Showing 18001 words to 21000 words out of 104570 words

Chapter 7 - SARAKI (The Accused Prince) HAUSA NOVEL

Ouummey   

05 Dec 2024

10741

se sun daki wanda Allah kaɗai yasan me ze faru in da hakan ya kasance.


Ƙurewa motar gaban sa ido yayi cikin son gano waye ya sha gaban sa sedai be yi nasara ba kasancewar motar me baƙin gilashi, cikin motar kuwa hannu na rawa Surayya ta danna kiran jami'an tsaron da ke police station nan gaba dasu kaɗan dan ƙa'ida ne akwai police station gaban duk kasuwannin garin.


Cikin Sa'a bugu biyu wani ɗan sanda yai picking call ɗin ta sanar dashi me ke faruwa, take ya shaida mata hadu nan tafe, cikin ɓacin rai baaba wanda asalin sunan sa Sageer ne ya fito daga motar dan ganin wane ɗan rainin hankalin ne ya tare masa hanya, a fusace ya kaiwa glass ɗin motar Surry wani mahaukacin bugu, ganin fa in aka cigaba da haka se iya fasa glass ɗin kuma ya damƙe ta yasa hankalin Surry tashi dan kallo ɗaya zaka yi wa baaba Kasan gawurtaccen ɗan Air ne, tunanin da ya zo kan Surayya yasa da hanzarin tai unlocking motar kana ta buɗe murfin da dukkan ƙarfin ta, take kuwa ya tafi ya daki kan baaba dake jiran a buɗe ya ciwa koma waye mutunci.


Faɗuwa yayi gefe kan sa na zubar jini dan ba ƙaramin dukan sa murfin yayi ba Gashi kuma ƙarfen motar me ƙwari ne sosai, a fusace yake neman miƙewa dan cin uban Surry da tana buɗe motar yaga macece, da sauri ta finciko kwalbar lemo da tasha tana hanyar zuwa club ɗin ta jefe shi da ita, take ta same shi a ka ya kuwa fasa ƙara dan sosai kwalbar ta shige shi, jiri ne ya fara ɗibar sa saboda jinin dake zuba wanda har se da ita kanta ta razana, da sauri ta ƙarasa motar da ta fara ƙoƙarin fito da Kisnah daga motar sedai ta kasa dan duk jikin ta ya saki hakan yasa ta ƙara nauyi sosai, da ƙyar Surayya ta tallafo ta jikin ta suka nufi motar ta suna yi suna layi kamar zasu faɗi dan Kisnah tafi Surry nauyi nesa ba kusa ba.


Ihu Surry ta saki jin shigar kwalba a gefen cikin ta wanda baaba ya daɓa mata dan baze bari taci bulus ba, sakin Kisnah tayi cikin jan numfashi a wahalce hakan yasa duk suka zube a wajen, tsabar taurin kai haka baaba ya miƙe jiri na ɗibar sa na komai ya ja su su biyun da hannu ɗaya ɗayan na dafe da kan sa, jiniyar motar ƴan sanda da yaji yasa ya sake su ya nufi faɗa wa motar da dan ya tsira saboda be manta kashedin baban da ba na in aka sake kama shi baze sake bailing ɗin shi ba, sedai ko kafin yakai mota tuni wani ɗan sanda ya sakar masa harbi a kafa da ya tilasta masa faɗuwa, da gudu wasu daga cikin ƴan sandan sukayi kan su Kisnah dake sheme a ƙasa bata hayyacin ta ga kuma Surayya dake zubar da jini a sume wasu kuma suka yi kan baaba aka sa masa ankwa a hannu sannan aka sashi a mota.......................✍️.










😭Wayyo Allah Kisnah ta😭 amma gaskiya baaba Allah ya isan mu😭 Surry mun gode miki Allah kuma ya baki lafiya😔.






