike tsaye ta nufi kitchen ta fara kici-kicin haɗawa Me gidan ta abinci da abin sha.

A can ɓangaren su Sadiya kuwa sun ƙara shiga *TSANANIN RAYUWA* gaba ɗaya rigar ba me shiga harkar su balle a taimaka musu haka suke tafi da rayuwarsu cikin yunwa da talauci ba damar su leƙo sai kaji anai musu dan kira ana cewa.

Talaucine ya sa Kawunsu guduwa ya barsu tunda ya gane su da Innarsu masu ƙashin tsiya ce haka suke jin irin wannan maganganun amma basa tankawa Sadiya ce take iya tanka musu.

Inna ce zaune a bakin rigarsu bacci ya ɗauke ta saboda tsananin ciwon cikin daya turnuketa Fatima tana kwance kusa da ita basu aune ba suka ji saukar ruwa a jikinsu tamkar ruwan sama.


*Taku har kullum A'ISHA YAHAYA TANKO ✍️*


*LAIFIN WAYE*



*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~



*NA MARUBUCIYA✍🏻* *AISHA YAHYA TANKO*



*PAGE 9

*__________📖 Dr ya jima Akan Hauwa'u Yana dube-dubensa daga bisani ya umarci Baba sa'a data kirawo ɗaya daga cikin Likitocin Mata.


Acan kuwa Likitocin Suna tsaye sunyi cirko-cirko a bakin ƙofar Suna sauraro.

Baba sa'a ta iskesu a haka ta isar da saƙon Dr.


ta biyo bayanta suka rankayo cikin ɗakin gaba ɗaya Suka tarar Dr Nasir Zaune gefe guda Yana girgiza kai fuskarsa cike da damuwa Mikewa tsaye yai Yana duban Hauwa'u "a gaskiya aikin nan ya dawo Baya Sakamakon Sosa wajen dan haka inaso Yanzu a gaggauta shiga da ita dakin tiyata nan da mintuna goma saboda gujewa matsala zanje na shirya kayan aiki kafin ku kawota". Yana gama fada ya ficewarsa daga cikin ɗakin.


Baba sa'a ta kurma ihu wanda ya karaɗe Asibitin baki Ɗaya.




Likita tai saurin rufe bakinta tace "idan baza kiyi shiru ba ki fita So kike yarinyarki ta ƙara samun matsala to ki kiyaye".

"Shikenan nayi shiru Amma dan Allah karku kashe min ita wallahi ina kaunarta kuma ita kaɗai ce ya'ta" inji Baba sa'a.

" Ai dama kashe mutane Muke yi da bakinki fa mukaji kince kinci Amanarta" inji Likita.

Wayarta ce tai ƙara tasa hannunta acikin Aljihun rigarta ta zaro wayar ta kara a kunnenta "ok tohm gamu nan zuwa" inji Likita ta Fara kici-kicin daga Hauwa'u da taimakon Baba sa'a suka ɗagata.

Acan ɗakin tiyata kuwa Dr Nasir ne sanye da kayan aiki Yana ta gyare-gyare yaji an turo ƙofa da ƙarfi tsayawa yai Yana kallon ikon Allah ganin yadda Hauwa'u ce kwance Akan doguwar kujera duk kamanninta sun sauya tausayin ta ya kama shi.



*AISHA YAHYA TANKO✍️*

*LAIFIN WAYE*










*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~



*NA MARUBUCIYA✍🏻* *AISHA YAHYA TANKO*



PAGE 10

__________📖 Nan da nan Dr. ya Fara kici-kicin yiwa Hauwa'u tiyata.


Acan harabar Asibiti kuwa Baba sa'a ce take kai da kawo ta zama kamar tababbiya Saboda irin surutan data keyi yasa Mutane hankulansu ya dawo wajenta.


Kafin kace kwabo Dr.ya kammala da Hauwa'u ya koma gefe guda Yana kallonta ya lalubi wayarsa ya daddana numbobi ya kara akunnensa ya kirawo Dr zahra.




