Showing 6001 words to 7941 words out of 7941 words
su suka tabbatar da suna da gudu na gaske. Wani irin gudu suke yi na fitar hankali yayin da zakunan ke biye da su a gigice suke jefa ƙafafuwansu cikin ciyayi suna sheka gudun ceton rayukansu.
A madadin su nausa hanyar da ta raba sai wani irin icce ƙayoyi ya tare musu hanya ya zame musu tamkar wata sihirtacciyar ƙofa.
Duk suka ja suka tsaya gaban wani mutumi dake duƙe riƙe da Sanda farin gashi me tsawo ya cika masa fuska.
Idanuwansa masu matuƙar kaifi da sheƙi suka sauke kansu inda suka durƙushe daga baya har zakunan sun fara doso su. cikin yanayi na fitar hayyaci suka yi bayansa suna rirriƙe shi.
Duk sun gama sadakarwa ajalin su yazo har numfashi na musu barazana yana fita da ƙyar ta bakunan su.
Ya ɗaga sandarsa ya buga ta ƙasa da ƙarfi. Take ƙasar wajen ta soma tsatstsagewa tana rugurgutsewa duka zakunan masu aiki da sihiri suka dakata gabanshi kawunansu a ƙasa ƙafafunsu na gaba a ƙasa alamun girmamawa.
Tasirin ƙwayar idonsa ta girmi tunanin me tunani lokaci guda suka ɓace shaharar ƙarfin ikonsa da girmansa a duniyar sihirtaccen iko ta sanya al’amarin juyewa daga Jejin da suke gurfane da sa ran rayuwa ko mutuwa suka tsinci kansu a wani Ƙaton waje da girmansa da tsarinsa ya isa zautarwa da fincikar tunanin mutum.
Wani gawurtaccen tsauni ne me cike da duwatsu baƙaƙe wulukin masu shsƙin haske inda ƙasan ƙananun duwatsun zinare ne masu ɗaukar hankali.
Gefe guda ruwa ne ke fesowa daga saman wani ƙaton duste me tsayin da ke girgiza ƙwaƙwale da faɗi na gaske a cure ruwa me haske na ban al'ajabi na fesowa ƙasa inda ruwan me haske haske ya taru yana kwaranya a ƙasa inda ruwan yay ma kansa ƙawanya saboda tsannain yawansa yana sulalewa a ƙasan wani waje da zurfinsa ya amshe duk ruwan dake malalewa ciki inda mutum na iya hango kwantattun kifaye na shawagi da jiƙaƙƙen yashi.
Abu mafi ƙayatarwa shi ne wasu bishiyu masu koreyen rasssa daga gefe-gefe da suka ƙawata darajan wajen da haɗuwan sa.
Tari suke yi sosai wanda ke barazanan tafiyar musu da numfashi.
Daga gaban wata kawatacciyar bukkar da ta ginu da sihiri wuta ke ci a da'ira sosai mai bada ɗumi, nan suka tsinci kansu wanda lokaci guda dumin ya shiga ratsa su tarin na tsagaitawa suka dinga sakin ajjiyar zuciya.
Sai sannan nutsuwa ta fara shigar su, suka soma gane yanayin da jikinsu ke yi abu na farko ƙishirwa da yunwa, sai kuma kwankwatsar da ilahirin jikinsu keyi.
Ruwa suka fara cin karo dashi cikin faffaɗan ƙoƙo kowanensu ya kafa kai yana sha sanyin ruwa da daɗinsa na amsa wa a bakunansu. Sai da suka ƙoshi da ruwan sannan suka fara sauƙe ajjiyar zuciya me sanyi wacce ke bayyanar da gajiyawarsu.
Wani farantin dutse
golden mai sheƙi guda biyu shaƙe da gashasshen naman Rago da kayan ciki dake tashin kamshin albasa da tafarnuwa wanda ke suraci ya dahu lugub sai ɗayan da ke shaƙe da kayan marmari abarba kankana da kuma lemon ɓaro da strawberry sai apple. kamar mayuwanta haka suke cin naman me shegen da daɗi wanda aka girkar musu da dutsen gishiri da zasu barbaɗa har da wasu yaji-yaji.
Duk iya cin su basu cinye duka ba suka bi da Kayan marmarin. Cikin su ya ɗauka sun yi ƙoshin da ya sasu jin har wani barci-barci.
Take duka suka baje babu tsaitsayawa sai barci..
Joyza kenan ɗaya daga cikin tsoffin dake ji da wani irin ƙarfin Sihiri suna mulkar dajikan duniyoyi mabanbanta tare da sihirtaccen iko me tasiri wa jinsin halittu, gawurtattu ne a fagen sihiri da sarrafa dabbobi da sauran halittun da suke so suna boye dajika a duniyoyi masu yawa tare da zinarai....
Zijjs
Tsohon ya dafa kanta yana bushewa da dariya Lokaci guda ya kira sunanta ya furta girmammun kalmomin sihiri.
"Zoya!