Duk wanda be min jajen abinda ya faru da Kisnah ba aradu bani ba shi eh😏












©️ Ouummey📚✍️














*Vote, comment and share fidabilillah.*








































Ouummey 09 (8/3/2022 3:51 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 9️⃣












_______________________📖 Asibiti aka wuce dasu su duka dan ceto ran su musamman Surayya da tafi su jigata.
Kula sosai ake basu ganin ƴan sanda ne suka kawo su, dressing akayi wa baaba a kan sa tare da ƙafar sa dan bullet ɗin be shiga ƙafar ba yadai shafe ta ne.


Allurai kawai aka yiwa Kisnah da zasu taimaka mata dawowa hayyacin ta da wuri ban da wannan ita kam bata cikin kowane haɗari, Surayya ce dama dai ke cikin matsala kasancewar kwalbar ta shige ta sosai dan se da akayi mata aiki aka cire guntuwar kwalbar da ta karye mata a jiki sannan aka ɗinke wajen, aluran kariya aka yi mata kafin a maida ita ɗakin hutu.


Ta can ɓangaren kawu kuwa yana can yana baccin sa hankali kwance da tunanin koma ina Kisnah take zuwa yanzu an kirea mata warning ɗin da ze tsoratar da ita a kansa.


Tun farar asuba da ya farka ya dannawa gang ɗin nasa kira batare da ya ko duba lokaci ko gabatar da sallah ba da ake ta kira a manyan masallatan kusa da su, seda tayi ringing ta gama har so biyu basu ɗauka kafin ana uku su ɗauka, be ko amsa sallamar da suka yi masa ba ya fara tambayar su batun aikin sa.


"Acan muka kwana oga amma har zuwa ɗazu karfe huɗu bata fito ba kuma kasan ƙarfe uku ake rufe club ɗin, da alamu dai ta lura da muna binta to ta bi wani, hakan yasa dole muka haƙura muka koma maɓoyar mu dan ƴan sanda suna fitowa patrol, sedai a tara gaba".


Cikin wani tuƙuƙin takaici da ɓacin rai kawu ya kashe wayar, tsantsan disappointment na wanzuwa kan fuskar sa dan ba abin da ya tsammaci ji ba kenan daga gare su.


*************


A hankali a hankali ta fara buɗe idanun ta da take jin sun mata nauyi sosai, dishi dishi take gani dole ta sake maida idaun ta rufe kan ta sake buɗewa, a sannu a sannu har ganin ta ya daidaita ta fara ganin komai normal, ƙarewa ɗakin kallo take cikin tunanin me kuma ya kawo ta asibiti dan a cikakken kallo ɗaya da tayi wa ɗakin ta tabbatar asibiti ne saboda gadajen dake jere a ɗakin, ƙarafan ƙarin ruwa da arin magani da ɗakin ke yi.


Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye dan nauyi da ko ina na jikin ta yayi mata, canular ƙarin ruwan dake hannun ta ta fisge har jini na rushing daga inda aka saka allurar amma bata damu ba, band ɗin kanta ta cisge ta ɗaure hannun dashi wanda hakan yasa doughnut ɗin da tayi wa gashin ta bajewa ya kwanta lamɓan a bayan ta.


Ƙafafunta ta zuro ƙasa da niyyar miƙewa sedai da sauri ta ɗauke cike da ƙyanƙyamin floor ɗin asibitin da yai jurwayen ƙura, hannu ta zura ta janyo takalman ta da bata san waye ya cire mata ba ta maida abin ta ƙafar ta sannan ta sauka, batare da tsayawa neman inda wani likita yake ko wanda ya kawo ta asibiti ba ta fice daga ɗakin, cikin Sa'a ba wanda ta haɗu dashi cikin ƴan sandan da suka kawo su ko likitan da ya karɓe su dan haka ta fice har bakin titin da ke gaban asibitin, napep ta tsayar ta shiga bayan ta faɗa masa inda ze Kaita, this is the first time of her being a motar haya kowace iri ce kuwa, kalle kalle take a titin har ta gane unguwar da take kafin ta sauke ajiyar zuciya.