Dr zahra ta shigo cikin ɗakin hannunta riƙe file ahankali ta nufo wajen Dr ta miƙa masa file ɗin hannu yasa ya karɓa yana duddubawa.


"Tab nifa lamarin yarinyar nan ya Fara bani tsoro Muna murna munyi nasarar aiki Amma yanzu ta dawo Mana da aiki Baya inji Dr zahra.


ya numfasa ahankali ya gyara Zamansa, "Allah dai ya rufa asiri fatan mu Allah yasa daga wannan sai kuma sallama" inji Dr Nasir ya dubi Hauwa'u wadda take kwance kamar gawa.


"innalillahi wa'inna ilaiyun raju'un Dr" inji Dr zahra gaba daya suka nufi karasa gadon da Hauwa'u take kwance Dr kifa kansa yai Akan gadon.yana salati hannu yasa Yana goge kwallar.



A Nan na kawo karshen Labarin kashi na daya mai Suna LAIFI WAYE mu hadu a kashi na biyu ƙofa a buɗe take ga duk me san ƙarin Bayani ya tuntubemin Akan wannan number din 08173846034


*AISHA YAHYA TANKO*

*LAIFIN WAYE*






*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*






*BY AISHA YAHAYA TANKO*✍️





*PAGE 11*





Gaba ɗaya suka yo kan Hauwa'u a kiɗime suna ƙoƙarin lalubo ruwan dake gefanta.

Dr ne ya yayyafa mata ruwan ta ɗan motsa kadan ta buɗe idonta

" Allah na gode ma da kika farka ina ne yake Miki ciwo?".

Hannu Dr yasa ya dakatar da ita ya nai mata nuni data fita ta basu waje su ƙara duba jikin Hauwa'u Baba Sa'a ta fice daga ɗakin jiki a sanyaye tana waige-waige kamar mara gaskiya tayi jigum a bakin kofar ɗakin tana share hawayen da suke kwaranyowa ta ƙuncinta tasa hannun ta share .

A can ɗakin da Hauwa'u take kwance kuwa su Dr ne suke duba ta suna ƙoƙarin gano abinda yake damunta a wannan lokacin.


Dr Zahra ce take rubutu a cikin file ɗin dake hannun ta.
Dr Nasir ne ya dubi Hauwa'u yace.

"Yanzu me yake miki ciwo a jikinki?".

Ta ɗan numfasa cikin ƙarfin hali tace.

"jikina ne yake ciwo ji nake kamar ana sassara min shi".

tana maganar ne cikin ƙarfin hali.

Murmushi yayi ya dubeta yace.

"Sannu ga magani nai na rubuta miki za'a siyo miki shi yanzu kisha insha Allah zaki ji daɗin jikinki fatana dai ki kula da kanki ki ƙara hakuri har kiji sauki ki koma gida hankalinki ya kwanta idan mijinki yazo kice ina san ganinshi a office ɗina akwai tambayoyin da zan masa".

Yana gama faɗa ya juya ya fice daga cikin ɗakin Dr Zahra tana biye dashi fitar su ke da wuya Baba Sa'a ta nufo su fuskarta cikin damuwa tace.

"Dr ya jikin nata dan Allah ka fada min halin data ke ciki kar ka ɓoye min komai".

Dariya yayi me ɗauke da nuna farin ciki yace.

"ki kwantarki da hankalinki na gano abinda yake damunta kuma in sha Allah ba wata damuwa yanzu dai ga magani nan ki siyo yanzu ake san tai amfani da shi".

Miƙa mata takardar yayi nufi office ɗinshi

Dr Zahra ta juyo wajen Baba Sa'a tana cewa.

"Ya kamata kiyi sauri ki siyo mata magani tasha yanzu kuma ki taho mata da abincin da zata ci".

Tana gama magana tabi bayan Dr Nasir tana murmushi.


Shigarsa office keda wuya ya zare glass ɗin dake idonsa ya zauna akan kujera yana duba file ɗin dake gabansa yaji an turo ƙofar office ana ƙoƙarin shigowa.


