Showing 3001 words to 6000 words out of 7941 words

Chapter 2 - SIHIRTACCEN IKO (COMPLETE) BY K_SHITU

k shitt   

28 Jun 2024

7162

ido bane ya koma ɗakinsa amma yana jin ba daɗi a ransa tunawa da duk randa Abbu ya gane tana zarya gidan abun ba zay ma kowa daɗi ba infact it isn't good ace wacce ba musulma ba na zaryan zo musu gida yanda aka sa ma Familynsu ido matsayin su na Iyalan Late Sarkin Musulmai na Liansa.
He believe no one would have the right to stop him, bai yarda da wani tsafi ba amma a Organisation nasu suna ta insisting zuwan su bincike akan Samun zinare da lu'u-lu'u Though shi arziƙinsa ya ishe shi no need for more struggling da babu nasara zuwa wata ƙasar buh shi ma yana son tabbatar da maganganun manyan members nasu shisa yay deciding zuwa ƙasar da Raysia.
Tsaki ya kuma yi yana jin haushi sosai yadda familyn sa ke ɗaukar abubuwa da girma mene a ciki don ya je ƙasar da babu yawan musulmai Yankin Foray ne zasu yi binciken.
Gefen zuciyansa na jin kaman akwai wani abu ba daidai ba.
Amaan kenan ɗaya daga cikin matasan familyn Late sultaan of liansa. Kakansu da ya rasu shi ne yay sarkin musulamai na Ƙasar Liansa da ke maƙwabtakar ƙasar nigeria. suna da yawa sosai family house ɗinsu baba ne kowa yana da arziƙinsa daidai amma akwai waɗanda nasu arziƙin ya shahara sosai wanda ya ƙara jawo ma family nasu popular sosai.
Matan da mazan duk suna da tarbiya sai waɗanda suke taɓa rashin ji a ɓoye tsarin family sun fi son auren yan uwansu ba wasu bare ba amma matasan da suka tasa suke ji da ƙwalisa da kuɗi sam basu da ra'ayin irin auren
Yawancin mazauna Liansa baƙaƙen fata ne sai kuma waɗanda ba yaren Ajoyl ba sune farare musulmai suna da yawa sosai da christain amma 'yan boko ne sosai masu riƙe al'ada, musamman ƙin auren bare ko wani yare daban da nasu.
Skin dinsu me kyau ne amma basu da haske ɓau din nan yawansu bakaƙe ne mazan ne masu haske amma suna da kyau sosai mai daukan hankali da farin jini.
Amaan da suka fi kira da Maan yana da farin jini kaman hauka saboda arzikinsa yana yawan harka da diamond da gold mom ɗinsa ma richest hajia ce da tayi kusan kowa ma bai dogara da kuɗin gidan ba suna neman na kansu ga boko sosai.
Friend ɗin sa cikin gidan Parook sai kuma ƙanwarsa meera Ammh ita ce favorite ɗin sa kuma mahaifiyar sai sauran yan uwan.
Yana da kyau sosai nutsuwa shi ne kawai yake taɓa rashin ji na mu'amula da waɗanda ba musulmai ba
wanda familyn basa son haka kuma yana da saran yin abubuwan da suka saɓa dokar gidan shi mutum ne mai son abubuwa daban da na kowa yana da fara'a baya iya boye abinda yake so da ƙi then yana da faɗa sosai.
Harkokin aiki na yawan haɗa shi da mata wanda suke sonshi amma shi baya ra'ayin musulma maran kamun kai infact he's not yet ready for marriage amma gidan ana bala'in son yay aure.
Kaman yadda suka saba fita bincike akan sababbin ababen da suka shigo duniya da wasu ƙasashe masu tsari daban da wanda aka sani a ƙasashe, Organisation ɗinsu haka gobe ma zasu baƙunci Ƙasar Raysia yankin foray.
abu guda yake tantama kai yaren mutanen amma kuma yana sa ran za a samu hausa people.
Da wannan tunanin yayi barci.