Tun da ta shigo motar mayen ƙamshin ta da ya kama jikin ta ko da bata saka ba balle ta ƙara wani yake tashi yana cika masa hanci, lumshe idanun sa yayi dan Allah yayi shi mutum me matuƙar so da ƙaunar ƙamshi sedai nata yayi ƙarfi da yawa shiyasa yake tashi sosai dan ko daga nesa mutum ze iya jin sa.


Kamar kullum yau ma t-shirt and jeans ne a jikin sa sedai masu ɗan tsada ne dan duk kuɗin da yake samu a sallamar sa tarawa yake yana ƙara sutura dan mutum ne shi me son ƙyale ƙyale a jikin sa, kansa na ƙasa bakin sa na ɗan motsi hannun sa sanye da counter yana pressing alamar dai tasbih yake yi.


Tun zaman ta bata san akwai wani a cikin napep ɗin ba se da traffic ya tsaida su daidai gaban wani me ɗan kiosk a gefen titi, ƙishirwar da ta addabe ta yasa ta neman ruwan da zata sha hakan yasa cikin muryar ta da bata gama dawowa daidai ba tai wa me napep ɗin magana dan ba ko sisi a hannun ta


"Excuse me drive, bani ɗari biyar mana se in haɗa maka da kuɗin ka in ka kaini".


"Ok". Kawai me napep yace tare da miƙo mata ɗari biyar ɗin da ta buƙata, karɓa tayi sannan ta juya side ɗin da ta hango me kiosk sedai wani ne a gefen side ɗin, batare da wata damuwa ba ta miƙawa na gefen nata kuɗin


"Help me collect some water please brother".


A hankali saraki da idanun sa ke kan counter ɗin hannun sa ya ɗago yana me sauke idanun sa kan hannun ta dake miƙo masa kuɗin, kamar baze karɓa ba se kuma ya saka nasa hannun ya zare kuɗin dake cikin yatsun ta cikin takatsantsan, ta ƙofar wajen sa ya miƙa kuɗin ya karɓo mata ruwan haɗe da canjin kana ya juyo ya miƙa mata, a side ɗin fuskar ta idanun sa suka sauka daidai lokacin da take gyara gashin ta da ya zubo ya rufe mata fuska, wani irin yamutsa fuska yayi ya ajiye mata ruwan nan gefe tare da kuɗin kana ya kau da kansa gefe yana kallon waje.


A zuciyar sa kuwa wani irin ƙyanƙyamin ta ne ya cika zuciyar shi ganin gashin kanta da duk a tunaninsa attach ne ta saka ga kuma yatsun hannun ta da tayi wa fixing long nails da suka sha pink jan farce, ko kaɗan be lura da kayan jikin ta ba dan kallo ɗaya yayi mata be sake marmarin kallon ta ba dan ko ba ya ƙyanƙyamin ta shi mutum ne me kiyaye doka da ƙa'idojin da Muslunci ya gindaya, ba wanda ya sake ko tari tun bayan thank you ɗin da tace masa Wanda nodding kan sa kurum yayi.


Bakin kasuwar da zeje aka ajiye shi, fitowar da tayi dan ta bashi damar fita yasa har ya lura da kayan jikin ta wanda jacket ɗin da ta ɗora ta suturta, wucewa akayi da ita bayan ya sallama me napep ɗin ya cigaba da takawa da ƙafa dan ƙara sawa shagon su, addu'a kawai yake wa ƴaƴan musulmai cikin ransa da sake godewa Ubangiji da yayi shi musulmi, a nashi hasashen ita ɗin kafira ce shiyasa har tayi wannan shigar ta kuma fito da ita dan su a wajen su hakan bakomai ba ne, shine fa yake godewa Allah da yayi shi musulmi, ya kuma tuna Masarautar su da irin yadda suke da tsauri kan yanayin shiga musamman ta ƴaƴa mata, addu'ar shiriya yayi mata dan duk inda yaga me laifi yakan ƙoƙarta yi masa fatan shiriya.


