Showing 3001 words to 6000 words out of 41188 words

Chapter 2 - MINISTER ASHRAF HAUSA NOVEL

26 Aug 2025

1898

Nabilah harta bud'e mota zata shiga ta tsaya tana cewa.

"Husnah dan Allah karki manta gobe ki fito da wuri tunda naji kince gidan kanwar Momyn zaki tafi" Kai Husnah ta d'aga tana cewa "ok sai Allah ya kaimu gobe ki gaida mun da Mum sosai Beelat" "ok bye" Nabilah ta fad'a tana shiga motarta itama saida ta Husnah ta wuce sannan tabi bayanta ita ta nufi Yalwawa Nabilah Kuma ta nufi Yadi ko a hanya tunanin yadda zata 6ullowa da al'amarin Sir Ähmäd takeyi amma ta bari a ranta tunda yau ta fad'a masa ya rabu da ita idan yaji shikenan idan baiji ba koda za'a 6ata masa paper saita fad'awa Daddy domin ya d'aukar mata mataki irin su Sir Ahmad ba mutanen da za'a zubawa ido bane domin shi mutum ne d'anye kuma ga6o ta tabbata matukar ta share bata fad'a anyi maganinsa ba uhmm tana tsoron abinda zai faru a gaba Allah ma ya kiyaye.

Horn tayi a kofar gate d'insu me gadin dake zaune ta ciki ya tashi ya bud'e mata ta shiga sakamakon tana sa rai maybe zata fita da yamma yasa bata Kai motarta cikin rumfar parking d'in motoci ta barta a baya baya ta kasheta tana fitowa ta shiga ciki tsit parlon kamar ba kowa sakamakon Hajiya Fatima tana bedroom kuma TV ba'a kunne yake ba shiyasa parlon yad'au wani irin shiru shirun ma har yayi waya part d'inta ta wuce domin haka kawai taji jikinta na mata ciwo saida ta had'a ruwa me zafi tayi wanka ta sake sabon shiri cikin dinkin wata kyakkyawar atamfa anyi mata dinkin buba yasha stone yanata walwala ta kashe d'auri ta dau'ki agogo ta saka da takalmi harda d'an kunne da sarka kamar wacce zatai ba'ko ta feshe jikinta da daddad'an turare sannan ta dau'ki phone d'inta ta dawo parlor ganin kiran Husnah yasa tai murmushi tasan abinda zata tambaye ta amma sakamakon yanxu Hajiya Fatima ta fito tana parlon yasa bata bi kiran ba ta bari saita koma part d'inta yadda xatafi yin wayar a sake karasowa tai tana zama ta kalli Hajiya Fatima dake binta sa kallo tace.

"Barka da gida Mami na fatan kin wuni lafiya"?.

Kai Hajiya Fatima ta d'aga tana cewa "lafiya kalau na wuni ya gajiyar school ya exam"? "Alhamdulillah Mami ina Daddy ko bai dawo ba"?.

"A'a ya dawo da wuri ma wanka yayi dai ya fita a gidan" ok kawai Nabilah tace tana d'age kafafunta daga kan carpet ta maida kan kujera ta tan'kwashe su bata sake cewa komai ba hankalinta nakan waya tana chatting d'agowa Hajiya Fatima tai tana cewa "amma Nabilah bakici abinci ba tun breakfast d'in safe shine kin dawo d'inma basaki mayar da hankali kici ba sai ulcer ta kama ki" murmushi Nabilah tai tana girgiza kai tace.

"Ai Mami ulcer bazata ta'ba kama niba".

Da mamaki Hajiya Fatima tace "meyasa bazata kamaki ba saboda da tana tsoron ki"? Dariya Nabilah tai tana cewa "a'a saboda 'kawata ce mun riga mun saba" "uhmmm" kawai shine abinda Hajiya Fatima tace tana kallon Nabilan wacce da gaske bazata ci abincin ba ta sake gyara zama tana mayar da hankalinta kan secreen d'in wayar tace.

"Nabilah d'azu Daddyn ki yazo yana nemanki nace kina school amma ya aje Miki kyautar daya kawo miki gashi can akan dinning banma d'auke sa nasa a fridge ba sai kinzo ki gani da kanki yaso kin dawo kun gaisa har yace zai jira ki taso sai kuma akai kiransa a waya shine suka fita tare da Daddyn naki".

