Showing 39001 words to 41188 words out of 41188 words
fad'a masa irin rashin arzikin da Hajiya Salmahn tazo tayi yace ya kirata ko yasa Sultan ya fad'a Mata sa'ko daga shi Alhaji Tajuddeen yace duk ranar da tsautsayi yasa ta kara shigo masa gida sai yasa hukuma ta kamata ran Alhaji Mukhtar yayi mugun 'baci jin abinda ya faru ya sani Salmah zatai yafi haka amma tunda shi yanzu baida iko akanta ba matarsa bace zaiyi maganin wanda ya isa dashi.
Suna gama waya da Alhaji Tajuddeen ya kira Hajiya Salmah lokacin suna tare da Sultan suna magana da mamaki take kallon numbar wayar Alhaji Mukhtar d'in kodai wrong number yayi kamar bazata daga ba sai kuma wata zuciyar tace ki amsa kiji me zaice miki akan wanne dalili ya kira ki kaita jinjina daidai wani Kiran ya shigo saboda na farkon ya katse da sauri ta d'aga tana karawa a kunne tai shiru taji me zaice daga can 6angaren Alhaji Mukhtar jin an d'aga yasa yace.
"Salmah".
Murmushi tai cike da rashin mutunci dan tasan akan meya kirata zaiyi mata magana tace "ya akai ya za'ai fad'i ka qara sunana kenan".
A karo na biyu ya sake cewa "Salmah hawainiyarki ta kiyayi ramata baki da iko akan Sultan yanzu nine mahaifin sa sai hukuncin daya yanke a kansa shi zaibi dolensa ko yana so ko baya so wato tsabar rashin hankali da rashin sanin ya kamata shine kika wanki kafa keda wasu shegun 'kawayen ki kikaje gidan yaya Tajo kikaiwa Fatima rashin arziki sannan kika zagi Nabilah harda ce mata karuwa? Hummm to bari kiji kece babbar katuwar karuwa Salmah amma ba 'yar data fito daga jinin yayana ba kaf alhalin mu babu na banza kin gane sannan wannan akwatunan da kika kar'bo kiyi gaggawar maido min domin ko zaki mutu sai Sultan ya auri Nabilah kinji na fad'a miki".
Ta'be baki Hajiya Salmah tai bayan ta gama sauraron sa tace "wallhi Alhaji na rantse da Allah bazai aureta ba ko zaka mutu kaima, akwatunan kuma da kake magana akai na karfi ne kazo ka 'kwata Ina jiranka mtwww" taja masa dogon tsaki a kunne da sauri ya janye wayar zuciyarsa na tafasa anya Salmah tana da tarbiyya kuwa? Yana nadama da dana sanin aurenta da yayi abun kunya ne a gareshi ace uwar 'ya'yansa ce take fad'a masa duk abinda yazo bakin ta wanda ya dace da wanda bai dace ba numfashi me mugun zafi ya fitar tsabar turirin dake cin ransa ya qara d'aga waya yana kiran numbar Sultan a lokacin suna maganar yadda za'ai kamu da gurin event shida Hajiya Salmah yaji wayarsa tana ringtone kallon secreen d'in wayar yayi ganin Abba 6aro-6aro yasa gabansa yayi wani irin fad'uwa zuciyarsa ta buga da karfi har saida ya runtse ido yana dafe 'kirji kafin da'kyar ya d'aga domin yasan yau Allah masanin irin guguwar da zata tashi idan ya koma gida ko Alhaji Mukhtar ya fahimci yana gurin Hajiya Salmah ne maybe saidai ya tsaya ya kwana anan indai ya bari ya gano haka.........................
"Sultan shakkar me kake ka d'aga man kar kaji tsoron komai ina tare dakai koda ace Alhaji ya juya maka baya nasan bazai wuce yace saika sa na mayar da akwatuna ba idan baka auri Nabilah ba bashi bakai saime danya tsine maka karka wani damu ka share shi ina tare dakai dan haka d'aga muji abinda zaice Ina daidai dashi" Hajiya Salmah ta karasa maganar harda zaro ido waje tana harare harare kamar Alhaji Mukhtar d'in ne a wajen.