Har ƙofar makeken mansion ɗin ta me napep ya Kaita yana ta mamakin yadda akayi me rayuwa cikin wannan gidan ta iya fita ba mota har ta shiga ta haya, wajen security ɗin bakin gate ta karɓi dubu uku ta miƙa wa me adaidaita, da hanzarin sa ya zari dubu ɗaya yana faɗa mata tayi kuskuren ƙara masa kuɗi, da murmushi kan fuskar ta ta sanar dashi ba wai mantuwa tayi ba tana sane ta ƙara masa tare da masa fatan alkhairi, addu'a sosai yayi mata lokacin har ta shige kafin yaja motar sa yayi gaba.


Gaisuwar da ma'aikata ke mata ta amsa a gurguje tana shigewa tanƙamemen falon nasu, bata tsaya duban komai ba ta haye saman ta da gudu dan wanka kawai take san yi shine dalilin barin ta asibitin batare da neman kowa ba, a wannan karon kam ta san dole ta haɗa da ruwan zafi dan gasa kanta, sosai taji daɗin ruwan zafin dan ruwa uku tayi sannan ta fito ta kunna shower ɗin ruwan sanyi dan ɗauraye jikin ta kamar yadda ta saba, shirya wa ta shiga yi bayan ta fito daga toilet ɗin tana ture duk wani tunanin abinda ya faru a ƙwaƙwalwar ta dan tana son samun hutu kafin komai, seda ta shirya cikin three quarter da ya ɗan wuce gwiwar ta hakan be sauka kan ƙafar ta ba da riga t-shirt da ta kama ta sosai, kan bed ta faɗa duk da kuwa tana jin yunwa akan ta fi buƙatar bacci kafin komai.


Bacci tayi sosai da se kusan sha biyu ta farka, a gigice ta tashi dan yunwar da ta azalzale ta, slippers ɗin ta masu taushi da akayiwa ado,n gashin damisa ta saka ta sauka ƙasa, da ido kawu dake zaune kan sofa ya bita har ta shige kitchen, da kanta ta dafa noodles shaf shaf sedai kallo ɗaya zaka wa plate ɗin kaji ta burge ka, veggies ne a cikin ta a awadace banda niƙaƙƙen naman da ta zuba, iya ƙamshin ta ka zai shaida maka ba ƙaramin daɗi zata yi a baki ba banda kuma yanda tayi plating abincin, kan dining ta zauna ta fara cin abin ta da zafin sa dan yadda take ji bazata iya jira har ta ɗan give ba bayaga haka tafi son cin abinci da ɗan zafi, ruwa ta kora bayan ta gama kana ta ja kujerar baya ta jingina jikin bayan kujerar ta lumshe idanun ta har taji ta koma daidai kafin ta tashi ta nufi hawa saman ta sedai tuni kawu ya dakatar da ita.


"Zo nan daughter, tun safe nake jiran ki farka dan muyi magana se kuma naga yanzu kin taso da yunwa shiyasa ban tare ki ba".


Ɗan juyowa tayi ta kalli kawu kafin kuma ta dawo cikin falon kamar yadda yace tayi, kan sofar dake opposite ɗin shi ta zauna cikin salon zaman ta na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, gyaran murya kawu da takaici ya cika wa ciki yayi kafin ya ɗan haɗe rai irin ba wasan nan


"Jiya a ina kika kwana".


Kallo ta ƙure kawu dashi kafin ta saki murmushi silently


"A club".


Harara yake mata a kaikaice kafin yace "Amma ya akayi mutane na basu ganki ba".


Surprisingly ta ƙanƙance idanun ta
"Mutanen ka, bangane ba, dama ka sa abi bayana ne?".


A ɗan daburce kawu ya gyara zama kafin ya ɗan dake
"Yes, sure nasa abi min bayanki a ganar min inda zaki dan yawon ki ya fara damuna".


