Showing 66001 words to 69000 words out of 104570 words

Chapter 23 - SARAKI (The Accused Prince) HAUSA NOVEL

Ouummey   

05 Dec 2024

10732

wannan Black bag ɗin taka ce tsarabar resort ne".


Ɗagowa yayi ya kalle ta ita kuma tana wa ma'aikatan da suka fito da bags ɗin magana akan su saka ragowar cikin Booth.


Kallon ta kawai yake yana admiring shigar jikin ta, yadda tayi kyau cikin kayan abu ne da ba za'a iya yiwa kallo ɗaya a kau da kai ba musamman ga irin shi da basu taɓa ganin ta da wau kayan ba apart from English wears da take sawa.


Sosai tayi masa kyau a ido kamar ya ɗauke ya ɓoye, se ta koma sak kamar Indians ɗin in ka cire sombrero ɗin da ta saka sedai hakan se ya bada wani style na daban.


Juyowa da tayi bayan ta gama magana da ma'aikatan yasa ya ɗauke idanun sa da sauri daga kan ta yana istigfar a ransa dan yasan ya saɓa ƙa'idar kallon da Musulunci ya sharɗan ta, kallon bag ɗin gaban sa tayi taga har lokacin tana nan ko matsara da ita bata yi ba


"Mudi ɗauki jakar nan ka kaiwa yaa ɗakin sa, yaa bashi key ɗin Please".


Be san me ya faru ba se samun kan shi yayi da miƙa key ɗin wanda ita kanta seda hakan ya bata mamaki dan bata yi tunanin ze bayar ɗin ba ta dai faɗa ne.


Ɗaukar jakar Mudi yayi yakai ɗakin kamar yadda tace ɗin sannan ya dawo masu da key ɗin, karɓa tayi ganin Sarakin kamar hankalin sa baya kan su dan se miƙa masa key ɗin ake amma kamar be san ana yi ba.


Bubbuga jikin motar tayi hakan yasa shi buɗe idon sa da ya rufe ya zuba su kan ta, da sauri ta kautar da nata idon dan jin yadda gaban ta ya faɗi da kallon nasa


"Muje yaa kaga ba Company muka nufa direct ba, kar muyi latti".


Buɗe murfin motar kawai yayi ya shiga batare da yace komai ba dan ko ya buɗe bakin be san me zai ce ba dan duk wasu kalaman bakin sa sun gudu tuni.


Shiga itama tayi ta zauna a seat ɗin ta ya tada motar suka fita daga gidan, har suka hau titi ba wanda ya kuma magana a cikin su se shine ya kai hannu ya kunna tafsir ɗin Suratul mu'umin daga bakin Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam (rabimahul lah).


"Yaa ba Company muka nufa direct ba, zamu fara zuwa Al~araby orphanage and home of the disabled". (ƘASAR MU A YAU).


Ta faɗa da sauri ganin ya ɗauki hanyar Company


"Okay". Yace bayan ya samo Muryar sa da ƙyar kafin ya yi amfani da Google map na motar ya nemo location ɗin orphanage ɗin sannan ya ɗau hanya.


Orphanage ɗin da ɗan tazara da inda suke dan a ƙalla 30 mins ne ya kai su, tun daga gare security ɗin wajen ke ta gaida su dan sun san Kisnah farin sani, wajen na daya daga wajejen da take matuƙar son zuwa watannin baya dan tana driving pleasure being with the kids.


Office ɗin Dr Imam khaleed suka nufa bayan sun fito daga motar wanda shine ainahin me orphanage ɗin haka kuma dama ta saba se ta fara zuwa sun gaisa kafin ta wuce wajen yaran duk da ba ko yaushe yake zama a orphanage ɗin be se ya samu dama amma yana ƙoƙarin shigowa kullum dan duba buƙatun yaran though akwai manager a gidan dake handling komai in baya nan sedai yau da take sauri ba zata iya tsayawa gaisawa dasu ba dan they have a lot dake jiran su a Company.


Cikin fara'a da mutunta juna suka gaisa da Imam khaleed dake ta Jan Saraki da hira wanda sedai yayi ta masa murmushi se ko amsar da bata gagara ba har suka yi sallama suka fito bayan sun sanar dashi security za su shigo da tsarabar yaran wadda Auntyn su tayi musu kamar yadda suke kiran Kisnahn.


Fuska cike da farin ciki yake ta yi musu godiya ba wai dan sun kawo abin da babu a gidan ba a'a se dan kulawa da ƙaunar da take nuna wa yaran a ko yaushe, bags ɗin da ke Booth securities ɗin suka fitar kamar yadda aka umarce su kana suka nufi office ɗin shugaban su dashi su kuma suka ja motar suka fita.