Dr Zahra ce ta shigo office ɗin ta ƙaraso inda yake ta ɗan rusuna gabansa ta ajiye masa file ɗin tana murmushi kallon -kallo suka da Dr Nasir.


Ta sakar mata wani irin kallo me dauke da abubuwa.






*AISHA YAHYA TANKO*✍️

*LAIFIN WAYE*




*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*







*BY AISHA YAHAYA TANKO*







*PAGE 12*




_Ina Amare 'yan ƙwalisa ko masu sha'awar koyon kwalliya nazo muku da sabon albishir *Hafcy-beauty-kn*,07038455700 ta shirya tsaf don gyara Amare su fito tas ta tanadi kayan kwalliya kala -kala wanda ake kira mai da tsohuwa yarinya duk mai buƙata ya tuntuɓemu a wannan Number acikin farashi me rahusa Tana gyara Amare tana koyar da ɗalibai shima cikin farashi me rahusa._
*08173846034*











Dr Nasir ne yai ƙarfin hali yayi ajiyar zuciya yace.

" Dr ya akai ne ko akwai wani abu ne?".

Cikin kissa take magana.

" A'a Dr daman zuwa nayi muyi sallama kafin na wuce gida amma idan na ƙarasa zan nemeka a waya ina fatan wayar tana kusa dakai?".


Ɗaga kai yayi alamar Eh bakinsa ya gaza furta komai tun shigowar Dr Zahra ya rasa abinda yake yawo a tsakiyar kansa komai ya tsaya masa.

Dr Zahra cikin ɗaga sauti tace.

"Dr ko baka ji abinda nace ba naga ka tafi tunanin Hauwa'u".


A firgice ya ɗago kansa yana dubanta cikin inda_inda A'a Dr jinai kaina ya sarawa.

Ta ƙara matsowa daf da shi tanai masa sannu fuskarta cike da tausayi juyawa tayi a hankali ta nufi kofar fita taji ya kira sunanta cikin muryar ta bata taɓa jin wani ɗa'na miji ya kira ba,tsayawa tai cak saboda yadda taji tsikar jikinta ta tashi ƙafafuwanta sunyi mata nauyi yadda baza su iya ɗaukarta ba.

"Bazaki ki bari na ƙarasa wannan aikin ba na kaiki gida ba kinji".


"Na gode da kulawarka amma a halin yanzu har an zo ɗaukata".

Ficewa tai cikin sauri ba tare data jira amsar da zai bata ba.

Miƙewa yai tsaye yana kai da kawo acikin office ɗin ya rasa abinda yake damunshi shin ina zai jefa rayuwarsa ko ya ƙarbi tayi Dr Zahra.to shin ina zai kai soyayyar da yake wa Hauwa'u wadda yake jinta har cikin zuciyarsa a haka dai yai ta tunanina daga ƙarshe ya yanke shawarar duk yadda zai yi ya ceci lafiyar Hauwa'u ya haɗa files din dake tule akan tebur ɗinshi ya sa glass ɗin idonsa ya dai shirya tsaf ya nufo kofar fita ya murɗata yaji kamar ana ƙoƙarin shigowa cikin office dakatawa yai yana jiran me shigowa Umar ya shigo fuskarsa cike da damuwa sallama yai wa Dr cikin ladabi

Dr ya bashi wajen zama shima ya zauna suka fuskanci juna na 'yan daƙiƙai kafin suyi magana.


"Dama cewa akai kana san ganina shine nazo naji ko lafiya?".

"Ban fahimci abinda kake nufi ba ban shaidaka ba daga ina kake kuma waya turoka?".

Wajena lokaci guda ya jero masa wannan tambayoyin.

Ya ɗan ɗago kai yana shafa ƙeya gumi ya fara sallama a fuskarsa duk da sanyin Ac amma be hana gumi kwarara ajikinsa ba.

"Ni sunana Umar ni ne mijin Hauwa'u".

Ya zare glass ɗin dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login