"Oh I see, so an dai tabbatar maka da club naje ko?".


"Sosai, sedai ba'a faɗa min inda kika kwana ba bayan ƙarfe uku ake rufe club, ke kuma se to nine na safe kika dawo gida".


"Na kwana gidan wani customer na ne, da matsala?". Ta faɗa tana ɗage masa hira ɗaya, baki buɗe kawu ya bita da kallo speechlessly dan duk yadda yake tunanin Kisnah ta nuna masa ta zarce nan.


Sama ta haye ganin kawu bai da abin cewa kuma, abinda be sani ba shine ta san yasa an bi bayan ta dan she's very sensitive hakan yasa ta lura da motar dake bin bayan ta duk da cewa a ƙware suke komai, ko da wannan incident ɗin be faru ba dama ta shirya plan ɗin da zata musu sedai kawai suji ta a gida.


Zama tayi kan gadon ta tana me tunano duk abinda ya faru jiya da dare da har ta ganta a asibiti, sosai komai da komai ke dawowa kan ta har abinda ya faru da Surry ta bisu, bawai Suma tayi ba a lokacin ko bata jin meke faruwa ba, tana jin komai sedai bata jin karfin jikin ta da bazata iya aikata komai ba haka kuma tana ji da ganin komai ne kamar a mafarki, kamar ba gaske ba, kamar a wata duniyar ba wadda take ciki ba.


Hawaye ne suka zubo idanun ta tuno yadda Surry tayi ƙoƙarin ceto ta da abinda ya sami Surryn.


Da sauri ta miƙe ta ciri wani pink Hill shoe kalar rigar jikin ta tare da scarf ta ɗaure kan ta wanda majority in zata skul ta ke ɗaurawa, wayoyin ta ta zuba cikin pocket kafin ta fara dialing number Meenah tana gangarowa daga step, a ɗan hanzarce ta katse Meenah dake ƙoƙarin fara tambayar yaya take wanda hakan ya zame wa duk ƴan Click ɗin nasu ɗabi'a tambayar ya junan su suka kwana


"Meenah Surry na asibiti fa, mu haɗu can yanzun nan, Ado Muhammad manya hospital, ki sanar dasu Leekha".


Bata tsaya jin me Meenahn zata ce ba ta katse wayar ta fita da sauri, a compound ta ɗau wata dark Ash motar ta ta fice da sauri hankalin ta a tashe sanin kome ya samu Surryn fa saboda ita ne.


"Wannan anyi sheɗaniyar yarinya".


"Ƴar iskar yarinya mara mutunci".


"Allah ya shirya amma wannan yarinya bata da tarbiyya".


Ire-iren waɗannan kalaman da an wanda ya fisu muni Kisnah ke ta samu wajen mutanen dake kan titin dama na gefe, wasu har dasu tsinuwa wasu kuma fatan shiriya, ita kam tuƙin ta take yi cikin son ganin ta isa hospital ɗin da wuri, a haka ta isa Allah yaso ma gate ɗin a buɗe yake dan haka ta shige, parking tayi ta fita da sauri ko amsa gaisuwar da ma'aikatan asibitin ke mata bata yi ba, kun san halin mutane ina suka ga me maiƙo ko da basu sanshi ba balle ita da sunan ta da hoton ta yayi tambari a gari.


Ɗakin da aka nuna mata matsayin na Surry ta shiga da sauri, wani irin ƙarnin magani da warin allura yasa ta kai hannu ta toshe hancin ta, da sauri ta juya ta fita zuwa wajen likitan da ya duba su, bayanin tana son a sallame su ta canja wa Surayya asibiti tayi masa, be ja da nisa ba ya yarda ya basu sallama bayan ya kira ƴan sandan da suka kawo su, cikin tsananin jin daɗin ganin ta ƴan sandan suka yarda da sauri dan sun san tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login