Ƙaddarorin Sihirtaccen ikon sharri..."
Duniyar ruwa!
ta tsinci kanta cikin babban tekun Lehyil..
Ahalin zoya sun ruɗe matuƙa akan batanta Zajjal sun bincike kaf sassan magarƙama babu zoya babu ko me kama da ita, sai jan mayafinta dake yashe haka tsohon dake ciki, wanda yake cikin ƙungiyar matsafan duniya...
Hakan ya haifar da rikici me girma tsakanin ahalin zoya da Zajjals wanda ya fusata mutane da dama dake yakin foray ciki harda Ahalin Shahan da mahaifiyarsa da ahalin zoya.
*PaidBook 300N VIP500 to subscribe pay 300 or 500N to this account 2329557913 UBA evidence of payment via 09117440993.*
(Kar ku bari ayi baku, Sihirtaccen iko Daga Alƙalamin jikar shitu zay ƙayartar da ku sosai ɗin nan in sha Allah🌝)
Saura Shafi ɗaya na gama free page, wanda bai biya nashi ba ya hanzarta.
Votes, Comments, Nd Follow❤🔥
*SIHIRTACCEN IKO!*
Arewabook@Kshitu.
#Last Free Page
To subscribe 300N VIP500 2329557913 UBA send your evidence of payment via 09117440983.
*Page 11&12*
Abin da ya fara dukan zuciyar Amaan Sallah, daga farkon zuwansu sun fara cin karo da abin da yayi ƙoƙarin tafiya da rayuwar su. Me zai faru a gaba ya zasu ci gaba da rayuwa haka gaba daya komai ya fice masa a rai.
a hankali maan ya miƙe yana ayyana abubuwa masu yawa a ransa, Shi Maan me ji da arziki da gatan rayuwa ya sha wannan wahalar jiya bai sa ran sake shakan iska ba a rayuwarshi zahiri bai taba ganin zakuna irin wadannan ba ko a zoo be fiye rawan kafan ganin zaki ba sai gashi da gaske ya gani Allah ya cece su da tuni an shafe rayuwansu.
Though be yi tunanin yanda ake fadan Al'ajabin kasar Raysia ya kai haka ba shi yasa yan'uwansa basu so zuwansa ba, lallai ya yarda har da aljanu a kasar.
Tunanin sa ya katse jin an dafa kafadansa,,, wani irin ihu yayi me sauti har saida muryarsa ta amsa ya runtsa ido. Duk yanda Hisham ya so ya rike dariyarsa ya kasa ya bude baki ya dinga kyalkyaka dariya sosai, da sauri ya bude idonsa yana kallon hisham da yake kallon sa yana dariya.
Ya ja ajiyar zuciya me karfi yana fidda numfashi ciki ƙosawa da tsaiwar yace, "Are you ok" da kyar ya tsayar da deiyan yace "No.. i can't imagine maan ne yake ihu yana jin tsoro, oh amazine!"
Be kula shi ba ya wuce bakin tuwan da ke gudana ya sanya hannu ya ɗibo yana watsa a fuska, wani ihun ya kuma yi yana kiran sunan Hisham ya koma gurin shi kamar zai kifa.
Sauran abokan tafiyar su ne suka fara tambayar shi yana lafiya,,cikin yanayin gajiyawa da tsoron faruwar wani abu mara kyau yake fadin "Shaam na gaji gaba daya bana jin akwai akhairi a nan, so nake mu koma Liansa." Hisham na shirin magana Dariyar sa tayi masu saujar bazata da ta hautsina gabadaya duniyarsu, wata irin dariya yake yi me ban tsoro kafin ya fara magana da muryarsa da ke a shaƙe kamar zai sarke "Liha`ihbn ooq, bddaq!"
Tunanin su bai gama kuncewa ba sai da Joyza ya bayyana wanda baya da wani banbanci da wanda ke tsaye yana dariya sun zama biyu iri daya babu abinda ya banbanta su. Beer ne ya ja da baya kamun ya fara gudu da karfin shi yana neman shige musu. Numfashi me zafi suka sauke sanda jinin Beer ya fallatsar musu a fuska ya fara ihu da kururu wani abu kamar maciji ya hadiye shi duka.
Ubangiji ne kawai ya san halin da suka shiga numfashin su na fita da matsanancin tsoro da ke zafafa kwakwalwa da sake rudarwa.
Dukkan su sun kasa motsi mokoshinsu ya bushe sosai.
Babu wanda be son guduwa amma beer ya zame musu ishara Joyza sun zama kaman butumbutumi ba me motsi cikin su.
Wata irin ƙara ke tashi har wata girgiza tsaunin ke yi, Alamun Dinaar na buƙatar jini...
Foray
Me ke shirin faruwa da Iko?