Murmushi Nabilah tai tana d'agowa kalle ta domin tunda taji tace Daddyn ta tasan wa take nufi aje wayar tai cikin zumud'i ta mi'ke tana zuwa ta d'auko kyakkyawar ledar dake she'kin tabuntaka balle kumà abinda yake ciki ta dawo tana zama har lokacin da murmushi akan fuskarta ganin kayayyakin da suke ciki yasa ta sake fad'ad'a murmushin ta cikin walwala tace.

"Wai Mami kina nufin Daddy Ash yazo gidan nan yau? Wayyo gashi bana nan".

Zaro ido Hajiya Fatima tai tana kallon ta da mamaki tace "Daddy Ash kuma Nabilah abokin uban naki guda kike kira da Ash"? Dariya Nabilah tai tana cewa "to Mami ba sunan shi bane"?.

"A'a ba sunan shi bane tunda ba Ashraf kika ce ba shi kuma sunansa kenan".

"Ai Mami da Ash da Ashraf duk d'aya ne".

"A gurinki ba amma ba d'aya bane tunda shifa ba yaro bane da saurayi ne saiki kirashi da hakan amma ubanki guda"?.

"To Mami bakiji akace dakai wasa da baban wani gara kayi da naka ba shiyasa nayi hakan".

"Au haba kenan yanzu zaki iya kiran naki tsohon da Daddy Taj ko? Tunda ai shima Tajuddeen yake".

Hhhh dariya Nabilah tai tana fiffito da kayan zallar chocolates ne kala kala sai yogurts da ice cream da tsadaddun biscuits humm Hajiya Fatima bata bud'a taga mene a ciki ba amma tasan za'a rina kallon Nabilah wacce ta 6are wata babbar chocolate tana sha tayi ta d'an girgiza kai tana cewa "wai mutum ya girma shekara ashirin da yan kai amma saboda babu qani yasa suke shagwa'ba ki yanzu irin wannan kayan za'ki haka kamar 'yar yaye"? Dariya Nabilah tai tana mi'ko mata guda d'aya tace "Mami kema gashi ki sha wadannan chocolates d'in na dabam ne bana yara bane" kai Hajiya Fatima ta girgiza "a'a nikam bazan sha zaki ba kema da kike wadansu abubuwan ganin ba wani sai kene da kina da qani ko qanwa baza kiyi wani abun ba koda kud'i" murmushi Nabilah tai tana hade kayayyakin ta mayar dasu cikin ledar tace.

"Shiyasa ya Sultan yake cewa wai Daddy's dina sune suka 6ata ni dashan abubuwa shiyasa ban damu da abinci ba shikam bazai yarda da wannan shaye shayen kayan za'kin ba dole ya koya min cin abinci".

Jin abinda Nabilan tace yasa Hajiya Fatima cews "oh nina manta ma d'azu da safe kunyi sa6ani kina tafiya school sai gashi ya shigo gidan yana neman ki nace masa kin tafiya makaranta shima a lokacin hospital zai tafi dana fad'a masa haka sai kawai ya juya ya fita ban sani ba ko yaje"?.

Kai Nabilah ta girgiza tana cewa "A yau ya Sultan yazo gidan nan Mami"? ta fad'a da surprise a fuskarta domin jiya da sukai waya ya fad'a mata zaiyi tafiya yau da safe ya akai kuma ya fasa d'an shiru tayi cikin nazari zuwa wani lokaci ta d'ago tana kallon Hajiya Fatima kamar zatai magana sai kuma ta fasa tana mi'kewa ta shige part d'inta ta d'auko hijab ta dawo parlon da mamaki Hajiya Fatima tace "Nabilah ina zuwa haka daga dawowar ki a school ko hutawa baki yiba balle kici abinci"? Kai Nabilah ta girgiza "no Mami na 'koshi zanje gidansu Daddy Mukhtar ne naji Yaya Sultan ya fasa tafiyar".

"Amma me yasa bazaki kirashi a waya ba dole sai kinje kinsan ba jininku ne ya had'u da yaran gidan ba musamman Rasheedat harda ita kanta matar gidan Hajiya Salmahn to me zakije kiyo".

"To ai Mami ba gurin ta zanje ko gurin yaran gidan ba ni gurin ya Sultan zanje".