D'agawa Sultan yayi yana daidaita muryarsa yace "hello Daddy ina yini"?.
Alhaji Mukhtar bai amsa masa ba domin ina yinin da yace sai ya sake fusata shi murya a kausashe yace "Sultan duk inda kake duk abinda kake komai muhimmancin sa ka katse shi yanzu kazo Ina neman ka a gida karka kuskura ka 6ata min lokaci" yana fad'in haka ya kashe Kiran dafe Kai Sultan yai yana cewa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Umma kinga abunda nake gudu ko shiyasa tun farko nace ku kyale na had'a wani lefen akai karki kar'bo akwatunan nan zai tada fitina gashi tun ba'a je ko'ina ba ni bansan yadda zanyi da rayuwata idan Abba yad'au fushi yana ji baya gani baya saukowa da wuri".
Ta'be baki Hajiya Salmah tai tana kallon sa da yadda lokaci guda ya susuce ya fita daga nutsuwar sa tace "oh akan wannan d'an abun shine har ka tada hankalinka? Hummn Sultan karka damu bakasan wace niba ganina kawai kake haka matsayin Umman ka idan na fito maka a kalata zaka sha mamaki dan haka tashi kaje karkasa tunanin komai a ranka kaje ka fuskance shi ka tsayar da idanuwanka cikin nashi Ina me tabbatar maka idan kayi haka zakai masa kwarjini zai rasa abunda zaice maka karshen wasan zakaji yace tashi ka tafi".
Da mamaki Sultan yace "Allah Umma"?.
Cikin yardar da taiwa kanta cewa hakan ne mafita da bashi 'kwarin gwiwa tace "kwarai kuwa jeka gwada Ina jiranka nan da bayan sallar isha" Kai Sultan ya d'aga yana sauke ajiyar zuciya yace "to amma Umma.....................
Kiran Alhaji Mukhtar daya sake shigowa wayarsa shine ya hana ya fad'a Mata abinda yake son fad'a da sauri ya mi'ke ko sai an jima baice mata ba yayi waje yad'au mota da mugun gudu ya nufi gida yana yin parking daidai Alhaji Mukhtar ya gaji da kiransa ya fito harabar gida ya tsaya a jikin mota kawai ya zubawa kofar gate ido yana jira yaji motsin Sultan d'in amma shiru sai yanzu.
Ko daidaita parking Sultan baiyi ba ya fita daga motar yazo inda Alhaji Mukhtar yake tsaye saidai ya kasa d'agowa ya tsayar da idanun nasa cikin nasa kamar yadda Hajiya Salmah tace masa bazai iya ba domin mahaifin sane yayi masa kwarjini kallonsa sosai Alhaji Mukhtar ya tsaya yi kamar me tunani daga baya ya jinjina kai yana jin kamar ya rufeshi da duka ya daure dai yakai zuciyarsa nesa saidai kana jin muryarsa kasan a fusace yake juyawa yayi yana bud'e murfin mota yace.
"Tashi ka shiga akwai inda zamuje".
Mi'kewa Sultan yayi da'kyar kamar mara lafiya ya zagaya d'ayan site d'in ya shiga Alhaji Mukhtar ya tada mota suka bar gidan tambayoyi ne sosai aran Sultan to yanzu ina zasuje meyasa ya d'auko shi a motarsa.......................
Tunanin sane ya katse jin ya tsayar da motar yana horn da sauri ya d'ago yana kallon gurin daidai me gadi ya bud'e kofa sun shiga fad'uwa gaban Sultan yahau yi bayan Alhaji Mukhtar ya parker da mota sun fito me suka zo yi a gidan su Nabilah kuma? Kai akwai wani abu da yake faruwa Allah yasa ba aure zaice an d'aura musu ba tabdijan daya shiga uku ya zaiyi da Hajeer me zai cewa Hajiya Salmah bazai iya fuskantar ta ba tuna hakan yasa ya zabura har saida Alhaji Mukhtar ya kalleshi amma ba kallon rahma ba kallo ne me cike dam da tsantsan fushi.