Foray
Tangaram na buɗe idanuwana muka kalli juna ni da Kawu ya matso kusa da ni cikin kulawa yana tambaya ta "Zoya a Soowe da waye da waye kika haɗu su wa kike mu'amala da su a makaranta, baki haɗu mace ko namiji tsofi masu kalan ƙwayan ido fari da tambari a hannayensu da goshi ko yatsunsu kore ?"
Na riƙe kaina da hannuwana ina son tuna tsohon da na haɗu da shi mai irin sifar da ya zayyana. Sai kuma na soma jin raina na ɓaci sosai idanuwana suka fara chanja kala cikin faɗa na bashi amsa "No"
Ya kallen da kyau yana so ya gane ni ce nake sarrafa kaina ko kuwa ya jefa mini tambaya da harshen Fore "Jnnah yhi?" na kauda kina gefe ina zura kafata ƙasa na miƙe tsaye.
Jiri naji ya rufe idanuwana na koma zaune ya ɗau wani ƙaramin tulun silver Ƙasar da ke ciki ya juye mata saman fuska. Ji na yi gabaɗayan jikina kamar ana jujjuya ni. Ya ɗebi ruwa ya miƙo mini na kafa kai na shanye.
Addu'a ya fara karantawa muna maimaitawa tare bayan wasu Daƙiƙu ya kira sunana "Zoya" na amsa masa da "Kayls mir" ya numfasa yana riƙo hannuna ya sake maimaita mini tambayarsa ta ɗazun.
Na rufe ido ina tunani nay saurin faɗin "Na tuna kawu a jirgi na haɗu da wani tsoho ya bani littafin Sihirtaccen Iko ina son sani wasu abubuwa na gidan mu kawu ka faɗa mun." cikin mamaki yace "Zoya littafin Sihirtaccen Iko me ya haɗa ki da tsohon?"
"Kyautar zinare nay masa shi ne ya bani"
Al'ajabi ya sa shi cewa "Zan iya ganin littafin ki kawo mini kar ki bari wani cikin gida ya sani" na miƙe na soma tafiya zuwa ɗakinmu ina isowa kofar na ji ƙwaran faduwar tangaram ya rotse na kalla ban ga komai ba na shiga ɗakin ƙasan na ɗau littafin na kare da Riga ta zuwa ɗakin kaka.
Ina isa ƙofar baba ya kira sunana "Zoya!" na juyo a hankali ina sake ɓoye littafin hannuna na amsa ya matso yana shafa kaina, "Ya jikinki kin ci abinci ko?" na gyaɗa masa kai a hankali ina murmushi ya dafa kafaɗa ta yana kallon hannuna "Ruqjiir?" ya tambaya miye na kasa bashi amsa sai ƙirjina da ya doka. ya ruƙo hannun yana kallon littafin sai kuma yace "Zinare" nayi murmushi sanda na ga maimakon littafi zinare ne hannuna bana son ya tambaye ni abinda zan da shi na rungume shi nay shigewata ɗakin kaka ina rufo ƙofar.
Na miƙa ma Kawu littafin da zummar ya karɓa ya girgiza mini kai yana faɗan "Ba zan iya karɓa ba, ban sani ba ko sihirin da yake ciki ya dinga sarrafa ni na ga alamun hakan a idonki akwai buƙatar tsarkake miki ruhinki kafin Iko ya soma cin galaba kanki yana sarrafa ki.
Ya ɗauko akwati dake ajiye ta ya buɗe na sanya littafin wanda a take ya zama zinare. Hakan ba sabon abu bane domin yankinmu da yawansu suna amfani da baƙin tsafi....
*PaidBook 300N VIP500 2329557913 UBA evidence of payment via 09117440993*


*SIHIRTACCEN IKO!*
ArewaBook @Kshitu.