Shi ne abinda Ahalin Zoya suke bincikawa tare da ga addu'o'i, Wanda sam basu tasiri wani kalar ruwa ake yi me hayaƙi wanda ke tabbatar da akwai abin da zai faru da Iko wanda Shedanh ke bayyanar da Sihirinsu wa duniya, adanannun Zinaren da ke taso da ɓoyayyun Ruhi ke fashewa a Tekunan wanda hakan ke haifar da matsananciyar azaba daga shedanu.. Wasu yankunan na kasar Raysia na bayyanar da abubuwa marasa kyau da fitina.
Ƙara sosai rufaffen ɗakin da suke ajiye abubuwa masu muhimmanci na al'adu ke yi da hayaniya, dukkanin su ba wanda bai razana ba sun haɗe waje guda suna addu'a amma babh abinda ya sauya.
Abin da zai faru ba zai yi kyau ba idan babu zoya suna buƙatarta a kusa da su ko ta halin ya idan ba haka ba zata shiga cikin mummunan tarkon Ikon sharri wanda zai iya tarwatsa rayuwar mutane da yawa.
Hakan ya sanya Kawu Yahiz keɓance kansa a ɗakin Da suke addu'a ya fito da wani faffaɗan zinare me kyawun gaske ya ɗaura hannunsa yana karanta wasu kalmomi na forain babu abinda yake gani. Ya sanya wuƙar zinarr ya tsage tafin hannunsa jinin ya dinga ɗiga a sama sai hayaƙi ya soma lulluɓe wajen,,fuskar zoya yake gani dishi-dishi cikin teku me bulan ruwa goshinta an liƙa Dinaar..A bincikensa da yayi cikin wasu sa'o'i ya fuskanci abubuwa masu girman gaske da ruɗarwa, Ikon Sharri na son Mallake jinin Zoya da Dinaar,, zata koma ƙarƙashin sarrafawar Ikon Sharri, zasu sanya baƙin zinare a zuciyarta wanda zai bayyana tasirin jininta.
Kawu Yahiz ya gama ɗora alhakin komai a kansa na Zoya ta kuɓuta ko a mallake ta, Baya da ƙarfin da zai iya ja da Ikon Sharri ya zai yi kenan idan bai yi wani abu ba akwai matsakar da zata biyo baya da zata iya shafe rayuwar su.
Ƙarar tarwatsewar zinaren da ke gabansa ne ya juyo da tunanin sa hayaƙin ya fara washewa yana yayewa, suka yi ido huɗu da Ariya sanye da bakaken kaya na shahararrun matsafa, masu sheƙin jinin Dinaar.
Ba abu ne me yiwuwa ba matsayin sa na wanda yake da cikakken sani akan Ikunan sharri na duniyoyi ya kasa fahimtar abin da yake a bayyane masu amfani da Bakin tsafi ne suke amfani da tufafin dake sanye jikinta da Jinin Dinaar me ke shirin faruwa Ariya ce ko wata daban daga cikin shedanu?
Muryarta ya ji da ta gama ruɗar da shi "Ni ce zan dawo da zoya yanzu, Ina buƙatar buɗaɗɗiyar hanyar zuwa Lehyil" ransa ya ayyana masa babu abinda zai yi me kyau da ya wuce taimakon zoya ya fizgi wani farin zinare dake saye a wuyansa ya fara karanta wasu irin kalmomi da sake shi ƙasa da ƙarfi yana ƙara amon sautin muryarsa, Rami me tsananin zurfi da ke cike da ruwa ya bayyana ta ja da baya baya ta dawo da iya ƙarfin ta ta faɗa ciki ta nutsa Ramin ya shafe.
Muryarta ya ji da ta gama ruɗar da shi "Ni ce zan dawo da zoya yanzu, Ina buƙatar buɗaɗɗiyar hanyar zuwa Lehyil" ransa ya ayyana masa babu abinda zai yi me kyau da ya wuce taimakon zoya ya fizgi wani farin zinare dake saye a wuyansa ya fara karanta wasu irin kalmomi ya sake shi ƙasa da ƙarfi yana ƙara amon sautin muryarsa, Rami me tsananin zurfi da ke cike da ruwa ya bayyana ta ja da baya baya ta dawo da iya ƙarfin ta ta faɗa ciki ta nutsa Ramin ya shafe.
Bayan awanni bakwai.
Sun yi nasarar kuɓutar da Zoya Sai dai ƙarfin ikonsu bai kai bincikar zuciyarta ba, Abinda yafi komai hatsari yanda zasu turata wafa duniyar ko wata ƙasar ta samu kuɓuta daga sharrin Ikunan...
*SIHIRTACCEN IKO! littafin kuɗi ne 300N 2329557913 UBA .*
_ End of free pages. _
Ma sha Allah na samu damar ƙare shafukan kyauta kaman yadda na faɗa da farko littafin kuɗi ne ku yi ƙoƙarin biya don karatu cikin salama, Yanxu ne wasan zai fara ina da tabbacin labarin zai ƙayatar da ku in sha Allah.
Ba zan yi dogon bayani ba, ku biya don ci gaba da karatu yanzu ne za a fara buga ainahin wasan.
#AMZOY❤🔥
#09117440993.
#K_SHITU MULTIMEDIA.