"Ok gurin Sultan d'in da zakije inace a gidan yake kuma d'anta ne ko asibitin doctor Sambon zaki bishi"? Hajiya Fatima ta fad'a tana qare mata kallo jiran amsa kai Nabilah ta girgiza tana cewa "a'a ba hospital zan bishi ba asalin gidansu zanje ba dad'ewa zanyi ba yanzu zan dawo".

"Humm Nabilah kenan ni harna rasa bakin magana wai da gaske ke a zuciyar ki son Sultan kike bayan kina kallon irin zaman da mahaifiyar sa Hajiya Salmah keyi damu ga fitsara gurin 'ya'yanta amma ke duk hakan yayi miki a haka kike son kije gidan matsayin surukarta bayan kinsan har gobe bata goyon bayan Sultan akan neman aurenki da yake yi haba Nabilah ina kika Kai tunanin ki ya kamata ki tsaya guri d'aya kiyi nazarin abinda kike son aikataw....................

Bata karasa maganar ba akai kiranta a waya dan haka ta mi'ke tana shiga part d'inta domin ta amsa kiran a nutse ba kamar tana parlon ba shiru Nabilah tai bayan wucewar Hajiya Fatima ta fad'a cikin tunani ta sani har gobe Hajiya Salmah bata son ala'kar ta da d'anta Sultan amma tunda ba Sultan d'in ne ya 'kita ba itama bazata watsa masa qasa a ido ba zata aureshi kodan samun farin cikin su ita dashi ai tasan duk tsiya ba gida d'aya zai zauna da Hajiya Salmahn ba balle yawan fitina ta ri'ka tashi, sauke numfashi tana mi'kewa ta dau'ki ledar chocolates da key d'in motarta ta shige part d'inta domin ta samu tayi taga magriba tayi gara taje tayi sallah yau yadda take jinta a gajiyen nan barci zatai da wuri ko jikin nata ta samu ya daina ciwon inta tashi.

***
Da dare har tayi shirin barci ta kwanta ko wayarta bata kashe ba tunanin ko Sultan zai kira kwanciyar ta da mintuna kad'an har barcin ya fara fisgarta kiran Sultan ya shigo da sauri ta bud'e ido tana tashi zaune ta d'auka ganin numbar wanda take tunani yasa saida taiwa secreen d'in wayar kiss kamar Sultan d'in take gani kafin ta d'aga tare da fara ido tana kashe murya tace.

"Hello ya Sultan barka da dare".

Shima a nasa 6angaren yana bedroom d'insa a kwance ya lullu'ba da bargo yana rungume da pillow ya sake gyara kwanciyarsa sosai yana murmushi yace.

"Ya kike Baby na"?.

"Ina lafiya ya Sultan ashe bakai barci ba naga goma ta kusa"?.

"Eh taya kike tunanin zan iya yin barci bayan a yau ban sanya ki cikin idanuwan da zasu barcin ba tunda safe na wuni da kewar ki gashi ban samu na dawo gida da wuri ba dana dawo daga hospital Ina sauri bayan nayi wanka da sallah ko tsayawa cin abinci banyi ba domin kar dare yayi na samu nazo gurinki sai kuma nayi ba'kon bazata abokina Sameer ne yazo min ziyara tun daga Miyetti shiyasa ban samu nazo ba amma ya kike fatan kin wuni lafiya"?.

Kaita d'aga kamar yana ganinta tace "lafiya kalau gaskiya nayi kewarka ya Sultan" ta fad'a a shagwa'be domin ba lefi ta riga data saba bata magana d'aya biyu saita saka shagwa'ba a ciki.

"Nima nayi kewar ki Baby gashi yanzu idanuwa na suna son ganinki ba hali shiyasa nake fatan da naje Indian nan na dawo zanyiwa Daddy magana kawai a d'aura min aure dake ki dawo kusa dani sai hankali na yafi kwanciya dama kullum cikin kishi da fargaba nake kwana da'kyar nake iya barci idan na tuna kullum sai kin fita waje kinje school samari suna ganinki suna kalle mun ke kada wani banzan yaji kinyi masa ya tareki da maganar so ko ya biyoki gidan ku hummm wallahi saina 6alla masa 'kafa na zubar masa da ha'kora" .


Hhhhh dariya Nabilah tai tana cewa "kai Yaya Sultan akwai kishi ji yadda kake magana da fad'a Kuma a misali na tambaye ka a bisa tsautsayi saika ganni tare da wani saurayin ina hira dashi ya zaka yi"?.