*Page 7&8*

Tafiyan 20hours suka yi daga Liansa zuwa Ƙasar Raysia. Daga nan jirgin su yayi landing a wani babban filin jirgi Su uku suka sauko kowanne riƙe da Box da Trolley suna jaye da trolleyn har zuwan su inda jiragen ƙasa ke tafiya suka saya coffee da gashesshen nama da zinaren da suka zo da shi.
Daga nan suka siya ticket na jirgin ƙasan da zai kaisu Soowe inda daga nan zasu bi Jirgin ruwa su isa Foray.
Suna jin dadin iskan da ke busa su cikin jirgin da ke gudu sosai sun maida hankali wajen kallon yanayin Yankin da ake tafiya da su akwai itace masu kyawu da burgewa da kuma tsuntsaye sai wasu mutane da suke taruwa gaban wuta da waɗanda sautin ganguna ke tashi suna rawa.
Tafiya me nisa suka yi kamin su wuce babbar kasuwa jirgin ya tsaya daga bayan wani ruwa da ya miƙe hanyar dama inda zasu tafi.
Ba sabon abu bane a wajen wasu mutanen da ke ziyartar wasu ƙasashen ganin su Liner, Maan da Hisham. Abinda ya ja hankulansu yanayin su na baƙaƙen fata sai ita Liner da tayi bleacing taui haske.
Da zinare suka fi yin kasuwanci da siye da sayarwar abubuwan bukata.
Tafiyar da za su yi daga nan Soowe ɗin zuwa Foray aƙalla zai ta dauke su tsawon kwan hudu.
jirgin ruwan guda ɗaya ne ya rage wanda zai tsaya a jejin garko da foray basu da zaɓin da ya wuce su bi don babu wani haka suka biya da zinare suka shiga.
Ba laifi akwai yalwan mutane jirgin kuma tsaf gwanin burgewa sai dai mutanen na ta kallon su matsayin su na baƙaƙen fata.
Maan ya maida hankali wajen amfani da wayansa liner kuma na magana da wani matashi da harshe turanci wanda da alama shi ma ba mazaunin ƙasar bane.
Sun lula an fara tafiya iska me dadi na kaɗawa ƙananun kifaye na shawagin cikin ruwa.

Foray
Cikin wasu ƴan kwanaki da dawowata ina yin wasu abubuwa kamar bani nake sarrafa kaina ba gefe guda kuma ni da kawu muna bincike akan littafin da yaren da aka yi amfani da shi na baƙaƙen matsafa.
Cikin dare na tashi na kasa barci nabi umurnin zuciyata ta hanayar daukan akwatin da muka kulle littafin.
Na buɗe shi ina saka hannayena na ɗauko littafin, babu haske sosai a ɗakin riya kuma tayi bacci na buɗe shafin tsakiya wanda haske da sheƙi ƙwayar idona ya haska mini rubutun da ke jiki sai kuma shati yatsu guda shida inda mutum zai iya saita yatsun hannunshi.
Wani irin duka naji kaina da ƙirjina yayi sanda na ɗora hannuna idanuwana rufe na ji ina karanto wasu kalmomin sihiri da suka zama game-gari ga mutanen foray dake aikata baƙin tsafi na gaske.
Buɗe idon da zan yi babu komai a hannuna sai zinare na ganni zauna ƙasa gefe ɗaya daga wajen wani dogo ice.
Na miƙe tsaye na doshi wata da'irar wuta da na hangi wani zaune, ƙaramin yaro ne yake shan ɗumi na ƙarasa inda yake ina dafa kafaɗun shi ya kallen ya fara ƙara da ƙarfi da ƙoƙarin fisge jikin shi.
ba ƙaramin tsorata yayi ba da ganin kalar kwayar ido ta.
Mahaifiyar yaron ta ƙaraso da gudu wajen lokacin har kalar ƙwayar idonshi ta sauya zuwa bula mai cizawa.
Ta fincike shi tana kiran sunana "Zoya!" nayi baya ina dafe kaina, sai sannan na gane inda nake na mike da gudu nayi hanyar gidanmu ƙofar a rufe take na ja baya da gudu na dira ta katanga duk da tana da tsawo sosai.
Parlor na tsaya ina sauƙe numfashi inuwar mutum me tsayi sosai nake gani a bayana rashin wadataccen haske ya hanani tabbatarwa sai kuma ƙarar wucewan wani abu mai firgitarwa shu-shuu da ƙarfi.
da ƙarfi aka fisgi gashin kaina na saki ƙara "Auhh!" na waiga da hanzari ganin waye babu kowa wajen sai sawun hannuwa da jini da aka dinga yin gaba.
A tsorace na dinga bin sawun hannun don ganin waye haske ya kawo ɗakin tarr.
Hanyar fitowa bayan gidanmu inda shuke-suke suke nayi amma babu alamun kowa sai ɗigo-ɗigon jini.
Na tsaya ina kallon gurin naji kamar mutum tsaye bayana dab da ni ana fesa mini ruwa na juya ƙarfi ina nishi babu kowa na ruga da gudu zuwa samn bene sai na kusa hawan ƙarshe sai a maida ni baya.
gaba daya na gaɓa tsorata ganin jini a bayana, wata murya mai kauci na dinga ji tana dariya a kunnena mai firgitarwa lokaci guda na gigice ina toshe kunnuwa.
daga sama naji an sheko min ruwa sha da kaina zuwa ƙafafuwana na kasa daurewa na sake gigitacciyar ƙara, cikin gaggawa suka fa fitowa da makwancinsu suna kunna fitilu hasken da suka gani parlor ya sanya su biyowa hanyar bene daga sama suka hango ta tsaye ta kulle idonta.
Anum ce ta fara saukowa tana cewa "Zoya me kike anan cikin dare?" faɗawa na yi jikinta ina wasu sambatu da ban san me nake faɗa ba.
Suka kama ni zuwa ɗakin kaka kawu yayi mini addu'a daga nan komai ya lafa riya ma ta kwanta nan Kawu ya tambaye ta da harshen Fore me ya fito da zoya dadare haka ta bashi amsa bata sani ba ta farka bata ganni ba sai kuma taji na.
Gari bai gama yin haske ba aka soma buga mana gida da ƙarfi sosai abin ya basu mamaki Matar kawu Moh Rukhsha ta buɗe.
Maaikatan magarƙama ne tare da Louqa mamar Shahan yaron da na riƙe daren jiya suka shigo cikin gidan kai-tsaye ba tare da jira ba.
Kayb ikinsu kaɗai sun isa shaida su waye.
Louqa ta nuna Baba tana faɗan "Wannan shi ne mahaifin yarinyar ya fito da ita"
baba na shirin magana macen ta katse shi "Muna buƙatar ganin yar ku da fita daren jiya" dukkanmu sai da muka tsorata ya tambaya "Zoya kuma" Louqa tace "Ita ce tayi amfanj da baƙin tsafi tana son kashe Shahan!"
Al'amarin ya matuƙar basu al'ajabi Anum tace "Anya ita zoyar kuma?" A fusace tace "Ba tantama nake yi ba Zajja me kuke jira ku tafi da ita gata chan zasu iya bin bayan mu idan suna tantama don tabbatarwa.
Yan uwana na gani suka damƙo ni matan su uku na kasa cewaa komai saboda yadda tunanina ya kunce ina kuma tantama ni zoya na fita da dare yaushe kuma hakan kasance
Kawu ne ya mara musu baya yana roƙo su ƙyale ni.
Abin da bai taɓa faruwa da wani ahalinmu ba kenan Zajjal su kama mutum suka tura ni cikin amalanken shanu aka ɗau hanyar magarƙama.
Ɗakin da wani tsoho yake suka tura ni ba tare da jiran jin ta bakina ba suka garƙame dakin, na dafe kaina cikin bakin ciki hawaye na bin kuncina.
Ido na ne ya nuno mini yatsun ƙafa koraye da wani tambari a ƙafa fara tas. ƙirjina ya buga da ƙarfi da hanzari na ɗaga ido muka kalli junan da wannan tsohon.
ƙirjina ya doka da ƙarfi na saurin kawar da idanuwana amma tasirin sihirinsa yayi ƙarfin da ba zan iya dakatar dashi daga abin da zai aikata...

