Showing 24001 words to 27000 words out of 36756 words

Chapter 9 - BAYAN WUYA COMPLETE HAUSA NOVEL

RIAMCOOL   

24 Nov 2024

5777

kuma ba zaki iya ba kije wajen Hajiya ta sam miki"

Jiki a mace ta miƙe dan babu yadda ta iya dole taje, kamar wacce ƙwai ya fashe mawa haka ta nufi part ɗin Mommi a hankali ta tura ƙofar Falon bakinta ɗauke da sallama

daga Mammi har Mommi shiru su kayi suna jifanta da ƙasƙantaccen kallo wanda ya saka ta kauda kanta gefe guda tana haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi, durƙusawa tayi tana sadda kanta ƙasa tare da furta "Hajiya kamar yadda Allah ya temakeki ki taimakeni wllh yunwa nake ji idan ban ci ba ji nake kamar zan mutu dan Allah ki bani Abinci naci" ta ƙarashe zancen tare da saukar wasu hawaye


kallon takaici Mommi ta bita dashi tana furta "A gidan uwarki zan baki Abinci ai wallahi wahala ce kin ɗaura aure da ita kenan shegiya jakar banza matsiyaciyar talaka, ƴar gidan talakawa marar Asali da galihu, har yanzu baki fara ganin komai ba na yankin azaba, wallahi sai kinyi da na sanin shigowarki gidan nan"

sosai mu nanan kalmomin da Mommi ta jefeta dashi suka tsayar mata a rai tare da ɗago idanunwanta tana duban Mommi dasu wacce ke ƙara jifanta da kallon tsana, "Fice man a Falo ko nayi miki shegen dukan da ba za'a iya ganeki ba shegiya mai kama da Mayun daji"

jiki a mace ta miƙe tana fita daga Falon,zuciyarta na mata wani kalar suya da zafi, ta ina zata fice ta bar wannan baƙin gida wan da y zame mata baƙin kurkuku, da ƙyar ta idasa fita daga Part ɗin tana nufar Garden ta nemi inuwa tana zama,Idanunwanta ta ɗaga tana kallon sama hawayen tausayin kanta na zubo mata da kuma tunanin Mamma da Yah Kahabir,

zamewa tayi daga zaune tana kwanciya tare da dafe cikinta wanda take jin tamkar babu komai a cikinsa, ga jikinta dake ta faman Kyarmar masassara,
Jin ƙarar tafiya na tunkaro inda take ya sakata tashi da ƙyar tana bin inda take jin sautin tafiyar da kallo, Tafiya yake cikin ɗan sassarfa jikinsa sanye Da Kayan Pajames Kafaɗar sa rataye da School bag

miƙewa tayi jikinta na rawar sanyi da karkarwa ta tunkaro ABEED tana zubewa a gabansa ",Ƴal laɓai dan Allah kai taimakeni da Abincin da zan ci yunwa nake ji" ta ƙarashe zancen da ƙyar sbd galabaitar da tayi


ɗago da fuskarsa yai yana kallonta tabbas dai wannan Ma'aikaciyar gidan ce "Amma taya kika zauna da yunwa baki ci Abinci ba, naga dai gidan ko ina wadace yake da Abinci" ya faɗa yana ƙarewa Muneebba kallo


"Naje ko ina sun ce babu ya ƙare sai an girka wani" ta faɗa tana kallonsa

Jim yayi sannan yace "ok bani minti biyu" da to ta amsa tana komawa inuwar ta zauna


bai fi minti biyun ba sai gashi ya fito da Flat ɗin Abinci da ruwa, waje ya samu ya zauna da murmushi ɗauke a fuskarsa ya miƙa mata, hannunta har ɓari da kyarma yake wajen amsar Abincin, buɗewa tayi taga Shinkafa ce da miya sai Salat da zaƙo_zaƙon nama a ciki, spoon ɗin ta fidda tana gyara zama tare da bismillah ta fara cin Abincin ba ƙaƙƙautawa hannu baka hannu ƙwarya, tun da ta fara cin Abinci yake kallonta da mamaki, don duk uban Abincin dake shaƙe a Flat ɗin sai da ta cinyesa tas, sannan tabi da ruwan sanyi,wani ni'ima taji na saukar mata, ɗago da idonta tayi tana furta "Nagode"