Duk da bata samu ganin yaran ba dan rashin zaman da bata yi ba haka suna lokacin sun shiga school amma fara'ar dake fuskar ta bata tafi ba ko kaɗan, a kullum in ta shiga gidan ji take kamar tana tare da family ɗin ta ne kuma family ɗin Nanar ta, ba ta fatan lokacin da zata daina ziyartar yaran a rayuwar ta dan wannan shine babban burin Nana har ta yi mata nisa dan haka ita kuma ta ɗauka wa kanta alƙawarin cigaba da kula da farin cikin Nana har ƙarshen rayuwar ta.


Har suka ƙara sa masana'antar fuskar ta na ɗauke da wannan fara'ar, da walwala da komai ta gaida da duk ma'aikatan wajen kafin suka haura office ɗin ta, yau ma aiki suka sha kamar ba zasu tafi gida ba har se da aka kira magrib kafin suka bar building ɗin, yau ɗin ma haka ya tsaya a kanta tayi dukkan sallolin akan lokacin su tun daga Azahar har zuwa magrib da suka yi a nan kafin suka wuce gida.


Cikin kwanakin haka suke kan ayyuka da kuma tsare tsare da suke ganin ze daƙile duk kan wata ta'asa dake faruwa a Company ɗin ta kuma kawo cigaba, alhamdulillah kuma an yi nasara sosai dan a kwanakin da suka biyo baya ba'a sake jin wasu ƙorafi akan ɓatan kuɗi ko kaya ba, haka ma ma'aikata dolen su suka mai da hankali kan aikin su dan ba wanda yake son a kore shi ko a rage masa matsayi kamar yadda Saraki ya tsara mata tayi threaten ɗin su.


Izuwa yanzu komai Masha Allah inda a ƙarshe Kisnah ta bawa Saraki post ɗin personal assistant ɗin ta haka kuma next kin ɗin ta wanda ze iya shiga office ɗin ta ya gabatar da ayyuka ko da bata nan.


Sannu a hankali suke ƙara shaƙuwa batare da ɗayan su ya ankara ba dan kusan ko da yaushe suna tare da juna, a office suna tare, a mota ma haka Kai hatta da gida dan da yawan ayyukan da basu ƙarasa a office ba haka zasu tattaro shi su kawo gida su zauna kan sa har se sun ga komai yayi dadai.


Zuwa yanzu kam alhamdulillah dan little by little kisnha ta bar yin shigar da take na rashin tsari, duk da ba wai tana saka atamfa ko shadda ko lace bane sedai tana saka decent dresses, so da yawa takan saka jeans da t-shirt Amma se ta ɗora mata kimono dake kai mata har ƙasa kuma ta ɗaura yafa scarf, hatta da straight skirts in ta saka se ta nemi jackets, after dresses ko overcoats ta ɗora musu hakan yasa ya fitar da kusan rabin wardrobe ɗin ta ta bawa Rayya wasu ragowar kuwa duka ta bawa Maigado dan native wears ne ita kuma ta sake sabon zubi da ta zauna tayi online shopping daga England sune take amfani dasu yanzu.


Duk da Maigado taji daɗin kayan amma hakan bashi ya hana ta yin baƙin ciki da takaici ba dan ita a gare ta ƙasƙanta ta Kisnah tayi da har zata bata kaya, alhalin kayan ko ɗan kwali bata taɓa ɗaura wa na daga cikin su, ranar haka suka zauna suka kashe lokaci wajen shirya plan ɗin tarwatsa Kisnah wanda dawowar Awwaf kaɗai suke jira komai ya fara tafiya kamar yadda suka tsara dan tuni Mommy ta amince da shawarar Aminiya kuma ƴar uwar ta da Jamila na auren Awwaf ɗin da Kisnah (ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta😏).




*****


Sati na uku kenan da fara aikin su tare kamar yadda a office ɗaya suke zama sedai an fitar masa da nasa table ɗin a side ɗaya na cikin offices ɗin ta dake kowanne Company, a yadda suka tsara duk tana zama a kowane Company ne tayi kwana biyu, ma'ana tana komawa kowane Company ne duk bayan kwana takwas, in taje K&S drinks yau da gobe to jibi da gata kuma se taje K&S construction, next is K&S couture......haka haka har ta zagaya duka sannan ta kuma dawo wa farko wanda suka fara da K&S constructions.