Jirgin ruwan na gudu sosai wanda hakan ya sa a maimakon tafiyar kwana uku zasu iya isowa cikin awanni arba'in da takwas.
Kamin isowar su abubuwa masu yawa sun faru na ban al'ajabi a bisa hanyarsu kawai Maan ya fara tantama da yanayin yadda suke abubuwa kamar ba mutane ba suna wata kalar tafiya a lankwashe wanda ke nuni da mutum bayi da cikakkiyar lafiya.
kasancewar sa mutum mai saurin fahimta da karantar hallayar yan Adam ya gane abubuwa masu yawa na yanda suke rayuwar su ɗabi'un nasu sun kwanta mishi yayinda tsarin wasu yaji bai masa ba nan take.
Be taɓa jin wani abu zai faɗar masa da gaba ba sai da duhu ya fara tsananta suka nausa tsakiyar ruwa dajika masu cike da namun dawa masu haɗari sun sanya su tsakiya hagun su da dama duk dajika ne.
Wata ƙara ce me sauti ke fita me kama da kuka da ya haɗe da gurnanin dabbobi da kukan tsuntsaye mai sauti.
wadanda ke cikin jirgin da ba mazaunan ƙasar Raysia ba sun fara tsorata da lamarin yanda jirgin wata tafiya kamar an riƙe shi inda Raysians ɗin ƙasar kuma suke harkokinsu da dariya suna shewa wasunsu duk da girman jirgin bai shahara ba sun yi amfani da tsafi saboda sanyin suna shan ɗumin wuta a da'ira da gasa kifi.
Kamar wasa aka basu kifi maan da hisham suka ƙi karɓa liner ta amsa tana ci da santi bata gama cinyawa ba maƙoshinta ya tokare ta soma aman wani baƙin abu lokaci guda ta fita hayyacin ta tana kakari sosai da alamun jigata.
dariya sosai irin ta zallar mugunta mutanen suka dinga yi da ƙarfi sai sautin dariyar ya haɗe da iska ya zama wani iri me ban tsoro ga wanda bay saba ba.
Cikin su ya debi ruwa jin duk sun chanja harshe suna magana suna nuno su...
*PaidBook 300N VIP500 2329557913 UBA evidence of payment via 09117440993.*