"Don't mind but You New house mad? ya tambayeta da ƴar dariya

Itama cike da jin kunya da kuma tausayin kanta ta ɗaga masa kai tana miƙewa



************************************
*YOLA*

*FATTU*

cikin ta shin hankali ta shiga bukkar da niyyar Jawo JODDi su bar rigar don tana jin tsoron Abinda zai biyo baya

kwance ta samesa ya ɗaga kansa sama idanunwansa a buɗe "JODDi zo muje" ta furta tana ƙara leƙawa


bai fahimci abin da take faɗa ba illa bin ta da ido da yake, kamar Fattu ta kurma ihu haka take ji sbd ta shin hankali

Jin hayaniya na tunkaro inda suke ya sakata leƙawa tana kallon dandazon Mutanen da suka nufo inda suke ko wane da makamai a hannunsu.........
[5/21, 8:13 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*BOOK 1*

*By: RIAMCOOL*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


*P.31&32*

______________Ganin Mutanen na ƙara tunkarosu ya saka jikinta kyarma don tabbas ta riga da tasan kashe mata Joddinta za ayi,ita kuma sai ta karɓi hukunci tsatstsaura idan har Ja'e bai mutu ba


da gudu ta tunkari JODDi hawaye na bin fuskarta hannunsa ta kama tana son miƙar dashi "JODDI miƙe mu tafi za su ƙaraso" ta furta tana son ta dashi


haɗe rai yayi yana ture hannunta tare da turata gefe guda yana kallonta, bata bi takan wannan ba ta ƙara tun karosa tana fashewa da kuka,ganin yadda suka shigo haiƙam da mugayen makamai a hannunsu, gabansa ta tsaya tana karesa tare da girgiza musu kai tana furta "ku ƙyalesa don Allah wallahi bai san komai ba, nice na dace da hukuncin ba shi b......"

bata idasa ba Baffalo ya ɗaga hannu ya wanketa da mari yana furta "Fattu kin cuceni Allah ya isa tsakanina dake, dama ashe yawon iskanci kike zuwa daga yau na fidda ki a jerin Ƴaƴana ki fidda ran cewar ke Ƴata ce, na barwa duniya ke Fattu, wallahi nayi da nasanin haifarki kin jawo man abin faɗa a gari" ya ƙarashe yana juyawa cikin ɓacin rai

Fattu kam dukkan wani aiki da ƙwalwarta keyi cak ta tsaya kalmar Allah ya isar da Mahaifinta yai mata na dawo mata da kuma furta ya barwa Duniya ita, "waye zata faɗa mawa ya yarda da cewar ita ba fasiƙa bace sannan abin da suke zato ba haka yake ba" ta faɗa wasu zafafan hawaye na bin kuncinta juyawa tayi da nufin ƙara kare Joddinta amma sai taga wayam babu shi, sai dai hayaniyar dake dakwai, da gudu ta fita tana nufar wajen cincirandon Matasan dake gewaye da JODDi, turesu tayi ta wuce, hannu ta ɗora a kai tana kurma ihu tare da son nufar in da Joddinta yake a kwance cikin jini malale gashi ko motsi ba yayi, riƙeta kam wani Hassanu Abokin Ja'e yai yana ƙara wanka mata mari, tare da fizgarta yana tafiya da ita duk cikin mutanen babu wanda yai yunƙurin da Katar dashi, kowa Allah wadai yake da Fattu,

cikin rashin Imani da tausayi Hassanu ya fizge zanin Fattu da kuma rigarta yai mata zigidir cikin Al'umma, Kuka riris take tana niyyar kare jikinta amma babu hali sbd mugun riƙon da akai mata, a haka suka dinga tafiya har aka isa fadar mai gari da ita, wan da nan ma mutane ne cike da ita daga Mata har maza, JODDi suka fara ɗaurewa a iccen bedi wanda jinin har yanzu bai daina zuba ba


Fattu ma ɗaureta sukai wacce ta kasa ɗaga kanta ta kalli kowa, idanunwanta basu daina zubar da hawaye ba,
Kowa na wajen tsit yai ana sauraren hukuncin da mai gari zai yanke, shiru mai gari yai yana kallon Ja'e wan da aka samu jinin ya tsaya domin harya farfaɗo,gyaran Murya mai gari yai ya fara magana "To kamar dai yadda kuka sani dukkan wani na cikin garin nan muka kama sa da aikata zina za muyi masa horo mai tsanani sannan mu koresa daga nahiyar garimmu, don haka hukuncin Fattu da za muyi mata ai mata bulala ɗari sannan idan an gama ina da buƙatar a kaita ɗakin duhu na cikin gidana,tayi tsawon wata biyu a ciki, kafin ta bar garin, sannan shi wannan akan kisan daya so aikatawa duk da ba mai hankali bane shima hukuncin kisa ya hau kansa ina da buƙatar a halin yanzu ku zazzaga masa fetur ku ƙonesa, Sannan kai Baban Fattu na janye Auren Fattu da Ja'e don haka kai ne zaka bayar da tarar Shanaye Goma"