Yau ma zaune suke a K&S drinks, kowa na fama da keyboard na system ɗin shi, a cikin drinks ɗin da aka fitar last week ne aka samu wasu gurɓatattu wanda kusan an rasa rayuka kimanin goma sha uku sanadin shan lemon hakan yasa mutane yin bore har suna batun maka kamfanin a kotu, wannan yasa hankalin su ya tashi da son ganin sun daƙile wannnan ɓarakar da ta ɓullo ta hanyar gano wace iriyar ƙwaya ce ko poison aka saka haka kuma taya ya ƙwayar ta shiga cikin wasu daga drinks ɗin yayin da wasu kuma babu tunda ko da case ɗin ya ɓullo aka dawo musu da goods ɗin daga wholesellers ɗin su an yi tasting majority dan har su sun sha kuma babu komai a ciki, sosai abin ya ɗaure wa jami'an binciken dake kan al'amarin kai wanda hakan ne yasa aka dakatar da batun shiga kotu har se an kammala bincike.


A hankali ya miƙa hannun sa ya ɗau hankerchief ɗin sa dake kan table ya goge gumin kan goshin sa kafin ya tura kujerar sa baya cikin sauke numfashi.


"A cikin ma'aikatan gurin nan aka haɗa baki akayi wannan abun, waye Emeka maji?".


Tsayar da abun da take yi cikin computer ɗin tare da maida hankalin ta kan sa


"Yana ɗaya daga cikin in charge masu kula da quantityn ingredients ɗin da ake zubawa yayin haɗa drinks ɗin".


Ta faɗa tana ƙure shi da idanu cikin son ƙarin bayani


"Come closer".


Da saurin ta kuwa ta bar seat ɗin ta zuwa table ɗin sa tare da jawo kujera ta zauna next to him, juyo mata screen ɗin system ɗin sa yayi yana mata playing vedio ɗin da yai pausing, shiru tayi ta zuba wa screen ɗin ido tana kallo cikin tsananin mamaki da rashin yarda da abinda take ganin har short video ɗin ya ƙare...........................✍️.
















©️ Ouummey 📚✍️.
















☑️Ote, comment and share fisabilillah.
























Ouummey 28 (8/20/2022 8:41 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________




















Ouummey 26 (8/20/2022 8:39 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 2️⃣6️⃣
























_________________________📖 Tare suka zauna a office ɗin suna ayyuka sedai ana kiran sallah ya dakata daga aikin da yake yi na bin record ɗin spendings na watan da ya wuce da ta nemi a kawo nata shine fa yake bin lissafin dan ganin ko daidai yake.


Da kallo ta bishi kafin ta kautar da kanta ta cigaba da shigar da bayanan da take cikin laptop ganin ya shiga toilet, be daɗe ba ya fito fuskar sa jiƙe da ruwa haka hannun rigar sa a nannaɗe yana ƙoƙarin saukar dashi da alama dai alwala yayi.


Ɗagowa tayi ta bishi da kallo jin fitowar sa sedai unfortunately idanuj ta ya sauka kan tsintsiyar hannun sa da yake ƙoƙarin sauke hannun rigar, wow kawai ta iya furtawa cikin ranta ganin yadda wasu kyawawan baƙin gashi suka kwakkwanta suka nannaɗe a jikin fatar hannun nasa, sosai ta kasa janye idanun ta kan hannun dan tana matuƙar son taga mutum na da gashin hannu da ƙafa, da sauri ta bi ƙafafun sa da kallo taga nan ma yana dashi ko kuwa sedai taga wandon sa a sake yake hakan yasa ta kuma maida kanta kan hannun nasa da ya gama sakin ɗaya ya koma ɗayan


Jikin shi ne ya bashi ana kallon sa dan haka ya ɗago dan yasan ita ce tun da su biyu ne a office ɗin, kanta kuwa ya sauke duban sa yaga yanda ta kafe hannun sa da kallo har bata ƙi ƙiftawa, sake bin trace ɗin in da take kallon yayi ya tabbatar hannun sa take kallon se ya bar ƙoƙarin sauke sleeve ɗin da yake ya ɓoye hannun a bayan sa hakan yasa ta farga ta maza ta gyara zama tana maida kanta kan system ɗin cike da kunyar da bata taɓa tunanin tana da ita ba.


Ficewa yayi ya tsaya bakin office ɗin ya gama gyara hannun rigar kafin ya wuce masallaci, ko da aka idar se da ya tsaya yayi addu'o'in sa kamar yadda ya saba kafin ya dawo har lokacin kuma tana kan aiki cikin system ga tarin tulin takardu gaban ta


"Miss lokacin sallah yayi, You leave the work kije kiyi se ki dawo ki cigaba".


Cak ta tsaya da aikin da take tana bin shi da kallo cikin tuno ita yaushe rabon ta da yin Sallah da rana irin haka, ita fa sallar ta se dare yayi take haɗe su duka tayi a lokaci ɗaya tayi ta huta dan ita bata san wannan gutsire gutsiren da ake yi, a yi ɗaya yanzu ayi wata anjima shiyasa take haɗe nata.