Jin tambayar datai masa yasa ya zabura har yana cilli da bargon daya lullu'ba ya soma girgiza kai tare da dafe saitin zuciyarsa dake bugawa yace "nooo Nabilah please dan Allah karki kara fad'ar irin haka idan ba so kike zuciyata ta buga ba" zaro ido tai tana cewa.

"kai ya Sultan ya zuciyarka ta buga kuma ni nayi ya? Kasan irin son da nake yi maka kuwa bana jin zan iya rayuwa idan batare dakai ba".

Kaiya jinjina yana sakin murmushin da saida ta jishi a kunnen ta yace "yauwa ko kefa Baby nagode sosai yanzu ki kwanta kiyi barcinki saboda kada ki makara gobe idan Allah ya tashe mu lafiya maybe kafin na wuce hospital zan biyo ta gidan naku ki kula min da kanki".

"Ok ya Sultan goodnight".

"Shikenan mu kwana lafiya Baby".

Sauke ajiyar zuciya tai bayan ya katse Kiran sai yanxu taji wani irin dad'i da iska mai sanyi tana ratsata sakamakon wayar da sukai amma da ta hana kanta sukuni lokaci guda ta koma kamar mara lafiya ita a zatonta ko laifi ma tayi masa domin ta sanshi da zuciya shiyasa duk abinda tasan zai 6ata masa rai bata yinsa ko menene qara gyara kwanciya tai tana sake rungumar pillow da murmushi akan fuskarta ta rufe ido tun tana tunani har barci ya d'auketa.

✨✨✨✨Saboda tasa abun a ranta ko barcin kirki batai ba sai mafarki iri iri har asuba sannan ta tashi duk jikinta ma ciwo yake da'kyar take takawa kamar mara lafiya ta shiga toilet tayo alwala ta fito tana saka kaya da hijab tai sallah bata tashi a gurin ba ta dau'ki al qur'ani ta bud'e ta fara karantawa a bayyane cikin zazza'kar muryarta me dad'in sauraro kafin gari yayi haske saida tayi izu biyar sannan ta rufe tayi addu'a ta shafa ta mi'ke tana mayar dashi inda ta d'auko kafin ta cire hijab d'in da kayan ta d'aura towel ta shiga wanka shaf shaf ta fito sauri take ta ta kammala shirinta sakamakon ta kwana da cewa Sultan zaizo kafin ya wuce asibiti haka ta tsara kwalliya mai kyau ta d'au wankan ala tsine uwar me 'karya hatta takalmin data saka a ranar yasan yau zatai muhimmin ba'ko d'aukar handbag d'inta tayi tana fitowa daga part d'inta tasan ba kowa a parlor yanzu idan ma ta fita sai iya 'yan aiki dan haka part d'in Daddynta ta shiga suna zaune tare da Hajiya Fatima suna zance ta shiga da sallama duk binta suke da kallo cikin mamaki yadda tayi kyau ta fito d'as da ita zama tai bayan ta gaisar dasu Alhaji Tajuddeen dahar lokacin yake kallon d'iyar tasa ya sauke numfashi tare da godewa Allah sannan yace.

"Nabilah yau ko gasar kyau ake yi a makarantar taku ne? Naga kin d'au wanka kamar zakije gano shugaban qasa"?.

Murmushi Nabilah tana kallon Hajiya Fatima dake mata kallon tasan saboda dawa tai wannan wankan tace "a'a Daddy zanyi ba'ko ne" da mamaki Alhaji Tajuddeen ya sake dubanta yana cewa "ba'ko kuma wanne iri Nabilah da wannan sassafen"? "Eh Daddy Yaya Sultan ne zaizo" ta fad'a tana d'agowa ta kallo Hajiya Fatima wacce ta d'an girgiza kai dama tasan sai shi murmushi Alhaji Tajuddeen yayi yana kallon ta yace "Ok yayi kyau Allah ya taimaka"..

"Amin" Nabilah tace tana mi'kewa zata fita tace "na tafi school Daddy da Mami" ta fad'a tana shirin fita dakatar da ita Alhaji Tajuddeen yayi da cewa "amma bakiyi breakfast ba Nabilah zaki tafi ki jira su dafa Miki ko indomie ce kici kar ulcer ta kama ki" kaita d'aga "to Daddy bari naje kitchen d'in" saida ta bud'e kofa ta fita Hajiya Fatima ta kalli Alhaji Tajuddeen tana cewa.