kan Baffalo a duƙe ya amsa da to kamar ya fashe da kuka a cikin ransa yana jin kamar ya shaƙe Fattu ta mutu, ji yake dama Fattun ce ta mutu ba wai ace ya bada shanayensa ba,

kowa na wajen yai na'am da zancen mai gari Fattu kuwa kuka take kamar ranta zai fita tana son kuncewa daga ɗaurin da aka yi mata domin ceton Joddinta ,duk da tsawar da bafaden mai gari ke mata bata dai na kici_kicin kuncewa ba,sharɓeɓiyar dorinar dake hannunsa ya ɗauka yana zuba mata a jiki wacce ta sakata shiɗewa wata azaba na ziyartarta, nan take farar fatar jikinta ta fara fashewa har jini na zuba,bata ida dawowa hayyacinta ba ya ƙara zuba mata wata wacce ta saka Numfashinta tsayawa cak jikinta na ƙara malalar da jini, dukkan wani mai tausayi da imani yaga halin da Fattu take sai ya tausaya mata,ba tare da tausayawa ba yai mata bulala ɗari cif lkc babu alamar rai a tare da ita,jikina duk ya ɓaci da jini kamar an yanka dabba kunceta sukai ana samun zani tare da lulluɓa mata a jikinta don an tabbatar data riga ta mutu


JODDi ma da zasu zazzaga masa Fetur liman ya hana sai dai dukan da sukai masa wanda ba zaka taɓa ganesa ba, dan lkcn ko numfashi babu a tare dashi, Umarni mai Gari ya bayar aka fita da gawarwakin su Fattu daga cikin garin




********************************

*MAMMA*

Zaune take waje guda tayi zugum duk abin duniya ya isheta tun ranar da Muneebba ta bar gidan hankalinta ya kasa kwanciya,ga miyagun mafarkan da take yi akan Muneebba, Mamma Ladiyo dake kallon Mamma tun da ta lula duniyar tunani tace "Wai Shatu ba zaki cire damuwa a ranki ba? Muneebba fa na cikin kwanciyar hankali dan fa baki ga yadda Uwar mijin ke nan da nan da ita,mu kammu mun ga karamci a gidan nan".

wata doguwar Ajiyar zuciya Mamma ta saki tana faɗin "Wallahi Mamma Ladiyo kwanan nan miyagun mafarkai nake akan Muneebba shi ya saka hankalina ƙin kwanciya"

Wani kallo Mamma Ladiyo ta bita dashi mai cike da tarin ma'anoni tana furta "Ayya ba abinda zai sameta sai Alkhairi Shatu ki kwantar da hankalinki A'ishah"

ɗaga mata kai Mamma tayi ba tare da zuciyarta ta nutsu ba akan zantukan Mamma Ladiyo,


Misalin ƙarfe 3 na dare Mamma Ladiyo ta miƙe tana leƙa fuskar Mamma wacce bacci ya ɗauke ta zanin jikinta ta kunce tana ɗauko ƙullin baƙar leda ta kunce tana barɗawa Mamma bisa jikinta tayi minti biyar tsaye a kanta tana wasu surutai kafin ta miƙe ta shiga ɗakin, Akwatin kayanta ta jawo tana buɗawa ta fito da wani madubi wan da yake lulluɓe da jan ƙyalle mai ratsin baƙi,yaye ƙyallen tayi tana buɗesa nan take wani baƙin duhu ya ƙara mamaye ɗakin baka jin motsin komai sai wani gurnani dake tashi zubewa tayi ƙasan madubin tare da kai goshinta ƙasa tana sujjada, tayi tsawon mituna a haka kafin ta ɗago tana duban madubin, wani kalar duhu ne ya mamaye madubin baka ganin komai a cikinsa, buɗe bakinta tayi ta fara wasu surutai masu wuyar ganewa da wata murya mai kama data yara aka fara faɗin "kurwa zanci ki bani kurwa naci ko ki bani na riƙe na dinga lasarta kwaɗayin kurwa nake"