#2023
#Real K_shitu🦋
#Amzoy❤‍🔥

*SIHIRTACCEN IKO!*
_©K_shitu Multimedia._


*Page 9&10*

Su duka ukun cikin su ya ɗure ruwa hatta maan ɗin shi ma ya fara shakkar wani abu ya faru dasu mara kyawu. Abin da yay matuƙar sake rikitar da su ƙarasowan su gaɓoɓin wani jeji hagu da dama inda jirgin ruwan ke tafiya kaɗan-kaɗan matuƙin ya dakata cikin harshen Fore yake bayani a nan zasu yada zango kowa zai iya fita ya shaƙata. idan gari yay haske zasu ci gaba da tafiya zasu iya fita daga jirgin. Tsalle-tsalle suka fara suna fitowa kamar wasu biri hakan yasa Su Amaan ma fara fita yanayin jejin da sanyi sosai suka bi ɓarin Dama inda Raysians ɗin kuma suka yi haggu da tawagarsu.
Baki daya waɗanda ba forains ɗin ba su Biyar ne Maan, Hisham, Liner, Beer, Chandni.
Chan cikin dajin suka soma tafiya ganin yanda Beer da Chandni ke ta magana da turanci ne yasa Maan yiwa Hisham alamu da idunuwa kar yace komai.
Wani waje ne suka kutso mai yalwar hasken farin wata inda ke kama da lambu wanda shimfiɗaɗɗiyar hanya ta miƙe mai yashi gefe kuma korayen ciyayi da shuke-shuken kayan marmari masu ƙamshi da daukan ido.
Sun shagala sosai da kallon tsarin wajen wanda yay matuƙar daukan hankalinsu sun manta da cewa dare ne ba rana ba hasken ya haskaka gaba dayan gurin.
Sun miƙa sosai suna ratsa shuke-shuken masu birgewa da ban shaawa. Liner da ta soma gajiya da kwadayin Ayaba ta sa hannu ta fizgo dami guda ta bare guda daya ta soma ci taste din me shegen dadi ta ji ta mikawa Chandni ita ma ta ci suna ta surutu.
Amaan ya so yaƙi cin komai sai dai lemon ɓawon da ya gani ya burge shi ya cire guda uku suka soma sha shi da Hisham dandanon me sanyin tsaki wanda yake da sanyi sanyi suka shanye suna kallon yanda haske ya cika wajen da suke tafiya.
Wasa wasa sai da suka kutsa sosai ciki sannan suka fara gajiyawa musamman su beer suka matsa musu su zauna su huta ba tare da Hishaam ya so hakan ba suka zauna bisa wasu abubuwa masu kama da naɗaɗɗen kunkuru.
Wata irin iska me ƙara da guguwa suka soma ji da ta tarkato ƙayoyi tana jijjiga bishiyu. suka doɗe kunnuwa a gigice ƙara ce mai masifaffen sauti daga sama inda lokaci guda ko ina yay baƙiƙƙirin da duhu sannan suka soma jin kukan manya manyan zakuna da gurnanin su.
Da wani irin speed Maan da hisham suka miƙe daga inda suke zaune hannayensu damke da na juna. Iskar ce ta fara lafawa sai wani irin kuka da ke tunkaro su mai haɗe da gurnani me tsoratarwa
Haske ne ya kawo ɓau dukkansu suka murje idanuwansu cike da firgici. da ƙyar suke ganin tawagar zakunan da ke wani irin kuka da gurnani.
Babu wanda cikinsa be yi ƙara me sauti ba sanda suka yi ido huɗu da zakuna masu wani kalan fata golden me azaban sheki.
Sai sannan dukannin

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login