"Zan yi duka in na koma gida, hankali na baze kwanta ba se na gama shigar da informations ɗin nan".


Ɗan zato ido yayi yana kallon ta


"Excuse me, bangane se kinje gida ba, sallar ce se kinje gida ko aikin?".


"Haba sallar dai, aikin nan ai bazan bar office ba yau se na ƙara sa shi bari ma in ƙara maida hankali ka gani".


Mamaki ne ya kusan kar shi daga zaunen da yake, sallar take batun se taje gida Sannan zata haɗa, La hula wala quwwat, wannan wace irin rayuwa ce, anya yarinyar nan na da ilimin addini ko yaya a tare da ita kuwa? Baya tunanin hakan ko da dai hakan be kamata ya zama abin mamaki ba in yayi duba da ɗabi'un ta da kuma ayyukan ta zuwa kan shigar ta, in yayi rantsuwa baze yi kaffara ba yarinyar nan bata ma san me ye addinin ba kwata kwata, ita dai kawai tana amsa sunan musulma ne amma kuwa iyayen ta sun cuce ta cuta mara adadi.


Haɗe ran sa yayi sosai dan ma kar ta samu wani fuskar yi masa musu ko wata magana


"Ki tashi kije ki yi sallah nace kar ki bari ranki ya ɓaci".


Sakin aikin tayi ta tsaya kallon shi cikin son yin magana sedai yadda ya haɗe gabas da yamma kamar wanda ke jiran ƙiris ya rufe ta da duka yasa ta miƙe tana ture system ɗin da ƙarfi har tana kusan faɗuwa, toilet ta nufa tana maganganu ƙasa ƙasa wanda bai jin me take faɗa ta shige.


Alwala tayi sedai gyaran dake cikin alwalar ba kaɗan bane, fitowa tayi tana goge fuska da towel ƙarami tare da nufar wani ɗaki me kyau me matsakaicin girma da akayi shi dan hutawa in an gaji da aiki ta shige, da ƙyar ta sami ƙaramin veil ta naɗa shi a kanta tayi Sallar.


Baki buɗe Saraki ya bita da kallo ganin ko minti biyu cikakku ba tayi da shiga ɗakin ba amma har ta fito kuma wai tana nufin tayi Sallah


"Kam bala'i". Ya furta batare da ma yasan yayi ba, lallai this girl is unbelievable, tabɗi, lallai Yana da aiki a gaban shi amma for now Bari ya ƙyale ta kar tursasawar tayi yawa har ta fara jin haushin sa tun da suna tare da sannu ze gyara ta ne da izinin Ubangiji.


Ɗauke kan sa yayi daga kanta ya cigaba da aikin sa itama haka har se can wani lokaci kafin ta ture system ɗin tana tura baki


"Yunwa nake ji sosai yaa".


Ko kallon ta be yi ba ya cigaba da aikin sa, to ban da ma rainin hankali d ta faɗa masa me take nufin yayi mata, ko tana nufin ya fita ya siyo mata abinci ne, ashe ko zata wuni da yunwar.


Ganin yadda yayi banza da ita yasa itama ta share shi ta janyo wayar ta, order ta bayar sannan ta jingina da kujerar da take kai tana rufe idanun ta, ba ƙaramin gajiya tayi ba wallahi, ga gajiyar tafiyar jiya bata gama sakin ta ba ga ta aiki da ta kuma rafke ta se take jin kamar ba ita ba dan rabon ta da aikin wahala irin haka tun tana level two kafin daga baya taji gaba ɗaya zaman Companies ɗin ya ishe ta ba ta so ta maida ragamar kula da komai hannun kawu.


Knocking ɗin da ake a ƙofar yasa ta miƙe ta ƙara sa tareda buɗe ƙofar dan shi kam ko motsawa be yi ba balle ta sa ran yaje ya buɗe, deliveryn restaurant ɗin da tayi order ne yayi handing mata packs ɗin ya juya dan tayi musu payment online.


Gaban sa ta ajiye Masa pack ɗaya ta wuce da ɗaya wajen ta ta ajiye, fridge ta buɗe ta ciro goran ruwa biyu da lemo ta ajiye masa nasa ta ajiye nata gaban ta, ba tare da damuwar komai ba na wai yana zaune ta buɗe pack ɗin ta ta soma cin fried sphagetti with veggies da pepper soup ɗin ta hankali kwance tana yi tana sipping drink ɗin ta har ta ƙoshi kafin ta tattare komai ta ajiye a gefe ta ɗau ruwan ta sha to her satisfaction.


Duk abinda take yi yana sane sedai be maida hankali kan ta ba dan yasan dana ta saba cin abinci in public

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login