"Amma Alhaji nikam sai nake ganin abun nan kamar akwai damuwa a cikinsa fa ni Kuma bana son tashin hankali" da alamun tambaya Alhaji Tajuddeen ya kalleta yana cewa "abun me"? "Auren Sultan da Nabilah har yanzu bana jin farin ciki akan haka kuma ba kowa bane sila sai mahaifiyar shi lefin Hajiya Salmah ne domin tun farko itace ta 6ata abun Kuma nasan har gobe tana nan akan bakanta tunda ta rantse ta sake rantsewa ba karo d'aya ba cewa indai itace ta haifi Sultan a cikinta bazata bari ya auri Nabilah ba na rasa me yake damunta".

"Oh akan haka ne hankalinki ya tashi dan ta fad'i wannan aiko tayi 'karya zan nuna mata kuskuren ta a fili ta hanyar aurawa Sultan Nabilah naga wanda zai hana kaf danginta idan basu taru basu isa su juya min ra'ayi ba balle ita maganar rantsuwa kuma tayi a banza idan anyi auren an gama sai tayi azumin kaffara domin indai kinga ba'ai auren nan ba to dama can Nabilah ba matar Sultan bace dan haka ki 'kyale ta shirmen banza take tunda shi yaron yana so an wuce gurin ai duk wani ihu bayan hari da zatai a banza bata Isa hana muyi abinda mukai niyya ba Mukhtar tun kafin yasanta nake tare da d'an uwa na tsawon rayuwar mu kinga sama takai wata bazata zo ta lalata mana zumunci da gur6ata mata ahli ba" kai Hajiya Fatima ta d'aga tana cewa "gaskiya ne shikenan Allah ya bamu ji da gani na gari bari naje naga wadannan sun gama aikin had'a breakfast d'in ne koda saura" mi'kewa tai tana fita domin ta gano.

**Fitowar Nabilah Sultan ya kirata duk zaton ta yana gida saida ta fito main parlor ta ganshi a zaune yasha farar rigar likitoci yana sanye da glass a idonsa hankalinsa yana kan wayar dake hannunsa karasawa tai tana lekawa taga me yake gani har baisan ta fito ba cin karo tayi da photonta cikin mamaki ta tsaya kallon photon domin bata san ma dashi a duniya ba sai yau data gani da alama bata sani ba yayi Mata tunda hankalinta ya karkata xuwa wani gurin dabam murmushi tai tana jinjina kai kafin tasa hannu ta kar'bi wayar tana cigaba da kallon photon yayi matukar kyau d'agowa Sultan yayi yana kallon ta daidai ta zauna yace.

"Gimbiya sarautar mata kin gama shiryawa ne school xaki tafi"?.

Kaita d'aga "eh na gama komai tafiya zanyi" mi'kewa yai yana cewa "ok muje na kaiki da kaina yau dama badan aiyuka sun min yawa ba kullum nine zan ri'ka zuwa ina kaiki amma hakan za'ai saina ri'ka fitowa da wuri yadda bazan makara a hospital ba muje" ya fad'a yana yin gaba mi'kewa tai tana bin bayansa har gaban motarsa ya bud'e Mata ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga yana tada motar suka bar gidan hankalinta nakan waya bata fargaba har suka je kwanar gidan yarima Saida taji ya tsaya ta d'ago ganinsu a inda batai tunanin zuwansu yanzu ba tasan maybe Husnah bata cikin makarantar tunda jiya tace mata Momyn ta tayi tafiya idan an tashi a school gidan 'kanwar Momyn nata zata wuce kafin ta dawo tuna hakan datai yasa ta kalli Sultan tana cewa.

"Ya Sultan please dan Allah muje ka shiga Yalwawa kota sabon titin I.M.G (ai em ji) ne ka d'auko qawata a gidan qanwar Momyn ta" jin abinda tace yasa shi kallonta yace "amma tun da baki fad'a min ba da nabi ta wajen Hasinah hotel sai na 6ullo ta titin gidan man Awajil ai zaifi min sauri saboda karna makara a zuwa hospital yau Ina da aiki sosai gashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login