Suna shiga parlor Alhaji Tajuddeen yana tsaye shima tun akan abinda Hajiya Salmah tazo tayi yana damunsa ganinsu tare da kuma yanayin da yake ganowa a tare da Alhaji Mukhtar da sauri yace "lafiya na ganku a haka Mukhtar"? Daidai sun karaso Alhaji Mukhtar ya jinjina kai yana cewa "eh lafiya yaya magana zamuyi" ya fad'a kafin ya juya inda Sultan yake ba zato Sultan yaji an kifeshi da mari kafin ya samu damar d'agowa Alhaji Mukhtar ya sake d'auke shi da wani mari" da mamaki Alhaji Tajuddeen yace.
"Subahanallahi Mukhtar me kake yi haka".
Alhaji Mukhtar baiyi magana ba sai rigar Sultan daya ri'ko yaci kwalarshi ransa na 'kuna ya hankad'o shi gaban Alhaji Tajuddeen cikin tsawa yace "dur'kusa ka bashi ha'kuri".
Da sabon mamaki Alhaji Tajuddeen yace "wai Mukhtar lafiyar kalau kuwa"?.
"Eh Yaya ina lafiya kuma a hayyacina nake kawai Sultan da Salmah sun kaini bango ne yau sai yadda Allah yayi nida Sultan ne zaiga fushi na wanda bai ta'ba gani ba bai Kuma San Ina dashi ba yanzu ya baka ha'kuri".
Da alamun tambaya Alhaji Tajuddeen yace "To ha'kurin me kake so ya bani yayi min wani abu ne"?..
"Kwarai ai shi yasan abinda yayi maka dan haka ya baka ha'kuri da farko kafin na fad'i abinda nake son fad'a" mayar da hankalinsa kan Sultan yayi yana cewa "ka bashi ha'kuri ko sai nayi shot dakai anan".
Da sauri Sultan ya durkusa har yana bugewa da kujera ya dafa kafafun Alhaji Tajuddeen yana cewa "dan Allah Daddy kayi hakuri dan Allah ka yafe min".
Kai Alhaji Tajuddeen ya girgiza yana cewa "ni babu abinda kai min Sultan tashi kaje" yana rufe baki Sultan ya mi'ke tsaye yana shirin ficewa daga parlon da sauri Alhaji Mukhtar ya mayar dashi qasa yana cewa "wallahi yaya Tajo saiya baka ha'kuri Kuma sai kace ka yafe masa idan ba haka ba ni bazan yafe masa ba".
"Haba Mukhtar ni meyayi min dan Allah ka rabu dashi".
"Yayi maka Yaya amma tunda lokaci ya wuce basai an dawo da baya ba kowa ya tuna bara baiji dad'in bana ba kawai ni ya baka ha'kuri ina ji shine zan gamsu".
"Idan ya bani ha'kurin shikenan ina komai ya wuce"?.
"Eh to banace ba amma dai ya fara baka ha'kurin naji".
"Ok sultan bani ha'kuri" Alhaji Tajuddeen ya fad'a da murmushin rigima irinta Alhaji Mukhtar a fuskarsa.
Kan Sultan a sunkuye yace "kayi hakuri Daddy dan Allah ka yafe min".
"Na yafe ka Sultan Allah ya yafe mana baki d'ayan mu, kallon Alhaji Mukhtar yayi yana cewa "ya bani ha'kurin shikenan ya wuce"?.
Kai Alhaji Mukhtar ya girgiza yana cewa "ya kusa wucewa dai abu na gaba da zakai ni kuma na yafeka shine kaje duk inda Hajiya Salmah takai akwatunan nan ka dawo min dasu gidan nan kafin ranka yai mummunan 6aci ni zaka mayar 'karamin mutum ka biyewa mahaifiyar ka tana d'ora ka akan gur6atacciyar hanya baza kasan kayi babban rashin Nabilah ba a rayuwar ka sai ranar daka gane gaskiya lokacin da ni kuma bazan saurareka ba".