ɗago da kanta Ladiyo tayi tana duban madubin tare da bugawa yarinyar dake cikin madubin tsawa tana faɗin "Julaisa kina bani aiki wallahi a gidan wa zan samo maki kurwa a cikin daren nan?"

dariyar mugunta Yarinyar ta fashe dashi tana faɗin "kin riga da kin san sharaɗin dana gindaya maki a duk lokacin dana nemi kurwa kika hana ni taki zan kama taki kuma dama irin taki nake kwaɗayi daga gani zata yi maiƙo da mai wai har kin ja kwaɗayina ya tas.....?"

bata idasa Mamma Ladiyo ta buga mata tsawa tana faɗin "Julaisa Aniyarki ta biki kika ƙara irin waɗannan baƙaƙen maganganun wallahi sai nayi maki mugun hukunci mai tsauri kin san yanzu dai ke baiwa tace baki da ikon a kaina har sai na karya maki sharaɗi don haka idan kurwa kike nema yanzu yanzu zani baki ita"

dariya yarinyar ta sake fashewa da ita tare da ƙwalalowa Mamma Ladiyo manyan idanunta tana fito da harshenta, miƙewa Mamma Ladiyo tayi tana fita daga ɗakin, kai tsaye inda Mamma ke kwance ta nufa,nan take wani abu mai kamar fara ya fara yawo a sama, damƙesa tayi tana murmushi ta shiga ɗakin, madubin ta kalla tare da miƙawa Yarinyar cikinsa farar, amsa Yarinyar tayi tana kallonsa sannan ta yatsina fuska tana kallon Mamma Ladiyo "wannan tayi ƙadas da yawa babu maiƙo daga gani ma ba zata ciyu ba sai dai na dinga lasarta,sannan jinin Mutumin can da nake sha yanzu babu yai nesa da iyalin nashi"


"na baki abinda kike so ban san wani dogon tsogwami ki ɓace man da gani" Mamma Ladiyo ta furta

dariya yarinyar ta sake fashewa da ita tana faɗin "ban so kika samo man kurwa ba naso ace taki ce na lashe dan kullum haɗiyar yawu nake, ɓacin rana kawai nake jira tazo naga kurwarki a hannuna"

Jan ƙyallen Mamma Ladiyo ta saka tana rufe madubin sannan ta ajiyesa cikin kayanta tana fitowa waje ta samu ta kwanta tana sakin wani sheɗanin murmushi tare da kallon Mamma



********************************

Tun da Muneebba taci Abinci ta miƙe ta nufi side ɗin ƴan aiki don a can ne aka mayar da ita, ko da taje waje ta samu tana kwanciya don jin masassarar ta ƙara rufeta ga kanta da bai daina ciwo ba, Indo ce ta shigo taga halin da MUNEEBBA take cikin tausayawa tai mata sannu sannan ta taimaka mata ta miƙe ta rakata wajen Doctor ɗin su tai mata Allura da bata maganin

Bayan kwana biyu

sosai gidan ya kacame da hidindimu kasancewar bikin Maheer daya matso anata hidima amma babu ango hakan ya sakasu dakatawa da wasu Event waɗanda suka shirya kuka sosai Maheer taci ganin irin halin da take ciki da kuma mijin da zata aura wanda bai ma san tana yi ba


zaune take fatar nan tata sai glowing take tayi sumul sai ɗaukar ido take saboda tsabar gyaran da tasha, kayan dake gabanta ta tisa tana kallo zuciyarta cunkushe da damuwa tayi nisa cikin tunani taji an dafa kafaɗarta wanda ya sakata juyowa tana duban Maheer wacce ta kafeta da ido murmushi ta ƙaƙalo tana dubanta "wai Maheer ba dai zaki cire damuwa a ranki ba kullum cikin tunani kike"

murmushin takaici ta saki wanda wasu zafafan hawaye na biyo kuncinta "ba zaki gane ba Iftihar" ta faɗa tana miƙewa........



Love Yhu All my Habibties, thanks for your comments, much love and ƙauna lodi_lodi🤩💖💖💖💖
[5/21, 8:17 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*Book 1*

*By Riamcool*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


*P.33&34*


koda Maheer ta miƙe iya Toilet ta faɗa tayo wanka fitowa tayi jikinta sanye da towel, wajen bakin Bed ta samu tana zama tare da kallon Iftihar wacce ke haɗa mata kayayyakinta tsab cikin Akwati "Iftie ina zaki tafi dasu ne? Maheer ta tambaya


Kallonta tayi tana furta "Maheer gidammu zamuje dake kamar baki san yau ne Mother's day ba, ki wuf ki shirya mu tafi dan yau hada Yaya Asad nasan zai zo"


Murmushi tayi tana miƙewa tare da shafa Lotion masu daɗin ƙamshi, sannan ta ɗan yi Kwalliya sama_sama, wani dakakken leshi blue mai ratsin pink sabo ta ɗauka ta saka, ba ƙaramin kyawu tayi ba, tsam haɗaɗɗiyar doguwar rigar tai mata, zama tai ta kashe ɗauri mai masifar kyau sannan ta ɗauki Haɗaɗdiyar sarƙar Gold da awarwaro ta saka, mayafin leshin ta ɗauka tana azawa a kai,ga haɗaɗɗun Flowers na ƙunshi da akai mata wanda zai tabbatar maka da cewar Amaryar ce, wani ƙayataccen murmushi ta saki tana ƙara bin jikinta da Mayun tururaku masu masifar ƙamshi


"Wow Mrs Asad BObbi wanna kyawu haka kamar zaki tafi gasar kyau" Zulaihat dake shigowa ta furta da ita da sauran ƙawayensu, dariya Maheer tayi tana juya idanu,zuzuta irin kyawun da Maheer tayi suka ci gaba da yi kanta na ƙara fasuwa


Sai bayan la'asar sannan dukkansu suka nufi gidan Mommi, cike gidan yake sosai anata hada_hadar biki,Kai tsaye Part ɗin Mommi suka nufa



*Muneebba*

Sauri _sauri take tafiya har tana neman yin tuntuɓe, bakinta ɗauke da bismillah ta tura ƙofar ɗakin tana shiga hannunta riƙe da tsintsiya alamun shara za tayi, tun daga Falon take ƙare masa kallo tana jijjiga kai, dubanta takai kan wani tangameman Photon Bobbi dake liƙe jikin bangon ɗakin, ƙare masa kallo take tana taɓe baki tare da ƙara godewa Allah da zata zauna ma ba tare daya santa ba duk da kasancewarsa Mijinta amma bata fatan haɗuwarta dashi, tun da shima kansa bata ita yake ba, cikin sauri ta gyara ɗakin kasancewar ba datti dan kullum sai ta gyara kuma da alamu ba'a amfani dashi yadda ta gyara sa haka zata zo ta iskesa shi yasa wani lokacin take kwanciyarta a ciki ganin babu mai amfani dashi, yau tana gamawa ta fice kanta ƙasa take tafiya dan hankalinta sam baya a jikinta, karo ɗin da taci da Mutum ne ya sakata ɗagowa da azama tana dubansa sai dai gabanta ne ya faɗi tana zaro manyan idanunta tare da ja baya ganin wanda ta bangaje, ba tare daya kulata ba ko ya kalleta ya ida haurawa sama yana kakkaɓe jikinsa tare da kakkaɓe inda ta shafesa "Yeah shine Bobbi dai Mijina" ta furta a hankali tana bin sa da ido


Daga kafaɗa tayi tana ida safkowa kai tsaye side ɗin da aka bata ta nufa dan tayi wanka, tura ƙofar Falon tayi taji ta a buɗe da mamaki ta shiga sai dai mamakinta ne ya koma ganin Mom zaune ta hakimce tana dubanta a ladabce ta durƙusa tana gaisar da ita, a yatsine ta amsa tana dubanta "ke ga kaya nan kiyi wanka ki saka zan turo miki da mai kwalliya yanzu, anjima za'ai Mother's day ɗin Mijinki da abiyar zamanki shine zan haɗeku koda wasa idan kika rufe fuskarki karki buɗe"


Da to ta amsa jiki a mace,tun da Mom ta fita ta samu damar fashewa da kuka ko zuciyarta zata samu salama, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta shiga wanka


fitowa tayi jikinta ɗaure da Towel jikinta ta goge sannan ta shafa Lotion tana zama, bata daɗe ba mai kwalliyar tazo ta tsantsara mata,make up haɗaɗɗen Bride Material red color ta saka, wanda ya fiddo ta tai masifar kyawu haɗaɗɗen ɗauri mai kwalliyar ta kashe mata wanda ya fiddota sosai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login