Jin abinda Alhaji Mukhtar yake fad'a yasa Alhaji Tajuddeen ya samu hasken abinda yake faruwa tsakanin su kaiya girgiza yana kallon Alhaji Mukhtar wanda fuskarsa ta gama cika ta batse da 6acin rai yace.
"Zaune Mukhtar muyi magana".
Zama Alhaji Mukhtar yayi sannan Alhaji Tajuddeen ya mayar da kallonsa kan Sultan yace "kaima gyara zamanka Sultan kar kafarka yai ciwo" gyara zama Sultan yayi kuma har lokacin ya kasa d'agowa ya kalli Alhaji Tajuddeen saboda kunya..........
Magana Alhaji Tajuddeen ya fara cikin nutsuwa ta sigar da zasu fahimce shi yace "Mukhtar dan Allah kabar Sultan ya auri za'bin ransa karka hanashi kuma kar kayi fushi dashi bakasan me Allah ya rufe ba a cikin wancan auren da yake so kowanne bawa da kalar tasa kaddarar insha Allahu daga yau na warware komai Babu maganar aure tsakanin ka da Nabilah saidai kuyi zumunci Allah ya baiwa kowa abokin zama na gari kai kuma Mukhtar abinda nake so dakai kayi hakuri kar kayi fushi da Sultan duk abinda kaga bai faru ba to Allah ne bai nufa ba ya kamata abun ya tsaya iya haka a fuskanci juna ayi ha'kuri kaji".
Kai Alhaji Mukhtar ya d'aga bawai dan ya ha'kura ba a nasa 6angaren amma dan kada Alhaji Tajuddeen ya fahimci har yanzu bai huce ba kuma bayan ya isa dashi bazaiji dad'i ba yasa ya sassauta fuskarsa yace "shikenan Yaya Allah ya rufa asiri ya wuce Allah ya baiwa Nabilah miji na gari wallahi da ace ina da wani d'an bayan Sultan a gobe sai an d'aura masa aure da Nabilah amma shikenan" ya fad'a yana jan 'kwafar daya kasa danneta sannan ya mi'ke bai sake cewa komai ba ya fita a parlon jikin Sultan ne yayi mugun sanyi amma kunya ta hana yacewa Alhaji Tajuddeen wani abu kawai yaci gaba da zama a gabansa yana jiran yaji me zaice............
"Sultan".
Yaji ya kira sunansa da'kyar ya iya amsa masa cigaba Alhaji Tajuddeen yayi "karka damu kaji nasan ba lefin ka bane bazaka ta'ba yin haka ba Saboda kana da tarbiyya nina sani ba komai tashi kaje sannan duk wani abu da kasan baka yi ba na 6angaren auren ka da wancan yarinyar nima ubane kamar Mukhtar kai min magana zanyi maka komai kaji" da'kyar Sultan yace to kamar me ciwon cinya ya tashi jiki a sa6ule ya fita a parlon murmushi Alhaji Tajuddeen yayi yana jinjina kai ya sani gaskiyar Alhaji Mukhtar bata yabon kaiba Sultan yayi babbar asarar rashin auren Nabilah amma bazai gane hakan yanzu ba sai nan gaba, mi'kewa yayi shima yana fita a gidan domin dama akwai gurin da zaije dalilin maganar da Hajiya Fatima ta fad'a masa ne ya hanashi fita amma tunda yanzu an gama da shafin kuma yaga kiran Alhaji Ashraf maybe yana son ganinsa ne bari yaje ya sameshi..............✍️ YUSRAHMS CE.
#300
Acc: 2410673902
Nm: Yusrah Musa Zenith Bank
Mai son ci gabansa should DM me kayi min magana ta wannan number tawa 👉+234 816 098 3083 Yusrah Musa Abubakar.
Y A
°•°•° U R °•°•°
°•°•°•°•°. S °•°•°•°•°
°•°•°
YMA DUTSE NEW WORLD 🌏
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